Showing 18001 words to 21000 words out of 86898 words
halin ruwa ba, uban me ya kaiki side d'in nasu,
ai dole tayi kama da Miesho kin tab'a ganin mai
kama da ita ko a kasashen su ne bare a kasa
r nan mai tsuffar aljanu, idan na sake ganin ki a side d'in
sai na ci ubanki,
me za'ayi da Fatima gayyar tsiya."
Ajeemal da yanzu shigowar sa ya b'ata fuska
"Mommy to ku ina ruwan ku da yarinyar nan, Daddy
shi yaji zai iya riketa imma aljanar ce meye ma
tsalar ku, tun da Aunty ce ke rukon ta ba ku
ba."
"Dalla tafi can ka ba muta ne guri, me ka sani a rayuwar yau."
cewar Umma Karima.
Mommy ko ashar ta auna masa, ya girgiza kai yaja
kafarsa ya yi gaba.
Lanar Lahadi aka kawo wa Feeryal kayan makarantar
t
a, ranar ba zama tun da aka gwada mata taki a cire har sai da Aunty ta lallab'a ta tayi bacci kafin a ka cire mata tana bacci bata sani ba.
Washegari ranar Monday da wuri Aunty tagama mata
shiri, tayi matukar kyau sosai cikin shigar uniform.
tagoya schoo
l bag d'in ta, sai tsalle take da murnar zata makaranta.
A can side d'in Mommy su Farida sun gama nasu shirin
suna zaune a dinning suna breakfast.
Mommy ta dube autarta Ameerah tashafa kanta tana fad'in
"Daddyn ku ya kafe sai da yasaka munafukar aljana
r
nan a makarantar ku, nasan kuma karshe ajin ku
za'a kaita, kar ki kuskura kirika bari tana zama
kusa da ke, bare ta manna miki damuwa;
idan tamiki wargi kici uwarta da duka,
dan aljanu
tsoron duka ne da su, shegiyar yarinya mayyar aljana 'ya'yana su
n fi karfin ki,
kuma kar wata ta raga mata acinku ba jinin ku bace
ita, babu abin da ya had'a ku da ita."
Farida da Sumayya suka girgiza kai alamun sunji gargad'in nata.
A b'angaren Umma karima kuwa
Harsu Bilkisu Saddika Rahama Nabila sun gama komai da
komai suna shirin fita,
tun tashin su Umma Karima ke musu bitar tsiya har kawo yanzu da zasu fita,
ta dubi Nabila karamar su ta harare ta tana fad'in
"Ba an iya tab'aki ki bud'e baki haa ba, duk san da naji labarin aljanar can tayi miki kallon banza baki
cire kwayar idanunta a hanun ki ba,
sai na ci kutumar uban ki da duka,
babu ragawa sakanin ku,
kurika yiwa shegiya dukar tsiya,
yar tsintuwa ce uban ku ba d'aya ba, ko ya mutu bata da gadon sa,
ita uwar kanzagin nata ma haka zata tashi a tutar babu, bat
a tab'a nishin haihuwa ba sai dai na kashi a shadda,
maza ku kama hanya bance ku ragarwa shegiya ba."
Aunty ta fito rike da Feeryal.
suna daf da fita bakin get d'in side d'in ta, ta ce
"Tsaya-tsaya y'anmatan Ammie, sa kafar ki ta dama kifara fita da shi,
sannan kice tawakkaltu'alallah walahaula'wala kuwwata illa billah, sai ki fita da kafar da ma."
baki ta wace har da d'an tsallenta.
sannan ta ce
"To Ammie,tawalkaltu alallah walahaula wala kuwwata illa billaaaah."
murumushi Aunty tayi, batayi mamakin yadda
ta iya addu'ar ba, dan ire-iren addu'o'in nan tana koya mata su sosai.
ta shafa kanta tana fad'in
"Yauwa y'anmata Ammie, to ban da kwad'ayi, ban da fad'a, ayi karatu sosai."
kai ta gyad'a tana murmushi itama, suka fito.
