Showing 51001 words to 54000 words out of 86898 words
ni yau naga karfin addu'a baki ji yanzu ma nayi ba, ai addu'a tana da amfani yana kora miyagu."
"Ai Hajiya wannan da kikayi yanzu ba addu'a ba ce, ki karanta shi a karance ba ki fad'a irin yadda kika fad'i yanzu ba,
a
yatul'kursiyu da suratul iklas da falaki da nasi, a duk sanda zaki kwanta ki karantasu sun'ishe ki komai da komai,
zasu karake daga sharrin komai."
Hajiya ta mara baki tana fad'in
"Ahaf wannan addu'ar da kike gani tun muna yawo da jajayen sawu muke ganin
amfanin sa, duk shi mukeyi da kawayen mu, muyi fad'a da uban kowa mu kwana lafiya, ai ko munga amfanin sa."
Hajiya Bishira ta girgiza kai tana fad'in
"Allah shi kyauta."
Sun so tafiya d'akunan su Hajiya ta ce sai dai fa su zauna su waye gari anan tun da
gari yakusa waye wa.
Washegari Hajiya ta d'agawa Daddy hankali a waya wai sai dai yadawo yanimo kafi a sa a gidan, miyagu nason ganin bayan su.
ya ce mata to yakusa dawowa.
Shirye-shiryen bikin Farida nadad'a matsowa.
uwar amarya Mommy ba zama.
anata ka
i kawo yadda biki zai gudana baza aji kunyar kawaye ba.
Mommy ce zaune a parlour tana waya da Hajiya'n Dubai wata kanwar su Daddy ce, wacce take da zama a can kasar Dubai.
takan zo Nigeria jifa-jifa dan mijinta yana nan Nigeria ita kuma tana can Dubai da
'ya'yan ta,
zaman ta yafi yawa a can.
Mommy dake rike da d'aya wayarta tana dudduba wasu arnan kayan d'aki da Hajiya'n Dubai ta turo mata,
ta gyara rukon wayar dake kare a kunnen ta tana cewa.
"Gaskiya Hajiya'n Dubai wad'annan set ukun duk sun min, duka z
a'a bada kud'in su a sako a jirgi a kawo."
daga cikin wayar Hajiya'n Dubai ta ce
"Wai dama Hajiya Halima ba wucewa da su can UK d'in za'ayi ba, Nigeria za'a kawo su?."
"Eh Nigeria za'a kawo su a zuba mata su a gidan ta dake nan, idan sun shigo kasar yazam
ana da suna da masaukin su mai kyau, a can UK kuma ai shi angon ma yagama shirya gidan sa da ke can yazuba komai babu abinda za'a tafi dashi daga nan,
idan kunje abinda kuka ga babu sai kuyi odan sa acan d'in kawai."
"Ah yayi hajiyar mu, ai harka ta jin ku
nya baiyi ba,ai ni sam bana son harkar karanta,
me za'ayi da jin kunya kana cikin kawaye karika kunyata, idan fa kikaga gidan da za'a zuba kayan nan ba wani na arziki bane, ba nagani a fad'a bane ,
kawai a basu gida, kada mushiga kunyar kawaye, ace kamar m
u aga gidan 'yar mu bai taka kara ya karya ba,
d'iya ga Alhaji Abubakar Fiya guda ace gidan ta zubin na talakawa, haba ina bazamuji wannan kunyar ba, kawaye suzo daga nesa suna yi mana kallon kasa-kasa, kallon raini,
kai ina da wuri ma zan shigo Nigeria na
je na duba gidan da kaina,
idan beyi ba gaskiya za'a basu gidan da za'a zuba kayan nan,
dan wlh ban yarda da harka ta jin kunya ba."
Mommy ta sheke da dariya tana fad'in
"Hajiyar Dubai tamu, ai duk in da za'ayi bazan bari aji kunya ba, ko kin mance wane n
e mijin Farida ne, Faruoq-Al'Hussain ne fa, kin san naira kuka take a family'n Al'Hussain,
da kanta Farida ta zab'i gidan da take so a cikin gidajen da mahaifinsa, Al-Hussain ya ce ya zab'i wanda za'a d'auko masa amaryarsa a saka ta ciki kafin bayan biki d
a kwana biyu su bar kasar."
