Showing 36001 words to 39000 words out of 45929 words

Chapter 13 - RAYUWAR NUR BY MAMAN NOORUL HUDAH

31 Oct 2025

4134

nasa aka yi miki a station da kuma bayyana gaskiya ashe ba kasheta akayi ba a hanun kidnappers ta mutu"

NUR tace"ba a hanun kidnappers ta mutu ba sawa akayi a kasheta kuma Wanda tayi hakan tana kusa da kai"

Idon shi ne ya fara canja kala yace"waye"

Hanunshi NUR ta kama tace"ba lallai bane ka yarda dani"

Yace"NUR a halin yanzu ko me kika fad'a min zan yarda koda kuwa uwatac...."rufe me baki NUR tayi

Tace"ba ita bace please karka zargi ummi da mugun dabi'a mahaifiyar ka ce kuma uwa ta gari,kuma ba kowa bane illah FATIMA"

Yace"wata FATIMAN?"

Tace"Fatima cousin dinka yariyar kanin mahaifinka kuma best friend dinka da Anty summaiya"

yace"what?"

tace"of cause"labarin komai ta bashi ta kare da cewa"wanan dalilin yasa anty summaiya ta bani kyautar TASLEEM domin tace"bata yarda da kowa ba tunda har yar uwarka zata iya kasheta"

da farko da na fara ganin Fatima ba tabbatar itace ba don gudun kar in zargi Wanda bata ji ba bata gani ba"

amma randa a ka sace TASLEEM sai na kamata ta na waya dasu bullet akan meyasa suka boye mata cewa yar summaiya na raye bata San ina bayanta ba,sai ma nuna mata da nayi banji abinda ta fada a wayar ba

dan in tabbatar na koma gida na d'auki hoton ta naje gidan yar uwar babawo a cikin gari babu b'ata lokaci ta kirashi a waya ya zo hotan Fatima da summaiya na nuna me nace ko ya waye ta

kallo d'aya yayi mata
yace"wanan ai ita ta bada kwangila kashe kawarta"godiya na mishi sanan na bar gidan shiyasa zakiya ke ta nima na bata ganni ba

dan gudun kar asirinta ya tonu yasa tayi ta zuga ka akan ina da hanun a sace summaiya dan kar a zargeta
please ina rokan alfarma da ka yafewa babawo domin ba karamin Taimakon mu yayi da summaiya ba"

kuma ka hukunta ta domin ta zalinci summaiya,ta so kashe TASLEEM a asibiti amma zakiya bata bar gun TASLEEM ba domin kafin a kaini station na fad'awa zakiya karta kuskura ta bar TASLEEM da ita,data gan ba hanya shine ta baka shawara canja mata asibiti amma da barci ya d'auketa zakiya ta gudu da tasleem,amma in baka yarda dani ba ga number babawo ka kira ka tambaye shi,Fatima ta Dade tana sonka kuma zata iyayin komai dan ta mallake ka"

yace"na yarda da ke ummul TASLEEM kuma na gode da taimako ki da kare TASLEEM da kika yi daga sharrin makiya"na miki alkawarin za a kama Fatima kafin bikin mu

rungumeta yayi gam yana hawaye,itama kuka take yana shafa bayanta

sanda ya tabbatar tayi shiru ya zaunar da ita

yace"let forget our sorrows for a while muyi maganar gaskiya kina so na?"

shiru tayi yace"ki yi magana mana NUR"girgiza me kai tayi alamun ah'ah

yace"meyasa".

tace"kai mugu ne"

Yace"karki damu zan koya miki inda zaki soni NUR domin bazan iya rayuwa babu ke ba"

sun yi hira sosai da soyayyaya sanan suka koma gida
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

G.W.F.
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Dedicated to my handsome brothers
πŸ…Ώ8⃣5⃣&8⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

a gidan ma a garden suka zauna yayi da hanun NUR ke cikin na Afan sai hira suke babu laifi ta sake dashi

zakiya na ganin su tace"ga yaya Afan sai zuwa zance yake amma ni ban ma San inda sir meer yake ba,hmmm ai wallahir be isa ba sai munje Nigeria zan sa yayi ta zuwa zance tun da ya kiyi a nan,ina amfanin soyyaya da tsoho?"

