Showing 15001 words to 18000 words out of 45929 words

Chapter 6 - RAYUWAR NUR BY MAMAN NOORUL HUDAH

31 Oct 2025

4132

duniya atleast nasan banda kowa"

Zubewa NUR tayi ta fashe da kuka tace"yi hakuri wallahi na tuba kuka take kamar an mata mutuwa hakan yasa zakiya tausaya mata

Ta sugunna ta d'aga ta,ta rungume tace"na yafe miki ni basan meyasa nike jin zafi a zuciyata ba in kina kuka ko cikin b'acin rai,babu damuwa in baki son fad'amin"

NUR tace"yanzu zan Sanar dake komai ke ce farin ciki na"

Fitowa tayi ta duba TASLEEM sai ta gan wasanta take a sakar gida bata Masan meke faruwa ba

Ganin haka yasa nur komawa d'akin ta rike hanun zakiya ta zaunar da ita itama zama tayi

Sanan tace"tabbas sir Afan shine mahaifin TASLEEM "

Zakiya tace "amma meyasa baki had'a su ba tunda kin San TASLEEM na bukatar tasan mahaifinta,kuma tana da lalurar dake bukatar kulawa sosai miye amfanin ajiye ta a nan tana wahala kudin makaranta da magani ma da k'yar bayan ga mahaifinta da kudi" dafa hanunta tayi tace"my NUR karki min mumunan fahimta amma ya ka mata TASLEEM ta San waye mahaifinta domin ni kadai zan iya fad'a miki zafin rashin Sanin mahaifa,bana son abinda ya same ni ya same TASLEEM "

Ajiyar zuciya NUR ta sauke sanan tace"zakiya ba wai naki maganar ki bane duk dama bana son rabuwa da TASLEEM amma ina bin maganar mahaifiyarta ne da tace"NUR ki rike hauwa da amana kuma kar ki yi gaggawar niman mahaifinta domin a halin yanzu ban yarda da kowa ba,wanda tasa a sato ni tana kusa da mahaifinta kuma zata iya yiwa ya'ta illa amma kar ki damu in lokaci yayi kaddara zata had'a su domin shi zai zo har Inda take ba sai kin nime shi ba,ki yi hakuri nasan zaki fuskanci kalubale ko a gun iyayen ki ne amma ki jure ki dauka wanan shine kaddararki,ki sakawa ya'ta suna hauwa uthman Adams"fashewa ta yi da kuka tace"zakiya a lokacin da take maganar tana yi ne tana shafa fuskarta har ta koma ga ubangijinta"

Itama zakiya kuka take NUR tace"a ranan da na fara ganin sir Afan kallo d'aya nayi mishi na shaida shi domin da muke makaranta na bude jakar summaiya ranan kin je lecture na gan hoton shi wanda tun ranan ban kara budewa ba hakan ma yasa na hana ki budewa,zakiya ina tsoro kar wani Abu ya sami TASLEEM domin bazan iya rayuwa babu ita ba,kuma ina gudun karya gano yar shi ce zai raba ni da ita"

Shiyasa ma yanzu nike son barin aiki a company amma duk inda naso bari company sai wani abu ya maida ni ga shi yau har gida ya biyo ni"

Zakiya tace"kila lokaci ne yayi,dole ne ma kiyi aiki a wanan company kuma a office din dan gane waye mugu cikin su,wanda ke da hanun akan sace summaiya ni ma ana wa bangaren zan sa miki ido akan sa sameer duk da dai kin ce mace ce amma a halin yanzu kowa suspect ne har da hajiya hafsat mahaifiyar Afan din kar ki damu ina tare dake"

Rungumeta NUR ta yi tace"nagode zakiya"

Bangaren sameer da Afan ko suna kaiwa gida kowa yayi part dinshi kowa da tunanin da yake sameer na tunanin hanyar da zaibi ya goge video shi kuma Afan hanyar da zaibi ya hukunta NUR gefe d'aya kuma ga tunanin TASLEEM a zuciyarshi

Bayan sati daya


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[10/06, 01:25] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS, WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to NANA KHADIJA KANO

