Showing 3001 words to 6000 words out of 40654 words
to ya Akai har kamanninta suka tsaya masa Kuma har aka Kara nuna masa ita a mafarki.yaja tsaki ahankali ya juya ya Kalli madam dins
a yaga sai baccinta take hankali kwance.
Bai tasheta ba saida ya dawo daga sallah yake tashinta tayi sallar duk da garin' ya Fara haske.
Tunda ta samu cikin Nan ta tsiro masa da hakan shikuma lelen ciki yasa ya barta take sallarta a makare.
******
To bayan sati guda da dawowarsu ne tafiya ta taso
Tafiyar da zasuyi zai mata rakiya zuwa India
Wanda in ita ta tafi sai ta haihu zata dawo acan zai barta.
Jirgin karfe goman safe zasu bi
Shiyasa yake ta mata fada Akan tayi tayi ta fito su wuce
tanata bata musu Lokaci
Duk dokinta na son tafiya yau sai yaga kamar bataso
Ta fito ta koma haka take tayi ya kai sau wurin biyar tana shige da fice tsakanin falo da bedroom dinta
Sai tazo falo sai ta koma ciki tace tayi mantuwar Abu kaza.
Fad
ansa ya tsawaita har yana cewa da biyu take wannan wulakanci Dan ta bata masa Rai ne kawai.
Ta taho ahankali ta fada jikinsa tana fadin"haba mijina,haba hasken zcyta,haba Aljannata,ban isa in wulakanta rayuwata kaf! Ba,Dan Allah ka daina fadin hakan,a d
uniyata Babu kamarka Alhajina,Aduniyata Babu Wanda nake ji da Gani da muradi kamarka hubbina, bazanyi Abu Dan na bata maka rai ba,walh sai nashiga dakin sai in manta abunda naje dauka,inbanda ma da Kai zamu tafi da fasawa zanyi,Amma in kana ganin ko inayin
hakan Dan wulakanci ne Dan Allah ka yafemin...ta durqusa agabansa.
Yai saurin dagota ya mannata da jikinsa yana kissin lips dinta yana fadin" _never mine my wifey_ komai ya wuce mutafi kawai nima komai Dan ke nake yinsa,Ina sonki ne sosai.
Ta shafo
sajensa Daya kewaye masa fuska ya Kara haskaka fuskarsa da Kara masa zatin kyau tace"nagode mijina Ina sonka !
Yace"nima haka muje ko,Tara saura fa.
Ya rigata fitowa daga cikin dakin hannunsa janye da akwatin nata ta biyoshi abaya tana Jin faduwar ga
ba Amma bazata iya gaya masa ba kada hankalinsa yatashi Addua kawai takeyi kasa kasa, tazo ficewa daga falonsu na karshe kawai ta saka kuka Wanda ita kanta Bata San dalilin yinsa ba, gudun kada ya gani yayi Mata fad'a ta goge hawayenta ta fice tana Jin wan
i bak'on Abu a Cikin zuciyarta
Wani iKon Allah da ban mamaki Ashe Lokaci ne yayi nata,Ashe bazata sake dawowa cikin gidan ba,Ashe kallon karshe tayiwa gidan da me gidan duka a yau.
Don sun kusa zuwa filin jirgin sama ne wani Hatsarin ya faru abin sai
ka tausaya in kana gun,don wata babbar Tifa ce ta kubucewa matuqin Tayo kan motarsu Alhaji ta banke su,Wanda duk kokarin da Alhaji keyi na ganin ya subucewa Lamarin Amma abun yaci tura Saida tifar ta hayesu ta illata motar tasu Dasu kansu.
Domin a take
ko asibiti ba,a je ba Hajiya Aziza tace ga garin ku Nan,Alh Hashim Kuma a sume aka zaquloshi ackn motar tasu Dake kasan tifar Nan akai asibiti dashi...... Muje zuwa.
*MATAR TSOHO..*
👩🏼
🦳
👨🏻
🦳
( _Ta gaban goshi_)
~page~ 0
️
⃣
3
️
⃣
_the
romantic book_
💗
{ ~a love story~}
*Writing by Nabilancy luv* Auntyn S&S
💘
_____Taimakon Gaggawa aka bawa Alh Hashim Wanda sai da ya kwana a Asibitin kana ya dawo haiyacinsa yana farfadowa bakinsa dauke da sunan matarsa.
In kana gurin dole
zai baka tausai ne sbd yanda yake nuna yana son ganinta.