"Yauwa yanzu naji zance ai ni na ma mance da ko d'an gidan wa d'iyar tawa zata aura, ah gaskiya mun baiwa jin kunya baya, Faruoq-Al'Hussain kai ka dace da d'iya ta."
suka sheke da dariya.
A b'angaren amarya Farida ma fa ba zama
, duk da ba a kasar nan zasu zauna da mijin nata ba,
a can UK in da yake aiki zasuyi zaman shekaru goma kafin su dawo Nigeria,
sabo da aikin sa da yake yi a can shekaru goma zaiyi ya gama ya dawo gida Nigeria.
ana ta shiga da fita.
Sai ana biki saura sati
Daddy ya dawo.
aiko Hajiya ta dira a kansa ko huta gajiya baiyi ba, ta ce ya d'auki Feeryal ya mai da ita tun da ya dawon.
sai da ya yi ta lallab'a ta ya ce tayi hakuri a gama biki tukun zai mai da ita.
da kyar ta yadda.
Tuni gidan Alhaji Abubakar Fiya y
a d'auki manya manyan baki na kusa da ma na kasashen ketare.
ciki kuwa harda Hajiya'n Dubai da iyalenta,
da kuma kayan d'akin da Mommy tasa akayi odan sa daga Dubai.
Tun ana saura kwana uku biki aka fara gudanar da shagulgulan biki,
a manya manyan Hall.
Amarya Farida ta amsa sunanta amarya dan kuwa dubbannin d'arurruwan mutane ne suka shaida d'aurin auren, Farida Abubakar Shitu Fiya da angonta Faruoq-Al'Hussain.
Bayan d'aura aure jama'a suka soma taruwa a Hall na musamman dake a cikin gidan ta can baya,
wan da aka tanade shi sabo da tarurruka, na cikin gida idan ya taso.
nan aka tanada domin gudanar da walima bayan d'aurin aure.
Aunty ce ke saukowa daga saman bene ta cab'a kwalli had'i da gwala-gwalai, tayi matukar kyau ta dawo yarinya d'anyiwa sharaf t
ammar ita ce amaryar,
sai baza kamshi take.
Aunty Hindu d'iyar baffan su Daddy ta saka gud'a tana fad'in
"Kaga Amarya a gidan Alhaji Abubakar Fiya, wlh babu wan da zai ganki ya ce shekarun ki goma da yin aure,
tamkar kece amaryar ai dole ki rika rikita yay
an namu, tsaruwa iya tsaruwa."
dariya ta bisu da shi ganin yadda duk parlour'n suka rud'e da zu-zu-ta-ta.
Aunty Hindu ta d'aga wayarta tana cewa
"Tsaya dan Allah na d'auke ki na turawa Yaya nasan tukuicina na daban ne yau."
"A'a huta abin ki ai gani a zahi
ri yafi gani a hoto, yanzun nan ma gurin sa na dosa."
Duk suka sheke da dariya har suna tafawa.
"Da gaskiyar ki wlh je ki gwada masa ya gani a zahiri wannan irin wanka, ba shigar bane sukayi miki kyau ke ce kikayi wa shigar kyau."
ita dai dariya tayi musu
tayi waje...........!
Mommyn Twins ce
πΊπΊ
*FEERYAL*
πΊπΊ
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp
number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*
ππ°
AINUWA
πΌ
RITER'S
β
πΌ
*
*
π¦
SSOCIATION
π€π»
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociati
on
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*
ππ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Bismillahirrahmanurrahim
π
Ώ
οΈ
14
Side d'in Daddy ta nufa ta kofar baya, dan tasan
ta ainahin kofar kam cike yake tam da mutane.
ai ko hakan take har cikin babban parlour'n sa ba'i ne maza ciki a ciki.