πŸ…Ώ3⃣7⃣&3⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Bayan sati d'aya zakiya ne zaune a office tana aiki shiko sameer na ciki,shima yana nashi aikin

Bangaren NUR ko tana shirin zuwa meeting da sir Afan a flims investment plan din da tayi ta dauka ta ba messager ya kai mota office din sir Afan ta shiga domin shi baya rufe office dinshi shiyasa yake hango NUR in tana aiki

Karasawa tayi tace"sir na gama zamu iya tafiya

Ba tare da ya kalleta ba yace"OK jira ni a waje "

Tace"toh"sanda ya share fiye da minti talatin sanan ya fito

Zakiya ko gajiya tayi da aiki ta tsaya tana hutawa a haka sameer ya fito ya ganta

Wani haushi ne ya kama shi ganin inda ta aza kafafu a sama tebur kamar wanda ke falon gidan ubanshi ga a/c ta kunna

A ranshi yace"yariyar nan na niman raina ni sai na tashi tsaye
Zamu shirya dole in nuna mata bana tsoronta"

Hade rai yayi yace"ke zo nan"

Tace"ina?"

Yace"biyo ni"

Bin shi tayi a baya suka shiga office,zama yayi

Yace"yariyar nan na fara ganin alaman kin raina ni"

Hayewa tayi saman tebur ta zauna suna fuskartan juna

Tace"sannu mutan da,me nayi kuma ne?"karashe maganar da d'aga me gira"

Yace"sauka kafin raina ya b'aci"

Tace"me ran naka yake jira da har yanzu bai b'aci ba"

yatsa shi ya nuna mata yace"ke"

Lankwasa yasar tayi tace"kai ba a nuna ni da yatsa sauke shi"

Yace"in kina so ki zauna a office din nan ki yi gaggawar goge wanan video ko in...."

Katse shi tayi cewa"me zakayi in naki gogewa?wallahi ka bi a hankali ko in nunawa ummi inta dawo in fact zan tura mata ta watsaap"

Yace"kina turawa ke ma zan tona miki asiri"

Tace"na me?

Yace"nima gayawa ummi zanyi ku karuwai ne kuma zaman kanku kuke yi"

Murmushi tayi tace"ka kira ta yanzu dan Allah wallahi ka ci darajar abu d'aya da sai na nuna maka kuskurenka na kirana da my NUR karuwai ko yanzu ba kyalle ka nayi ba sai na hukunta ka mashayi kawai"tana kaiwa nan ta bar office din

har zata fita ta dawo kuma tace"ni zan iya d'auka komai amma in aka tabo mai NUR ban San meyasa ba sai inji jinina ya fara gudu a 360 kuma in haka ta faru zan iya cin mutuncin koma waye.so beware"tana gamawa ta bar office din

Toilet ta shiga ta kunna famfo ta wasawa kanta ruwa sanan ta saki kuka mai karfi

Domin ta ji zafin Kiran su da yayi da karuwai amma bata son ya gane shiyasa bata yi kuka a gaban shi ba dan kar ya gane weakness dinta

Tafi minti ashirin tana kuka sanan ta wanke fuska ta fito ta cigaba da aiki kamar babu abinda ya faru

bangaren NUR ko cikin kwarewa tayi bayanin plan din ginin da tayi planing a meeting inda kowa ya gamsu har da tafa mata daga karshe akayi signing contract din wa Afsaman building company

Afan yace"ke bani files di nan inyi sighing in turawa audit department na flims suyi treating in sun gama su turawa sameer yaduba"

tace"toh"

Jakarta ta fara dubawa bata gani ba tace"sir yi hakuri na manta da shi a mota"

ai a fusace yace"ke meyasa baki San komai ba sai bin maza eh"kowa a wajen sanda ya juya ya kalleta

