Showing 24001 words to 27000 words out of 40654 words
da lafiya ne tunda ka fada min tana da juna biyu, gashi ba sanin Kan gidan
nayi ba bare na hauro naji ko da damuwa ne".
"A'a ba komai kinsan Baby Bata fiye son abinci ba Saida na Dan lallaba ta".
"Ayya! Sorry".
Iyabo ta fada tana nufar zuhra wadda ta Dan zauna akan hannun two seater.
Wani irin kamshi ne yayi Mata sallama a ha
ncinta Mai azabar Dadi sai taji nata turaren da take gani ya Kai ya kawo ya dusashe kamar Bata saka komai ba, taso ta rungumeta zuhrar taki hakan ta Mika Mata hannu tana fad'in "Sabahul khair ya ukty marhababiki".
Zukudi Iyabo tayi Dan ko za'a kasheta Ba
ta San abinda zuhrar ta fada ba.
Dan murmushi Alhajin yayi ganin Iyabo ta rasa abin fada.
"Gaisheki tayi kin San Babyn tawa balarabiya ce Kuma baturiya".
Wani quta taji aranta wani dunqulallen kishi Daya tsaye mata arai ya narke mata ya gudanya ya shi
ge cikinta saida ta dafe gun cikin kissa tace"Ayya sorry my sis,good morning.
Murmushi zuhra tayi ta kama hannunta tace mata"karki damu inajin hausar ma,fatan kin tashi lafiya,ya bakunta.
Iyabo tace"Lfy Alhamdulillah,yakamata ace kina karyawa da wur
i Aunty saboda bake kadai bace,gashi lokacin yin Kari zai wuce muje dining an gama shirya komai fa.
Akaro na biyu zuhra takara murmusawa tace"to ba komai za,a daure aringa yin Hakan nagode.
Kafin iyabo ta sake yin magana akaro na biyu har Alhaji Yaja
abarsa sunyi dining Arear.
Iyabo tabi bayansu idonta akan kyakykyawan hips din Zuhra dayafi nata kyan tsari.
Aranta tana aiyana wannan rawar jikin da Alhaji yakeyi akanta bawai iya sbd kyan jikin zuhra da kyanta bane da alamun tana hada masa da asir
i hhuumm tana tsoron Hausawa fa bare Yan Kano da ake yawan Bata labarinsu na iya rike miji da sanin siddabarun wasunsu duk da ance mata wai akwaisu da tsayawa tsayin Daka na yin Addua ita kam zata bawa KANAWA mamaki Dan bazata bari wannan yar yarinyar ta g
agareta ba saidai ita ta gagareta don Babu ragwage a Lagos sbd su da arnan kan dutse suke ta,ammali dole ne ta Kara zage damtse bazatai sanya akan Alhaji ba.
Don ita Abu biyune yasa ta Aureshi dadewarsu tare tana mugun sonshi Yana mata wulakanci taci Al
washi akansa,da Kuma kudinsa,tana son saita tatseshi sosai ta haihu dashi itama ko zata samu gado.
Bata a haiyacin ta suka gama breakfast din sbd yanda Taga iskancin shagwabar da Zuhra keta zubawa Alhaji shikuma Yana karba a jikinsa take duk ta narke ma
sa wai abinci kadan zataci shikuma yanata mata dole Yana Bata abaki
Daurewa kawai iyabo tayi na zama agun daga karshe ma ta tashi tayi dakinta ranta abace.
Amma adaren data shiga dakinsa ta fara wani bubbutsarewa tana son yaga fushinta inya tambaya t
ace masa akan abinda sukai mata ne da safe.
Aikuwa Daya Ankara da yanayinta sai yace mata ko batada lafiya ne.?
To anan fa ta narke masa harda kuka wai itakam abinda yai akan zuhra bataji dadiba da alamun bazaiyi adalci atsakaninsu ba.
A maimaikon
ya rarrasheta tunda amarya ce AA sai ya hade Rai yace mata indai bazata dauke ido tayi hkr akan duk abinda zaiyi ackn gidansa da matar sa ba to ita ranta zaita Baci abanza.
Tayi sakato tana kallonsa yanata fada na ba gaira ba dalili,da alamun asirin da
akai masa ya bar jikinsa tun ba,aje koina ba.
Taja ajiyar zcy tace"to kayi hkr ranka ya Dade.