Can ta hangi motar dake kaisu Ame
erah school bakin get d'in dide d'in
Hajiya Nafisat ya d'auko Sahla ya karaso zai d'auki Mimi.
suna tsaye motar
ta karaso, direba yafito da sauri yad'an risina ya gaida Aunty kana ya bud'e marfin baya in da Meimei da Sahla suke zaune ciki.
baki Miemie ta
washe da ganin Feeryal tana fad'in
"Zakije school inmu?."
Aunty ta maso jikin motar ta d'aga ta cak tasaka cikin motar gefen Miemie tana fad'in
"Ita ma ta zama y'ar school d'in ku yanzu."
aiko Meimei ta matsa ta gyara ta zauna tana ta murna.
Sahla ko fusk
a ta b'ata sai hararar Feeryal take, ga dukkan alamu itama ta sami hud'ubar tsiyai daga gurun uwar ta Hajiya Nafisat.
Aunty tayi musu Allah ya tsare, direba yaja motar zuwa bakin get d'in side in Umma Karima.
ya d'auki Nabila, su Bilkisu suka leko cikin m
otar suna hararar Feeryal, sai da motar d'aukar su suma tayi musu hon kafin suka bar jikin motar.
Direba ya ja motar zuwa side d'in Mommy.
su Farida suna tsaye agurin ga motar su ta iso yana ta musu hon,
amma suka ki shiga suna zaman jiran isowar motar da
Feeryal take ciki.
direba ya sauka da sauri ya bud'ewa Amerrah ya ce
"Shigo da sauri kada mu makara."
ta leko cikin motar sai kuma ta yamusa fuska ta ce
"Ni dai bazan shiga a matse ni ba, ai a gurin zamata ta zauna sai dai ta fita na shiga."
ta nuna Feer
yal da yatsa.
direba ya ce "Haba Ameerah dukkan ku yarane ai nan ya ishe ku, to zo ki zauna a gaba ke."
kafa tashiga bubbugawa kasa tana fad'in
"Ni bazan zauna a gaba ba, sai dai ta fita."
Farida ta ce
"Bazata zauna a gaba ba sai dai ita ta fita ta tado g
aba, ko kuma tabi wata motar."
Bilkisu da Saddika suka leko daga motar su suna fad'in
"In bazata fita ba, ki fitar da ita da karfi Farida tun da ba motar ubanta bane."
Da sauri Isa direba ya ce
"A'a ku tsaya, fito ke ki dawo gaba."
ya janyo hanun Feeryal
yafito da ita yasakata a gaba.
kana yakoma mazaunen sa yaja motar suka nufi babban get d'in fita daga gidan duka.
su Farida suka shige nasu motar suma bayan sun gama aika mata da mugun kallo.
Suna isa makarantar duk suka fito, Miemie ta rike hanun Feeryal
Ameerah ta ce
"Sake ta ba 'yar'uwar ki bace."
Miemie ta make kafad'a ta ce
"Ai Ammah ta ce y'ar'uwa ta ce itama."
harran su tayi
"To kar kubi bayana kubi hanyar ku daban."
Ameerah tayi gaba tana hararar su.
duk wan da yazo wucewa in ys hango Feeryal sa
i ya tsaya ya kalleta, yara 'yan'uwan ta da kuma manya,
kowa sai fad'i ya ke
"La ga baturiya ta shigo school d'in mu."
ta dawo abin kallo har wad'an da ke cikin ajijjuwa leken ta suke.
Ajin su Ameerah kuwa a ka bata, tana shiga aji kuwa yara suka mike s
una fad'in
"Laa ga baturiya laa ga baturiya."
Ameerah tayi musu tsawa
"Dalla ku zauna! waya ce muku baturiya ce to aljana ce, mayya bakuga idon ta ba."
hele yaran suka kuma suna leko fuskarta wasu suna fad'in
"Ga aljana ga aljana."
wasu ko daga cikin yara
n basu yarda ba.
Miemie ta ruko hannunta ta ce
"Ku bari fa ba aljana bace 'yar'uwa ta ce."
jin hayaniyar su yasa malami shigowa ajin ya yi musu tsawa, nan kowa ya ni mi guri ya zauna.........!
