Showing 21001 words to 24000 words out of 40654 words
Yana fadin"Ina godiya da wannan karramawar my baby,walh Dadin ki na rudani baby,ke ta dabance Wanda yasamu irinki indai ya Kara Aure to saidai kaddara.
Kamar ta magantu Kuma saitayi shiru Dan tafison ya magantu da kansa,tunda Taga shakku yakeji.
Jin tayi shiru yanata barin zance saiyace mata "wai baby ko ke bakiji dadin bane.?
Cikin murya kasa kasa tace"Eh to da sauki,dayake dama inciki ya mika ana jin sauyi ni dama jin dadin zai ragu kai aka turawa,kaga dole sai mun sake yin hkr ma agaba,sa
nnan yawan takurar ma akwai matsala,a daga min kafa dai zuwa wani lokacin.
Yace"Aa baby kiyi hkr zuwa lokaci kadan dai,kafin Nan kanwarki tazo ta karbi ragamar saiki huta Amma mijinki kinsan mabuqaci ne bazan iya ba,kiyi hkr banyi niyyar ma na fada Miki
a yanzu ba walh Kinga mgnr Auren Nan da yarinyar Nan ta Lagos ne yatashi da Alhaji murtala yazo kwanaki sunje da kawu sunyi magana ansaka Rana yanzun ma saura sati biyu dama wata guda aka tsaida,karki damu baby matsayinki na Nan a zcyta saima karuwa da y
ake tayi Dan Allah kiyimin uzuri walh ji nake kamar Dole akai min na Amince saikin tayani ma da addua tunda naga ke akwai tsayuwar dare baby mu kuwa Maza mundawo agajiye sallar saita farilla muka Fi bada kaimi Dan ma kina kokarin tusani gaba Daren juma,a i
nayin nafilar cikin dare Amma kam Ina Neman taimakonki baby walh.
Ba tace dashi kanzil ba
Saida yace mata"baby bazaki taimaki mijin naki ba knn kikai shiru?
Ajiyar zcy taja kana tace"hhuumm Allah ya taimaka mana Baki daya.
Tab lallai yarinyar N
an ta koyi gashi knn ta ruwan sanyi,ya aiyana Hakan kana yasake shigewa jikinta yace "nayi niyyar na raba muku gida,to Amma gidana dake Nasarawa GRA babba ne Kuma angamashi ya tsaru sosai yai kyau shi nakeso mukoma idan amarya ta tare,Kinga saiki fara shir
in komawa Nan da kwana goma ko sati guda an zuba komai aciki gobe murja zatazo kuje kuyi siyayyar kayan kicin Wanda kike da bukata zan Saka Miki kudi a account dinki hade Dana fadar kishiya miliyan biyar zan Saka Miki.
Cewa tayi"sunyi yawa,kasaka na kay
an kicin kawai.
Yace"bakya da bukatar kudin fadar kishiyar kenan?!
Tace"to ai ance fadar kishiya,nikuma ba,a fada min ba ma sai yanzu ko ince sai yau,Kuma Babu Wanda nima zan fadawa,kaga kudin baida Amfani knn.
Yaja ajiyar zcy Shima ya na fadin"ba
by saidai in fushi zakiyi da kudina,saidai in anbata mk Rai zaki rike aranki ne,Kuma bazanso Hakan ba.
Tace"bakai min komai ba,haka Allah ya rubutu a zanen Allon kaddarata kar kaji komai Ina tayaka murna Kuma gida na bar mata sabon gida ta zauna can da
kai Amma nikam ba inda zanje ai ni tsohuwar gida ce Ina tsohon gidan.
Shiru kawai yayi bazai biye mata ba,Dan so take ta gasashi ata Nan ma da alamar ta,Dan haka awashe gari saiga ALH Sadi shi da murja ankai kararta akan bazata koma sabon gida ba.
Su
ka tisata agaba suna mata fada da nasiha.
Ganin girman Alhaji Sadi da mutuntashi da takeyi yasa ta Aminta akan cewar zata koma din,Nan da sati ma insha Allahu.
Ya nuna mata jin dadinsa na amintar tata,sannan yasaka mata Albarka Shima yai mata Alkawar
in tsayawa tsayin Daka akan ganin an mutuntata a Auren bazai bari ta shiga wata damuwa akan Hakan ba harda ce mata"walh inhar amaryar tazo tayi giggiwar Bata Miki Rai ko ganin ta cusguna Miki to
saidai ta fita bazan lamuntaba zan ringa Turo murja tagano m
in komai,ke dai karki zama me ajiye Abu arai Dan karki cutu sbd bake kadai bace kinji.