washe gari ya kama birthday din su NUR kuma ana gobe zasu koma gida

NUR da zakiya suka je har d'akin alhaji tsoho suna niman alfarma akan ya bari ayi komai a Nigeria domin sun fi son ayi komai gidan uban su

alhaji ya yarda kuma ya jijina hankalin su albarka yasa musu suka tashi

NUR na komawa dakinta ta gan gift a saman gado,an rubuta to my lightness of my day a bayan ansa Afan

budewa ta fara yi sai ta gan babban penti ne na zanen ta abin ya matukar tafiya da ita kallo take tana murmushi

na biyu ta bude ta gan nata ne da zakiya shima yayi kyau sosai

na karshen kuma itace da TASLEEM,rungume penti tayi tana dariya

wani paper ne ya fado,tana budewa ta gan an rubuta my lady may i have the pleasure of taking you out for dinner tonight

ai NUR bata San sanda murmushi ya sub'uce mata ba tace"yes"rungume takardan tayi tana jin wani yanayi na ratsa ta Wanda bata San dalilin ba

a haka zakiya ta shigo ta sameta tace"my NUR ki shirya ga ihsan ta zo da cake"

tace"alright"

wanka suka yi suka saka kaya iri d'aya da kwaliya ga kamshi na tashi

tun kan su sauka daga stairs kamshin su ya sanar da mutane da ke kasa sun iso

a hankali suke saukowa inda idon kowa ke kansu Afan ko ji yake kamar ya je ya rungume NUR dan ta bala'in tafiyar da hankali shi

shiko sameer kallon zakiya yake kamar bai taba ganin ta ba

ba tare da b'ata lokaci ba suka yanka cake kowa ya basu kyauta ciki harda TASLEEM

a falon alhaji aka ci abinci NUR da zakiya ko dadi kamar ya kashe su ba ma kamar NUR da wanan shine farko birthday da zatayi da yan uwanta Abba zakiya ya kira zakiya akan ta zabi kome take so ita da NUR"

tace"mota"

shima abbansu da ya kira abinda yace"kenan"

da misalin karfe 8:pm bayan NUR ta gama sallah domin zakiya na fashin sallah zakiya ta shigo dakin cikin wata rubber gown ya bala'in yi mata kyau

NUR tace"ina zuwa haka aka sha kwalliya"

tace"zamu fita ne da sir meer"

NUR tace"ai baki isa ba sai kin min kwaliya tukuna"

zakiya tace"my NUR ni ban gane miki ba kin ce baki son yaya amma in zaki gunshi sai ki ta kwaliya alhalin da ko powder baki shafawa,tell me are you in love?because I can see love in the air"

NUR tace"nifa ba son shi nike ba,toh miye ne dan nayi kwaliya kema ba kina yi ba?"

zakiya tace"hmmmm I see,toh sa kaya mana in miki yana jirana waje"

itama roba gown tasa baki ya bala'in mata kyau kamar in sace ta in gudu

zama tayi gaban madubi zakiya ta fara mata kwaliya pin zakiya ta Ciro ta kama mata suma ta zubo wasu gaba ta kama da pin dan kar ya dame ta na bayan kuma ta kama a sakiya ba Karamin kyau NUR tayi ba,ta d'auko galle ja zata sa zakiya tace"me zaki yi?"

NUR tace"d'aurawa zanyi"

zakiya tace"what?ke wace irin yar kauye ne?ai ba sai kin d'aura ba"

tace"wallahi kunya nike ji ga kanya nan ya kamani ya zanyi tafiya a gaban shi haka?"

zakiya tace"hmmm ai in kina kunya sai ya dauke ki yar kauye"

NUR tace"ko?amma ke dan ki sabane"

zakiya tace"na tafi in kin gan dama ki saka hijabi ke kika sani

gaban madubi NUR ta tsaya tana juyawa amma haka kawai ta ji tana son ya ganta haka domin ita kanta tasan tayi kyau

zakiya na fitowa ta tarar da sameer yana jiranta a balcony yana ganin ta ya bude baki yana kallonta har ta karaso be sani ba iska ta hure me a fuska ya lumshe ido ya kuma bude su

yace"you are beautiful dear "

tace"I know"

haushi ne ya kamashi be ce komai ba har suka karashe dai-dai motan shi

Shiga yayi yana jira ta shigo amma taki yace"shigo mana ko kin fasa ne?"

