Showing 3001 words to 6000 words out of 45929 words

Chapter 2 - RAYUWAR NUR BY MAMAN NOORUL HUDAH

31 Oct 2025

4135

shi ke rikon NUR

abun mamakin rasuwar hauwa da wata shida alhaji ya nace sai an aura me maimuna abin ba karamin mamakin ya baiwa umma shi ba,amma ba abin mamakin bane domin tasan halin abokiyar zamanta watoh anty amarya,tasan aikin asiri ne

haka aka yi domin an aura me maimuna amma sai Inda tayi
dashi ita dai mahaifiyar shi sai addu'a take me

bayan shekara goma sha biyar
[05/06, 15:23] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

πŸ…Ώ7⃣&8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Bayan shekara goma sha biyar abubuwa da dama sun faru yanzu har NUR ta girma sai dai har yanzu mahaifinta bai bata kulawa domin ko wajen mahaifiyarshi baya zuwa ko ya zo shiyar anty amarya yake zuwa domin an asirce shi

NUR Nada shekara goma sha shida ta gama sekandari dinta har ta rubu ta jamb sai dai bata ci ba

Ganin tana samun kulawa yasa waje hajiyar shi yasa maimuna tada siya akan a dawo da NUR gunta da hajiya ta nuna bata yarda ba mijin su watoh mahaifin alhaji abubakar malam musa har duka yaso yayi wa hajiya a cewar shi ya'da gidan ubanshi za a hana ta zuwa dan tana so ta raba kan gidan shi ai da maimuna da abubakar duk d'aya ne"

Babu inda ta iya haka ta hakura

Har gida abban NUR ya zo ya dauke ta,bayan komawarta gida da kwana uku NUR ta fara fuskanta rayuwa domin ita da baiwa babu babanci

Domin kowani aiki na gidan ita keyi kama daga wanki dibo ruwa komai ita keyi a haka ma sa an gan damar bata abinci

Mahaifinta bai damu da ya San halin da take ciki ba domin in ya fita tun safe sai dare gashi wani tsoron maimuna yake ji

Bayan shekara daya da dawowa NUR gidan kowa ya ganta sai tausaya mata domin ta lalace kulle kanta take tasha kuka a daki domin har hajiya maimuna ta hanata zuwa gidan abinda ke damun ta shine bata da kowa da zata fadawa damuwarta gashi ta sake rubuta jamb na biyu amma bata ci ba

Hakan yasa ta sami mahaifinta da maganar zuwa makaranta domin tayi sa'a maimuna bata gida ranar

Ganin bata nan yasa Abba saurare ta har shafa kanta yace" amma ai baki jamb ba"

Tace"eh Abba amma remedial zanyi a federal university technology minna (FUTMIN)"

Yace"toh zanyi wa abokina magana a nan yake koyarwa "

Tace"nagode abba na"

Yace"ba komai amma karki sanar da mummy ki"

Tace"toh Abba"

Cikin kankani lokaci aka kammala komai na tafiyar makaranta ta sai ranar tafiyar Abba ya sanar da maimuna hakan ko ba karamin haushi ya bata ba har gurin boka ta koma


Tace asirin da tayi me ya fara karyewa tunda har zai iya munafurta ta ya kai NUR makaranta ba tare da izinin ta ba"boka ko ya tabbatar masu ita da mahaifiyata hajiya maryam zai raba NUR da mahaifinta harta hajiya ma,

Har makaranta Abba ya kawota yayi mata abin ya dace a gaban shi ta shiga hostel shi kuma ya koma kano

Bayan sati biyu NUR ne kwance a hostel sai ga wata budurwa tayi sallama

Tashi NUR tayi ta amsa salamarta

Zakiya ta kalleta tace"sunana Aisha idris daga bauci amma ana kirana zakiya "

NUR tace"NURUL HUDAH Abubakar musa daga kano ana cemin NUR"

Zakiya tace"ai dole sunan da tsayi,daga admin aka turo ni nan"

NUR tace"bismillah"

Zakiya tace"amma ya naga muna d'an so muyi kama ne?"

NUR tayi murmushi tace "haka ne bama d'an ba munyi kama sai dai kamar na fiki haske ke kuma kin fini kiba"

Zakiya tace"da fatan zamu zama kawaye?"

