Showing 30001 words to 33000 words out of 40654 words

Chapter 11 - MATAR TSOHO COMPLETE

30 Sep 2026

1428

yajikanta.

Ya murmusa yace"Amin, hakane,yanzun Nafison asaka masa sunan Aminina da mukai quruciya tare yai hatsari aranar Muna cikin waya dashi ahanyarsa ta zuwa gurina ya baro Maidu

guri ALH BILAL Allah yajikanshi bazan taba mantawa dashi ba,shine ya fara bani kudin da nafara da kasuwancina har Allah ya sakamin nasini sannan ayaransa ma yasaka sunana ya Saka sunan Alhajina Daya rasu haka zalika Autarsa ma sunanta Amina suna ce da Ita

Meenal Allah sarki duk yanamin Kara ne saboda yaga bana haihuwa alokacin Allah yajikansa dai.

Yakarashe maganar da goge hawaye Daya zubo masa.

Jikinta yai sanyi tace"Allah sarki Allah yai masa Rahama,Amma dai kana gano iyalan nasa ko?

Ya gyada kai

yace"duk wata Ina kai musu ziyara ai yanzun Hakan ma Ranar da zaki tafi zanje musu,Naso na Auri matarsa ma alokacin sai aka samu wani tsaiko Har daga Baya ma tayi Aurenta Amma yaran suna gabanta sun girma Amma dai ko yaushe Ina taimaka musu ko banje ba du

k da ba,a cikin wani Hali na wahala suke ba don yabar musu dukiya.

Ta muskuta tace"Allah yajikansa da Rahama dai.

Yace"Amin.

****. ****

Zuhra na gab da haihuwa watan da EDD dinta Yakama Alhaji yasaka mata Ranar tafiya.

Ana gobe zata tafi yaka

ita gidansu ta wuni.

Khairat kawar Arziki ta shigo mata tare suka wuni,alokacin kana kallonta kaga tana kan gab'a don alamomin haihuwa na gab sun nuna.

Sai dare yaxo ya dauketa inna da baba suka bita da fatan Alkairi,Shima sunata Saka masa Albarka da

godiya na hidimar da yake dasu Dan yau ma dayazo gidan da kayan abinci yazo musu aboot shinkafa buhu da taliya da garin semo dasu Mai fari da ja jarka jarka

Wannan abin kadai da yakewa iyayanta yake Kara burgeta takejin Kuma dadin samuwarsa gareta tana

yawan godewa Allah Daya cika mata burinta dole ne taso Alhaji har karshen rayuwarta.

*****

Tafiya ta kama yau duk sai ta tashi Bata jin dadin jikinta

Gabanta nata faduwa na rabuwa dashi da zatai na Yan wasu watannin"Chu-chuna nashiga damuwa, walh jin

ake kamar kar natafi nakeji,walh zanyi missing naka.

Tuki yake Yana mata kallon love yace"meye na damuwa babyna,karfa ki manta in ana zuwa England acikin kwana bibbiyu zanje,duk lokacin da kikai missing babyna na bukatata ki sanarmin zantaho sannan ma g

a vedio call ai okay?

Ta gyada kai tana murmusa

Shikuwa dauriya kawai yake,tuno masa da matarsa Hajiya Aziza data rasu asanadin hatsarin da sukai ga ciki bare Kuma itama aranar da zasui rabuwar karshe ta ringa fada masa zatai missing gashi tana nuna

kamar karsu Rabu.

Hajiya Jamila kanwarsa acan Tashar jirgin suka tararta itama tazo yiwa matar Yaya Zuhra sallama.

Mijinta ne yakawota suka gaggaisa kana suka ringa mata fatan Alkairi.

Akan idonsu jirginsu zuhra ya tashi

Alhaji Yaja ajiyar zuci

ya Yana jin wata kewa data fara ziyartarsa.

Muje zuwa

*MATAR TSOHO..*

👨🏻

‍

🦳

👩🏼

‍

🦳

(_sta gaban goshi_)

Nabilancy Love

💘

Page 17

Tunda zuhra ta sauka a kasar takejin wani farin ciki na shigarta tabbas ba don sanadin Auren ALH Hashi

m ba tanajin da harta koma ga mahaliiccinta bazata tazo kasar waje ba,gashi har kasa me tsarki ma take hangen zuwa agaba,taja ajiyar zcy tana me godiya ga Allahnta.

Daddyn twins da kansa yazo daukanta shi da matarsa sunata nuna murnar zuwanta

Taji da

dyn wannan tarba da dokin da suke nuna mata tabbas su din mutanene masu karamci haka zalika har wani girma suke Bata na matar Yaya.

Aka ringa inaka Saka inaka sauke da ita.kayan cima iri iri saida ta Ture.

Alh murtala mutum me mutunci agaba yasata Ya

na mata barkwanci da Hira ba ruwansa.

Haka itama Hajiya Laila suka qule adakin da aka ware mata tana tayata Hira har tai bacci

Da safe taita leko ta tana son taga ta tashi akawo mata breakfast Amma zuhra Bata tashi ba sai 10am dama tayi sallar asuba,

wannan kam Bata wuceta Dan akan abin sallarta koyaushe takejin Kiran assalatu akunnenta.