A sanyaye tace"To nagode sosai Alhaji Allah yakara girma.
Yace"Amin,ya Mike Yana dire mata kudi a envelope Yana fadin"ga tukuici da kudin fadar kishiya daga Ni,Dol
lars ne masu kauri ki karba kyauta na Baki,haka zalika Shima inya Baki ki karba wannan hakkin kine Allah yakara mk hakri da juriya.
Tace"Amin nagode sosai.
Alhajin nata na gun baice komai ba sai kallonta dayake cikin tausayawa ji yake tayi kankanta d
a cewar wai za,ai mata kishiya Amma ya ya iya? Babu
Suna fita suka qule da murja adaki murjar tajata tana fadin"kiyi hakuri!kiyi hakuri!kiyi hakuri Zuhra girma ne zai hau kanki,Kuma wannan rubutaccen Al,amari ne Babu me turarshi.
Zuhra kawai saita fa
she da kuka,tuntuni takeso ta koka Amma takasa sai yanzun da tayi kukan taji hawaye ya zubo sannan taji sanyin zcy.
Murja tace"Ai ki godewa Allah ma sbd Alhaji na kaunarki kinsamu miji har shakkarki yakeji,yagaya ogana,haka zalika Ina me shawartarki aka
n ki amshe kudinki na fadar kishiyar ma ai ke gaba ta kaiki ke da nakeson inkin haihu mu Jone da business mu fantama mu ringa sana,ar mu tare a bude mana boutique mu bazaza kayanmu Yan waje Kuma ahannunsu zamu samu kudin,inason ma kicire kishi aranki Dan m
e yasa na zama ta gaban goshi agun Mijina sbd na rike makaman zama da miji Babu me cewa inada kishiya ai ko yaushe nice abakinsa nice axcyrsa ba boka ba malam
Kema inason Hakan ta kasance yanzun zan Miki Karin haske akan wasu abubuwan da zaki karu da K
uma yanda zaki zauna da kishiya qalau Amma Rike adduar ma shine akan gaba sai juriya akan Sex.
Nan dai murja ta ringa mata karatun sanka sanka har zuhra ta gamsu.
Anan murja ta wuni kana suka wuce wani katafaren babban store da Garba karfe ya Bude na
furnitures da kayan kicin Yan waje.
Acan sukai siyayyar komai na kayan kicin sun kashe yai miliyan Daya da Rabi aka lodo musu abayan MOTA zuhra tajasu suka dawo gida Dan hannunta ya fada a tukin,
Suna tare da murja taji saukar babban alert na mili
yan uku tare da ganin sako yace mata Na fadar kishiyar da ba,aso ne Amma adaure akarba ko ba Dan shi ba ko don rokon Alfaramar abokinsa.
Murmushi tayi tana nunawa murja.
Dariya sosai murja tayi tace"ai yanzun fa ke kam zakiyi ta samun kudi ne agunsa
ke dai ki Gina kanki da iyayanki sbd itama intazo kokarin Hakan zatai.
Gyada kai kawai zuhra takeyi tana hangen wane zama zasui agaba,shin ma zata iya jurar ganin mijinta da wata...???
Muje zuwa
*MATAR TSOHO*..
👨🏻
🦳
👩🏼
🦳
(Ta gaban goshi)
_The Romantic and love story_
❤
️
💗
*Writing by Nabilancy Love* Auntyn S&S
Page 13
Acikin satin dasu Inna zasu dawo daga Umara ne aka daura Auren Alhaji Hashim da Rahama iyabo Bai yadda yayi rawar kafa da giggiwar wasu angwaye ba sbd shakkun zu
hra dayakeyi bayason yai abinda zaija ayi masa daru adaga masa hankali Dan lallabata yakeyi Daya fita zai kirata awaya yaji lafiyarta abinda da baya mata ma yanzun Yana ta kirkirowa ne Dan ya faranta mata.
Ita dai tanata daurewa ne saboda inganta lafiya
r babynta dake cikinta.