Ya rikita likitocin yana musu zancen Hajiya Azeeza don yana matuqar son matarsa haka zalika kuma yasan tana dauke da gudan jininsa ajikinta,sannan yana tausanta na yanda take marainiya Kuma gata
mace me iya lelen miji.
Duk yanda Akai ta boye masa Saida ya gano daga baya,sbd an shiga kwana na hudu a Asibitin suna jirgashi akan hajiyarsa na Emergency room zai ganta Nan da kwana biyu,sai Kuma gashi labarin mutuwarta ya riskeshi alokacin da suka ga
ya fara samun lafiya don yana Gane mutane haka zalika ba wata lalura da take damunsa Wanda zai rikita masa lissafi inyajin.
A zatonsu ko zai jure zai nuna jarumtaka sai gashi yana musu kuka wiwi Yana fadin ya shiga uku yayi rashin mace tagari me kauna
rsa tsakani da Allah.
Sukaita bashi Baki da rarrashinsa Dan ya kwantar da hankalinsa.
A dole sun sallameshi sbd ya samu nutsuwa aguri guda sannan yaje yai zaman karbar Makokin matarsa.
'yan uwansa na Nesa sunzo mata da maza saboda Suma labarin mu
tuwarta ya girgizasu ba kadan ba tunda ttaje musu sallama Ashe ganawar ta Kare, kalilan ne Basu Samu zuwa ba,haka zalika itama nata 'yan uwan na Nesa wasu Kuma da suke nesa sosai 'yan chadi Tasha Addua daga can inda suke.
Bayan sati biyu da Rasuwar Ha
jiya,Alh hashim yana zaune ne kawai ba uuhhumm ba A,a ba ci ba Sha sai an masa Dole.
Sau Tari ma da aka watse din da me gadinsa kawai suke zama,Wanda Me gadin nashi ke debe masa kewa da hirarraki da tausarshi in yaga ya shiga damuwa, don bini bini zaiyi
tagumi ko ya hau sambatun maganar Hajiya Azeeza Tana masa kaza bata son Taga yana halin damuwa,bata yin kaza da kaza sbd kar ta bata masa,yakan dau tsahon mintina yana yabon kyawawan halinta Wanda baba me gadi ne kawai yasan ta yanda yake bi dashi yake da
wowa dashi haiyacinsa.
Bayan sadakar arba'in ne aka shiga kawowa Alhajin tallar hotunan Mata zawarawa da 'yan Mata Suma a can gida adamawa da Maiduguri duk sun matsa lamba ya koma gida yayi aure tunda yayi biyu a Nan duk Babu gashi abunda ake rad'e-radin
baya haihuwa ya kau tunda marigayiya da juna biyu ta rasu, duka dai Babu inda ya bada fuskar amsar tayin da akayi Masa.
A yau ma suna zaune Alh na kan farar kujera a farfajiyar cikin gidan,shikuma baba me gadi yana zaune Akan tabarma akusa dashi
Hira
suke Amma can Baba megadi yaji shiru Alh ya dauke wuta.
Baba Isuhu Yana kallon fuskar Alh yaga hawaye na zubowa Akan kuncinsa kana yaga ya zuba uban tagumi hankalin dai baya tare dashi.
Baba Isuhu cikin tausayawa yahau fadin " Subhanallahi! Wannan A
bu da me yai kama ace Abu ba zaiyi sauki ba,maimakon yai baya saidai yai gaba?! Haba Alh Kai fa yaka mata ka fada a dauka,kayi fada ajika,meyasa kake neman kassara kanka ne,Alh Kullu Nafseen fa zaikatul maut,dukkan Mai Rai saiya dandani dacin mutuwar Nan,w
ataran muma fa 'Yan zamu koma ga mahalicci, ai yanzu Addu'ar ka take bukata ba kuka ba, meyasa bazaka ringa yiwa Hajiya Addua ba?ai yanzu Adfu'arka tafi tunane tunanen da bazasu bulle maka da kyau ba...."