D'akin kwanan sa direct ta wuce, tana shiga ta kirasa a waya.
ganin mai kiran nasa yasashi mike acikin jama'a ya nufi bedroom d'in sa, d
omin amsa kiran.
ya tura kofar yana kokarin kuma maida kiran dan ya yanke,
sai ganin ta ya yi tsaye cikin d'akin.
ido ya bud'e da kyau ya kura mata su, itako murmushi take sakar masa.
a hankali ya tako ya iso in da take.
hannu ta mika ta sakalo wuyan sa, t
ana cigaba da aika masa murmushi.
cikin sanyin muryar ta mai kara masa kaunar ta.
ta ce
"Daddy tun d'azu nake son ganin ka mutane sun min fin karfi."
ta karasa maganar da kashe masa ido.
wani numfashi ya sauke, sai kawai ya rungume ta ya na fad'in
"Godiya
ya tabbata ga Ubangijin daya mallakamin wannan kyakkyawar tsuffar."
ya d'ago ya manna mata kiss a goshi.
d'an zame jikin ta tayi tana fad'in
"Daddy ka fara tsufa fa."
"Ina da ke ai ita ma tsufar bata isa ta dumfaro ni ba, sai dai ta tsaya a iya shekaru."
dariya ta yi ta ce
"Yau fa ka aurar da 'ya tsufa ya dad'a bayyana ga furfuran ka sun karu."
ta karashe maganar da muryar dariya.
kumatun ta yaja ya ce
"To kar ki bari tsufar tai mana tasiri, ki san yadda zakiyi ki yake sa tun kafin a fara kiran mijin ki da
tsoho, shi ke nan ke ma kin tsufa."
dariya duk sukayi wa junan su.
Ya matsa can jikin bedside drower ya danna ma dannin bud'e sa, gilashin jiki ya zuge, yad'auko d'aya daga cikin makullan motocin da suke ciki.
ya zo ya mika mata.
ta karb'a tana bin key'n
da ido sannan ta ce
"Na mene ne wannan?."
ya ce "Naki ne tukuicin wannan kwalliyar."
wani lallausar murmushi ta sake ta rungume shi tana fad'in
"Godiya marar adadi, naji dad'i dad'in da bazai fad'u ba."
murmushi ya bita dashi, yana matukar jin dad'i ya yi
mata kyauta yaga tana nuna yabawa da jin dad'in kyautar da ya yi mata.
yana daga cikin abin da yake dad'a kara girman fadarta a cikin birnin zuciyarsa.
Bata jin kanta ita wata ce dan mahaifinta yana da dukiya, ko min kankancin kyauta takan nuna jin dad
'in ta mara misaltuwa.
akasin sauran matansa da iyayensu ba koman komai ba sai fad'in ran tsiya.
Da sauri Miemie ta shige side d'in Aunty, ta haura sama da sauri tashige d'akin Feeryal.
tana zaune sunata wasa da kawayen ta, wan da ita take ganin su.
Miem
ie ta ce
"Feeryal taso muje ayi mana kwalliya ga mai kwalli tana kan yi wa su Ameerah, a side d'in Hajiya,
muje gurin walima ke bazaki je bane?."
"Ni bazan je ba Ammie na ta ce nazauna nayi wasa na a nan kije kawai abinki."
"Dan Allah taso muje gasu Umaima
'n Dubai ma sun zo zo muje ki gansu."
ta janyo hannunta suka fita.
tun kafin su karasa sauka daga stairs hankalin 'yan cikin parlour'n ya dawo kansu.
wad'an da dama sunsan Feeryal d'in tun tana jaririya,
suna ta mamakin girman ta da yanayin tsarin zubin ha
littarta.
wad'an da kuma basu santa ba suna binta da kallon rashin sani, kallon itama daga cikin ba'in da suka zo daga kasashen turai suke mata.
Har sun zo shiga parlour'n Hajiya,
Feeryal tayi baya da sauri a matukar tsorace.
Miemie ta ce
"Hajiya bazata
miki komai ba zo muje, kar a gamawa Ameerah a kama yi ma wani."
hannu Feeryal ta d'aga baki na rawa ta ce
"Ga mage can ni dai bazan je ba."
"Baya komai fa ki zo mu shiga."
"A'a ni bazan shiga ba!."
tayi maganar tana ja da baya a mugun tsorace, tamkar zat
a shid'e.