Hajiya Laila matar Alhaji murtala kaninsa ta kirata awaya aranar daurin Auren tayi mata ban Baki da yar Nasiharmu ta mata akan hkr da kau da kai in za.ai maka kishiya taji dadi sosai tai mata godiya har tace mata twins Hassan da
Alhussain ne basa jin dadi sbd hakuri Daya tisasu agaba Amma taso zuwa Nigeria sbd ta jima batazo ba dama tun kafin ta haihun gashi tayi shekara da haihuwa Kuma tana kewar gida.
Sunsha Hira sosai kamar sun Saba da juna kafin suka Rabu awayar Dan mijin n
ata ma Alh murtala Bai samu zuwa ba Shima tunda ba wani dadewa yayi da tafiya ba Kuma dama dashi akai komai.
Haka itama Hajiya Jamila kanwarsa tazo sabon gidan da suka koma na taya Dan ,uwanta murna tareda Yi masa Allah yasanya Alkairin Aure.
Itama j
ininsu ya hadu sosai da Zuhra suka qule adaki tana mata nasiha da ban Baki Sanna da ban hkr itama ta tausheta akan wannan kishiya da tai mata shigar sauri tunda Auren nata ma yaushe akai da baifi watannin ba.
Hajiya Jamila mace me kirki sosai ta manyant
a Amma haihuwa ce itama shiru tanata nema Allah Bai Bata ba,Tasha yin bari dai sun fawwalawa Allah duk da ba wuce haihuwar tayi ba,batafi irin 35 years ba ga mijinta da Rufin asiri Yana da kudi ba laifi Amma baikai yayan nata ba,Yana matuqar son ta suna ci
kin Kano Amma baya barinta yawon bin dangi duk me son ganinta saidai yazo inda take sannan sukan taimakawa dangi Wanda basu dashi suma.
Tace da Zuhra idan Allah ya saukeki zan kawo Miki magungunan mallaka na matsi Dana Sha Wanda zaki Kara gyara kanki t
unda mu dole Muna bangaren Uwar gida ai,Dan ma wayo zakuyi mana ki gudu Turai gidan Yaya ki haihu acan da ai mune agaban gaba in an tashi haihuwar yanzun kuwa saidai Hajiya Laila ta shige gaba.
Murmushi kawai zuhra tayi tace"ni ma ba haka naso ba,naso y
a barni anan Amma yace acan zanfi samun kulawa agun likitocin can daga lokacin Daya Isa yin awo wata shida ko bakwai zai kainin.
Hajiya Jamila tace"Eh Hakan yayi,nima Ina bayan Yaya fa,Abu ne anata nemansa sai yanzun yasamu na baya ya zama tarihi Allah
dai ya saukeki Lfy,Allah ya bamu yataki.
Zuhra tace"Amin, ke ma insha Allahu zakiyi,zan turo Miki zoman inayi bazaki Dade ba insha Allahu.
Hajiya Jamila tace"kayya,to Amma dai bari ince Allah yasa.
Aranar da aka kawo amarya dayake tana tare da dan
gin miji dasu murja shiyasa bataji wata damuwa aranta ba har taro ya watse Dan murja ma sai dare sosai da aka rako ango gun amarya kana mijinta ya dauketa suka tafi.
Khairat makwabciyarta Kuma kawarta itace kadai ta kwana gunta sbd ita budurwa ce sannan
batada matsala da gida ummanta kawar inna ce gashi dama ummar tata ita ta tsaya akan komai na lamarin zuhrar sbd innar Bata Nan shiyasa damuwar zuhra fa kadan ce.
Hajiya Jamila kuwa tun aranar me gidanta Shima yazo suka wuce Danladi Nasidi gidansu Bai
yadda ta kwana ba kamar yanda taso.
Dayake bayan ladidi sun samu Karin wata me aikin shiyasa washe garin da amarya ta tare Babu Bata lokaci gida ya gyaru yai qalqal kamar ba,ai taro acikinsa ba.
Ladidi da Abula sun gyare koina sannan suka Dora abin K
arin kumallo da wuri suka gama da gaggawa suka jere a dining.
