Showing 6001 words to 9000 words out of 45929 words

Chapter 3 - RAYUWAR NUR BY MAMAN NOORUL HUDAH

31 Oct 2025

4127

gaban hajiya tace"nagode ummina bazan mata da kulawar ki ba a gareni"

kiran NUR tayi a waya tace"gata nan dawowa minna dan dama ta fada mata abin da ta tarar a gida"

a makaranta suka hadu kowa sai kuka yake da yike ana hutu hakan yasa zakiya niman agent ya kama musu daki

bayan shekara biyar......

na gan comment akan rayuwar nur ya ba Ku tausayi wasu ma har kuka suka yi,abinda nike so shine a duk lokacin da ka ji labarin da ya taba ki,ba kuka ya kamata ki yi ba amma ki koyi darasi domin duniyar nan abin tsoro ne, muna dai rayuwa be amma bamu San wake son mu ba,Allah yasa mudace
[06/06, 13:24] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

dedicated to my husband nagode da sopport dinka Allah ya bar mu tare,you always help me with my novels,kaine mai editing mistake I have nothing to say than to thank you my husband. u are the best
πŸ…Ώ1⃣3⃣&1⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Bayan shekara biyar suka kammala karatun su da taimakon kudin dake account din zakiya sai dai tun a final year kudin ya kare ga TASLEEM ma na zuwa makaranta domin nursery 2 take,per time aiki NUR ta nima a inda suka koyi computer ana biyan ta dubu goma kafin result dinsu ya fito

Sai dai TASLEEM na da shekara biyar alamun asthma ya fara bayyana basa wata basu kwanta a asibiti ba da farko ce musu akayi nimonia ne

Result na fitowa NUR ta nimi aiki a wani building company da taimakon Allah ta samu ana biyan ta dubu arba'in da biyar domin degree take dashi

Zakiya ko ta nimi aiki amma bata dace ba

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda mai gidan da suke haya ya koresu saboda basu biya

NUR ko ta nimi wani karamin gida domin daki d'aya ne Sai bayin garwa ko sillin babu ga gidan na laka,dubu goma a shekara da farko zakiya tace"baza ta zauna ba"

NUR tace"hakuri zakiyi muna cikin jarabawa ne kin gan ba kudi bane damu"

Da k'yar ta yarda gashi ta hana abbanta taimaka musu domin hajiya ta mata kashedi

A haka suke rayuwarsu uku sai dai kudin NUR akan TASLEEM yake karewa domin yanzu an gane asthma ne

NUR na matukan son TASLEEM infact ita ce rayuwarta domin zata iya yin komai dan farin cikin TASLEEM

A haka suke rayuwa inda yanzu TASLEEM nada shekara bakwai ko makaranta zata da inhailer ta a jaka

Halayen NUR da zakiya ya banbanta,domin NUR tana da sanyi bata son hayaniya,NUR fara ce Sol kyakyawa ce a jin farko tsayawa fadin kyaunta b'ata lokaci ne komai nasu iri d'aya ne da zakiya domin suna matukar kama sai dai NUR tafi zakiya haske da tsayi ita kuma zakiya ta fita kiba kadan amma ba kowa ke lura da haka ba domin suna matukar ruda jama'a

In kana son ka gan b'acin rai NUR ka taba TASLEEM domin TASLEEM ita ce weakness dinta NUR tana da addini sosai domin tun tana gun kakarta ta sauke,bata bacci kullum sai nafila

Zakiya ko irin yan Matan nan ne masu baki da masifa bata daukan raini a gun kowa ga raini bala'i

Itama akwai addini amma baza ka gane hakan ba sai kun zauna tare

Sai dai fa zakiya tana da wani hali na zuwa club da dare kuma duk randa taje toh da safe za a ganta da kudi

NUR tayi mata nasiha ta gaji amma ba canji

Zakiya na matukan kaunar NUR da TASLEEM amma kullum sai ta tunawa NUR akan karta manta a ko wani lokaci za a iya raba ta da TASLEEM domin dole wata rana siri zai fito

Itako NUR abin da ta tsana kenan a ce za a raba ta da TASLEEM

Har fushi take da zakiya in ta mata maganar,

TASLEEM ko babban burin ta shine ta gan daddy ta domin a makaranta kowa na bada labarin daddy shi ita sai dai tayi shiru