NUR tace"me zai hana in ganin ki naji ina son ki har zuciyata"

Zakiya tace"nima haka"

Cikin sati biyu suna shaku da juna domin kowa a makaranta kallon yan biyu ake musu

Haka suka cigaba da karatu inda suka wata uku a makaranta sai dai zakiya ta lura ba a taba kiran NUR a gidan ba itako kullum sai an kirata sau uku a rana fiye ma da haka domin zakiya irin yaran da aka shagwaba ne in tana waya da Abba ta sai ka dau da saurayi take domin shagwaba take zuba me har ummanta

Suna zaune suna hira zakiya tace "my NUR tunda nike dake ban taba jin an kira ki ba"

Fashe da kuka NUR tayi cikin kuka nur ta bata labarin rayuwar ta hawaye ne ya wanke wa zakiya fuska

Cikin kuka ta fara lallashin ta tana cewa "karki damu NUR kina dani inshaallah zan zaman yar uwa a gare ki" lallashin ta tayi har tayi shiru suka ci gaba da hira

Zakiya tace "jibi birthday dina"

NUR tace"nima haka besty"

Zakiya tace "wow!zamuyi celebrating kenan"

NUR tace" ni ban taba yi ba"

Zakiya tace "karki damu jibi Abba zai taho mana cake gobe mu shiga cikin gari mu siyi riga iri d'aya"

NUR tace"OK"

Zakiya tace "karki damu ina da kudi"

Ranar birthday Abba zakiya ya zo minna a gate ya tsaya ya kira ta a waya yace yana waje

Da salle ta mike tace"my NUR muje abbana na waje"

Tace"toh muje amma kin ji dadi a ce Abba ya baro aiki ya zo minna saboda birthday dubi girman bauchi fa"

Zakiya tace"hmmm ai Abba zai iya fiye da haka"

Zakiya na ganin shi taje da gudu ta rungumeshi tana me kukan shagwaba itako NUR kallonsu take cike da birgewa

D'angowa zakiya tayi daga jikin abbanta tace "abba ga kawata da NUR da nike baka labari"

Idonshi na haduwa da ita gaban shi ya fadi domin na karamin kama suka yi da zakiya ba

Gaishe shi NUR tayi ya amsa yace"ke yar wani gari ne?"

NUR tace "kano" ai sai yaji kamar ya dauke Zakiya su gudu

Yawo ya kaisu da siyya washe gari ya koma bauci

Yana kaiwa ya sanar da matarshi hajiya balkisu ya gan mai kama da zakiya

Ai sai ta mike tace ".......




Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fan
Pls share
[05/06, 18:42] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interlingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to my groups

πŸ…Ώ9⃣&1⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ai sai ta mike cikin fargaba tace"alhaji dole a canja wa zakiya makaranta karka manta saboda wanan dalili mu ka baro kano zuwa bauchi wallahir in asiri nan ta fito ban San ya zamu kare ba domin zakiya ce ta maye mana gurbin rashin haihuwar mu Wanda ba kowa ya San yar sintuwa bace"

Abba zakiya yace"karki damu domin na lura yaran basu dauki kamar tasu da wata manufa ba kuma san da na tambayi NUR din ta tabbatar min ita kadai iyayen ta suka haifa,kuma har wuyan ta na kalla babu wanan sarkar dake wuyan zakiya "

Hajiya balkisu tace"dole a raba zakiya da wanan sarka domin za a iya gane ta"

Murmushin takaici alhaji yayi yace"hajiya ki manta zakiya bata son rabuwa da wanan sarka ko kin manta daru da akayi tayi da ita akan an cire mata sarka"

Tace"hakane babu wanda ya isah ya raba ta da wanan sarka "

Washe gari alhaji ya kira zakiya akan cewa zai canja mata makaranta amma zakiya ta rikice me akan baza ta iya rabuwa da NUR ba,babu Inda ya iya haka ya hakura

Watani goma suka yi a makaranta sanan suka koma gida da k'yar suka rabu da juna harda kuka,

NUR na komawa gida ta koma gidan jiya har yafi ta da domin maimuna azabtar da ita take

