Showing 1 words to 3000 words out of 45929 words
ο»Ώ[04/06, 14:35] Maman noorul huda marubuciya: πππππ
RAYUWAR NUR
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,interlingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Wanan labarin kagagen labari banyi shi dan cin zarafin kowa ba.
WARNING
Ban yarda wani ko wata ta canja min labari ko ta wata siga ba in haka ta faru Allah ya isa.in kunni yaji jiki ya tsira.please be warn
NOTE:duk Wanda bata fara bibiya daga farko ba ta jira documents bana so sai nayi nisa a ta bina PC
Barka da sallah masoyana Allah ya maimaita mana(amin)
dedicated to my fans all over the world.wish you all happy eidil-fitir
π
Ώ1β£&2β£
please fans zaku gan nayi left a groups haka ta faru ne sakamakon matsala da watsapp dina ya samu please kuyi add dina a wanda nayi left ko a turo min links ta PC
Bismillahir Rahmanir Rahim
Monday ta kasance rana ne da mutane ke busy domin masu zuwa aiki na zuwa yan makaranta ma haka kamar inda kuka sani ko bature na tsoron monday
Wata budurwa na hango da bazata wuci shekara ashirin da biyar ba rike da hanun wata yar yariya da bazata wuce shekara bakwai ba sanye da uniform din makaranta boko green and white check
Yariyar sai zuba take tana cewa"mummy yaushe za ki nuna min daddy na kowa a makarantar mu sai maganar daddy su suke"
Murmushi tayi tace"very soon my dear ai na kutsa nuna miki shi,ya tafi humura ne"
Yariyar tace"toh amma mummy ban taba ganin sh......."bata karasa ba sakamakon ihun da tayi mata
Tace"meyasa baki jin magana ne eh? Bana hana ki maganar daddy ki ba?akwai abinda kike bukata ne da bana yi miki shi a matsayi na na mummy ki?"
Hawaye ne ya cika idon TASLEEM cikin kuka tace"sorry mummy dan Allah kiyi hakuri"
Kallonta NUR tayi sai taji ba dadi tace"no dear iam soory please don't cry"rungumeta NUR tayi tace"share hawayenki"
Sharewa tayi tace"mummy ance in bamu biya kudin makaranta ba za a kore mu gobe"
Shiru tayi amma a zuciyarta tunani take ina zata samu kudi ta biya mata kudin makaranta a wanan halin suka ci gaba da tafiya har suka kai gate din makarantar,kodaden Jakarta ta bude zip ta ciro wani face mask ta bata tace"karki manta kisa lokacin break banda wasa cikin kura,please baby don't be careless bana so ki samu attack"
Tasleem tace"mummy zan kula da kaina,kema ki kula da kanki"dukawa nur tayi ta kissing dinta a goshi tace"sai kin dawo kiyi karatu"
tace"toh"tafiya ta fara d'angawa NUR hanun
sanda ta gan shigewar ta makaranta sanan ta juya,agogo hanunta ta duba ta gan 8:12am zaro ido tayi tace"oh no iam in trouble yau muna da meeting by 8:am gashi za a yi mana introducing sabon C E O,gudu ta fara yi tana tare abin hawa amma Wanda ya tsaya domin a cike yake kasancewar ranan Monday ne
haka ta cigaba da tafiya sai dai bata yi nisa ba takalmi kafanta ya sinke
cirewa tayi ta rike a hanun ta cigaba da tafiya
AFSAMAN building company
wani hadadden gaye ne zaune a wani hadadden office tsayawa fad'a kyau din office din bata lokacine ga workers sun tsaya gaban shi sai fad'a yake yace"manager wani irin aiki kuke bakwai la'akari da lokaci eh?a ce har 8:40 staff bata zo aiki ba kuma ta San tana da presentation by 8:am"
manager yace"sorry sir Afan zata iso yanzu"
Afan yace"you should be sorry for yourself because I won't hesitate to sak u both,domin in muka yi loosing contract din nan I will make sure you pay dearly with your job.a ce wai saboda wata banza baza mu tafi meeting ba. wai dan ita tayi plan din building din wanan wani irin carelessness ne?ita kadai ta iya drawing?kallon wani daga cikin staff din yayi yace"what is your name?"
