Showing 1 words to 3000 words out of 40654 words

Chapter 1 - MATAR TSOHO COMPLETE

30 Sep 2026

1422

*MATAR TSOHO..*

👨🏻

‍

🦳

👩🏼

‍

🦳

(_Ta gaban goshi_)

~part1~ 0

️

⃣

1

️

⃣

_the romantic book_

💗

{ ~a love story~}

*Nabilancy love*

💘

_Auntyn S and S_

*Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai, an fara rubuta wannan littafi ayau sunday. 06-10-

2024 Allah yasa mukai karshensa lafiya*

Wannan littafin k'irk'irarran labari ne ba'ayi shi Dan wani ko wata ba idan yayi dai-dai da wani b'angare na rayuwarka/ki arashi ne kawai aka samu.

✨✨✨

_______A hankali cikin Nutsuwa suke tafiya har su

ka zo inda zasu rabu Zuhta ta shigo gidan nasu, yayin da khairat ta wuce tunda ita nasu gidan da 'yar tazara tsakaninsu.

Da sallama dauke a bakinta ta shigo gidan ,tsayawa tayi Cak! hangen mahaifiyarta da tayi a gaban murhu tana ta fama da firfita wuta ic

en da take girki dashi yanata hayaqi da alama danye ko Kuma ruwan jiya da aka kwana ana yinsa yayi Masa duka, daga gefe ga garin tuwo nan tana tankadensa, da alamun Aiki ya kacame mata duk ta wahala, ga ba k'oshin lafiya gareta ba yau da lafiya gobe Babu

.

Sosai inna saude ta bawa zuhra tausayi ji tayi wasu zafafan hawaye sun zubo mata bisa kuncinta.bata gogeba saita dulmiya Dan guntun tunanin Daya zame mata jiki.

Inama mafarkinta na kullum ya tabbata,inama Allah ya cika mata burinta yakawo mata irin mi

jin datakeso ta Aura a kwana kusa,mijin kere sa'a irin sugar daddy dinnan,Wanda zai jikata da nera itada iyayanta ko da bashi da lokacin kamsa da Nata itakam zata iya sbd samun farin cikin iyayanta da ita kanta...sai ga hawaye Shar!!!!

A hankali tasa ba

yan hannunta ta goge,takanji Inama ita wata ce,inama tana da Hali da iyayanta basu Sha wahala ba kam,da ta gatanta su kam,Dan tun tasowarta take ganinsu awannan Hali Babu Wanda yake Jin dadin rayuwa cikinsu mahaifinta ya Nemo dakyar ita Kuma mahaifiyarta

ta dafa dakyar,tabbas da tana da kudi gas zata Siya mata don ta huta wannan hayakin.

Ta karasa shiga cikin gidan tana me karayin sallama

Kafin innar ta Amsa mata harta isa gabanta tai saurin tallafa mata wajen tayata firfitar wutar.

Inna taja gef

e tana kallonta tana mata Godiya da shi Albarka.

Aikuwa cikin iKon Allah a cikin sakanni zuhra ta dage sai da Taga wutar ta kama taci gaba da ci kana ta dago tana kallon innar da murmushi kan fuskarta tana fadin"Sannu inna, da alama itacen Nan sun Sha r

uwan jiya duba kiga wance har ruwa yake fita ta kasansa".

Dan murmushi innar tayi "ai kece da sannu zuhra, kin dawo lafiya? Naga yau kamar kun dawo da wuri".

Zuhra ta Amsa da cewa"lafiya qlau inna, ai kin San idan akaga da alamun hadari a garin basa Bari

a Kai biyar da rabi ake tashi saboda yaran da suke nesa ba'a San lokacin da ruwan ze tsaya ba, bari na karashen tankaden ki huta tunda na dawo zanyi miki tuwon Sai kiyi miyar kada ruwa ya sauko".

"To ai zuhra zama Bai kama ki ba ma,don mahadin miyar b

asu hadu ba zuwa zakiyi gun babanki ma ki karbo mana wani abun agunsa akarasa cefanen miyar Dan ko attaruhu Babu bare Mai da maggi kuka da wake kawai na Siya da yarinya takawo talla dazu a 'Yan canjin Dake hannuna".