Yanzu da zakiya da NUR suna da shekara ashirin da biyar

Wanan kenan


Cigaban labari


masu bina PC akan bana zuba love a littafai na,toh ina so ko sani ni ba wanan ya dameni ba,ya kamata Ku gane abubuwa na faruwa a duniya mai yasa zamu b'ata lokacin mu akan rubuta soyayya,a film soyyaya komai soyayya is high time we know what we are doing and learn from mistakes of other people let not waist time writing and reading what is not important.ba wai ina nufin babu kyau karanta littafin soyayya bane but kowa ya San soyayya novel ba ya faruwa a zahiri sai ka gan ance mata da miji har suka kare rayuwar su basa fad'a kuma shi ke mata wanka(I laugh in Spanish)please marubuta ya kamata mu ajiye maganar soyayya a gefe mu fara rubuta abinda zai amfani al'uma,

in akwai Wanda na b'ata wa rai a magana na ya yi hakuri

Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv my fans
Pls share
[06/06, 20:38] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

πŸ…Ώ1⃣5⃣&1⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Toshewa zakiya baki NUR tayi tace"inshaallah babu wanda zai raba ni da TASLEEM"

Zakiya tace"hmmm Allah ya sa"

Misalin 2:30pm NUR tace"zakiya bari inje in dauko TASLEEM a makaranta"

Zakiya tace"toh sai kin dawo"

Bayan minti 30 sai gasu sun shigo da sallama

TASLEEM ta gaida zakiya ta amsa

TASLEEM ta kalli NUR dake zuba mata taliya tace"mummy gobe ance mu kawo kudin makaranta in ba haka ba za a Kore mu"

NUR tace"toh allah ya kaimu,ga abinci yi sauri ki ci ki tafi islamiya"

Bayan TASLEEM ta ci abinci ta gama tayi sallah NUR tayi mata shiri zuwa islamiyya ta tafi

Tana barin gidan NUR tayi tagumi

Zakiya tace"lafiya kika yi tagumi?"

Ajiyar zuciya NUR ta sauke tace"zakiya babu ko sisi hanun na ga maganar kudin makaranta TASLEEM,ga maganin ta sun kare inhailer ma kadan ya rage,ban San ya zanyi ba in ta samu attack,gashi aikin dogara na dashi an Kore ni"

Zakiya tace"gaskiya ne akwai matsala musamman maganar magugunar TASLEEM domin ba zan manta attack dinta na karshe ba,babu Wanda ya San zata rayu,amma ya kike ganin zamuyi?"

NUR tace"gobe inshaallah zan fita niman aiki,kema dun Allah ki zo muje tare ki daina zuwa club da wanan barcin asara"

Murmushi zakiya tayi tace"toh ni wallahi raini ne ban so,in kaje niman aiki ayi ta raina ka ana baka doka"

NUR tace"ba dole ba tunda bake keda company ba"

Zakiya zata yi magana sai ga TASLEEM ta shigo da sallama

Da mamaki NUR ta kalleta tace"me ya dawo da ke a wanan lokacin?"

TASLEEM tace"korata akayi ban biya kudin makaranta ba"

Kafin NUR tayi magana zakiya ta mike tace"muje in gan Wanda ya kore ki,a ce saban son abin duniya islamiyya ma sai an biya abinda a da sadaka ake ba dawa ranan laraba amma yanzu sai a ce sai an biya nasu ma har dubu biyu,a haka ma bamu taba kin biya ba sai wanan wata amma saboda rashin kara da yiwa mutane uzuri shine zasu koro ki,muje in gan malamin"

NUR tace"kyalesu kawai in na samu zan biya"

Zakiya tace"wallahir sai naje"

hijabi tasa sanan ta saka TASLEEM gaba sai islamiyya

Suna kaiwa zakiya tace"baby kaini wajen malamin da ya koro ki"

Malami na aji yana koyarwa zakiya tace"kira shi"

Yana fitowa ya tarar da zakiya tsaye bayan sun gaisa

Zakiya tace"malam yanzu abinda kayi ka kyauta?"