a rude mutumin yace"sir dani kake?"
yace"no da kaina nike, wai meke damun Ku ne?"
mutumin yace"sorry si..."be karasa ba sir Afan ya katseshi da cewa"my friend will u keep quite and tell me you bitter name "
a rude mutumin yace"sunana isah garba a urban planing department nike,ina zama ne a anguwan sarki,matana d'aya da ya......"makalewa sauran maganan yayi sakamakon d'anga me hanun da Afan yayi
yace"sunan ka na tambaya ba tarihin rayuwar ka ba"
isah ko duk zufa ya jika shi saboda rudewa dan a gaban su ya kori mutane uku a aiki cikin rudeawa yace"yi hakuri sir"
Afan yace"meyasa Baka yi handling project din ba"
jiki na rawa isah yace"ai rabawa a ka yi ni nike handling na government house"
sir Afan zaiyi magana sai ga sameer ya shigo yace"bro wai har yanzu bata iso ba,company fa sai kirana suke"
cikin jin haushi Afan yace"eh bata iso ba"
sameer yace"gaskiya she deserve to be purnish"
Afan yace"live that to me"
zama sameer yayi yace"matsala talakawa kenan an taimaka musu amma sai sun kai ka iyaka"
NUR ko da kafa ta tako da takalma a hanun ta, tana shigowa ta tarar da manager zaune yayi tagumi a desk din receptionist na audit department
karasawa tayi tace"sir lafiya?"
ai d'angowa yayi yace"ina kika shiga ne NUR?ai ina ga yau zamu rasa aiki mu"
tace"yi hakuri wallahi na kai TASLEEM ne makaranta kuma ban samu abin hawa ba kasan yanayi anguwan mu"
yace"toh kije C E O office amma kiyi ta duk wata addu'a data zo bakin ki domin mutane uku ya kora da safen nan"
jiki sanyaye ta karasa office din tana zuwa ta tarar da su zaune suna hira da sameer da salama ta karasa cikin office din
tace"......."
sai na gan comment zan cigaba Wanda kuma suke groups dina basa comments in an turo novel Bama nawa kadai ba.toh zan cire su dan ban gan amfanin zama su a group din ba
yan groups dina bakwai kyauta min wallahi sai ayi ta niman novel daga farko amma a ce babu Wanda zai taimaka sai na turo da kaina ko kuma in mutum ya gaji da tambaya a group ya biyo ni P C.wai meyasa kuke min haka ne?
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
[04/06, 18:20] Maman noorul huda marubuciya: πππππ
RAYUWAR NUR
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
DEDICATED TO ANTY SHAMSIYYA (MAMAN FATI)
π
Ώ3β£&4β£
Bismilahir Rahmanir Rahim
tace"good morning sir"juyowa suka yi suka kalleta daga sama har kasa rike take da takalmi a hanun ta
sameer yace"ikon Allah wai meke damun manager company nan ne?nifa shiyasa ban so na biyo Ku Nigeria ba amma ummi ta matsa gashi yanzu sun bar mahaukaciya ta shigo maka office "dangowa NUR tayi ta kalleshi da mamaki sana ta kalli jikinta,sanye take da dogon rigar atampa green yana da touches na farin flower sai farin hijabi iya guiwa,sai takalmin ta a hanun
ba tare da Afan yayi magana ba ya dauki waya ya kira office din manager company
manager na ganin kira ya mike jiki na rawa ya d'aga kiran
yace" OK gani nan zuwa"
cikin minti biyu ya isa office din Afan ya tarar dasu zaune NUR a tsaye shiko Afan rubutu yake yi
karasawa yayi zaiyi magana Afan ya d'anga me hanun ba tare da ya kalleshi ba,shiru manager yayi
sanda ya share wasu mintina ya dago kai ya kalleshi yace"manager miye haka?"yayi maganar ne tare da nuna NUR
manager yace"ai itace wanda ake jira nurul hudah abdallah"
ai sai suka hada baki da cewa"what!!!"
sameer yace"dama wanan banza ake jira eh?"