Mommyn Twins ce
πΊπΊ
*FEERYAL*
πΊπΊ
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*____________________________________*
*
ππ°
AINUWA
πΌ
RITER'S
β
πΌ
*
*
π¦
SSOCIATION
π€π»
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.F
acebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*
ππ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
π
Ώ
οΈ
6
Kullum tare direba ke kaisu makaranta ita da Mie
mie da Ameerah autar Mommy da Nabila 'yar Umma Karima, sai Sahla d'iyar Hajiya Nafisat kuma dukkanninsu ajinsu d'aya.
Bilkisu Saddika Rahama Farida Sumayya duk suna ajin gaba da su, su yanzu suna ajin farko a secondary, su makarantar su daban.
mazan ma h
aka.
Duk san da suka dawo daga makaranta da kuka Feeryal take dawowa,
wani lokacin kuma da bushasshen hawaye a fuska,
wani bin da toshasshiyar murya, taci kuka har ta gode wa Allah.
idan Aunty ta tambaye ta saita ce mata
Ameerah ce da Nabila da Sahala suk
a bigeta suka kuma ce mata mayyar aljana.
Kusan kullum da kuka take dawowa.
Aunty ta rarrasheta ta bata hakuri.
Yau da sukaje makaran ta kuwa ana fita break Ameerah da Sahla da Nabila, suka tara yara suka rika jifanta da takalmar su suna fad'in
"Aljana ma
yya aljana mayya."
idan yaran zasu bari Ameerah ta ce
"Kucigaba da jifanta aljana ce ta b'ace a cikin mu."
Da gudu Miemie ta iso gurin ta tana zube akasa tanata rusar kuka.
ta tattareta ta kare ta da jikinta tana fad'in
"Kurabu da ita ku kyale ta, Allah z
an kira Uncle."
daga can wata Anty'n su taga abin da suke ta taho da bulala aiko duk suka dare suka gudu.
Ana tashi direba yazo d'aukarsu, suna ribibin shiga mota, Miemie ta shige motar ta miko wa Feeryal hanu tana fad'in
"Shigo Feeryal ga guri ki zauna a
nan."
Ameerah dake bayanta ta fizgo ta ta rure ta gefe, ta fad'i a kasa ta fasa baki.
"Mayyar aljana bazaki zauna min agurin zama ta ba."
Ameerah ta fad'a tana harararta.
Sahla ta sa kafa ta take mata hanu.
ta saki kara me karfi tana yarfe hannun da dafe
bakinta in da ya fashe.
Da sauri Isa direba ya zago in da suke yana fad'in
"Kai-kai ku bari mana zaku ji mata ciwo ne,
sannu kinji tashi zo ki shiga gaba."
ya ruko kafad'arta ya mikar da ita ya bud'e gidan gaba ya sakata.
Ko da suka isa gida ganin ta da
fasashen baki, cike da damu Aunty ke tambayar ta ya akayi ta ji ciwon.
kwalla ta fara tana jan shasheka.
ta ruko hanun ta suka zauna kan kujera
"Yi shiru Feeryal garin ya kika fad'i kika fasa baki, kirika yi a hankali kinji ko."
ido ta matse sai ga kwalla
, d'an karamin bakin ta ta cuno cikin tsiririn muryarta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce
"Ba Ameerah ce ta ture ni nafad'i na fasa baki na ba, takuma ce min yayyar aljana,
Sahla kuma ta takamin hannu da kafarta."
ta karashe magamar da matsar kwalla tan
a yarfe hannun nata.
shiru Aunty tayi idanunta a kanta acikin ranta take fad'in
"Lallai kuwa akwai damuwa in har suma yaran halin iyayen nasu suka d'auko."
kanta ta shafa alamun rarrashi ta ce
"Yi hakuri 'yanmatan Ammie bazasu sake dukanki ba."
"Ammie wai
ni mayyar aljana ce?."
ta jefo mata tambayar fuskarta tam da son jin amsar.
"Inji wa? karya suke ke ba aljana bace kuma ba mayya ba."
"Ai Ameerah da Nabila da Sahla sun ce ni mayyar aljana ce sun tara yara suna ta jifa na."
ran Aunty ya b'aci cikin jin zaf
in abin ta ce
"Zan ja musu kunne bazasu kara ba,
zo muje ki cire uniform kiyi wanka sai kici abinci ko."
ta janyo hanunta suka shige bedroom...