Afan yace"yes gaskiya ne maza ta ke bi domin zaman kanta take karama da ita tasan dadin namiji"

hawaye tab a idon nur,wani dattijo ya kalleta yace"ya'ta zo nan"

da k'yar ta ja kafafunta da yayi mata nauyi ta karasa gaban shi

yace"ki daina bin maza kin ji ba abu ne me kyau ba,me kike nima gaki da kyau ga ilimi"

bata iya magana ba sai ma fashewa da kuka da tayi

shiko manager din flims sai signal yake mata

Afan a ranshi yace "sai kin yi da na sanin mari na da kika yi a gaban staff dina bazan kawai"

a haka meeting ya tashi jiki sayaye NUR ta bar building din taje ta shiga mota tana shiga Afan yace"get out"

fita tayi ta karasa bakin titi ta tari napep ta shiga bata koma office ba makaranta su TASLEEM taje ta d'auketa suka tafi gida

sameer ko bayan sun gama magana da zakiya tunani ya fara inda zai kwace wayarta sai dai damuwarshi tace ba wayar ta kadai yake ba

amma ya dau alwashin goge shi ko ta halin kaka koda kuwa na wayar ta ce kadai

4:pm zakiya ta koma gida ganin NUR tayi fuska a kumbure alamun ta sha kuka,ganin haka yasa ta boye nata damuwa tace"my NUR meya faru ne na gan fuskarki haka"

NUR ta fashe da kuka cikin kuka ta bata labarin abinda ya faru

abin ya matukar taba zakiya amma sai ta daure tace"daga yau karki kara yi me kuka,kuma ki cigaba da aikin ki saboda TASLEEM zamu jure cin fuskar shi da mun gano Wanda ya bawa su bullet aiki zamu mika me yar'shi mu kara gaba domin nima ina son in fara niman iyaye na da taimako wanan abin wuyar

Ciro shi tayi ta nunawa NUR

NUR tace"kullum in na gan wanan abin wuyar sai yayi kamar na taba ganin shi a wani wuri"

zakiya tace"kullum haka kike cewa amma har yau baki tuna ba,ki shirya TASLEEM mu ajiyeta a islmiyya DJ ya kaimu bye-pass koyon mota"

tace"toh"

a islamillaya suka ajiye TASLEEM sanan DJ ya kaisu bye-pass inda NUR zata koya mota domin zakiya ta iya kuma tayi haka ne dan kar su zauna cikin damuwa"

Cameroon

ummi ne zaune gaban alhaji tsoho watoh mahaifinsu

yace"hafsat wai har yazun baki koma Nigeria ba"

tace"inashaallah zan koma sati nan dama kasuwanci ne ya rike ni a nan"

yace"



maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
[10/06, 02:26] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we the best among the rest.

Dedicated to AYSHMAN 4real (indo)

πŸ…Ώ3⃣9⃣&4⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"amma ya maganar yaran da kika ce suna kama da hauwa"

Ummi tace"suna aiki a company mu a Nigeria abinda ke d'aure min kai shine sun ce su ba yan uwa bane domin d'ayan sunanta NURUL HUDAH ABUBAKAR MUSA

D'ayan kuma AISHA IDRIS amma ana ce mata zakiya abba wallahi kamar su d'aya babu ko babanci

Amma da na tambaye su ko su yan biyu ne sai suka ce ah'ah kawance ne kawai NUR tafi kama da hauwa harda murya kuma nafi kyautata zaton itace yar hauwa domin daga sunan mahaifinta za a gane,sai dai ita kuma zakiya kamarta d'aya da yaya Mohammed (Abban sameer)daman kasan hauwa tafi kama da shi"

Yace"amma baki tambayi sunan mahaifiyarta ba"

Ummi tace"na tambayesu ita zakiyar tace balkisu ita kuma NUR tace hauwa ka gan alamu sun nuna NUR ce yariyar hauwa,har kano naje gidan alhaji abubakar amma aka tabbatar min yana asibitin Saudi ba lafiya wata na tarar da alamun matar shi ne sunanta maimuna abun mamaki ina tambayarta hauwa ta hau ni da fad'a ta Kore ni,washe gari na dawo na tambayi mai gadi nan yake sanar min hauwa ta dade da rasuwa wajen haihuwar yar'ta NUR nace me ina NUR din take nan yake sanar min NUR ta bar gidan sanadiyar dawowa gida da tayi da jaririya mahaifinta ya koreta wanda tun lokacin ya kwanta ciwo,nace toh ya nuna min gidan mahaifan alhaji"