tace"in baka so in fasa ka fito ka bude min kofa"

babu musu ya fito ya bude mata kofa ta shiga sai fad'a take
tace"matsala aure mutan da kenan basu iya soyyaya ba domin lokacin su ya wuce ni dai an had'a ni da aiki da aka had'a ni da tsoho"

parking yayi ya jawota jikin shi yace"ni kike kira tsoho?toh nan da sati uku kacal zan nuna miki ni ba tsoho bane kuma zan miki abinda wani mai karanci shekaru ba zai miki ba"

(zakiya kin shiga uku)

NUR ko har d'aki Afan ya zo ganin shiru bata fito ba tana ganin shi ta d'auki hijab zata saka

yace"no angel na fison ki a haka kallonta yayi daga sama zuwa kasa sanan yace "muje ko?

tace"eh"

yauma restaurant suka je inda yayi ta janta da hira tun ta na jin kunya har ta sake

zakiya ko Suna kaiwa restaurant da sameer yayi reserve kafin su fita yace"dun Allah kaki hau Samar tebur"

tace"akan me nifa nafiso saman domin Abba na ko aiki yake ina saman tebur"

a ranshi yace"Abba ka hada da aiki"

ai ko saman ta hawo amma da shike su biyu ne kawai sai bai dameshi ba

washe gari
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


Dedicated to new Hausa writers group

πŸ…Ώ8⃣7⃣&8⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Washe gari da safe su NUR suka shirya da manya akwatina

Suka fito falo inda kowa ke jiran su

Bayan sun sallame su ummi tace"ki bar TASLEEM a nan tunda ba a yi Hutu ba in zamu taho sai mu taho tare

Tace"toh"

Ihsan tace"yanzu ina kukayi kano ko bauchi?*

Zakiya tace"bauchi "

Motan sameer zakiya ta shiga ita kuma NUR na motan Afan a mota Afan ya amshi wayar NUR ya bata wani sabo tace"akwai numbobi na a ciki please ka bani in kwashe"

yace"no dear bana son kina waya da kowa domin jiya naji manager ya kira ki wai yana son Ku gaisa"

tace"amma ai babu komai tsakani na da shi kuma akwai numbobin mutane da nike so in gaiyata biki"ta karashe magana kamar zata yi kuka

yace"NUR bana son musu a rayuwata karki b'ata min rai"shiru tayi

zakiya ko sa sameer tayi gaba kamar d'anta tace"wallahi in baka zo zancen nan ba sai ka ga ba dai-dai ba"

yace"wai miye a wanan zancen ne da kika hana ni sakat mu da zamu yi aure sai mun b'ata wa kan mu lokaci muna wani zance kamar yara"

tace"toh ai ni yariya ce kaine tsoho dan haka ina sha'awa zance ka min ayi aure,bama kamar inda saurayi zai ce ina sonki sai ka gan budurwa ta kama ba kin gallenta ta rufe fuska cikin jin kunya tace da gaske masoyina ?"

dariya ne ya sub'uce me yace"hmm an hada ni da aiki"

NUR ko hawaye take yi na takaici kwace mata da Afan yayi shiko share ta yayi ba wai dan baya jin zafin kukanta ba amma baya jin zai iya bata wayar

a wanan yanayi suka isa airport akwatinta ya ciro a booth

zama suka yi suna jira a kira su

ganin taki yin shiru yasa shi cewa"ke miye haka?"

tace"babu komai"

yace"then look at me"kin kallonshi tayi shiko hakan ba karamin b'ata me rai yayi ba

a fusace yace"NUR i said look at me"yanda yayi maganar cikin d'aga murya yasa ta fashewa da kuka sai kuma ya ji ba dadi

tashi tayi da gudu ta fara shiga jirgi dama an kira su

duk abinda ya faru a idon zakiya da sameer,karasawa zakiya tayi gaban Afan tace"gaskiya yaya bana jin dadi inda kake sa my NUR kuka in haka ya cigaba zan sa ta fasa auren kuma wallahi zan d'au mataki domin zan manta kai d'an uwa mu ne"tana gama magana ta wuce abinta domin laifin Afan ta shafi sameer

sameer ya kalleshi yace"ya kamata ka rage zafin rai domin zaka iya samu matsala da NUR ita da ya kamata ka ta lallashi shine kake mata ihu

yace"inshaallah zan daina nima ba da son raina bane"

