Showing 9001 words to 12000 words out of 45929 words
ita
Zakiya tace"yi hakuri my NUR bazan kara ba na daina zuwa club din"
Shiru NUR tayi har suka shiga elevator din building
Wajen manager suka je yana ganinta yace"NUR meya kawo ki?"
Tace"wajen hajiya hafsat muka zo ita tace muzo"
Yace"OK kune ashe tace in kun zo a kai Ku office dinta,Ku biyoni"
Har office din hajiya ya kaisu
Bayan sun gaisa ta amshi takardu su
Tace"ke zakiya da sameer zaki yi aiki domin shine babba a audit department kuma abinda kika karanta kenan so kene p-a dinshi"
Zakiya tace"toh nagode hajiya"
Hajiya hafsat tace"kuyi ta kirana da ummi ko baku so in zama ummi Ku?
Murmushi suka yi cikin jin kunya suka ce muna so
Tace"NUR ke da Afan zaki yi aiki"gaban NUR ne ya fadi tace"ummi a canja min department"
Ummi tace"meyasa?"labarin abinda ya faru tsakanin ta da Afan ta bata
Ummi tace"muje in me magana be isa ya Kore ki ba yara kena sai bakin hali"
Sanda ummi ta nunawa zakiya office din ta da sameer sai dai be zo ba sakamakon ciwon kai da ya tashi dashi
Bajewa zakiya tayi a kujera bayan ta kunna a/c
Har office din Afan ummi ta kai NUR yana ganin NUR yace"ummi ina kika samo wanan mahaukaciyar?"
Rai b'ace ummi tace"lafiyar ka kuwa ka gan tayi kama da mahaukaciya ce?ka kiyaye ni"
Yace"yi hakuri"
Ummi tace"gata nan tare zaku yi ta aiki kuma ban amince ka walakantata ba"
Yace"toh"tashi ummi tayi tace"NUR a yi aiki lafiya"
Ummi na fita Afan ya kalli NUR daga sama har kasa yace"watoh na Kore ki shine kika je kika hada ni da mahaifiyata ko?"
Girgiza kai NUR tayi tace"wallahi ban....."buga tebur da yayi ne yasa tayi shiru
Yace"yi min shiru munafuka alguguma ni zaki maida yaro"
Hawaye ne ya fara fita a idanun NUR cikin kuka tace"yi hakuri"
Yace"sorry for yourself"
Kallonshi tayi tana hawaye
A fusace yace"bar kallo na"
Jiki a matukar sanyaye ta fita taje ta zauna
Sai karfe 10 sameer ya shigo office a inda p-a ke zama kafin ka shiga office dinshi ya tarar da zakiya ta kife kai tana barci dan zakiya akwai barci in tana barci sai ka sace ta bata sani ba
rai b'ace yace"what the hell"buga tebur din yayi,a firgice ta mike tana raba idanu
Yace"follow me"ba tare da ya kalleta ba dan ummi ta Riga da sanan dashi an samo me p-a
Office dinshi ta bishi zama yayi yana kallonta daga sama har kasa
Yace.......
Maman
Noorul
Huda
Luv u my fans
Pls share
[07/06, 17:47] Maman noorul huda marubuciya: πππππ
RAYUWAR NUR
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
π
Ώ2β£1β£&2β£2β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Sanda ya gama kallonta daga sama har kasa sanan yace"ke ya sunan ki?"
Share shi tayi kamar ba da ita yake ba
Buga tebur yayi yace"dake fa nike magana kin share ni,kina wani kallo na kamar kin sanni"
Murmushi tayi tace"yi hakuri malam kayi min kama da Wanda na sani ne,sunana Aisha idris amma ana kirana da zakiya"
Yace"watoh dan raini hankali shekaran jiya kika ce sunan ki NUR dan mu kore ki zaki wani dawo da wata sallo da sunan zakiya,toh bari in fada miki karki gan dan ummi ta kawoki ki ce zaki nimi ki kawo min iskanci da raini wallahi in kika raina ni korar ki zanyi,mayya kawai"
Ga mamakin sameer sai ya gan tayi murmushi tace"an gama oga amma kaima ka bi a hankali domin ni din nan da kake gani bana d'aukar raini,kuma ina dai-dai da ko wani d'an iska,kuma karka ce da kai nike"
a ranshi yace"watoh dan rainin hankali ta kirani da d'an iska kuma wai ba dani take ba"a fili
Yace"ni kike fad'awa maganar banza,toh ki koma gida na sallame ki"
Tace"ba ka da ikon yin hakan domin ba kai ka kawo ni ba,hajiya kadai ke da wanan ikon"ta karashe magana da murguda me baki"
A ranshi yace"ikon Allah ummi ta jawo mun raini da ta kawo min wanan yar iska"
Katse shi tayi da cewa akwai aikin da zanyi ne ko na koma na cigaba da barci?"