Da dare Tasha kayan bacci tana kwance ajikinsa bayan dawowa daga duniyar jin dadin Aure tana masa Shafa tana fadin"Amma my love naji kamar kana waya kana c
ewa madam Dinka ba,anan zata haihu ba meyesa ka zabi Hakan?
Kai tsaye yace mata"saboda matsayinta ya wuce misali araina sannan Dan so za.a Haifa min ne shiyasa nakeso su samu kulawa dukkansu ban gamsu da kulawar likitocin Nigeria ba.
Cikin jin haush
in maganarsa tace"gaskiyane lokacin Abu ayishi.
Bayan kwana biyu yazo mata da batun wai xaikai madam gidansu zasuje suyiwa iyayanta sannu da zuwa sun dawo daga Umara.
Ta Dade tana tunani bayan tafiyarsu ashe kenan Dama Yar masu kudi ce kenan shiyasa
yake fifitata yake mata wannan rawar jikin,to amma duk kudinsa Kuma?
Tasha Alwashin koma dai meye zatai ta bibiyarsa taji shin wacece zuhran.
****
Satinta biyu da zuwa gidan bakin kishinta muraran ya fara fitowa ko magana saita Daina yiwa zuhra Dan Ta
ga da gaske mijin na hannunta,ko fushi tayi dashi agaban uban kowa zai nuna zaucewarsa Yana rawar jikin akanta haka zalika indai zatai magana akanta marar dadi yanzun ya nuna mata bacin ransa,bakin cikin ta ma zuhrar Bata shiga shirginta ko saukowa tayi ka
sa Bata sakewa suyi doguwar magana shiyasa kawai ta dauke mata.
Amma tayi kokarin janyo Abula me aikinsu ta nuna mata kudi sosai danta Aminta da ita ta samu hanyar da zata cuci zuhra tunda saida na jikinka
akafi saurin cutarka ita Kuwa Tasha Alwashin sa
ita zama sanadin fitar cikin jikin zuhra.
Ranar wata laraba girkin zuhra ne ta sauko kasa sbd ta bawa Masu Aiki umarni akan abinda zasu dafa agidan ita Kuma tayiwa Alhajinta special cook Wanda Bata yadda suyi masa ita keyi don ya Saba da girkinta.
Ka
wai taji anbangajeta takusa faduwa Amma data dago kai Taga iyabo ce sai Bata kula taba don batada lokacin yin fada da kishiya bare ba ita kadai bace.
Tayi tsammanin iyabon zata Bata hkr saitaga tai mata banzan kallo ta wuce abinta.
Murmushi tayi kawa
i aranta tace Allah ya kyauta wasu yaren dai ba tarbiyayya data ido.
Iyabo tayi zaton ko zuhrar zata gayawa Alhaji saitaji tsit baice mata komai ba
Sai Ranar girkinta suna kwance tanata masa ya. Wasanni na welcome na b4 sex sai ta rage murya tace ma
sa"wai my love iyayan zuhra masu kudi ne da naji sunje Umara? Gashi kamar kafi Nan Nan da ita akaina ko dai kai yaron babanta ne?
Dariya yayi Baisan bugun ciki bane ya saki Baki yace"Ah haba Dan Ina yaron babanta Kuma sai akace zanyi banbanci atsakanink
u,to ba haka bane asalima babanta shine yayi gadin gidan Nan nawa alokacin da ban Aureta ba shekara da shekaru munyi zaman qalau da Amana dashi tun matata ta fari data biyun da suka rasu Ina ganin mutuncin iyayanta Saudiyya ma ni na biya musu sukaje kema i
dan da Rabo zan biyawa naki agaba.
Ajiyar zcy taja ackn ranta tace"waw anzo wajen.
A fili tace"kai Amma nagode Allah yakara arziki.
Yace Amin.
To fa tunda iyabo taji wannan Batu saita tsiri yin habaici wa zuhran intaga ta sauko.
Data ganta t
a sauko main falo saitazo kusa da ita ta zauna suyi shiru ba Wanda zai tanka
Daga baya Kuma sai iyabo ta kashe kayan kallon tana fadin "arziki daga sama ne dai Munsan komai ba sabo akai da Jin sanyin AC ba saida mukaxo gidan miji,bare kallon ma anan mu
ka Saba.
Zuhra najin Hakan take mikewa ta haye sama Bata ce mata uffan duk da batasan nufinta na fadin mata wadannan maganganun ba.