Yace"ko naje babu Wanda zai kula ni domin duk an asirce su mahaifiyar shi ce zata saurare ni kuma tana Saudi tana jinyar d'an ta"

Dana tambaye shi inda zan samu NUR shine yace"bai sani ba amma yana zaton zan same ta a minna ne domin nan take makaranta a da"

Shiyasa dana buge ta a titi na bita har gida na gan yar Wanda yanzu zata kai shekara bakwai itama yar kamar su d'aya da Afan shiyasa na yarda yar NUR ne kuma ina kyautata zaton bata hanyar aure aka same ta ba jinin ne kawai yasa yar tayi kama da Afan
Dana tambaye su mahaifinta sai suka fara kame-kame a lokacin bana son in matsa musu saboda ina tsoron kar su gudu

amma tabbas zakiya yar hauwa ce sai dai wani ikon Allah jira nike abubukar ya dawo in tambaye shi ko yan biyu ne domin shi kadai ke da hanyar ansa wanan tambaya

alhaji tsoho yace"yanzu da gaske hauwa ta rasu kenan?"yana magana ne yana hawaye

ummi tace"Abba ya kamata a bar kukan nan haka addu'a take bukata tun ina Nigeria ake kukan nan babu ma kamar sameer domin shi kadai yayi mata farin sani da yake yana da shekara sha biyar tayi aure"ta karashe maganar cikin kuka

alhaji tsoho yace"Allah jikan ki hauwa yasa kin huta kuma aljana shine makoman ki na yafe miki duniya da lahira nima na gane kuskurena,na rashin yi miki gata a baya Allah yasa kin hadu da mahaifiyar ki"

ummi tace"amin abba sai dai har yanzu ban sanar dasu afan ba ina jira a tabbatar tukuna"

alhaji yace"hakan yayi domin na San ba hankali ne dasu ba"

ummi tace "ai na gargade su kan na taho kar su sake su wulakanta su"

bayan wata d'aya sameer ne zaune yana tunanin haryar da zai bi dan goge video wayar zakiya domin ta fara kaishi bango

yace"amma ai tace akwai a wayar wasu,dole ne ma in goge shi ko ta halin kaka"

ai be gama tunani ba ta shigo tsalle tayi ta haye tebur tana fuskantar shi tace"ya dai"hade da d'aga me gira

yace"ke miye haka wanan wani irin iskanci ne da rainin wayau eh zaki wani haye min tebur"

tace"ni ba surutu ya kawo ni ba zuwa nayi in fad'a ma duk randa sir Afan ya kara hantarar my NUR wallahi zan saki video nan"

a ranshi yace"dole in yi wani abu ayau domin yariyar nan ta gama raina ni"a fili kuma yace"me yayi kuma?"

tace"jiya zuba mata drinks a jiki yayi a public harda wani kiranta yar iska"

sameer yace"toh kije zan yi wani Abu akai"

tace"da yafi maka"

tana fita ta kira messager tace"ya je restaurant ya siyo mata abinci da cock me sanyi"

yace"toh"har zai tafi sameer ya kira shi yace"ya shigo"

yana shiga ciki sameer ya kulle kofa ya ciro wani magani a drawer yace"in ka siyi cock ka bude ka saka mata guda ukun nan"

messenger yace"an gama oga"kudi ya Ciro mai yawa ya bashi

sanan yace".......


are you ready guys?let have fun

maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
[10/06, 13:40] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Ddecated to mom noorul hudah fans group

πŸ…Ώ4⃣1⃣&4⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Sanan yace"ina fatan cock din gora ta aike ka?"