Afan yace"what insult"
NUR tace"dan Allah kuyi hakuri wallahi ban samu abin hawa bane"
Afan yace"yi wa mutane shiru ke har kin isa in jira ki?"kallon manager yayi yace"wani irin mutane kuke diba eh?wanan bata kai matsayin yin aiki a nan office din ba,a bata takardan sallama"
ai tuni kuka ya kubcewa NUR sugunawa tayi har kasa ta rike me kafa tace"bawan Allah ka dubi girman Allah da annabi ka rufa min asiri ka barni in cigaba da aikina,wallahi dashi nike samu muci abinci nida ya'ta in biya mata kudin makaranta na roke ka ka rufa min asiri ya'ta na da lalurar chronic asthma da wanan aiki Nike biya mata kudin magani ka rufa min asiri"kuka ne ya ci karfin ta
shiko manager duk tausayin ta ya kama shi
Afan ko ture ta yayida kafa yace"how dear you touch me with you filthy hands"
ai sai ta zube kasa tace"ko baza ka yafe min dun komai ba ka dubi halin da ya'ta zata shiga in na rasa aiki na"
fashewa da dariya sameer yayi yace"toh sai me?ita yar taki bata da uba ne?"
tace"bata da shi ni kadai take dashi,nima ita kadai gareni dan Allah Ku dubi girman Allah Ku yafe min nayi alkawarin bazan kara zuwa latti ba"
Afan yace"get out"
manager yace"sir a yi mata hafuwa"
kafin Afan yayi magana sameer ya riga shi da cewa"take this thing out of this building "
jiki na rawa manager yace"NUR tashi muje"
tashi tayi tana cewa"sir ka dubi girman Allah ka barni na cigaba da aikina,nasan ko baka da ya'ai kana da kanwa kuma ai wata rana zasu nimi taimako a gun wasu"
a fusace sameer yace"wai me kake jira ne baka fita da ita ba"
jan hanunta manager yayi zuwa waje sai kuka take
shiko Afan cigaba yayi da aikin shi
sameer yace"bro bari in kira flims investment na fada musu su danga meeting din har sai mun shirya"
Afan yace"urmmmm"
jawota waje manager yayi har haraban building din ta zauna a kasa tana kuka
cikin tausayawa manager yace"ki yi hakuri basu da imani ki je ki nimi wani aiki"
cikin kuka tace"ba komai nike tunani ba illah halin da TASLEEM zata shiga wallahi da aikin nan na dogara fa,ga maganar asthma dinta ina zan samu kudi siya mata magani?
manager yace"da zaki ji shawara na da kin kai ta wajen abban ta ki cigaba da rayuwar ki shima ya cigaba daga inda kika tsaya,domin gaskiya kina wahala a kanta,dubi fa baki da takalmin kanki"
girgiza kai tayi tace"TASLEEM bata da kowa sai ni mummy ta.ita ce farin cikina wallahi bani da wani buri da ya wuce kullum na ganta tana farin ciki"
manager yace"rasuwa mahaifinta yayi"
tace"ah'a"
yace"oh cikin shage kika kayi domin a iya sanina baki da aure "
tashi tayi tace"nagode manager zan tafi gida"ta barshi tsaye
takawa tayi tayi har ta isa anguwan su,wani gida laka na gan ta shiga daki daya ne ciki sai bayi ko kicin babu sai balle a ce sillin da sallama ta shiga ta bude labulan daki
data budurwa ce kwance sai barci take,kallonta NUR tayi ta girgiza kai tace"a ce mutum yayi ta barci "
ja mata kafa tayi tace"zakiya!zakiya!!zakiya!!! "
a na ukun ne ta tashi tana murje idanu cikin magagin barci tace" ya na gan kin dawo?"
fashewa tayi da kuka ai da sauri zakiya ta mine ta zaune tace"subhannallah meya same ki?"
cikin kuka ta bata labarin komai da ya faru a office
zakiya tace"kutumar uba ke kika kyale su har suka miki wulakanta ki,amma babu komai ki kyale su"
tace"ai dole ma domin bani da Inda zanyi dasu"
zakiya tace"karki samu Allah za kawo wani aiki,kije akwai taliya a tukunya"
zuwa tayi ta bude tunkuya ta gan taliyar kad'an ne,rufeawa tayi ta dawo ta zauna
zakiya tace"baza ki ci bane?"