Yace"me nayi baiwar Allah "

Tace"ka hana yariya karatu akan bata biya kudi ba sai a wani korota alhalin bawai an saba rike kudin bane ba a biya"

Malam yace"ai ba ita kadai aka kora ba"

Tace"malam wai in tambaye ka"

Yace"ina ji"

Zakiya tace"kasuwanci kake ko niman lada"

Yace"niman lada"

Tace"good ashe bai kamata kana amsa kudin wata ba goma ya kamata ana baka duk laraba in mutum yayi niya"

Yace"a goma ma sai anyi niya,ina fa da iyalai"

Tace"sai ka nimi aiki kana zuwa da safe bawai ka dogara da islamiyya ba,ai da bakin ka kace niman lada kake ba kasuwanci ba"

Ai shiru yayi domin ta gama daure shi

Kallon TASLEEM zakiya tayi tace"ina ne ajin Ku?

Tace"gashi can"tayi mata nuni da hanun"

Zakiya tace" yi sauri ki shige ki yi karatu"

Yana ganin shigan ta tace"malam sai anjima"tayi tafiyarta

Shiko sake baki yayi yana kallonta

Washe gari

Da sassafe NUR ta shirya zakiya tace"ina zuwa"

NUR tace"zan shiga bari ne niman aiki ko za a dace,ki kula da TASLEEM domin yau baza ta school ba,please karki barta ita kadai domin tun jiya numfashinta ke sama"

Zakiya tace"toh sai kin dawo Allah yasa a dace"

Tace"amin"

Yawo NUR tayi a cikin gari sai dai duk inda taje sai a ce ba vacancy

Gajiya tayi da yawo ta samu wani dakali ta zauna hana hutawa ga kishin ruwa

Zaman ta ba dadewa ba wayarta tayi kara zakiya ce

Da sauri ta d'aga

Zakiya tace"hello NUR TASLEEM ta samu attack gashi inhailer ya kare"

Ai a rude ta mike tace"gani nan zuwa "

Gudu ta farayi ba tare da ta kula a titi take ba

Ko duba hanya bata yi ba ta shige titi

Ji kake kiiiiii ai buge ta

Ta fadi kasa wata mata ce ta fito

Tana fitowa ta.....

Ku gyra zama cause the real fun has just begun

Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[07/06, 02:13] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


Dedicated to all my fans especially Wanda basa group di na,ina yi Ku sosai nagode da kaunar ku.


πŸ…Ώ1⃣7⃣&1⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Wata dattijuwar mata ce ta fito

Tana fitowa ta karasa inda NUR ta fadi

Tace"sannu tashi muje asibiti yar nan"

NUR na tashiwa ta dauki jakarta tace"karki damu hajiya ba wani ciwo na ji ba"

Jin muryar NUR yasa matar juyowa ta kalleta,ai sai taji murya kamar na kanwata hauwa

Tace"no dear bari muje asibiti a duba ki ga jini na zuba a goshin ki"

Ai sai NUR ta fashe da kuka tana cewa sauri nike TASLEEM ba lafiya"

A rude tace"subhannallah wacece TASLEEM?"

NUR tace"ya'ta ce yanzu aka kirani asthma ta ya tashi kuma wallahi bani da ko sisi ki taimaka min hajiya kar ta mutu dan naga alamar kina da kudi,ki taimaki rayuwata"

Murmushi hajiya tayi tace"toh yi sauri ki shiga mota muje"da sauri ta shiga motar

Suna kaiwa gida suka tarar da zakiya zaune da TASLEEM kwance a jikinta tana numfashi sama-sama domin abin ya fara sakin ta

Da mamaki NUR ta kalli zakiya tace"ina kuka samo inhailer?"

Zakiya tace"da naji shiru baki dawo ba har idonta ya fara kafewa sai nayi tunanin ko kin dawo babu kudi hanun ki shine nayi gudu naje shagon uche nace ya bani inhailer ba tare da ya San babu kudi tare dani ba,yana mika min na gudu na dawo gida na bata"

Rungume zakiya NUR tayi tana kuka tace"nagode Allah ya bar mu tare"

Zakiya tace"miye haka ko kin manta nima TASLEEM ya'ta ce?"

Itako hajiya shiru tayi tana kallon su da yanayin gidan duk sai taji tausayin su ga wani abu da zuciyarta ke raya mata

Tace"Ku dauko ta muje asibiti duk ta wahala"San da tayi magana zakiya ta lura da ita.