Washegari kamar ko yaushe da wuri ta gama mata shirin tafiya school ta ruko ta suka fito, can ta hangi motar k
aisu school a bakin get na side d'in Hajiya Nafisat zai fara d'auko Sahla ita ce side d'in su ke karshe,
kafin yazo ya d'auki Miemie ya gangaro ya d'auki Feeryal d'in sai kuma Nabila sai Ameerah a karshen d'auka.
bata tsaya jiran sai ya karaso ganin Sahla
ma bata fito ba,
suka toko da kafa har zuwa kofar get d'in side in Mommy.
anan suka tsaya harya d'au Sahla Miemie yazo ya d'au Nabila
ya karaso.
dai-dai lokacin kuwa su Ameerah suka fito.
Farida da Sumayya duk suka d'auke kai kamar basu gantaba,
bare ta sa
ran samun gaisuwa daga gare su.
dan dama basu da wannan tarfiyyar ganin babba su gaishe shi.
Aunty ta ce
"Ameerah Nabila Sahla, me yasa kuke dukan Feeryal kurika yadda ita a kasa tana jin ciwo? 'yar'uwar ku ce fa itama, ku da zakuga wani yana yi mata ku h
ana amma ku kuke dukanta, kar ku sake dukanta kanwar ku ce kun ji."
maganar Farida tajiyo daga bayan su
"Ah mu ba kanwar mu bace kada ki danganta mu da ita, meye had'in aljana da mutum."
Aunty ta juyo tana kallon yadda Farida take wani yamutsa fuska.
"Kuma
mayya ba mai idon mayu."
cewar Ameerah tana hararar Feeryal.
Ganin yaran suna shirin yi mata rashin kunya ta ce
"Kul ingaya muku ni ba sa'arku bace, zan farfasawa yarinya baki, idan tace zatayi min rashin kunya, wata a cikin ku tasake tab'ata ta ga yadd
a zanyi da ita."
Gajeren tsaki Farida tayi taja hannun Sumayya ta ce "Zo mu tafi kar mu tsaya b'ata lokacin mu anan."
tawani murgud'a baki cike da fitsara, suka shige motarsu da yanzu ya karaso gurin.
Aunty ta ce
"Dukan tsiya zanyi wa yarinya idan tace za
ta zage ni fitsararrun banza kawai,
kuma wlh wata a cikin ku tasake tab'ata ta gani."
Isa direba yashiga bata hakuri, kana yabud'e wa Feeryal gaba Aunty ta sakata tana musu Allah ya tsare..
kana ta juya ta koma side d'in ta...
Duk da gargad'in da Aunty ta
yi musu baisa sun ji ba, yau ma sai da suka tara yara sukayi ta jifanta,
ta dawo da jikin ta fusu-fusu.
kullum kuwa haka suke yi mata, su tara yara suyita jifanta suna ce mata aljana mayya.
abun su Ameerah sai gaba ya ke, lura da yadda suka sako ta gaba, r
anar malaman su suka tarasu suka zanesu gaba d'ayan su da yaran da suke tarawa.
Kasancewar ranar juma'a ne da wuri a ka taso su a makaranta,
a mota Ameerah nata jan hanci sabo da ba kad'an ba dukan ya shige ta,tarika hararar Feeryal tana kwafa.
suna isa g
ida, Ameerah aka fara saukewa kofarsu kafin Nabila, sai Feeryal.
Miemie ta leko ta jikin gilashin mota ta ce
"Feeryal gobe weekend zakizo garden muyi wasa?."
ido Feeryal ta d'an waro cike da jin dad'in abun da Miemie ta fad'a, dan tana son wasa sosai.
tab
ud'e d'an karamin bakinta tana d'an wawware idanunta irin abin yazo mata a bazata.
ta ce
"A Garden d'in Ammah in ki? zan zo da baby na ma, ke ma zaki zo da naki?"