Yace"what?barci a wanan office din?"
Tace"toh in ba aiki me mutum zaiyi?ai sai hutu"
Murmushi yayi a ranshi yace"aiki ko yanzu za ki gan aiki"file ya dibo diyawa ya mika mata yace"gashi kije ki had'a figure din a zuba a computer so nike ki gama aikin nan yau"
Kallonshi tayi ta kalli file din tace"toh ba damuwa"kwashe file din tayi zata bar office din sai yace"zo nan"
Zuwa tayi ta tsaya a gabanshi rike da file din
Yace"ina son ki sani bana son shishigi da iyayi kuma duk lokacin da zaki shigo office dina kiyi sallama in kika ji shiru ki koma,bana son latti "
Tace"OK sir"ta juya zata wuce
Yace"ke wayace ki tafi?"
Tace"na dau ko ka gama ne ai oga"
Yace"zaki iya tafiya"
Tana fitowa ta zauna ta kunna computer ta fara aiki
Bangaren NUR ko bayan ta zauna Afan ya kwaso mata project yace"tayi planing din building"
Tace"sir kafin na fara aikin sai na gan filin da irin unguwar da za a yi gini saboda nasan inda zan fara"
Kallonta yayi a ranshi yace"ashe ta San abinda take yi"a fili
Yace"Ok,bari zamu meeting in muna dawowa zamu biya"
Tace"OK sir"
Yace"banson sir,kiyi tacewa sir Afan"
Tace "OK sir Afan" zama tayi tana treating file din dake gabanta cikin kankani lokaci ta gama"
Zakiya ko aiki take hankali kwance ga a/c ta bude tana jin dadi a fili tace"nayi missing A/c ai ko dan wanan A/c zanyi ta zuwa aiki,gashi my NUR na fushi dani"
Shiko sameer zama yayi yana zuke-zuken shi na sigari
Domin shi baya son yin aiki yanzu ma aikin shine ya kwashe ya bawa zakiya tayi kuma jira yake ta kawo ya duba ko tayi kuskure dan ya samu abinda zai rike ummi ta koreta
Zakiya tana cikin aiki sai wari sigari take ji,tun tana ji kad'an kad'an har abin yayi yawa tashi tayi taje dai-dai bakin office din shi tayi sallama
So biyu bai amsa ba
Sameer dake zaune yana busa sigari jin sallama yasa shi tashi da wuri ya fara fesa turare ya kwashe Wanda yasha a wani karamin plate ya buye
D'aga murya yayi yace"waye ne?"
Zakiya tace"nine"
Yace"lafiya?"
Rasa me zata ce tayi sai tayi shiru
Yace"nace me kike so?"
Ai sai tace"ummi ne ta aiko ni"
Jin ummi ya kara d'aga me hankali sweet ya Ciro a aljihu yasa a baki dan a zatan shi tare da ummi suke
Yace"shigo"Shiga office din zakiya tayi tana dube -dube har ta hango karamin plate din daya boye a karkashin kujera
Ganin bata da niya magana gashi sai kallo wuri take kamar me niman Abu yasa shi
cewa
Ke lafiya?ina ummi take?"
zakiya tace"sir kamar warin sigari ko?"
yace"a ina kika ji?"
tace"wallahi da nike aiki wari ya dame ni kuma nasan a nan department din ne shine nace bari in zo in ma magana saboda bai kamata ana shaye-shaye a cikin building din nan ba ya kamata ka dau mataki"
kallonta yayi yace"ke ban son iskanci tunda nike babu Wanda ya taba cewa yaji warin sigari a wanan company sai ke watoh kin fi kowa hanci kenan ko"
zakiya tace"........
gaskiya zan daina posting dan na lura baku shirya ba,saboda comment ma gagaran Ku yake sai turo min emojis da sticker ake instead of comment ko Sharhi,ai kamar wahalan banza nike kullum ina takura kaina dan in faranta muku amma comment ya gagare ku, gaskiya in ban gan canji yau ba zan ajiye labarin nima in huta,
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
[08/06, 01:37] Maman noorul huda marubuciya: πππππ
RAYUWAR NUR
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,intelligent, and expert writers,we are the best among the rest.