Kai .Alhajin ya hau girgizawa yana fadin"Baba baza
ka Gane ba,bazaka fahimci yanda naji a mutuwar Nan ba ne,rayuwar nake jin ta kassara Kuma kamar na tashi daga Aiki,walh Baba Gani nake bazan sake samun mace tagari kamar ta ba,Gani nake daga kanta nagama Aure domin.....da sauri Baba ya dakatar dashi yana f
adin"Daina fadin haka Alh ai kamar ma yanzun ka fara Aure,sbd nafarko ba tsofewa kayi ba,ko Ayanzu zaka dau budurwa,haka zalika baka ajiye Kwan ka a duniya ba kaga kuwa yanzu ne ma zaka fara fafutukar iyali tunda Allah yasa da Kwan haihuwar ai lokacin Bai
kure ba, ayi Addu'a a nemi zabin Allah duk abinda yayi Babu sabon aiki da dalilin yinsa sai dai muce Allah yayi musu Rahama yasa can yafi Nan"
Alh ya tsaida idonsa Akan baba yana fadin"bana Jin zan samu macen da zata so ni tsakani da Allah kamar Hajiya A
zeeza,Ina tsoron mata baba,matan ma Manyan mata sbd nayi Auren irinsu abaya banji Dadi ba lokacin sun fitini Aliya,haka zalika yawancinsu idonsu a bude yake to yanzun idan nace zan
Auri yarinya me karancin shekaru ma Ina zanje nemanta? Wa zai yarda ya bani
Alhalin ga shekaru sun fara baiyana atare Dani?"
Baba Isuhu yai Jim kansa a kasa Yana nazarin abinda bakinsa ke son furtawa Yana kwabar zuciyarsa akan hakan kafin ya Sami k'arfin gwiwar dago a sukwane, yace da Alhaji cikin murya Mai rauni "Ni zan baka
'ya ka Aura inhar zaka iya had'a zuri'a Dani ka kuma rike min bisa Amana,inhar bazaka Raina ba zan maka wannan kyautar zan baka Auren 'Yata ZUHRA...
Alh ya zaro idanu yace"to fa! Dama kana da 'ya budurwa ne Baba Isuhu? Shin da gaske kunnuwa ne ke jiye
min ka aminta zaka bani Auren 'yarka ko mafarki nake.?
Gyara zama baba yayi kana yace"Ina Alhaji yake?.
Alh Hashim yace "ga ni baba.ina tare dakai.
Baba Isuhu yace"Zan baka Auren ZUHRA saboda mu Kara danqon zumunci tsakaninmu,haka zalika saboda t
ausai na halin da kake ciki da Kuma ganin dacewarku da ZUHRA don nayi Amanna da cewar zakai dace da abinda kake ganin ka rasa zai dawo maka,ZUHRA me biyayya ce haka zalika mace ce ta gari ce insha Allah,ni na haifi ZUHRA 'yar cikina ce Kuma ita kagani kwan
aki tazo gidannan karbar saqo guna aranar daka dawo daga tafiya, ka Samu lokaci saika ganta idan Allah yasa tayi maka shike nan kafin dai Allah yasa hankalinka ya kwanta kaga wadda tayi maka ai ka rage zaman kadaicin da kakeyi bana Jin dad'in ganinka a hak
a".
Alh Hashim riskar kansa yayi Cikin wani Hamshaqin farin ciki,yaji wani Haske ya bayyana ackn duniyarsa,wata annashuwa ta dira ackn Kirjinsa tabbas yana fatan hakan ya zamo Alkairi domin juma,ar da zatai kyau tundaga laraba ake ganeta,take Kuma sai g
a hoton fuskar yarinyar ya bayyana yana yai masa gizo
Tana kallonsa tana zuba murmushin sace zcy,sai ya hau murmusawa shi kadai yasan me yakeji a wannan lokacin
Sai yanzu take Jin takaicin rashin tsayawar da yayi a ranar da take gaishe su daya tsay
a ya amsa gaisuwarta,ya tuna yanda ya basar da ita yai mata biris ko gaisuwar bai amsa ba sai yaji wata Nadamar hakan ta shigeshi don yasan bataji dadin abinda yai ba. A ckn yar nutsuwar Daya samu saiya gyara zama ya Dubi Baba bayan ya tattara hankalins
a waje daya yana duban baban "Na amince baba,indai tsatson kace to na aminta nasan zatayi nagarta in Sha Allah. To Amma Baba wani hanzari ba gudun ba, kana ganin bazamu tilastata ba duba da shekaruna ita Kuma yarinya qarama? ......muje zuwa
*MATAR TSOHO
..*
👨🏻
🦳
👩🏼
🦳
(_Ta gaban goshi_)
~page~0
️
⃣
4
️
⃣
_The Romantic book_
💗
{ ~alove story~}
*Nabilancy luv*
💘
Auntyn S&S
Farin ciki ne marar misaltuwa ya baibaye Baba Isuhu na Jin Alh hashim ya aminta da qudirin Daya kawo masa na A
uren zuhra.