NIGERIA

su zakiya sun isa bauchi lafiya ba karamin murna hajiya balkisu tayi ba,nan dai ta hau hidima dasu kamar ta goya su

(waiwaye)ina labarin maimuna?

bayan mainuna da mahaifiyarta sun bar gidan alhaji da niyar shiga duniya

a titi suka tsaya suna tare duk wani mota da suka hango

wani arniyar mota ce ta faka,da gudu suka karasa maimuna tace"alhaji lift muke so zuwa abuja"

alhajin yace"Ku shigo"

shiga suka yi yaja mota,a mota suke ta hiran duniyarcin su duk alhajin na ji

a ranshi yace"irin Ku nike so sinannu"

a fili kuma yace"ke ya sunan ki da sauri maimuna tace"maimuna "

yace"me zai hana in kaiku gida na ni dai ba mata ne dani ba Dan na lura kuma yan duniya ne Irina"

wani shu'umin murmushi hajiya maryam tayi tace"babu komai alhaji"

yace"amma da sharadin kome nace kuyi zakuyi"

suka ce sun amince

Abuja

wani makeken gida alhaji ya paka a waje ya shiga ciki ya bude kasancewar gidan ba mai gadi

ya dawo ya shiga duk girman gidan alhaji babu kowa balle mai gadi ciki ya kaisu bayan sun yi wanka sun ci abinci sun huta su ko dadi suke sun samu gidan hutu

da dare yayi alhajin ya shiga dakin da suke kwance da katon akwati tashi suka yi suka zauna

umurta su yayi da su tube kayan jikin su ba tare da tunanin komai ba suka tube babu tsoron Allah

shima tubewa yayi ya jawo hajiya maryam ya fara wasa da ita tana biye me

gajeren wanda jikin shi ya tube ai suna ganin halinta shi nan take maimunatu ta sume domin girma da tsayin shi ko a tarihi bata taba ji ba

hajiya maryam ko kuka ta fashe dashi tana bashi hakuri amma ko a jikin shi

yana shiganta ta saki wani kara har da amai amma ko a jikin shi San da ya d'au awa biyar tuni ta sume sanan ya sauka yace"kana nan yan iska"

akwatin ya bude sai ga katon maciji ya bayyana yace"je ka ci abinci"ai sai maciji ya fara tafiya har ya shige hajiya maryam"

bayan minti talatin macijin ya fito ya koma akwati alhajin ya kulle

ruwa ya kwarara musu,a razane suka farka yace ke biyo ni domin ita wancan ta gama aiki

rokon shi maimuna tayi amma ya ki saurarenta da asuba abinda yayiwa hajiya shi yayiwa maimuna sanda suka d'auki wata d'aya alhajin na kawo karnika suna kwana dasu kafin s ya kore su ba tare da ya basu ko sisi ba,wari suke domin har susa ke fita jikinsu

yana koransu suka fara yawu a cikin garin abuja suna baran abinci amma babu Wanda ya taimaka musu in banda gudun su da akeyi

jikin su ne ya fara b'arewa domin sun ribe har rai yayi halinshi inda kafin maimuna ta mutu ta dinga kuka tana tuna abubuwan da ta aikata da kuma tunanin ya zata had'a ido da ubangijinta

a bakin hanya gawan su yake sun ishe mutane da wari yasa aka kwashe su zuwa daji aka binne su ba tare da an sallace gawan su ba

ya Allah kasa muyi kyaukyawan karshe domin duk Wanda ya mutu ba ayi me sallah ba yayi babban asara