Miemie ta ce
"Ke ba garden in Ammah na ba, a babban garden na bayan sede d'in su Ya Ajeema
l, zaki zo?."
kai ta gyad'a mata, duk da bata tab'a sanin da wannan garden d'in da take fad'a a cikin gidan ba,
ya ma za'ayi ta sani ita da ba ko ina take zuwaba a cikin gidan.
daga makaranta sai side d'in su.
ko side d'in su Miemie'n ma baifi a kirgaba
zuwanta side d'in,
shima d'in da Ammie'nta suka je.
Miemie ta koma ta zauna kan sit, direba yaja suka nufi side d'insu.
Feeryal ko ta zuba a guje tayi cikin nasu side d'in tana fad'in
"Ammie na dawo Ammie na dawo."
da sauri Aunty dake shirya abinci kan d
inning ta bud'e mata hannu ta taho da gudu ta fad'a jikin ta.
Aunty ta rungume ta tana cewa
"Oyoyo 'yammatan Ammie an dawo ya karatu."
sai ta cirota a jikin ta tana kallon fuskanta da mamakin ganin yau babu hawaye kan fuskar nata.
"Yau ba'ayi kuka ba ke na
n?."
kai ta gyad'a
"Ai yau su Ameerah basu bigeni ba, Uncle da Aunty sun ce zasu zane su in suka kuma duka na."
"Ah gaskiya Uncle da Aunty sun kyauta, daga yanzu bazasu sake dukan ki ba."
murmushi tayi sai kuma ta ce
"Ammie gobe weekend zamuyi wasa a garde
n da Miemie."
d'an shiru Aunty ta yi tana kallon ta,
tasan dole su Ameerah suna gurin.
dan duk ran Saturday and Sunday yaran gidan manya da kananun su suna had'uwa a babban garden d'in gidan, ayi ciye-ceye da shaye-shaye da tand'e-tand'e.
Kafa tashiga bu
gawa kasa tana ce wa
"Ammie zanje Ammie zanje."
"Feeryal su Ameerah fa zasuje suma, kiyi zaman ki kawai a nan."
d'an karamin bakin ta ta turo gaba tana shirin yin kuka, Aunty ta ja kumatun ta ta ce
"To naji zakije shi ke nan, taho muje a cire Uniform."
Wa
shegari da safe Miemie tabiyo wa Feeryal sutafi,
badun Aunty taso ba ta barta suka tafi.
kaf yaran gidan sun hallara, masu wasa suna yi masu ciye-ciye suna ta kai.
tun daga can Sahla ta hango su Miemie da sauri ta matsa in da Ameerah take, ta nuna mata su
da hannu.
Ameerah tawani taune baki tuno da bulalar da tasha jiya akan Feeryal.
da sauri ta tafi ta sha gabansu Miemie, ta ware kafafunta ta bud'e hannayenta.
"Baza ta shiga ba ai nan ba gidan su bane gidan mu ne."
cewar Ameerah tana hararar Feeryal.
Miemi
e ta ce
"Wasa zamuyi kibari Ameerah."
da gudu Sahla da Nabila suka zo in da suke.
Nabila ta ce
"Yauwa Ameerah kin tuna dukanmu da jiya akayi akan."
"Ai rama kayanmu zamuyi."
cewar Sahla tana gyara hannun rigarta.
ai ko kan kace me suka rufu a kanta duka t
a ko ta ina suke kai mata.
Miemie tarika jansu tana fad'in
su daina.
ganin bazasu bari ba tayi gudu taje gurin su Farida
"Aunty Farida Aunty Bilkisu ku hana su Ameerah dukan Feeryal, gafa yadda suke dukanta."
Farida ta waigo ta kalli in da suke ta ce
"Su
ci ubanta dan uwarta wayace tazo nan ko an gayyace ta ne."
Bilkisu ta ce
"Su faffasawa shegiya aljana baki ko zata b'ace mana a gida."
Da gudu Miemie ta juya ganin ba taimakon ta zasuyi ba,
tayi gurin Ajeemal da ta hango yafito daga b'angarensu, zai fita
damuwar sa.
"Ya Ajeemal Ya Ajeemal gasu Ameerah can suna dukan Feeryal."
da sauri ya yi in da suke yana fad'in
"Kai bakuda hankali ne."
aiko suna ganin