Yace"eh shine"

Yace"good da dabara zaka bude inda baza ta gane an bude ba"

Yace"inshaallahu sir zanyi shi cikin natsuwa"

NUR ko tana cikin aiki wayarta tayi kara tana d'agawa

Tace"hello anty"

Anty su TASLEEM ne tace"ki yi sauri ki zo ki d'auki hauwa ta samu attack amma da sauki mun bata inhailer sai dai mun tashi domin 3:39 ne yanzu kuma mun ji shiru Baki zo ba"

Jiki na rawa NUR tace"gani nan zuwa yanzu nan"

Ko kallon Afan bata yi ba ta d'auki jaka ta tafiyar ta tafiya take tana hada wa da gudu a hanyarta na barin department dinsu har zata shiga elevator tayi karo da wata mata kyakyawa da gani zata ja shekaru har wayarta ya fadi,daukowa NUR tayi ta mika mata

Tace "dan Allah ki yi hakuri baiwar Allah wallahi ban kula bane"

Matan tace"babu komai"cikin fara'a tayi magana suna had'a ido NUR ta ji wani mumunan fad'iwar gaba

Matar ko kwarjini NUR ta mata

NUR bata yi magana ba ta shige elevator tana tunanin kamar ta taba jin muryar matan a wani wuri

Matar na shiga ta tsaya a receptionist tace"tana nima C E O na company "

Receptionist tace"ba ya nan ya je meeting "

Matar tace"OK in ya dawo ki ce mai FATIMA cousin din shi ta zo daga kano"

Tace"OK ma"bayan Fatima ta tafi

Manager yace"meyasa kika ce mata baya nan bayan yana ciki"

Tace"shi yace duk Wanda ya zo in ce ya fita yana son ya huta"

Yace"alright "

Zakiya ko messenger ya kawo mata abinci amma bata ci ba domin wani aiki aka kawo mata daga admin tayi treating

Ga aikin na da yawa har 4:30 yayi bata wuce ba kowa ya tafi ita kadai ta rage da sameer

Tsaki tayi tace"tun d'azun ina nan bana komai ba bani aiki ba sai yanzu a ce gobe da safe ake so"

Sai misallin 5:39 ta gama wani yunwa ne ya kamata,abincin ta bude ta ji shi da sanyi ai sai ta bude cock ta kurbe duka ko digo bata rage

Tace"bari in d'an huta kafin in tafi gida

Bayan Minti biyar sai kanta ya fara juyawa

Can anjima ta mike ta fara rawa dai-dai nan sai ga sameer ya fito ganinta a wanan halin ya sashi yin murmushi yace"yau za a yi ta ta kare karasawa yayi ya jata zuwa office din shi ya kunna waka a waya tana rawa

Can anjima ta kwanta a kasa ta fashe da kuka cikin maye tace"ni bani da kowa a duniya sai my NUR sun toni akayi ban San iyaye na ba,tashi tayi ta kama me riga tace"kasan Inda mu ke ji ni da my NUR na rashin yan'uwa?"

jin surutan da take yi yasa ya ajiye karamin cameran dake hanunshi a table yace"ai in mutum baya hayyacin shi yafi fadin gaskiya bari in ji maza nawa ta bi ko wanan ma ya isheni

ta kara cewa my NUR na da uba amma bata dace da uba na gari ba shiyasa

kecewa tayi da dariya tace"kasan waye abbana?alhaji idris mai gwal shine abbana mai kudi ne in fada ma a lokacin da nike tare dasu rayuwar sarauta nike yi,domin abinda nike so shi ake yi kawai rana d'aya ummina tace"ni ba yar'ta bane,shafa kumatun shi tayi tace sai ta Kore ni wai itama ta samu nata cikin
hakan yasa muke rayuwa nida my NUR amma sai mutane suke mana kallon karuwai"

kuka mai hade da dariya tayi sanan tace"ni narasa ta inda zan fara niman iyaye na ina son in ji dalilin su na yardani da suka yi a bola tun ina jinjira"

jikin sameer ne yayi sanyi yace"toh ai ke da NUR yan biyu ne"

dariya tayi har da rike ciki tace"ina ganin ka mai hankali Ashe kai sha-shasha ne ni da NUR ba yan biyu bane kama mu kayi ita tasan asalinta"

yace"how comes?wanan ba gaskiya bane akwai magana a kasa"

zakiya tace"ko blackmailing dinka da nike yi ina yi ne dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login