NUR tace"no zan baiwa TASLEEM kar ta dawo ta rasa Wanda zata ci"
zakiya tace"kefa?"
tace"karki damu ni damuwata inda zan samu kudin makaranta TASLEEM ne"
zakiya tace"ke dai komai ki ce TASLEEM,ina guje miki ranar da dangin ta zasu gane ta su kwaceta a gun ki"
hawaye ne ya ciko a idon NUR tace"ba amin ba,TASLEEM har a bada ya'ta ce"
zakiya tace"ki daina yaudaran kanki domin bake kika haifeta ba"
toshewa zakiya baki tayi tace"please ki daina fadi
wacece NUR
maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
[05/06, 02:09] Maman noorul huda marubuciya: πππππ
RAYUWAR NUR
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,interlingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Dedicated to my humble family
π
Ώ5β£&6β£
Bismilahir Rahmanir Rahim
NURUL hudah Abubakar musa ya'ce ga alhaji alhaji abubakar musa da marigayiya hajiya hauwa musa,
Hajiya hauwa yar asalin kasan Cameroon ne,kasuwanci ya kai alhaji Abubakar Cameroon inda ya hadu da hajiya hauwa har suka fara soyayya sai dai mahaifinta be so ba saboda baya son suyi auren nisa ya fison ta auri yar kasan Cameroon kasancewar su uku ya haifa itace auta kuma mafi soyuwa a zuciyar shi domin ya fi sonta.tana da yaya mohd sai me bin shi hafsat
Shima a nashi bangaren hakane domin yan uwan shi basu amince ba most especially matar mahaifin shi watoh hajiya maryam (anty amarya)domin ta so a ce ya auri yar'ta maimuna agolan gidan domin a bazawara mahaifin shi ya auro ta amma ya nuna in ba hauwa ba sai rijiya hakan ba karamin haushi ya bata ba kuma ta dau alwashin raba su ko ta halin kaka
babu Inda mahaifin hauwa be yi ba akan ta rabu da alhaji abubakar amma taki har yaya ta hafsat tazo domin a lokacin tana aure a cikin garin Cameroon da yaron ta d'aya uthman amma ana kiran shi da afan d'an shekara 10 tayi mata nasiha akan ta hakura tunda mahaifinsu baya so amma taki shi babban yaya yayi mata nasiha amma ta nuna in bats auri abubakar ba zata iya rasa rayuwarta
cikin b'acin rai mahaifinsu ya amince bisa sharadi babu shi babu ita kuma karta kuskura ta dawo me gida,ba karamin tashi hankali ta shiga da furucin shi ba amma bata jin zata iya hakura da auren domin a lokacin kuruciya na diban ta
cikin kankanin lokaci aka daura mata aure ba tare da yan uwanta sun gan fuskar angon ba domin yaya mohd fushi yayi yaki zuwa dauri auren ma.mahaifinsu ne kawai ya San shi,bayan an daura aure aka tafi da hauwa Nigeria sai kuka take domin kap dangin su babu Wanda ya rako ta
a na kaita direct kano aka kaita family house din alhaji abubakar mahaifiyashi ko sai Murna take tana na nan da ita domin haka kawai ta ji kaunar ta har zuciyarta
anty amarya ko kamar ta kurma ihu dan bakin ciki ita da yar'ta maimuna sai zagaye daki suke
washe gari aka kai amarya dakin mijin ta nasarawa G R A kano
soyyaya suke gudanarwa son ransu bayan wata tara da auren su,hajiya hauwa ne zaume da katoton cikinta tana shan kankana sai ga alhaji ya shigo
yace"sanu da hutawa?"
tace"yauwa alhaji ya aiki?