Da suka tashi bayan sun kintsa kansu zuhra ta saka wata ubansu Dubai abaya kalar dark brown ta saka veil din rigar tayi rolling, sai tayi wani mahaukacin kyau kamar ka dauketa ka boye ga jik
in Nan ya kwanta kamar Bata shiga rana ga cikin yabi jikinta sai ta wani murje tayi free. khairat sai kallonta take yi kamar yau ta Fara ganinta " Wow sister ba karya kinyi kyau wallahi ni banga abunda Alhaji ya gani ba jikin matar can ba, me Kamar wann
an wace tsiya ze tsinta a jikin waccen Mai suffar samudawan farko, mace ba wani Abu na Jan hankalin namiji. To kenan turaka zaki ringa zuwa ko shi zai ringa zuwa Kuna sharing na bed gudai?"
Wata harara Zuhra ta zubawa khairat tace "Babu inda zanje walh
,indai bazai shigo min ba ba zanje Masa ba ai Babu aji ma a ringa kwamacala a gado Daya wlh da jikinsa ma ze rabu Dana ce ya raba kowa ya dauki Bari daya".
Ta fada tana zumburo Baki.
Dariya khairat tayi tana karewa zuhrar kallo ganin bilhaqqi da iya gask
iyar ta tayi maganar.
"kin manta kin daukarwa murja fa alkawarin yin kissa kala kala to Kinga zuwan ma na,a cikin kissa fa walh kada kiyi sake Yar yarabawa ta kwace Miki miji, garin kallon ruwa kwado yayi Miki k'afa, ki Kama mijinki da salon da ze dunga
rikita Masa lissafi duk lokacin da baya tare dake yaji ya matsu Yana Allah-Allah ya komo gareki".
Dariya zuhra tayi tace"kaji khairat da wata magana yaushe har kikasan shika shikan da kaidojin turaka da har zakice zuwan ta shine yin kissar Sam ba haka b
ane".
Dan murmusawa khairat tayi ke nifa to be frank na tsorata ma da ganin amaryar Nan taki wlh, wata qedara da ita,wannan banga ta inda tayi Kama da budurwa bace sai dai a kirata da budurbuzur Dan kam tafi kama da bazawara may be dai ma kisan Boko ce
".
Wata dariya ce ta kubcewa Zuhra Bata shirts ba " Amma wlh khairat Baki da kirki, mutum.ya auro mace gari ya garara tun daga lagos kizo kima mata irin wannan yarfen, ke nifa Babu ruwan biri da gada abinda zai hadoni da ita sbd Ina sama tana kasa tay
i sabgarta inyi tawa ni fa Babu wacce zatazo ma inbiye mata tasamin tension su suka Jiyo su karata can a hanyar k"araye Daman kusan sa'annin juna ne Sai suji da kayan ahekarunsu ni nawa Ido ne idan ta ritso da in gani".
Khairat tace"ai naga shekarunta n
a Tsakar kanta zata iya finki wayo shiyasa nace saikin kula Kuma saikin dage fa.
Zuhra tace"ke nifa na rike Allah,na Kuma tabbatar bazan tabe ba, miji Kuma tunda ya tabbatar Ina gaban goshi to bani da damuwa kota sisin kwabo wlh zanta Addu'a Ubangiji ya
yi mini tsari daga dukkan sharrin data kunso ta shigo dashi".
Khairat tace"to Allah yasa mu dace.
Zuhra tace"Amin,bari na kunna data na tabo inna a vedio call inganta ko naji sanyi".
" Ai sauransu kwana uku dai su dawo dai nasan Kamar a Kan k'aya kike
ko?".
Khairat ta fad'a.
"Bari kawai wlh na matsu su dawo ai Hutu Zan dauka na two weeks yanda zasu samu damar Gane juna".
Wata dariya khairat din ta fashe da ita tana fad'in "Tab kice match Zaki taro an fad'a Miki Yana hauka ne shi da ze barki kiyi Mas
a mugun Wasa ai waccen 'yar cikon benci ce, Allah ne kadai yasa karatun bebe a cikin auren nasu".
Kafin zuhra tayi magana Ladidi tayi knocking, gaishe dasu ladidin tayi kafin tace "Aunty zuhra Amarya tace a fada Miki ki fito kuyi break".
"Wata sabuwa Wai
inji 'yan caca da farawa da iyawa". zuhra ta fad'a a zuciyarta.
"Ladidi jeki fada mata ba yanzu nake yin break ba suyi nasu kawai".
Juyawa ladidin tayi tana tunanin yau Auntyn tata Sai a hankali kenan.
Lokacin da Ladidi ta shigo lokacin Iyabon din ta K
ara fitowa ita da Alhajin tana jikinsa sai magana take Masa k'asa-k'asa cikin kissa da kinaya irin na tsaffin bariki.