Ajiyar zuciya Zuhrar taka kafin tace

"to inna bari naje gun nashi,Allah yasa dai da kudi ahannun nashi,tunda kika ga yau baizo mana ba alamu ya nuna Babu kanta shiyasa Bai leko ba,tunda Ubangidan nashi baya gari Amma bari inje din dai".

Tana gama fadin hakan ta gyara hijabin Dake jikinta t

a fice da sauri.

Inna ta bita da kallon tausayi saboda kafin ta tafi islamiyya ma zuhran ba wani abin kirki ta samu taciba gashi ta dawo bata huta ba ta aiketa Amma bata nuna komai ba tabbas bazata daina yiwa yarinyar Nan Addua ba saboda tana musu biyay

ya ga hakuri da hangen nesa ta daga hannunta sama tana me fadin"ya Allah ka kawowa yarinyar Nan Inda zata huta,Allah ka bata miji Nagari.

***** ***** *****

Tafiya take sauri-sauri tunda da 'yar tazara a tsakanin unguwarsu da inda mahaifin nata yake ai

kin gadin.

Sai da ta gama karewa katon gidan kallo tana aiyana inama itace acikin gidan,inama gidan mallakin ta ne ko na mijinta.

"Ajib du'aina ya Rabbi" ta fad'a a hankali tana Jin wani Abu Yana Mata Kai komo a Cikin zuciyarta, Bata Raina yanda Allah y

a yisu ba Amma tana neman tsari da talauci tunda Annabin Rahama yace mu nemi tsari dashi.

Bayan gama zancen zucin ne ta hau bugun kofar a hankali .

Yana zaune a bakin Dan dakinsa da yake kwana Akan benci yaji bugun.

Ya ajiye 'Yar radion Daya kunna y

ana sauraren labaren yamma na Aminci radio

Yakarasa da sauri yana tambayar "waye?".

Cikin sitiryar muryarta ta shige fadin nice"

Fad'ad'a fara'arsa yayi Jin muryar shalelensa ce da sauri ya bude mata kofar ta shige daga ciki tana masa barka da hu

tawa.

Bayan ya rufe Yar karamar kofar Dake jikin get din Wanda ta shigo ta ciki ya tararta ta zauna Akan Dan dandamalin bakin kofar dakin nashi.

Cikin maraukakikn farin ciki ya shiga fadin "ya Baki zauna Akan bencin ba.? Tashi koma Kai mana".

Mu

rmushi tayi Cikin Jin tausayisa tace. "Aa Baba barni anan din ma ina wuni, ya aikin ?

Ya zauna Akan bencin yana amsa gaisuwar tata yana tambayar ko taje islamiyya yau?

Tace "naje baba,sauka dai ta taho munkusa yin walimar sauka an tsaida Rana,sai

dai sun Saka mana kudi dayawa da zamu Kai saboda akwai ankon shadda da suka fitar ga kudin Allon zaiyana ga Kuma na hijab Shima da zamui iri Daya".

Ya gyada Kai yace "to Allah ya bani iKon Baki ki Kai musu,zai kai kwana nawa Nan gaba,?Allah yasa kafin N

an dai Alhaji yadawo garin'

Ta jinjina Kai tace"goma ga watan gobe ne.

Yayi dariya yace"Ah yo ai kafin Nan yadawo insha Allahu,saboda a satin Nan ma nake saran dawowarsa Dan ma ba waya a hannuna bamui waya ba kwana biyu Amma nasan Yana kan hanya in S

ha Allah tunda da iyalinsa ya tafi".

'To Allah ya dawo dasu lafiya, Baba daman Miya inna zata kada Kuma Babu komai a kasa sai abunda baza'a rasa ba shine tace inzo gunka ko za'a samu na cefanen miyar".

'To Bari mu gani Lamarin ne sai hakuri ga Mai k'ara

min karfi sai hamdala". Laluben aljihun wandonsa ya duba na dama yaji wayam

Saida ya laluba sosai ana hagun yaji kudi ya cirosu duka

Yahau kirgawa yaga Naira Dari biyu da hamsin ne

Ya bata yana fadin "ga wannan maza tashi kikai mata nasan dai b

a isa zasui ba Amma angode Allah Daya horesu din ma Kinga ko tafashi kada tayi,kota hada da karbar bashin wani Abu na miyar,insha Allahu inanan tafe da Alhaji yadawo zata ganni ki bata hakuri kinji,Allah yai mk Albarka kema".