Sati hudu sukayi result dinsu ya fito inda suka samu 200 level direct,NUR ko ta zabi course din urban and regional planing domin ta iya drawing da kera abubuwa, ita kuma zakiya account and auditing

Har zazzabi NUR tayi saboda kewar zakiya duk da kullum suna waya sai a mai take babu lafiya

A ranar da aka bude makaranta ranar NUR ta shirya domin ta gommace ta koma makaranta zakiya tayi jinyar ta domin ko ta zauna gida ba kulawa zata samu ba

A garaji Abbanta ya sauketa ta Shiga mota kasuwa inda ta tarar da wata kyakyawar mata mai tsohon ciki

Gaisheta tayi ta amsa da fara'a jinginawa NUR tayi jikinta,ai sai ta ji da zafi gashi tana numfashi a wahale

Matar tace"baiwar Allah kamar baki da lafiya ko?"

NUR tace"eh"

Tace"toh meyasa baki sha magani ba?"

Tace"nasha"

Matar tace"mu gan irinshi"bude hand bag NUR tayi ta Ciro panaldo"

Matar ta kalli driver tace"please ina zamu samu chemist a nan?"

Yace"ga chemist can bada kudi a anso miki"Biro ta ciro da takarda ta rubuta sunan magani ta bashi da kudi"

Bayan minti goma sha biyar ya dawo da maganin ta bawa NUR ta sha

Tace"sunana Dr summaiya kefa"

Nur tace"NURUL HUDAH"

Tace"ina zaki? gashi baki da lafiya"

NUR tace"makaranta "

Summaiya tace"amma be kamata a barki ki tafi ba bayan baki da lafiya"kallaon driver summaiya tayi tace"driver me Muke jira"

Yace"ai motar be cika ba"

Tace"muje cata zamu dauka"kallonta NUR tayi tace"bani da kudi"

Summaiya tace"karki damu zan biya"

Jaka ta jawo ta biya driver ta biya shi sanan ya ja Mota

A mota summaiya sai Jan NUR take da hira domin ta fuskance tana da damuwa tun NUR na nokewa har ta saki jiki da ita ta zayyana mata labarin ta

Sai dai abinda basu sani ba tun a kano wata bakar mota ke bin su gashi har sun kusa shigowa minna sai dai a daji suke


Kafin driver ya ankara motar tasha gaban shi ji kake kiiiiiiii karan Jan birki bayan motar suka bude suka Ciro summaiya

Fitowa NUR tayi ta kama kafar dayan dama su uku ne

Tuni driver ya gudu ya bar mota

D'aya daga cikin su yace"babawo in bata sake ka ba ka hado da ita mu huta

Ai ko daukar NUR yayi suka shiga daji wanda ba karamin tafiya sukayi ba kafin suka kai wani gidan da ba gama ginawa ba nan aka sauke su a ka daura NUR summaiya ko tuni numfashin ta ya fara sama da kasa domin tana da asthma

Waya bullet ya ciro ya kara a kunni a speaker yasa muryar mace naji tace"kun gama aikin?"

Bullet yace"eh"

jin muryar Wanda tayi magana yasa
Summaiya dangowa da k'yar ta tace"Fatima me nayi miki kika sa a sato ni"da k'yar take magana

Fatima ta kece da dariya tace"ke ko kika min laifi,bullet kashe min ita da abinda ke cikinta"

Yace"an gama"kallon d'aya daga cikin su yayi yace"babawo kai zaka yi gadin su zamu anso cocaine musha kafin mu aiwatar da aikin mu,wanan shine gwajin ka na farko kuma kai zaka kasheta"

Jiki na rawa yace"toh oga"da alamun sabon Shiga ne


Suna tafiya ba da dadewa ba summaiya ta fara nakuda,kokarin kwance kanta NUR ta fara yi ganin haka yasa babawo ya kwanceta yace"ki taimaka mata ina waje"

Tace"toh"

Da gudu ta karasa inda take tana mata sannu

Bayan minti 40 summaiya ta haiho kyakyawar yarta mace sai dai jini sai zuba yake ga numfashinta bai dawo dai-dai ba

Daukar yariyar tayi ta kalla sanan ta mikawa NUR tace"na baki ita kyauta ki rike ta amana sunanta hauwa suna ne da mahaifinta ke burin sa mata daga yau baza ki kara kukan rashin yan uwa ba domin a halin yanzu ke kadai na yarda da ita sunan mahaifinta
UTHMAN SULEIMAN ADAMS