Bayan tayi wanka ta Saka doguwar Riga tayi roll da veil din rigar tana son fita falo ta gaida mutan gidan tana tunanin ko basu tashi ba tunda weekend ne.

Tayi ky

au sosai tamkar ba me tsohon ciki ba,Inka ganta kamar me yaron ciki fuskarta fayau ta Kara wani annurin haske,cikin qurt dashi don baiyi tirtsitsi ba.

Tana da niyyar fita saiga Hajiya Laila ta shigo itada twins da suke kira Aryan da Ayaan.

Yara masu

kyau kamar larabawa ga wayo.

Gani Daya da sukai mata jiya saigashi sun dafeta suna fadin"Aunty good morning.

Ta kyalkyale da dariya tana Kara jansu jikinta

Yaran sun burgeta ga wayo ga wayewa.

Hajiya Laila tace"kai!ku saki Aunty karku kadata hab

a mana Ayaan,Aryan Kaine babba Amma kaima zaka biye masa ku dafeta haka inta Fadi fa.

Dariya zuhra tayi tana Shafa kansu tace"Ah momy ki barsu mana ai Auntyn suce ko.

Suka gyada kai atare.

Hajiya Laila tace"Tom muje ayi breakfast ko Aunty,inata zu

wa ganin ko kin tashi naga kinata baccin gajiya.

Tayi murmushi tace"aikam dai Nasha bacci, nayi zaton ma Kuma Baku tashi ba naga Yau sat.

Hajiya Laila tace"ga Yaran Nan ai masu tashin wuri haka suke tun basu kai haba,tun suna goye suke hananu komawa

bacci sai in suna gun lesson ne muke samun muyi na Rana.

Zuhra ta kama hannunsu dukkansu suka fice Hajiya na gaba suna bayanta.

Aranar zuhra Tasha kiran vedio call gun Mijinta suna Shan hirar soyayya Yana nuna yai missing nata.

Kwananta biyu da z

uwa kasar ta fara zuwa asibitin da suka Bude mata file babban asibiti ne ko acan.

Yarage saura sati Daya Edd dinta yacika suna zaune a falo da Hajiya Laila suna Hira tacewa hajiyar"walh momyn twins Ina tsoron haihuwa ayanzun da abin ya doso inata jin fa

rgaba wai da wahala ne sosai?

Murmushi Hajiya Laila tayi tace"ah karki damu idan Allah ma ya Baki da sauki saikiga kamar kiftawar ido anyi angama an wuce gun,ke da muke Miki Adduar Allah yasa tagwaye ne.

Zaro idanu tayi tace"kai ata farin,Kuma da yar

intata.! Aa dayan ma tsoronta nake fa.

Dariya mom twins tayi tace"nima da nayi ai kamar ta farin ce tunda a farkon ai b'ari nayi ba haihuwa ba,ke dai Allah ya Baki da sauki.

Zuhra tace"Amin.

Adaren ta ringajin wani irin ciwon mara na fitar hayyaci

.

Aganinta tunda har EDD Bai cika ba to ba haihuwa bace batasan ana iya karawa ko ragewa ba.

Duk da ko ajiya da sukai magana da innarta ta waya ta gaya mata Amma Sam Bata kawo ita zata rage din ba.

Aifa ashe haihuwa ce ta taho ranga ranga haka suk

a kwasheta adaren sukai asibiti da ita agigice don ta jigata matuqa tana ta kiran sunan Allah

Hankalin Alh Hashim yatashi matuqa dayaji cewar suna asibiti da ita don Shima a lissafinsa dai haihuwa da saura.

Tana ta Shan bakar wahala don sai naguda t

a taho gadan gadan sai Kuma ta tsaya cak!

Alh murtala yayi shawara da Hajiya Laila cewar gara ayi mata Aiki kawai a fiddo jaririn ko ta huta.

Ta amince tare da ce masa"Hakan ma zaifi Amma ka kira Yaya hashim yanzun kaji me zaice.

Kafin ya kirashi

saiga kiransa take kuwa ya amince sbd hankalinsa ba,a kwance yake ba jin yanda take Shan bakar wahala ji yake kamar yai tsuntsuwa ya ganshi a Turai duk da yai booking flat.

Cikin Ikon me sama,u Ana shirin shigar da zuhra operation an Saka mata kayan ti

yata anshigarta sai faya ta fashe saiga kan Jariri ya taho take likitoci matan suka Bata taimakon gaggawa Wajen fito mata da babyn.

Adaidai lokacin Kuma ALH Hashim ya diro kafarsa acikin filin jirgin Yana jin wani farin ciki da fargaba alokaci Daya suka l

ullubeshi.

Addua yahau Yi yana yi yana Nanatawa yayin da yake tuno matarsa Yana Neman mata sauki gun Rabbi.