Kudin ta karb'a tana fad'in

"Allahumma Amin Baba kaima ubangiji ya duba Lamarin ka".

"Amin ya Rabbi Fad'imat zuhuriyya"

Ta mike tana masa sallama.

Hon sukaji a bakin get ana dannawa ba kakkautawa karar ya cika koina.

Ai da rawar jiki baba isuhu ya tafi yana fara'a yana godi

ya ga Allah Ganin Alhajin ne yadawo.

Ya wangale get yana daga masa hannu da yi masa sannu da zuwa.

Adaidai wannan lokaci ne Kuma zuhra ta taho zata fita a gidan ta rabe a gefe guda ta basu guri don su wuce kana ta samu damar fita.

Shi kuma Alhaji

Wanda matarsa ke gefe cikin motar ya Kalli zuhra ya dauke kansa kawai.

Gaisuwar ma da zuhran ke miko musu sai matarsa ce ta Amsa.

Shi hankalinsa yai gaba dama shi ba ma,abocin kallon mata ba don indai gimbiyarsa na gefensa baya ta kowa sai ita.

I

ta dai zuhra ta fice Agidan tana ta zancen zuci ga wata faduwar gaba data sameta tun had'a Ido da tayii da Alhajin, saboda duk zuwan da takeyi wurin Baban Bata tab'a dacen ganinsa ba sai yau, innar ta Kuma ba mutum bace Mai shishshigin neman gidin zama bar

e ta cusa kanta wurin matar gidan, duk da ba wani Abu sukeyi na turo a gidan ba tunda taji baba Yana yawan fad'ar bashi da Yara Mai gidan Bai tab'a haihuwa ba....

*MATAR TSOHO..*

👨🏻

‍

🦳

👩🏼

‍

🦳

( _Ta gaban goshi_)

*Nabilancy luv*

💘

( _A

untyn S and S_)

~page~ 0

️

⃣

2

️

⃣

_the romantic book_

💗

{ ~a love story)

____ Har zuhra taje gida zuciyar ta tana bugawa da sauri-sauri abinda ya Bata mamaki kenan,dan ita dai a tarihin rayuwarta wannan shine karo na farko da taji irin wannan emo

tion din dan taga wani d'a namiji gaskiya, Kuma ita tayi mamakin ganin ubangidan Baban nata haka, ita fa ta d'auka irin dattawan Nan ne sai taga ba haka ta ganshi ba ai da suran yarinta a jikinsa gashi smart dashi duk da Babu fara'a a fuskarsa. Tsaki taja

a hankali

"To Ina ruwa na da smartness dinsa ko fara'arsa tunda ba damuwata bane" har tazo gida abin na Mata Kai kawo duk kuwa da k'ok'arin yakice shi da take k'ok'arin yi daga ranta.

**** ***** ****

Alhaji Hashim Hamshakin Dan kasuwa ne me kudi

sosai wanda sunansa yayi fice a Cikin da wajen jihar ya shahara kwarai da gaske,,Kuma mawadaci ne sannan me kyan Hali da tausayin Talakawa ga taimakon Wanda Bai dashi, Allah ya hore Masa taimakon na qasa dashi hannunsa a sake yake wurin badawa.

Duk Dan A

dam baya wuce jarabawar mahalicci, to Shima duk yawan dukiyar da Allah ya hore masa matsalar shi guda daya ce wadda take tab'a masa

zuciya, take Kuma yamutsa nutsuwarsa da farin cikinsa, itace ta rashin haihuwa.

Bai taba haihuwa ba,yana son yaga kwansa a

duniya Amma Ina Allah Bai bashi ba duk da bawai Yana da matsala bane. "A'a yaga manyan likitoci da dama akan matsalar gida da waje Amma kowanne zaice masa lafiyar sa qlau,ya Auri mata biyu matarsa ta farkon sukai tsahon shekaru goma Sha biyar da Aure tun A

uren saurayi da budurwa Bata tab'a ki batan wata ba. Allah yayi mata Rasuwa tayi mutuwar fujia sun kwanta tare Amma basu tashi tare ba don adaren ta cika Babu cuta kawai ajali.