Jin shiru yasa babawo shigowa yace kuyi sauri mu gudu tunda ta haihu NUR ko kuka take tana cewa"please karki mutu anty amma idonta ya fara kafewa

Babawo ko hawaye yake yace"ki yafe min kuma ki daure muje asibiti,wallahi ba laifina bane nayi karatu amma ba aikin yi ga mahaifiyata a asibiti ana niman dubu dari uku a yi mata aiki shiyasa na fara wanan sana'a,wallahi bazan yafewa kai na ba in wani Abu ya same ki"

Kallonshi tayi tace"na yafe maka duniya da lahira"sarka wuyanta ta Ciro da d'an kuni ta mika me

Tace"ka sayar zai isheka biyan kudin asibiti"

Kuka yake karasawa yayi zai taimaka mata ta girgiza kai tace"ka taimaka ka gudu da su karka bari komai ya same su"
Yace"toh"kama hanun NUR tayi tana murmushi har hanun ya sake


NUR ko


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[06/06, 01:13] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to GORGEOUS WRITERS FORUM

πŸ…Ώ1⃣1⃣&1⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Murmushi tayi tana shafa fuskar NUR har hanunta ya saki alamun rai yayi halinsa

NUR ko wani kuka ta saki da karfi da Sauri babawo ya toshe mata baki ga jaririyar ma kuka take

Babawo yace"ki tashi mu gudu kafin su cin mana a nan

Hijabin jikinta ta cire ta nade jaririyar,babawo ya rufe idon summaiya

NUR tace"a nan zamu barta?"

Yace"eh mana domin in mun tafi da gawar ta zamu shiga Matsala tashi muje"

Tashi tayi suna gudu a daji har suka fito titi

Cikin ikon Allah suka tarar da motar da direba ya gudu ya bari da makulli jikin shi

Bude mata gidan baya babawo yayi yace"shiga muje"

Tana shiga ya ta da mota sai hayan cikin gari

Motar su na barin wajen su bullet suka shigo

Direct gidan yar uwarshi ya kaita wanka akayiwa jaririya be boyewa yar uwar tashi komai ba ya sanar da ita, har kuka tayi saboda tausayi summaiya sanan ta ja wa babawo kunni akan bin abokan banza kaya kala uku ya suyo musu

A na gamawa yace"yanzu ina kikayi ne?"

NUR tace"FUTMIN"

Yace"muje domin zamar ki tare dani yana da hasari dana sauke ki zan San Inda zanyi da motan"

Tace"toh"har makaranta ya sauke ta,ta fito da kayar ta a booth har zata wuce

Babawo yace"ji mana ga sauran kayar ki"

Tace"ba kaya na bane kayan marigayiya ce"

Yace"kwashe wata rana zaiyi miki amfani tunda ga yarta a hanun ki"

Ba tare da tayi magana ba ta kwashi kayan

Tana shiga ta tarar da zakiya kwance

Zakiya na jin sallamarta ta mike tace"my NUR kin dade fa tun dazun nike jira kuma saboda ke na dawo yau"

Kafin NUR tayi magana jaririyar ta sala ihu

Zaro ido zakiya tayi tace"ina kika samo baby"

Ciro ta NUR tayi ta zauna sanan ta zayyana mata komai

Cikin kuka zakiya tace"lallai duniyar nan,amma muje station a nime yan uwanta domin su amshi jaririyar su"

Ai sai NUR ta zube kasa tana kuka tana rokon zakiya akan cewa karta fada kowa domin ta zama yar'ta kuma baza ta iya rabuwa da ita ba"

Zakiya tace"me zaki fada a gida?"