Sai aranar da girkin zuhra ya shiga ta fito kicin kenan da saurinta tanason taje bedroom dinta takira Alhaji tace yata
ho mata da fruit Wanda duk Ranar girkinta take shanshu yau ta manta Bata bashi sallahu ba sbd
sun kare a firji shikuma saita bukata yake kawosu sbd iyabo Bata damu dasu ba
Kawai taji an bangajeta da karfi saida takai kasa.
Yau hakurinta ya kare tana
dagowa takai hannu zata Mari iyabo sai iyabon tai saurin gocewa tana mamakin zuhran tana fadin"kut'!ai walh karki sake kice zaki Dora hannunki akan fuskata Dan walh saina rama kasa kasa zanyi dake banza jaka ballagaza yar me gadi.
Wa'iyazubillahi!kan z
uhra yadauki juyawa tashin hankali Wanda ba,asaka masa Rana,ta Kalli iyabo da kankantattun idanunta cikin bacin rai tace"ki iya bakinki.
Iyabo tayi guda tayi juyi tana fadin"idan ban iyaba me zakiyi?walh duk makirci da asirinki Baki Isa ki gagareni ba,K
uma zama Daram acikin gidannan Dan haka walh inma Dan kina da ciki kike mana fi'ili to Munsan komai don talauci ne yaiwa iyaye yawa aka likawa me kudi hahahahah Auran sadaka kawai.
Rintse idanu zuhra tayi ta kasa jurewa saiga hawaye.
Ta Bude ido tana
niyyar ta kwabawa iyabo magana daidai ita sai Taga wayam har ta bar gun.
Tayi baya da sauri ta dafe jikin bango tana kiran sunan Allah tsabar tashin hankalin ma sai ga wani Abu dataji Yana fita ta kasanta
Danshin da taji agabanta ne yasa ta shiga ta
shin hankali ta kwala Kara tana kiran ladidi da take can kicin tana aiki....
Wayyo atara agaba.
Muje zuwa.*MATAR TSOHO.*
👨🏻
🦳
👩🏼
🦳
(ta gaban goshi)
The romantic and love story
*Writing by Nabilancy luv*
💘
Auntyn S and S
Page
14
Karar ihun da Zuhra keyi ne ya Ankarar da Ladidi me Aiki ta firgice ta dire wukar hannunta da take yanka alaiyahu,ta yunqura zata fito akicin din knn Kuma sai tajiyo muryar uwar dakin nata tana kwalla mata kira ai a rikice ta Kara gudu Wajen fitowa
falon.
Hankalin Ladidi yatashi mutuqa gaya ganin zuhra a durqushe ackn wani Hali tana dafe da ciki ga jini na bin kafarta.
Da sauri taje ta rikota tana fadin"wayyo Allah Aunty me zan gani,meya faru dake haka.?
Zuhra ba Baki sai yarfar da hannu kawai
tana ciccijewa sbd cikinta ne yahau murdawa take.
Ganin haka yasa Ladidi ta koma kicin ta dauko wayarta tahau kiran murja don ta sanarta.
Alokacin murjar na tare da Mijinta ALH Nasidi suna tafe akan hanya sundawo daga shopping
Murja ta tsorata j
in ladidi tace mata ga halin da zuhran take.
Ai ALH Nasidi ba shiri ya juya akalar motarsa ya nufi gidan ALH Sadin saboda su kaiwa Zuhra taimakon gaggawa.
Asibitin da suke zuwa can suka kaita aka karbeta emergency aka Bata taimakon gaggawa cikin kula
wa
Murja tace da mijinta"honey ka kira mijinta ka sanar masa mana plz,ni walh Tsoro na ma kar ace cikin Nan ya bare,sbd anata murnar samunsa gashi lokacin zuwansa duniya yakusa Allah Sarki Zuhra natausaya mata Allah ya tsayar mata da wannan masifa dai
da take tunkarota.
Alh Nasidi yace"Amin dai,ai nakirashi fa Bai daga ba,lokacin da kika shiga gidan fito da itan,inaga ko yashiga meeting ne zai kira ni inyaga ni.
Murja tace"to ko me ya assasa mata Hakan?
Alh yace"koma meye ai likita zai fada.
Cikin awa Daya komai ya daidaita agame da Zuhra likitocin sunyi iya bakin kokarinsu na ganin jinin ya tsaya Kuma cikin iKon Allah cikin Bai fita ba yananan,Dan haka kafin wani lokacin an Kara mata jini leda biyu.