π
Ώ2β£3β£&2β£4β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Zakiya tace"oga ba haka bane ai be kamata bane, amma in kayi fushi kayi hakuri zan fad'awa ummi tasan abinyi tunda kai baza ka dauki mataki ba, kuma gaskiya bana son warin sigari na ma tsane me sha yana sa numfashi na yayi ta daukewa,kar a zo a cutar dani"tana gama magana ta juya zata wuce tana dariya kasa-kasa
Da Sauri yace"ina zaki?"
Tace"wajen ummi"
Yace"ba sai kin fad'a mata ba zan San abinda za ayi"
Murmushi tayi kasa-kasa a ranta tace"ashe zargin da nike ya tabbata bai son asan yana shaye-shaye" juyowa tayi ba tare da tayi magana ba ta fara tafiya
Yace"ke ina zaki ne?"
Tace"windo zan duba dan warin daga office din nan ya ke fitowa shine nike son in duba ko nan ake makalewa"
Jawota yayi yace"nace ki bari zanyi bincike"
Tace"OK"
Barin office din tayi tana murmushi kasa-kasa
Shiko sameer tana fita yace"na shiga uku an hado ni da mayya ,wallahi ni wani lokaci rikid'a take,wani lokaci tana min kama da ummi,wani lokaci kuma alhaji tsoho gashi farko dana fara ganinta a office din Afan fara ce Sol bata da kiba yau kuma ta d'anyi duhu ga kiba,nidai naga ta kaina tunda aka had'a ni da mayya tunda nike babu wanda ya taba zargina da shaye-shaye sai ita gashi ummi ta gargade ni akan bata son a koreta,Allah kadai yasan safi da tayiwa ummi
NUR ko aiki take tana duba agogo saboda lokacin tashin su TASLEEM ya kusa a makaranta
Shiko Afan sai kallonta yake da gefen ido
Tana ganin 2:30 yayi ta mike ta karasa gaban Afan tace"sir ina son in tafi gida d'auko ya'ta a makaranta"
Yace"koma ki zauna ai 4:pm ne lokacin tashi sai lokaci yayi zaki tafi"
NUR tace"please sir kayi hakuri wallahi zata ta jirana"
Afan yace"toh ki kira mahaifinta mana "
NUR tace"bata da kowa sai ni"
Yace"what kina nufin bata da uba?"
Eh NUR tace a takaice
yace" rasuwa yayi ne"
NUR tace"ah'ah"
Dariyar rainin hankali yayi yace"Ashe shegiya ce"
Cikin b'acin rai NUR tace"ni ya'ta ba shegiya bace"
Yace"oh rashin kunya zaki min kenan?"
Tace"yi hakuri sir amma bazan yarda kowa ya sheganta min ya'ba a gabana please"
Afan yace"ashe baki da kunya toh ki koma ki zauna,toh in ba shegiya ba wacece?"