Gaisawa suka yi da zakiya,hajiya sai kallonta take kamar ta taba saninta

NUR tace"zakiya shirya muje a duba ta"kafin zakiya ta mike sai ga uche ya fado dakin ko sallama babu yace"give me money"

Zakiya tace"I don't have money in na samu zan kawo maka"

Yace"that one na lie sai kin bani kudi na"ganin zai ta da hankalin jama'a yasa haji tambayar shi nawa kudin ta biya shi

Ya bar gidan


Cikin minti goma zakiya ta shirya hajiya ta kaisu asibiti

Bayan an duba TASLEEM harda Karin ruwa NUR ta zauna kusa da ita hajiya ko na tsaye

NUR tace"hajiya nagode Allah ya saka da alhairi"

Murmushi tayi tace"babu komai amma yaya sunan ki ne?"

NUR tace"NURUL HUDAH"

Hajiya tace"OK NUR amma ya kamata kuyi ta kula da ita saboda wanan ciwon da kike gani ba abin wasa bane ba wuya ya halaka mutum kun dai ji abinda likita ya fad'a tana bukatar kulawa kuma tayi ta yawo da inhailer ta"

NUR tace"wallahi hajiya ina kokari jiya nan ne ya kare kuma babu kudi hannu na shiyasa ban siya ba har biyu nike siya in ajiye saboda emergency "

Hajiya tace"toh a dai kula domin in gaya miki matar d'an na Afan tayi fama da wanan ciwon shiyasa da na gan TASLEEM sai na tuna ta domin suna d'an yanayi"

NUR tace"Allah sarki,Allah ya bata lafiya"

Hajiya zata yi magana sai ga zakiya ta shigo da sallama da kular abinci hanunta"

Hajiya tace"har kin dawo?"

Zakiya tace"eh na dawo"

NUR ta kalli zakiya tace"ina kika samu kudi kika daho abinci?"

Susa keya zakiya tayi tana murmushi tace"ki ci nasan tun safe baki karya ba"

Hajiya tace"wai NUR in tambaye ki ina mijin ki"

NUR tace"ai ban taba aure ba"

Tace"toh yariyar waye wanan?"

Tace"ya'ta ce"

Hajiya tace"toh tayaya kika samo ta in baki taba aure ba"

Hawaye ne ya fara bin kumatun NUR,ganin NUR na kuka ga zakiya tayi suru-suru da idanu yasa hajiya cewa"it OK in baki son ki sanar dani amma ina zaki har na bige ki?"

Zakiya a ranta tace"wanan matar akwai bin didigi"

NUR tace"aiki naje nima amma ban samu ba"

Hajiya tace"wani qualification kike dashi"

NUR tace"degree "
Hajiya tace"wani course?"

Tace"urban and regional planing"

Hajiya tace"wani grade?

Tace"second class upper"

Tace"good,kefa zakiya"

Zakiya tace"degree,account and auditing first class lower ".

Hajiya tace" gobe Ku same ni a AFSAMAN building company karfe 7:30

NUR zata yi magana zakiya ta katseta da inshaallah zamu zo

Hajiya tace"in ruwan ya kare za a sallame Ku ni zan tafi"kudi ta mikawa NUR sanan suka yi sallama

Tana fita NUR tace"miyasa kika hana in fada mata nan nike aiki da aka koreni"

Zakiya tace"ina ruwan ki da yan iskan nan da alamu ita ke da company in ta dauke ki babu Wanda ya isa ya Kore ki"

NUR tace"Allah yasa"

Misalin karfe 6:12pm aka sallame su"

NUR ta kalli TASLEEM tace"baby me zaki ci?"

TASLEEM tace".......



Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[07/06, 14:54] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers, we are the best among the rest.

dedicated to iya latifa
πŸ…Ώ1⃣9⃣&2⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

TASLEEM tace"ni naman kaza zan ci"

NUR tace"toh muje hanya in siya miki"

Zakiya tace"har dani zan ci"

Murmushi NUR tayi tace"sannu hajiya wanan kudin da kike gani gobe zan je in biyawa TASLEEM kudin makaranta da takardu ga islamiya"

Zakiya tace"dubu talatin ne ba zai hana mu cin kaji ba"

NUR tace"naji zan siya muku"

Zakiya tace"har da kema in baki ci ba bazan ci ba"

NUR tayi murmushi tace"toh naji madam"a hanyar su ta komawa gida suka siyi gasashiyar kaza

Suna kaiwa gida suka sa a tare suna ci

Zakiya tace"Allah yayi wa hajiyar nan albarka gashi sanadiyarta muci kaza"

NUR tace"amin"

Hira suke suna cin Kazan har suka gama

Da misallin karfe 9:00 na dare zakiya ta shirya cikin riga da wando jeans ya bala'in kamata dama yawanci irin kayan take yawan sawa

Kwaliya tayi sanan tasa takalmi a hankali ta tako zuwa inda NUR ke kwace hanun ta kai dai-dai fuskarta dan tabbatarwa ko tayi barci

Ajiyar zuciya ta sauke tace"Allah nagode ma da kasa tayi barci da yanzu sai ta rufe ni da wa'azi ta hana ni zuwa club"

A hankali take tafiya har ta fita daga dakin ta ja musu kofa

NUR dake kwance tana jin duk motsin zakiya har ta bar gidan girgiza kai tayi tace"Allah ya shirya ki"

A club ko zakiya sai rawa take amma babu wanda ya zo manna mata kudi kamar inda aka saba

Gajiya tayi da rawa ta koma gefe ta zauna

Wani gaye ne ya zo ya taba ta yace"babe muje mana mu huta ko nawa kike so zan biya ki"

Hararanshi tayi tace"ni ba irin matan nan bane"

Dariya raini hankali yayi yace"kar ki raina min hankali mana ai duk wata mace arziki ba a ganinta a irin wurin nan"

Tsaki tayi ta bar wajen wasu yan mata biyu dake kallonsu suka kece da dariya

D'aya tace"jibeta fa yar rainin hankali wai ita kamilla"

Ta biyu tace"ke dai bari ga ta da farin jinin bala'i kowa ya ganta sai ya kyasa jiya ma ba inda cash mony beyi da ita ba akan su je su huta zai bada dubu dari amma taki"

Zee tace"ai ta bani haushi wallahi"

Zakiya na barin wajen suka yi karo da wani gaye,fadiwa yayi har kasa da alamun ya sha giya ya bugu

Cikin masifa tace"kai baka gani ne?"

Tashi gayen yayi ya fara magana cikin maye sai rufe ido yake yana cewa"yi hakuri masoyiyata zo muje muyi rawa"

Kwace hanunta tayi tace"karka kara taba ni mashayi kawai"

Ai sai ya rike kunni shi yace"yi hakuri madam"

Inda yayi magana cikin maye sai abin ya bata dariya

Zuwa yayi yana rawa in ya fadi ya tashi sai dariya take

Girgiza kai tayi tace"kai giya baiyi ba wallahi"

Shiko cigaba yayi da rawa an taru ana mai dariya domin kwata-kwata baya hayyaci shi

Murmushi tayi tace"bari in ciro waya ta inyi video in naje gida in nunawa my NUR na San zata sha dariya"

Waya ta ciro ta shiga video ta fara kwashe shi tana dariya

Cikin rawa ya cire wando jikin shi ya rage shi da boxers ai sai aka fara ihu dan wajen su abin burgewa ne

In ka cire zakiya dake dariya tana kwasheshi a waya

Da ya gaji sai ya zube kasa yana kwarara amai har ya b'ata jikinshi har a wanan lokacin zakiya na kwashe shi

Barci ne yayi awon gaba dashi

Sai misallin 12:am

Zakiya tasa DJ sauketa a gida da shike sun saba dashi

Tana kaiwa gida tayi wanka ta dauro alwala ta tada sallah nafila a haka NUR ta farka daga barci ta gan ta

Tace"hmm fuska biyu"

Itama alwala tayi ta tada nata sallah

Washe gari da asuba suka farka suka yi sallah asuba harda TASLEEM dan duk asuba sai NUR ta tasheta tayi sallah

Da misallin karfe 7:00 suka bar gida sanda suka kai TASLEEM makaranta NUR ta biya mata kudi sanan suka tafi AFSAMAN building company
amma NUR taki magana da zakiya domin fushi take da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login