"Ke Miemie me kike yi a nan ana can anayi wa su Ameerah kwalliya ke kina nan, gashi har an watse an tafi gurin walima, kiyi maza kije a yi miki."
cewar Hajiya data fito zata gurin walimar tana gyara zaman mayafin ta.
ido ta gwalalo kan Feeryal d
ake ja da baya da baya.
"Me zan gani haka me ya kawo wannan aljanar nan?
ke Miemie kifita idona na rufe, ban rabaki da wancan yarinyar mai kamata faran mayu ba,
kin d'auko ta zaki kaita cikin jikoki na ta lashe su da maita ko ta shige jikinsu,
kar ki sake
ki shiga min b'angare mayyar banza mayyar hofi ko na had'a ki da karnuka su yayyaga min namarki anan."
Ai da gudu Feeryal ta juya tayi waje.
Uwar amarya Mommy ta fito da ka kawayen ta zasu gurin walima, ta cab'a kwalliya cikin wani arnen lashi mai tsada
r gaske tasha d'inkin manyan mata,
matan masu nera.
Umma Karima ita ma da nata kawayen kusan shiga iri d'aya sukayi da Mommy sai dai kalar leshin ta daban ne amma mai tsadar ce ita ma.
Motar Hajiya Luba ne ya kunno kansa cikin gidan.
bayan ta nunawa secur
ity pas d'in gayyatar ta,
suka bud'e mata get ta shigo.
Mommy suka tsaya suna zaman jiranta su karaso dan ta gane motar ta.
a babban parking lot d'in gidan in da motoci ke cike tam nagidan dana jama'ar da suka sami halarta bikin ke tare.
direban ta ya dai-
dai parking.
Hajiya Luba suka fito ita da wata budurwar yarinya.
suka karasa in da su Mommy ke tsaye.
suka rungumi juna da Mommy,
Hajiya Luba ta saki Mommy tana fad'in
"Kaga uwar gida a gidan Alhaji Abubakar Fiya, Allah dai yasa bamu makara a walimar ba."
"Kun dai kusan makara dan har an fara, na ce gajiyar jiya ce ta hanaki isowa da wuri, to ya gajiyar jiyan."
"Wlh ke kam dai ingaya miki bawai gajiya bace ta zaunar da ni, d'iyarki ce gata nan Kuraiba ta b'ata min lokaci, kin san shirin 'yammata sai a hanka
li, a fenta nan a fenta can,
ke Kuraiba ga Mommyn ku nan ki gaida surukan ki."
Budurwar da aka kira da Kuraiba ta ce
Ina yini."
ta fad'a a takaice.
Mommy tayi murmushi tana amsawa da
"Lafiya lau Kuraiba ya school."
ta ce "Alhmdulillah."
"Kuraiba fa an g
irma nakai 1y rabon da na ganta,
har tafi Farida a tsaye."
cewar Mommy, tana dubanta da murmushi.
Hajiya Luba ta ce
"Ni da nayi zaton ma lokaci guda za'a had'a bikinsu a wuce gurin."
"A'a dai adai bi d'aya bayan d'aya, ayi shi daban-daban ai zaifi dad'i, s
urukar tawa ko ba laifi."
cewar Mommy tana duban Kuraiba.
"Da dai mun karasa kar a gama muna tsaye muna wata maganar muyi wacce take gaban mu, abar wannan da ba'a san yuwuwarsa ba tukun."
cewar Umma Karima da tun farin maganar ta had'e rai da alama dai ak
wai wata a kasa,d'ayan biyu ko bata son faruwan lamarin da suke magana a kai ko kuma akasin haka.
Hajiya Luba ta ce
"Ai Insha'allahu Kuraiba ita ce surukar Alhaji Abubakar Fiya na farko, mudai karasa wanda ake cikin yanzu dai kawai, kafin zuwan nasu lokac
in."
FEERYAL data fito daga side d'in Hajiya da sauri, sukayi kicib'us da su zasu wuce.
Mommy ta bita da harara tana fad'in
"Ke kutumar uban ki bakya gani ne zaki bige mutane yarinyar banza kawai."
Umma Karima ta kai mata zunguri a goshi tana cewa
"Tsinta
cciyar mage bata mage wuce ki je in da aka gayyace ki."