Tace"sir in kana so ka tsira da mutuncin ka karka kara kiran ya'ta da shegiya dan ba zan d'auka ba,domin akan TASLEEM zan iya rabuwa da kowa banda zakiya "juyawa tayi ta je wajen zamanta ta dauki Jakarta har zata fita
Yace" in kika fita karki dawo"
Ba tare da ta juyowa ba tace"akan ya'ta zan iya barin aikin nan,saboda aikin nan zan bar ya'ta a bakin titi?toh ni ba zan iya ba,yama za ka San da haka tunda baka San darajar ya'ya ba,amma ina son ka sani wata rana yar ka ko kanwar ka zata iya fad'awa a halin da nike ciki,in aka masu haka ya za ka ji?"tana kaiwa nan ta yi tafiyar ta
Tana barin office din ya fad'a duniyar tunani,yace"wai ni yau akewa gorin haihuwa nan take ya tuna marigayiyar matan shi ga wani tsanan NUR na ratsa shi
yace"Allah sarki summaiya da kina raye da yanzu yar mu nada shekara 7
tunawa yayi da ranan da summaiya ta dawo daga asibiti ta fad'a me tayi scarning kuma ya Nuna ya'mace zata haifa.ba zai taba mantawa ba irin farin ciki da yayi ba a take yace mata sunan yar hauwa'u kasancewar sunan kanwar mahaifiyar shi ne"
Ko ta kan zakiya NUR bata bi ba ta bar building din cike da b'acin rai na kiran TASLEEM da yayi da shegiya
A gate suka yi karo da sameer ko kallonshi bata yi ba ta wuce shi
Shiko ya bi ta da kallon yace"ikon Allah Ashe zargina ta tabbata gaskiya mayya ce,tunda gata da wani kalar kaya jikinta"
Yana Shiga office kuma ya tarar da zakiya tayi bake-bake tana cin abinci da minerals a gabanta
Da gudu ya shige office har yana hade kafafu yace"yariyar nan aljanane yanzu kuma da take cin abinci da abbana take kama"
itako zakiya kallonshi ta cigaba da yi tana lashe hanun a ranta tace"kowa da kalar haukanshi shi kuma wanan me ya tsoratashi"
Wanene AFAN da SAMEER
UTHMAN SULEIMAN ADAMS (AFAN) shine asalin sunan shi d'an ne ga marigayi barrister SULEIMAN ADAMS
da mahaifiyarshi hajiya HAFSAT
su uku mahaifansu suka haifa shi da kanen shi mata biyu zainab da ihsan Wanda yanzu duk suna gidan miji
su asalin yan Cameroon ne AFAN ya taba aure shekaru takwas da suka wuce amma matar shi ta rasu Wanda ake zargin yan garkuwa (kidnaper)da mutane suka kasheta a lokacin tana da tsohon ciki a hanyarta ta zuwa minna daga kano kasancewar ita yar asalin minna ne,sai dai lokacin da aka ga gawanta baga ciki tare da ita ba wanda da dukan alamun an tabbatar da ta haihu amma babu jaririya a inda aka gan gawanta
AFAN na matukar son matar shi summaiya Wanda suka hadu a makaranta lodon ta hanyar wata cousin dinshi fatima watoh yariyar kanin mahafinshi domin Fatima kawar summaiya ce Wanda summaiya bata da wata kamarta
sai dai abin da summaiya bata sani ba shine Fatima ta dade tana son Afan tun tana yariya amma yana ganin ta tare da summaiya ya nuna yana sonta ita kuma ta amince,hakan ba karamin d'agawa Fatima hankali yayi ba amma sai ta daure a fili ta nuna tana farin cikin alakar summaiya da Afan amma a zahirin gaskiya ba haka bane
dama kawai take nima ta raba su koda hakan kuwa na nufin kashe summaiya ne
bayan sun kammala karatun su a London inda ita summaiya ta zama cikakiyar likita,ita kuma Fatima yar jarida shi kuma Afan Architect
kowa ya koma kasan shi ita summayya ta dawo gida Nigeria Fatima da Afan suka koma Cameroon
ba tare da b'ata lokaci ba s waliyan Afan suka zo Nigeria niman auren summaiya inda akayi komai cikin kankanin lokaci
bayan auren su summaiya da wata uku Allah ya bata ciki kafin ta fad'awa Afan sanda ta sanar da Fatima sai dai hakan da tayi ba karamin b'atawa Fatima rai yayi ba amma sai ta nuna tayi murna
cikin summaiya na shigan watan haihuwa ta nace zata gida ta haihu Wanda Afan bai so ba amma sai mahaifiyarshi tasa baki akan ya bari taje tunda ta nace