Cikin gurmamawa irin ta ubangida da yaronsa duk da ba wata tazara bace Mai yawa a tsakanin su sai dai Yana yin Babu data danne Baba isuhu shine zakaga kamar tazarar Mai yawa ce. Yace "Hana Alhaji ai ko wuta nace zuhra ta shiga matuk'ar tasan
bazata cutu ba Kuma zanyi farin Ciki zata shiga to ballentana maganar aure, sai ko daga b'angarenka Amma Ni dai na baka kayi Shawara kome kenan Kuma sai naji daga baya tunda Gaggawa aikin shaidan ne".
Tabbas kowanne bangaren anyi dace su sun dace shi ya d
ace Dan ko Banza yasan Ranar daina gadinsa ya kusa,wahalarsa tazo karshe Dan yasan Alhaji bazai bari yaci gaba da zaman gate ba.
Cikin nutsuwa Alhajin ya dubi Baba isuhun Yana Dan murmushi "Haba malam Aiko daga makotanka ka yaba da tarbiyyar yarinya kayi
min magana a irin wannan gabar bazan watsa maka k'asa a idanu ba, ballantana 'yar cikinka kai Dana zauna da Kai shekara da shekaru ban tab'a samunka da wani Abu na ashsha ba,to Ni kuwa Idan ba marar gdyr Allah ba yaushe Zan maida hannun kyauta baya, nagod
e jazakumullahu khairan Allah ya bani ikon tij'ata amana".
"Alhamdulillah naji Dadi matuqa gaya Alhaji Ubangiji ya tabbatar da Alkairi kaga ba sai an dau wani dogon Lokaci ba tunda ba wata bidia za.ai ba kawai ma tunda saukar su ta Karato sai a daura Aure
n aranar saukar tasu, ai hakan Bai Zama da takurawa ba ko?".
Ajiyar zuciya Alhajin ya saki kana ya murmusa yace"Ashe yarinyar Hafiza ce Kai Masha Allah naji Dadi sosai Allah ya Albarkaci lamarin Hakan yayi,kada kace zaka wahalar da kanka wajen yin wasu
wahalhalun kayan Aure Baba,wannan duk nauyin yana kaina ko da ba ni zaka bawa ita ba,zan iya daukar wannan Ragamar,Zan Bada kudin komai da komai haka zalika akwai komai a gidannan sabbi ne kaga ba sai tazo da komai ba inba kayan sawarta ba,gidan Nan ma ba
dadewa zamui Aciki ba da zarar nagama ginin da nake na GRA zamu koma,kaima insha Allahu a ranar da aka Daura Auren ka gama Aikinka koma ince daga Rana irin ta yau ka huta kawai baba,inyaso inma jari ne sai in baka ka kama wata sana'ar ka nutsu wuri Daya za
muyi maganar dai Amma kayi Shawarar abinda zaka ringa sayarwa ko Kuma na nemar maka rumfa a Cikin kasuwa a fara muga abinda ubangiji zeyi".
Dadi ya cika baba Isuhu ya kama Baki yana fadin"Tofa! Masha Allah. Alhaji ayi haka Kuma ai duniya saita zageni
ace sayar maka da 'yar nayi, haba tsakanin mu ai Babu haka, itama sadaki kawai zaka bada sauran kayi Mata a gida".
Girgiza Kai Alhaji yahau yi yana fadin"ai ko me nayi baba ban biya ba,ka gama min komai nasan akwai kauna da Amana atsakaninmu ba kowa zai i
ya min abinda Kai ba,nasan saboda Allah kayi kuma don tausai na Nima kaga dole ne naga na kyautata kaidai kasawa Abin Albarka shine kawai.
Baba Isuhu yace"To shikenan,Ubangiji ya tabbatar da Alkairi yasa ayi a sa,a
Alhaji yace "Amin baba.
*****
***** *****
Ai fa innar ZUHRA ba karamin farin ciki tayi da Jin wannan labarin ba.tayi ta godiya ga Allah domin 'yarta dama ba zance take ba,zuhra bata kula kowanne saurayi tunda tayi Candy take zaman gida inba islamiyya ta fita ba bata zuwa ko kofar gi
da,ita Kuma ba wasu kawaye take Tuammali dasu ba hakan baya yiwa Inna saude Dadi saboda tasan inba fitar take ba to a ina saurayi zai ganta yace yana sonta har ayi Aure.