Ganin wurin dining din fayau ba kowa yasa ta canza fuska saboda tayi targeting din zuhrar ne akan tayi wannan ganin sai Kuma aka Samu aka
sin hakan.
Ranta a hade ta kalli ladidi dake durkushe tana gaishe da Alhajin.
Cikin Hausa radau kamar Jakar Kano tace "ke Ina sister din tawa ne na ganki ke kadai?".
Dan risinawa ladidin tayi tana fad'in "Auntyn tace kuyi kawai ita ba yanzu take yin bre
ak ba".
Kafin tayi magana Alhajin ya rigata.
"What! Me take nufi? Bayan tasan ba ita kadai bace zata ce Wai ba yanzu take break ba".
Bai bi ta Kan abinda Iyabo ke fada Masa ba ya nufi sama har hade steps yake yi.
Khairat ce ta tashi ta nufi wurin mirro
r da sauri ta dauko tsaradedden turarenta ARABIAN TREASURE na kamfanin Al-Haramaini, ta mik'awa Zuhrar " Kara fesa tawa nasan wlh Alhajinki (chu-chu) he's on the way".
Ta fada tana dariya, Dan filo zuhrar ta jefawa khairat "wlh Baki da kirki".
Turo kofar
da akayi ya Hana khairat fadar abinda tayi niyya.
Alhajin ne ya shigo Shar dashi Yana baza k'amshin turare.
Wani bakin ciki ne ya lullube zuhra gani tayi har wani gyallin goshi yakeyi saboda tsabar kishin da yake azalzalarta.
Amma saita danne, ta kawar
da kai, a faffafe ya amsa gaisuwar da khairat ke masa duk hankalinsa Yana Kan zuhrar.
Gurin da take zaune ya karasa ita Kuma khairat tayi waje direct down stairs tayi.
"My baby love menene....?.
Warrr tayi Masa da idanunta "me Kuma nayi my chu-chu nif
a bana Jin cin komai ko kana son nayi maka amai ne?".
Nan da Nan ya rude Yana Zama kusa da ita Yana shigo da ita jikinsa Yana Dan shafa cikin da hannunsa.
"D'azu Kuma kina jin Ina knocking Amma Kika shareni ko? Kuma na kiraki a waya Kika ki dauka, kin ky
auta min kenan?".
Shagwab'e masa fuska tayi "nifa banji ba Kuma wayar Bata kusa Dani ance ba'a kwana da waya a kusa saboda radiation".
Ta fada tana d'an kwanciya a jikinsa.
Idanun iyabo kur tana kallon stairs din, Jin sound din takalmi yasa ya ta k'ara
gyara Zama tana baza attached din da suka zubo a kafadarta, murmushi ta Fara tayi zaton ita ce zuhrar Amma Kuma ya Babu Alhajin,to me ya tsaya yi adakin nata da har Bai biyo ta ba.? Ta rasa amsa
Da sauri ta nufi khairat tana karairaya "haba sister Dan
me kikak'i fitowa Saida my one ya biki?".
Dan turus khairat tayi tana ganin bariki zallah.
"Sannu Aunty bani bace zuhrar ita suna sama, Ina kwana?".
Ta fada tana kallon iyabon.
"Oh abeg kiyi hakuri kinsan ban santa ba".
"Ok ba damuwa"
Hanyar fita kha
irat ta nufa tabar iyabo a tsaye a wurin kamar wadda ruwa ya cinye.
Saida suka shafe kusan minti goma sannan suka nufo kasa, har lokacin Iyabon na tsaye a inda khairat ta barta, tunda suka Fara gagarowa Iyabon ta zubawa Zuhra idanu,ba haka ta zaci ganinta
ba sai taji duk ta Raina
kanta Dan yarinyar tayi Babu karya tasan badan qulunboton da ta yiwa Alhajin ba Babu abinda zeyi da ita Yana da kamar wannan.
Hade girar sama da kasa tayi Dan ta shaqa a Kan dadewar da Alhajin yayi a wurinta.
Har suka karasa sau
kowa Bata motsa ba daga inda take tsaye.
Wurinta ya nufo Yana fadin "Yaya dai madam meya faru?".
Wayancewa tayi tana kirkirar murmushin dole.
"Nothing Ina tunanin ko sister Bata