a ranan da zata dawo Nigeria Fatima ta fara kira ta sanar mata zata shigo Nigeria amma zata shigo kano su gan juna kafin ta wuce minna
kasancewar fatima a kano take aiki tana zama da yayar mahaifiyarta domin mahaifiyarta Nigeria ce,tun bayan gama makarantar ta ta dawo Nigeria
fatima na jin summaiya zata zo Nigeria kuma sai ta biyo kano zata je minna hakan yasa ta bada kwangila kashe summaiya wa su bullet
sanda summaiya tayi kwana biyu a kano sanan ta shiga motar minna
a nan su bullet suka samu nasarar sace ta da wata yar makaranta zuwa daji sai dai kafin su kasheta sun dawo sun tarar da ita a mace kuma basu gan cikin jikinta ba ga wanda ke gadin ta da ita yar makaranta sun gudu
bayan kwana uku
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
[08/06, 02:07] Maman noorul huda marubuciya: πππππ
RAYUWAR NUR
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
gaskiya naji dadin comment dinku jiya yanzu na yarda kuna matukar so RAYUWAR NUR
π
Ώ2β£5β£&2β£6β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Bayan kwana uku police suka tarar da gawan summaiya a wani gida da ba gama ginawa ba
Mutuwa summaiya ya taba kowa da yara da manya domin summaiya macece mai kirki ga son talakawa da taimakon na kasa da ita
An danganta mutuwarta ne da yar garkuwa da mutane kasancewar ba a gan wani shaidan da zai nuna cewa kasheta akayi ba domin babu albin bindiga ko wani abu,sai dai abin da ya daurewa mutane kai ba a gan abinda ta haifa ba mahaifinta alhaji nasir ya fi kyautata zaton asthma ne ya kasheta
Hakan yasa ba ayi bincike ba sai dai police sunyi alkawarin zasu kamo duk wanda hanunshi ke ciki
Itako Fatima ba karamin dadi ta ji ba burinta ya cika na raba summaiya da Afan
Da ta tambayi su bullet yar da summaiya ta haifa sai suka mata karya cewa sun kashe ta sun wurgata cikin rafi hakan yasa ta kwantar da hankalinta
Sai dai ta dau alwashin kau da duk mace da ta had'a dangantaka da Afan
Bayan rasuwar summaiya da shekara biyu mahaifin fatima yace"ta fito da miji ya gaji da ganinta haka"
A shekara na uku mahaifinta yayi mata aure da d'an abokin shi domin taki fito da miji da ta tunkari Afan ya nuna mata baya sonta,son da yake mata na yan uwantaka ne ba na aure ba
shekara Fatima uku da yin aure ta kashe aurenta domin bata hakura da Afan ba
Sameer ko
SAMEER Mohammed Suleiman shine cikeken sunan shi d'an ne ga alhaji Mohammed Suleiman
mahaifinshi yaya ne ga mahaifiyar Afan sameer ya ba Afan shekara uku sai dai baka taba sani domin bashi da aboki da ya wuce Afan
sameer ya taba soyyaya da wata shuwa Arab mai suna safeena yana mutuwar sonta amma daga karshe ta yaudare shi ta hanyar auren babban abokin shi Bayan ta gama cime kudi wanda bayan aurene ya gane bakin su d'aya da abokin shi aliyu shi ya turo ta dan su samu kudi
tunda daga wanan lokacin ya daina yarda da abokai sai dai d'an uwanshi Afan
sanadiyar wanan yaudarar ne ya fad'a a harkan shaye-shaye kuma ya tsani mace
sameer karshen d'an duniya ne sai dai baya zina ga wulakanta d'an Adam halin shi d'aya da Afan sai dai Afan baya shan komai hasalima baisan sameer nayi ba
abinda ya kawo su Nigeria shine niman kanwar mahaifiyasu hauwa wanda kakarsu alhaji tsoho yasa a nimo ta domin ya yafe mata
sai dai suna zuwa Nigeria suka gan ana gwanjon wani company building a minna
hajiya hafsat ta siya suka canja sunan zuwa AFSAMAN wanda aka hada sunan Afan da sameer sai Suleiman
wanda Afan yana zama ne dan yana son yayi binciken mutuwar summaiya da kuma yar'sa shikuma sameer haka kawai yaji garin yayi me
sai dai fa gayun nan biyu sun hadu kuma farare ne Sol
wanan kenan
cigaban labari
maman
noorul
Hudah
luv u my fans
pls share
[08/06, 13:49] Maman noorul huda marubuciya: πππππ
RAYUWAR NUR
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGOUGEOUS WRITERS FORUMπ