Tasan inhar ta gayawa zuhran wannan labari itama zataji Dadi tunda ta fahimci yarin
yar batajin dadin yanda suke cikin quncin Talaucin tasan Kuma zatai Amanna da Alh Hashim tunda ba wani agabanta.
Saidai Kuma kash!ba wannan tunanin ne na inna ya dore ba,domin bayan ta gama sauraron abinda ke tafe da innar har innar ta Dora da fadin"Kin
ga Amincewarki itace Jin dadinmu,yardarki itace farin cikinmu,Aurenki da Alhaji Kuma shine zuwan samuwar Warakar mu.....Cak! Innar taja Tunga da kalamanta na ganin zuhran tana zubarda hawaye
Inna Tasha mamaki don bata kawo za.ai hakan ba domin kuwa 'ya
rta me hakuri ce da son abinda sukeso Amma saita dafa kafadar zuhran tace "ya Akai diyata,?me ya saki zubar hawaye.? Nasan dama bazaki so Alhaji ba sbd shekarunsa,Amma Ina me Baki shawara Akan gara ki aminta da wannan hadin don zaki fi Jin dadin zama da m
e tarin shekaru Akan zama da yaro danyen jini awannan zamani. Tabbas ni da nake mahaifinkiyarki naji dadin wannan lamarin na Kuma aminta Ina fatan kema zaki aminta,Dan Allah karki watsawa mahaifinki kasa a Idanunsa.
Jiki a sanyaye Zuhra ta Kalli inna ta
ce"inna bazan taba qin abinda kukeso ba,bazan ki karbar tayin Nan ba,ko bana so zan zauna da Alhaji har muddin Rai,farin cikinku shine nawa Farin ciki ne yasani kuka bawai wani Abu ba,kicewa Baba na Amince.
Inna tahau Saka mata Albarka tana mata godiya.
Da baba yaji Abinda tace Shima yaji Dadi yaita shi mata Albarka washe garin ma ya wuni Agidan yana bawa zuhra Baki da kalamai masu kwantar da zcy Akan Alhaji.
Tun daga ranar Alhaji ya dakatar dashi Akan Aiki ya fara hutawa daga ranar yace zai canza
me gadi,ya shaka masa kudi na sallama wai kafin a Gama kwaramniyar biki Kuma ya Fara fita kasuwa .hakan yaiwa baba dadi saidai akwai sabo Dan sun Dade da Aalhajin.
Kuma ya tsaida ranar da za Azo ayi musu Aiki acikin gidan za'ai plasta da daben tsakar g
ida da fenti dama gidan Duk ya wahala gidan kasa ne.
Haka zalika a ranar da zai kawo kudin Aure aranar yace ayi mata Albishir kan cewar zaizo gunta su gaisa.
Da baba ya gaya mata hakan ta Amsa Ckn sakin fuska Amma acan kasan zcyrta ba murna take ba s
bd Babu son Alhaji ack,ita kam ta amince ne kawai sbd su Amma kam bata shiryi Aure awannan Lokaci ba duk da qudirinta na Auren sugar daddy to Amma aranar farko da suka hadu taganshi saitaga kamar
zaiyi wulakanci duk da Bata tabajin babanta yakawo kushensa
ba,to ko zaman hkr yake dashi ne,?sbd alokacin Data gaidashi fa bataga fuska ba,kai ita tsohon datake son Aure ma Wanda yafishi ne ko shekaru ko arzikin.
Dama burinta karatu me tsayi da ace suna dashi knn,tabbas da Alhaji zai barta tayi karatu sosai ara
yuwa da ta soshi kam,Ita tafi kaunar tayi karatu Amma tunda Hakan ta kasance zataso ta samu cigaba agaba.
*****
A kowanne bangaren aka fara shirye shiryen Aure,gidansu zuhra Dangi kowa murna yake idan akaji Wanda zata Aura don Ansan irin Arzikin Alhaji d
on ya shahara sunansa ya zaga gari haka zalika Ansan wanene shi don yana taimakon marasa shi.
Shima anashi bangaren haikan ya fara Shirin angwancewa shida wasu tsirarun danginsa na jiki jikinsa da abokansa suketa shirinsu,gidan sake fenti sannan an fidd
a tsoffin kayan duk da ba wani dad'ewa sukayi ba, ganin