Yaji mutuwar Hajiya Aliya sosai kafatanin Yan uwansa ba kusa suke ba,wasun s

u suna Meduguri wasu Kuma suna yobe wasu Yola Amma akwai tsiraru anan garin.

Kafin ya Auri matarsa ta yanzu da suke tare ya jima sbd shi mutum ne me qawaxuci idan yasaka mutum aransa da wuya ya iya fitarwa akusa,yana da saurin sabo da Kuma nuna soyayya

sosai Akan Abu,Hajiya Aliya sunyi zaman qalau tayi masa matuqar biyayya tasan ta kan yanda zata zauna dashi duk fadansa da saurin fushinsa tasan yanda take saukar dashi,ta lakanci halayyarsa da abinda yakeso da Wanda bayaso,ba,a taba Jin kansuba,yakaita ha

jji yakaita Umara ba adadi Da ace sun sami haihuwa da tuni sun Aurar in macece haka in saurayi ne da tuni ya tasa ya zama saurayi.

Shekarunsa sunja Amma sbd gayunsa da gyara da cin me kyau ga boko data Ratsashi Inka kalleshi bazaka taba cewa yakai sheka

ra hamsin ba, d'auka zakayi baifi irin arba'in din Nan ba.

Alh Hashim babban Dan KASUWA ne yana da plazozi a kasuwanni kusan uku, wasu ya bada hayarsu wasu Kuma yasaka kaya ya nada yaransa masu Amana Akai.

Ya kanje kwatano, Istanbul, Dubai, Saudia da

sauran kasashen ketare domin sarin kayayyakin da yake business irinsu yadikan maza Yan ubansun da shaddoji manya da atamfofi da lasa lasai da materials Kai har da mayafai ga turarika kala kala

Yawan fitar da zakka da taimako da sadaka da Yakeyi ne yasa

Allah yake Kara bunkasa masa Dukiya.

A gefe guda yana da gidan Mai me zaman kansa da reshikan ke a jahohi guda uku Kuma DUK akwai masu kular masa tamkar yana gurin.

Duk inda kaga gidan Mai me suna *A.A.H petroleum Nig LTD* to na Alh Hashim ne don tu

n bayan Rasuwar Hajiya Aliya Daya Auri Wannan matar tasa da yake matuqar ji da ita Wanda suke DiGa madarar soyayya ya bude wannan gidan Mai me farkon Harafinsu don kowacce da harafin A sunanta ya fara nashi Kuma da H,hakan yasa ya hade ya sakawa gidan man

nasa farkon sunan nasu sbd son da yakewa masu sunan.

A farko da Hajiya Aziza tazo gidansa taso ta nuna kishinta Akan yanda yake yawan ambato mata matarsa data rasu Hajiya Aliya,zance Daya ko biyu sai yasako ta.

Sai da tayi masa bore Akan bataso ya da

ina sbd ita fa tana da kishi sosai bazata lamunci aringa nuna anfison matacciya akanta ba

Tun da ya hade Rai bata sake ganin dariyar sa ba

Haka walwala ko farin ciki Shima ya daina mata.

Dakyar ta shawo kansa sannan ta bashi hkr.

Yace mata sai

dai tayi hkr bawai don taji haushi bane,sabo ne dayai da hakan sai a hankali zai rabu da kaunar sunan Amma tabishi a sannu

Hakan kuwa tayi ta ringa hkr dashi da halayyarsa har ta gano shi tasan Kuma wanene shi

A hankali Kuma tayi kokarin mantar das

hi magana ko batu na soyayyar matarsa Hajiya Aliya.

To zamansu dai yayi dai-dai ya zama sai yanzu yanda yake Jin kauna da dadin zama da Hajiya Aziza ko margayya baiji hakan ba.

Idan akace muku kissa da kanainaya da biyayya to angama in akazo gun Haji

ya Aziza.

Gata Yar wanka Yar kwatallewa, da kwalisa tasan kanta matuk'a gata da juriya yayin sex Sam Bata nuna ta gaji gashi Allah yayi Mata baiwa komai nata atsaye car!! Kamar bata taba haihuwa ba.

Duk da a bazawara ya Aureta haihuwar ta biyu Agidan

mijinta na baya Amma yaran basa zama mutuwa suke.