Na biyun yakusa karewa su murja na rece
ption saiga kiran ALH Sadi awayar ALH Nasidi ya biyo Daya ga missed call dinsa har biyu.
Kai tsaye ALH Nasidi yace masa duk inda yake yataho yanzun Asibitin D.H.City work matarsa na kwance cikin wani Hali.
A kidime ALH Sadi yace"wacce matar tawa.?
"Uwar gida ce take zubda jini,me aikinta ta kirani intafe ahanya da madam shine muka garzayo da ita asibiti Kuma cikin taimakon Allah....
Katseshi yayi a rikice "wa'iyazubillahi!Allah yasa dai cikin Bai zube ba.?
Alh Nasidi yace"A'a ka kwantar da h
ankalinka yanzun likita ya tabbatar mana da ciki yananan Amma ana mata Karin jini.
Ajiyar zcy ya sauke Yana fadin"Nagode ganinan.
*****
Ko dayazo Kai tsaye office din likita ya zarce shi da Alhaji Nasidin suna son suji musabbabin ko wani Abu Tasha Y
aja mata Hakan.
Likitan ya kwantar musu da hankali Yana me sanar musu ciki yananan qalau da alamun tsautsayi ta gamu dashi dai na bugewa ko dai faduwa inta tashi a bacci sa tambayeta sbd su a gwajin da sukai mata basuga ko wani Abu Tasha daya haifar da
problem din ba,magunguna ya rubuta musu kana yace akula sosai saboda komai zai iya faruwa da cikin yanzun ma Allah ne ya tsare Dan da ba,ai saurin kawota ba zai iya fita.
Jikin ALH Sadi a sanyaye suka fito a office din likita suka nufi dakin da aka kwan
tarta.
Bacci take abinta fuskarta tayi fayaut tayi wani kyau hancin Nan yakara fitowa ga cikin yai mata kyau Dan ma batada girman ciki.
Ya qura mata idanu Yana aiyana da cikin Nan ya zube da kwana zaiyi kuka Dan bazai iya jurar hkr a lokaci guda ba.
Alh Nasidi yai masa sallama yatafi Yana me bashi shawarar adakatar ta da Aiki kowanne irine tunda tana da Yan Aiki sbd gudun matsala agaba.
Sukai sallama Alhaji Sadi na Kara musu godiya,Murja tace Zatazo gida tunda yau za,a sallamesun.
Yana zaune
agaban gadon idonsa akanta har jinin ya kare,Bai yadda ya sanar agidansu ba,yasan hankalinsu ne zai tashi dama wayarta ma akashe take tunda Shima yakira yaji akashe Daya fito a meeting kafin Alh Nasidi yakirashin.
Wajen magriba bayan Allurar baccin da
akai mata ta saketa ta Farka da addua cikin Ranta.
Tana ganin Alhajinta akusa da ita saita murmusa masa.
Shima murmushin ya sakar mata,kana ya kama hannunta Yana mata sannu.
Daya tambayeta Ina yake mata ciwo yanzun,sai tace masa ba koina.
Dan h
aka sai kawai ya nema musu sallama.
Da suka taho ahanya yake tambayar ta na abinda ya faru.
Bata gaya masa ba saita boye sbd karta hadashi da amaryarsa yace a kafar bene ta Fadi.
Ya rintse idonsa yanajin abun aransa kamar yanzun ya faru,kamar Kuma
ajikinsa yakeji.
Sai yace mata"baby Allah ya takaitamin wahala,Allah yatsaremin abinda ke cikinki,Banda Allah yasa Su Alhaji sun kawoki asibiti da wuri da tuni wani zancen ake ba wannan ba,gashi likita yace sai an sake kula don in Hakan tasake faruwa a
gaba dole arasa guda daga cikinku Kinga ai bazanso inga kowanne ba,Dan haka na yanke hukuncin zaki dawo sakina da komai naki gara ki sauko kasa ki bar benen Nan kar asami matsala,ai tun farko saida
nace ki zabi kusa Dani tunda dakina Yana kasa kikace ke ki
nfi son Saman,to yanzun...
Tayi saurin katseshi da cewar "Dan Allah ka barni asaman zan kiyaye fa,sbd kaga idan nadawo dakinka matarka bazataji dadi ba tunda tana zuwa ta kwana acikinsa Ranar girkinta.
Yace"Ni ne keda Alhakin tsara komai Bata Isa taq
i magana ta ba,Dan haka daga yau zata koma kwanan dakinta in yaso in Ina Ra,ayinta zanbita ran kwananta.