Tace"karki damu"

Zakiya tace"toh me za a bata kin gan tana kuka gashi sai tsoso hanun take alamun yunwa"

NUR tace"raka ni pharmacist in samo mata madara"

Haka fa rayuwa ta cigaba da tafiya inda NUR ke raino TASLEEM da taimakon madara kowa a makaranta yayi mamakin ganinta da baby masu gulma nayi amma ko a jikinta dama basa kula mutane"

Yanzu sun shekara da dawowa makaranta har TASLEEM tayi wayau tana d'an takawa sai dai bata yarda da kowa sai NUR da zakiya gashi kowa nasan d'auka ta domin tana da sha'awa gata bulbul dan ta fara cin abinci,

da akayi hutu NUR taki tafiya gida wai zata koyi computer gashi tana fargaba zuwa gida da tasleem hakan yasa zakiya ta sanar da abbanta zata tsaya ta koyi computer.

be hanata ba sai ma dadi da yaji domin baya son ta dawo ta tarar da bala'in umminta da take cewa a dole sai ya kore zakiya saboda ta samu ciki,babu inda baiyi da ita ba akan ta hakura zakiya ta cigaba da zama dasu kila ma sanadiyar ta ne Allah ya basu nasu"

amma tace"ba haka ba dama tana zama da ita ne saboda bata da haihuwa tunda Allah ya basu toh bata gan me zakiya zata musu ba ai sunyi kokari da yar suntuwa"

sanda suka shekara kuma babu wanda ya nimi NUR a gida,a yau driver ya zo ya kwashe su "

shima driver yayi mamakin ganin NUR da goyo,zakiya ta rungume NUR tace"sai muyi waya"wasa take tayi da TASLEEM a bayan NUR sai dariya take,kissing nata tayi sanan ta shige mota

kano

NUR ne zaune a kasa tiles gaban Abba ga TASLEEM gabanta

Abba yace"ke nike jira ki fada min ina kika samo yar nan"

NUR tace"ya'ta ce amma....."kafin ta karasa maimuna tayi tafi tace"cikin shage a gidan nan shiyasa da akayi hutu kika ki dawowa gida ashe kina can kina iskanci,nidai alhaji kasan Inda zakayi da ita kar a b'ata mana zuri'a"

cikin b'acin rai Abba yace"ke yar waye wanan?"

cikin kuka NUR tace"ya'ta ce amma ba ni....."saukar mari taji a kumatu

yace"kafin makotan su San wanan labari zan kai ta gidan marayu"

maimuna tace"ai alhaji babu shakka yar'ta ce ga kama nan Ashe shiyasa kwanaki da ta dawo hutu take ta amai"

Abba yace"toh amma shekara d'aya kenan da tafiyar ta makaranta kuma da gani yariyar nan ta shekara toh in ma ciki tayi kama ta ai a ce yar na wata uku ko biyu"

maimuna tace"kai alhaji raba kanka da d'an yau boye cikin tayi damun ina kyautata zato da tsohon ciki ta dawo"

Abba yace"na baki nan da kwana uku ki yanke shawara ko ki bari a kaita gidan marayu ko ki bar mu gida"yana kaiwa nan ya bar falon

rungume TASLEEM NUR tayi ta saki kuka tana cewa"bazan bari a raba ni da ya'ta ba"

washe gari maimuna ta Shiga makota ta fara raba zance akan cewa NUR tayi cikin shage,hakan yasa jama'a na nuna Abba in yana tafiya abin ba karamin b'ata me rai yayi ba yana dawowa gida ya fito da NUR akan sai ta ba da TASLEEM ya kai gidan marayu.kankameta NUR tayi taki badawa,cikin fushi yace"ta barme gidan shi

ai ko ta goya TASLEEM ta hada kayar ta sai garaji

bangaren zakiya ko ta tatar da tashin hankali da bata yi zato ba hajiya balkisu ta da bala'i akan sai alhaji ya kori zakiya da yaki sai tace"ai dama yar karuwan shi ya kawo mata gida"

itako zakiya kuka take kamar ranta zai fita jin cewa ita tar suntuwa ce bata da asali

har alhaji ya dauko Biro da takadda zai sake hajiya zakiya ta suguna ta roke shi

tace"bana son zama sila rabuwar ku Abba karka damu zan tafi amma dan alla ka sanar dani inda kuka since ni"

yace"yi hakuri ya'ta ban so ki san wanan sirri ta wanan hanyar ba,a bola bayan gidan mu a kano muka since ki,ina da tabbacin sarka wuyan ki zai taimaka miki wajen niman family ki domin dashi muka since ki"

tace"toh nagode Abba har abada kai ne mahaifina"karasawa tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login