"Wace ce wannan d'in?."
cewar Hajiya Kuba tana nuna ta.
tsaki Mommy taja ta ce
"Yarinyar da Hajiya Fatimah ta tsinto mana."
"Wai ita ce haka anya ba sato musu yarinyar mutane tayi ba a asibitin wata
kasa ba kuwa?
bata shiga US after 2 mon before kawo yarinyar gidan nan ba."
Mommy ta ce
"Hm zata iya ai dan rashin haihuwa babu abun da bazai iya sata ba, an gama yawon gurin malamai niman maganin haihuwa an rasa ai dole ta b'ullo ta wata hanyar."
"Amma d
ai tayi asara, taraba yarinya da danginta dubi kyakkyawar yarinya fa dan Allah."
cewar sauran kawayen nasu.
Feeryal bakin get na side d'in Aunty ta tsaya har saida su Mommy suka wuce kafin ta dawo ta d'au hularta da ya fad'i lokacin da Umma Karima ta zung
ure ta.
Ta sunkuya ta d'au hularta tana mikewa, ta saki murmushi ganin wad'an da suke kusa da ita ta ce
"Laa Chuchu Chulu baku tafi ba da man?."
"Babu tafi ba muma mun tsaya jin wa'azin ne mu je gurin walimar dan anyi nisa da farawa kar a gama babu je ba.
"
"Ni dai bazan je ba, akwai su Mommy a gurin zasu kore ni ko su duke ne."
"Baza suyi miki ko mai ba zo muje, bazamu zauna ma a kusa da su ba."
yatsa ta saka a hab'arta ta ce
"Kun tabbata."
"Mun tabbata."
suka had'a baki wajen fad'a.
Suka sakata a tsakiy
a suna tafe a hankali suka nufi gurin da ake gudanar da walimar.
har suka dumfaro filin gadan-gadan babu wanda ya lura da su.
malamar da take gudanar da walimar ita ta fara lura da su.
zumbur ta mike tsaye tana fad'in
"Yaaaku jama'a ko shin kuna ganin abin
da nake gani kuwa!?."
Gabakid'aya jama'ar gurin sukabi inda take nunawa da hannu.
nan da nan gurin ya kace da hayaniya had'e da kururuwan mata suna fad'in
"Wayyo ga zakuna zakuna sun shigo gida."
tuni mata suka fara hargitsewa suna niman mafaka domin ce
ton rayuwar su.
zo kaga mata in da suke zubewa kan kujeru suna karya kujeru.
Mommy da aka tureta a kan kujera ta zube kasa shirim, ta kasa ko da iya motsawa tsabar tsoro tana baje a kasa jikinta na rawa.
idanunta a kan Feeryal da manya-manyan zakunan da s
uka sakata a tsakiya.
suna cigaba da dumfaro gurin gadan-gadan.
Hajiya kuwa da rarrafe take tafiya ta tafi bayan wasu kujeru can ta b'oye, ta rufe idanunta gam-gam.
tana karanto addu'ar ta da ta saba
"Wasayyahu wasayyahu wasayyahuuuuu yasin me manjaga li
'eelafi kafa bakwai yasin kafa dubu lakadija'akum kafa d'ari ba d'aya."
Mata sai karo da juna ake ana zubewa kasa, sai ihu da niman agaji.
Ganin haka yasa Feeryal taja ta tsaya.
tana bin jama'ar da kallo.
tsoro taji ganin idon Mommy a kanta sai ta ju
ya da sauri ta gudu, tana gudun kada Mommy'n ta taso ta bige ta, dan a zaton ta, zuwan gurin su da tayi ne yasa ran Mommy b'aci, kuma ta rigada ta san cewa ta hanata zuwa in da suke.
Side d'in su ta koma ta haye upstair tana hango yadda mata ke gudu suna
fad'uwa suna karya kujeru.
Dariya ta tuntsure da shi hango wata katuwar mata ta zube kasa timm , mata sai zubewa a kanta suke sai ihu take kurmawa takasa tashi.
tana ta juya katon d'uwawu a kasa.
"Ke Feeryal."
da sauri ta juyo jin maganar Aunty