yace"lafiya"zama yayi yana bata labari kasuwancin shi tana murmushi ai bayan minti talatin sai ta fara ihu ga ruwa na bin kafanta
cikin tashin hankali ya kikimeta sai mota dai'dai nan sai ga maimunatu ta shigo,shiga motar tayi bi su asibiti
sai dai sun share awa biyar a asibiti babu labarin haihuwa,tuni maimuna ta sanar da mahaifiyarta halin da ake ciki
dariya anty amarya tayi tace" lokaci yayi da zamu aiwatar da kudirin mu,itama dariya maimunan tayi tace"toh ya za ayi ne?"
kome ta fad'a mata oho sai tace"haka nike son ki mummy na"
bayan kakar wuya da hauwa ta sha ta haihu tagwayen mata,nurse ne ta fito ta sanar da alhaji amma bata fad'a me yan biyu bane an dai fad'a me ta sauka lafiya
cikin tashin hankali yace"amma hauwa na lafiya ko?"bai damu da ya tambayi ko me aka damu ba
nurse tace"kalau amma yaje lab a diba me jini domin tana bukatan jini kasancewar ta zubar da jini dayawa"
yace"toh amma zata samu lafiya ko?"
tace"inshaallah"duk maimuna na jin su"
bangaren hauwa ko bayan an gyra ta da ya'yan aka kaisu dakin hutu jini kawai ake jira a sa mata
kallon ya'ya tayi tace"nurse wacece babban?"tana magana ne cikin karfin hali
dauko ta aka yi aka mika mata
kallonta hauwa tayi tace"ya'ta"tana hawaye domin yan uwanta ta tuna.abin wuyar wuyan ta ta Ciro mai bala'ib kyau ta samata kasancewar yana da wuri ragewa da karawa domin kowa a gidan na da irin shi kama daga kan yaya mohammed har anty hafsat
itako maimuna jira take nurse ta fito ta shiga ta aiwatar da kudirinta domin tuni hajiya marya ta aiko da allurar da zata yi mata
nurse ko na fita ba da dadewa ba sai maimuna ta shiga dan har hauwa ta fara bacci
karasawa maimuna tayi ta kama hanunta ta soka allura ai sai hauwa ta bude ido tace"lafiya maimuna"
maimuna tace"kashe ki zanyi domin na dade ina kaunar Abubakar kuma zan iya yin komai dan in mallake shi domin yana da dukiya"
hawaye ne ya fara bin kumatun hauwa domin tasan ta gama yawo tunda maimuna ta riga da ta yi mata alurar mutuwa
nadama bijirewa mahaifinta ne ya lulubeta,tana ji tana gani maimuna ta dauki d'aya daga cikin yaran,wanda ta sanya wa sarka amma bata da karfin tashi zata dauki d'ayan sai jinjiran ta sala ihu ai da sauri ta ijiyeta
tace in na tafi da wanan ai sai asiri na ya tonu amma bari in je da wanan in dawo in na dawo sai na tafi da ita nasan kafin lokacin tayi barci"
fitan maimuna ba da dadewa ba sai ga nurse ta shigo amma abin mamaki babu d'ayan jinjiri itako hauwa sai cewa take ya'ta an tafi da ita"
da gudu nurse ta ruga sai office din Dr dinsu mai asibiti ta sanar da shi
tashi Dr Ibrahim yayi yace"what?an sanar dasu ne yan biyu ta haifa?"
nurse habiba tace"no ban fad'a mata ba"
yace"OK good kar a fad'a me domin in hakan ta fito mutane zasu guji asibitin mu "
tace"yes sir"
yace" toh muje ward din"
suna zuwa da minti goma sai ga alhaji ya shigo da ledar jini ya tarar da hauwa tana fisge-fisge tana cewa alhaji yan biyu na haifa an tafi da d'ayan"
yace"waye ya tafi da ita"
zata yi magana ta kasa domin babu karfi jikinta sai nuni take da kofa"
Dr Ibrahim yace"alhaji yariya d'aya ta haifa kuma gata nan.ina jin zafin ciwo ne yasa take surutu"
ai karasawa yayi ya rike hanunta sai dai ga mamakin shi hanun ya sake
jijjigata ya fara yi yana haiwa ki mike dan Allah karki min haka amma ina rai yayi halin shi domin ta rasu
bayan sati danya da rasuwar hauwa aka sanyawa yar noorul hudah (light of guidance)inda mahaifiyar