Shiyasa a yanzu da take tare da Alh Hashim suketa Addua da damuwa na rashin samun rabo

Anjejje saudiyya an roki Ubangiji sau ba adadi Akan dai son samuwar ciki

Duka a cikin shekara ta biyar da Aur

ensu

Har sun fidda Rai Sai gashi Babu zato Babu tsammani Ciki ya bullo a jikinta.

Aikuwa ansha murna,hatta likitan dayai masa Albishir na samuwar cikin Kujerar Umara aka bashi.

To da yake marainiya ce ba uwa ba uba shiyasa yake tausayin ta da kaun

ar ta sosai.

Haka itama aranar da akace tana da cikin Alh ajikinta har kuka tayi don murna sbd tana ganin Allah zai bata abokan shawara don har ta fidda Rai da samun 'ya'ya aduniya sbd batada kowa anan garin haka acan damaturun ma Daya Aurota ba wai dan

gin gareta rututu ba,ita Daya jal iyaye suka haifa suka Kuma rasu, sai dangin mamanta wasu da suke a chadi Kuma sunyi nisa sai dai a waya suke gaisawa

Wannan ciki na jikinta suna matuqar lelensa domin angama tsara ma ba anan za.a haifeshi ba, a India za

ta haihu tun cikin na wata biyar angama shiri na tafiya zatai renon cikin acan angama komai da likitan da zata ringa mata awo duk wata da gidan da zata zauna an biya kudin komai har zuwa a haihun.

Yasan dai India bazatai masa Nisa ba dayaji son ganinta

zaiyi viza ya tafi cikin sati guda inyaso.

Kafin lokacin tafiyar ya kaita Yola gun danginsa na can Dana Maiduguri har gun danginta zata zagayasu suyi sallama cikin satikan da zaiyi a tafiyar da zaiyi Dubai Shima zaiyi wani zama da wasu Manajoji na kamfani

acan.

To wannan shine dadewar da yai bayanan haka Kuma Daya dawo yaje ya daukota a Yola suka kwana Daya a hotel acan sassafe suka rankayo kano zuwa gidansa.

*******

A daren nan da suka dawo ga gajiya ajikin Alhaji Bai iya Aikata komai ba duk wata k

ewa da yai nata haka ya kalleta ya bar ta Bai iya tagaza komai na tarayyar Aure da Ita ba,duk son sa na Sex sbd Bai da kuzari gashi da saurin bacci sai jinsa tayi yana Jan rago (munshari)

Ita dama tsoronta naci na sex irin na Alh Amma tana son hutu taus

ayinsa kawai takeji da tai masa sabo gashi Kuma sunyi kewar juna sun Dade basu haduwa sbd ko kwanan hotel da sukai ba suyi komai ba.

A wannan dare mafarki Alh yayi da wata yarinya kyakykyawar gaske Amma daganinta bata da yawan shekaru wai gasu a garden

na gidan suna soyayya tana ta zuba masa shawagaba shi kuma yana biye mata duk ya susuce a kanta.

A yanda yake da son soyayya sai biye mata yake yana lallabata yana bata ice cream a Baki, Daya baya Kuma ya dauko zubunan gold da azurfa Yana saka Mata a duka

yatsunta, kallonsa tayi ta Kara shagwab'e fuska ta Fara k'ok'arin cire zobunan daga yatsunta.

Hannuwan ya rik'e Yana girgiza Mata Kai Yana fad'in.

"This is our Babies.....".

Yayi mamaki matuqa gaya Daya farka da Asuba Kiran sallah na assalatu ne da a

ke rairawa ya shiga cikin kunnensa ya tashe shi.

Firgigit yatashi yana Addua tare da mutstsika idonsa

Ya gaskata dai mafarkin ne,to Amma wacce yarinya ce hakan.? Me hakan ke nufi ne ga Wata mahaukaciyar desire data Kama shi, a hankali ya furta "ya S

alam....!.

Ya taba shigen mafarkin Nan fa,Amma na yau ya rikitashi da aka haska masa 'yar yarinyar Nan Kuma me kama da wacce yagani dazu acikin gidansa Daya dawo yatarar ta da me gadin gidan nashi,Wanda alamu ya nuna kamar wurinsa tazo Dan yaga lokacin

data tsuga tana fad'a masa wata maganar Cikin ladabi.

To shi dai yasan Gani Daya yai mata ya kauda Kai ganin ma daga nesa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login