(ga mata masu aikata muyagun aiyuka kamar hajiya da maimuna ya kamata Ku tuba Ku koma ga Allah domin Allah ba zai barku ba sai ya sakawa Wanda kuka zalinta kuma kuna cikin hasara a ranan gobe kiyama kamar inda Allah yayi mana bayyani a suratul-Al-Asr

kamar haka: bismillahir Rahmanir Rahim

wal asar :ina rantsuwa da zamani
inal insana lafi khusir:lalle mutum yana cikin hasara,
Il lal lazina aamaanuu wa amilus saalihaati wa tawasau bil haq qi wa tawasau bis sabir:face wadanda suka yi wa juna wassiya da bin gaskiya,kuma suka yiwa juna wasiyya da yin hakuri(su kan basu cikin hasara)

(shiyasa yana da kyau mutum ya kasance mai hakuri da zamani mu gujin son zuciya dan karmu kasance cikin hasararu ran lahira ranan da babu mai taimakon mu domin bokaye ma na ta Kansu)Allah yasa mu dace

cigaban labari

su NUR ko
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to mom fareesa my best friend nagode da kaunar ki a gareni kuma Allah ya kara basira ya raya miki zuri'a gaskiya ina yin ki sosai to me u are the best writer.thanks alot
πŸ…Ώ8⃣9⃣&9⃣0⃣

Bismillallhi Rahmanir Rahim.

su NUR ko gata suke gani wajen hajiya balki Inda ba tare da b'ata lokaci ba aka fara gyra su kuma Abba ya amince ayi komai a bauchi a cewa shi ai duk gida ne kuma bazai iya biyan alhaji idris ba da irin tarbiyar da yayi wa zakiya

kuma iya gata hajiya na kokari

a yau kwanan su biyar da zuwa bauchi amma ko magana NUR ba ta yi da Afan ba ya kira ya gaji da karshe ma kashe wayar tayi

hakan da tayi ba karamin b'atawa Afan rai yayi ba kamar zaiyi hauka

a yau ya d'au alwashin yin magana da NUR ko ta wani hali koda kuwa zaije Nigeria ne"

kiran zakiya yayi yace"ta kaiwa NUR waya"

tace"toh tana ciki bari in kai mata wayan"

a kan gado ta sameta zaune tace"gashi yaya ne"ta mika mata wayar ansa tayi

Afan yace"NUR kina jina "

tace"urmmmm"

yace"wani dalili ne yasa kika ki d'agawa waya na har na tsawon kwana biyar?"

shiru tayi a fusace yace"NUR iam talking to you"ai sai ta fashe da kuka zakiya dake tsaye gaban wadrobe ta girgaza kai

har zata kashe wayar Afan yace"wallahi in kika kuskura kika kashemin waya zaki sha mamaki na"

cikin kuka tace"ni ba kashewa zanyi ba"

yace"toh d'auko laptop muyi video call"

tace"toh"tare da yanke wayar

zakiya ta kalleta tace"ya kamata ki daina yiwa karamin Abu kuka"

ai fusace NUR tace"ina ruwan ki dani ne bana son sa ido"mamaki da tsoro ne ya kama zakiya domin tunda suke NUR bata taba yi mata magana haka ba amma sai ta yi shiru

d'auko laptop tayi suka fara magana yace"NUR yaushe raini ya shiga tsakani na da ke ne?kin raina ni a ce zan kira ki kashe waya"masifa yake mata ai ga mamakin shi ya ji

tace"wai me ka d'auke ni ne eh?kullum sai ka ta min fad'a gaskiya in ba ka rage zafin rai ka ba zan fasa auren zan kira alhaji in fad'a me na fasa ai ba kai kadai bane namiji kuma ko yau aka ce in fito da Wanda nike so zan fitar"

yace"NUR ni kike fad'awa kina da samari?"

tace"eh din kaima ai rana nan a gabana Fatima ta kira ka, ka d'auka harda wani kashe mata murya kana ce mata dear kamar baka san ita ta kashe summaiya ba sai ka ta takura ni"

a ranshi yace"na shiga uku"a fili kuma yace"haba my lightness meyasa kike magana haka nayi magana da Fatima ne dan karta san nasan sirrinta kuma jira nike tayi kuskure Wanda nasan zata yi kuma maganar kashe murya karki min sharrin haka maganata yake"

tace"ai ni na dade da sanin ba sona

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login