Zuhra dai tayi shiru kawai tunda ya dage.
Shikuwa da sukaje gida da dare CCTV camera ya kunna yaga Kuma abinda ya faru shiyasa yaji bacin ran da
Bai taba jiba arayuwarsa
Zuhra ta boye masa abinda ya faru tsakanin ta da iyabo gashinan yaga iyabonce ta bangaje ta tayi gaba abinta,Bata tsaya ma ta taimaketa ba sannan da alamun fada ne tsakaninsu.
Ita zuhra ma ta mance da maganar da iyabo ta yab
'a mata na cewar ita yar me gadi ce,Kuma Tasha Alwashin ta cikin ruwan sanyi zata tambayi Alhajin yanda akai har iyabo tasan da mahaifinta yayi aikin gadi,tunda tasan inba abakin Alhaji taji ba ai Babu.
Shikuwa cin mutunci sosai ya yiwa iyabon,Kuma agab
an zuhra yayi shi har kunna mata CCTV cameran yayi Taga komai
Jikinta yai sanyi Bata zaci zai kawo tunanin bincikar Hakan ba,batasan ware lokaci yake ba Wajen bincikar komai na abinda yakai yakawo agdn.
Dan haka yai mata dole akan ta bawa zuhra haku
ri,cikin kissa ta durqusa kuwa ta bada hkr harda cewa sharrin shaidan ne insha Allahu Hakan bazai Kara faruwa ba.
Cikin hade Rai da tsare gida yai mata worning da kakkausar muryace yace"inason insanar mk da cewa wannan cikin na jikin zuhra tukuici ne ub
angiji yaimin duba da Aikin Alkairin da nake yiwa Al,umma da Kuma rokon da nake masa akoyaushe akan samuwar ckn ba dare ba Rana duk zuwan da nakeyi Umara da hajji Ina rokon Akan Allah ya azurtani da samuwar cikin sbd shekaruna sunja inason inga kwaina,to k
uwa tunda Allah ya bani baikamata inyi sanya Wajen kulawa dashiba,wallahi!wallahi! Akansa zan iya komai Dan haka kisaka aranki cewar indai aka Sami matsala agaba ata bangarenki walh kinji na rantse saiya zamto abakin Aurenki.
Cikin kidima ta kissa tace"
Ayya Alhaji Hakan ma bazata Kara faruwa ba,zan kiyaye,plz and plz kuyi hkr bada gayya nayi ba.
Zuhra ta murmusa tace"da zcy Daya nake zaune dake Dan haka ki kiyaye.
Aranar dama zuhran ke dashi aikuwa ya ringa Nan Nan da ita.
Bayan sallar ishsha'i
ma tare suka fita sukaje yai mata shopping na kayan kwalam da maqulashe na abinda takeso kana sukaje pharmacy ya siyi
magungunan da likita ya rubuta mata su na Karin lafiyar cikin,Dan ma ance musu baby na nan da karsashinsa da lafiyarsa,itama tana jin Haka
n dan yawan motsin da yakeyi ita kam tazaci ma twins ne sai da scanning ya nuna dayane,Kuma Namiji kana ta fahimta,lallai Maza tun suna ciki ba dama ne
😄
Fitar da sukai ta sake qona zcyr iyabo,gashi basu dawo ba sai Wajen Sha Daya na dare,dakyar bacci
ya dauketa ta kwana bakin ciki sosai,sannan Tasha Alwashin itama saita samu cikin Nan kota karfi dayaji ne,sbd bokanta ma yace batada Rabo itada Alhaji tabbas ko awaje saitayi cikin itama.
Kawai sai zcyrta ta ringa Bata shawara akan ta lallaba me gadins
u ya ringa kwanciya da ita ko zata samu ciki suyi komai ckn sirri da sharadi Amma zata zuba masa kudi a aljihu dole ne.
Amaimaikon Aiko masa da Abinci da suke saita tsiri kawo masa in Alhaji baya Nan.
Da Allah ma ya Bata sa,a sai Alhaji yayi tafiya S
am ta mance da CCTV camera agidan in tana Abu kwakwalwarta rufewa takeyi ido ma ya rufe
Shi atashin farko dayaji kudi saiya amince mata ilu me idon cin nera baya ma tsoron ya rasa Aikinsa.
Kullum in zasu kebe takan bashi naira dubu goma shikuma sai
yace kyanta asati sau