Acan bangaren iyayanta ma tunda yasanar musu suka tashi tsaye da addua suna nema mata saukin gun Allah,baba ma har rubutu yasa akai mata yakaiwa

Alh Hashim yace yatafar mata dashi.inna kuwa akan abin sallah ta kwana.

Shi Alhaji Hashim ma Daya iso England Bai tuno da wani rubutun ba saida yashigo cikin asibitin agigice Yana tambayar yanda ake ciki sai yaji Albishir kan cewar ai yanzun ma ta haihu

cikin iKon Allah An samu namiji.

Ai durqushewa yayi agun Yana me godiya ga Allah yai sujjada Yana hamdala farin ciki ya lullube masa zcy.

Murmushi kawai ALH murtala yakeyi ai dole yayan nasa yai wannan murna haka sbd shekaru sunja har an fidda Rai fa

,ga Yar,uwar sa can ma Hajiya Jamila na bukatar haihuwa itama an jarabceta duk da Bata Daina addua da Saka Raina Amma itama ma suna mata fatan Alkairi da fatan dacewa irin hakan.

Hajiya Laila ma murmushi kawai take zubawa tana godiya ga Allah.

Hankal

insu Bai Kara kwanciya ba ma saida aka fito da ita da babyn lafiyar Allah.

Ai baibayeta sukai suna mata sannu.

A haiyacin ta aka fito da ita tunda jariri ya fito taji tamkar an yaye Mata ciwon da damuwar dake cinta arai na yanda ta galabaita Amma sai

gashi yanzun qlau take jinta.

Itama cikin ranta hamdala kawai takeyi,ranta yai fari dataga har Alhajinta yazo ,da aka Bata dakin hutu ne taso ta danyi bacci,Amma sai suka bukaci abata sallama aranar saboda agida sai tafi hutawar.

Sai dare aka gama k

omai suka maidata gida.

Yasakasu agaba Yana musu kiss yana yaba kyan yaro

Tanata zuba murmushi tana fadin"my Chu-chu dakai fa yayi kama.

Ya girgiza kai yace"Ina! mohd Bilal dake yake kama,wannan kyan naki ne baby.

Tace"to Allah yaraya mana shi,

Amma su inna fa? Ka sanar musu?

Yai saurin zaro waya a aljihunsa yace"ohhhh!kaii!!walh Shaf murna ta mantarni komai,bari nai musu Albishir ko inbaki ki gaya musu.?

Tasan zolayarta yake ba iyawa zatai ba.

Amma saitace"kasan zan iya wannan rashin kun

yar kenan.?

Yayi dariya yace"to ni bari nayi.

Take ya sanar musu wannan abin farin ciki

Aikuwa inna taringa rangada guda tana fadin aturo mata hoton angonta yanzun nan tasaka masa Albarka..

Aikuwa da Alhaji ya turo bayan Hajiya Laila ta kawo s

hi data shiryashi yasha hotuna kala kala.

Inna da malam sukaita kallonshi suna santin kyansa da girmansa Anata masa Addua.

Baba Fadi yake"Allah yarayaka mohd Bilal.!

Inna tace"Ah!sunan zaici kenan?ashe Kasani ma malam.

Yace"Eh ai nasan burinsa ke

nan yasaka sunan Amininsa Daya rasu,ko yaushe abaya yakance inhar Namiji Allah ya bashi to sunan da zai Saka kenan.

****"

A can Turai kuwa yaro Bilal Yana ta Shan gata gun iyaya,Daya motsa ALH zaice Maza bashi nononshi yasha.

Ita Kuma da shagwaba za

tayi fuskar kuka tace"walh da zafi fa Chu-chu,ni dai ka samo Madara ahada masa walh acici ne.

Ya kyalkyale mata da dariya yace"haba raguwa daure dai,Amma dai My son bazaisha Madara ba aringa kiransa rainon Madara haka kawai,gara kiyita hakuri zaki Saba

ne.

Tayi masa banza tana tunanin Mafita Dan kam bazata Saba da wahala ba itakam.

Hajiya Laila ita ta kawo karshen Rigimar kafin yatafi tace zata sai wani abin bakin fida da ake kafawa akan breast sai baby yaita zuqa yazaci Kaine yasha cikin dadin rai

,uwa Kuma taji saukin.

Haka kuwa akai taje store ta samo mata me kyau da tsada.

Saida boy yayi kwana biyar Alhaji yakoma Nigeria da shirin za,ai radin suna ayi mata gyaran gida sai yadawo intayi 3 week ta Kara hutawa sai ayi suna anutse a kama babban

hotel Dan kam baza.ai karanta ba komai za,ayishi ba kwauro sai ansan yasamu magaji.

Ai kuwa Daya dawo Nigeria sosai dangi da abokan arziki sukai ta tayashi murna

Murja ce akan gaba Wajen rubuta tsare tsare na abubuwan da za.ai Ranar Taron suna,na a

bubuwan da za a bugo irinsu memo da kalanda da littafi exercise book me dauke da hoton baby,sannan za.ai stickers ta likawa ajikin kayan robobi na Rabo Amma sai acikin satin insun dawo yadai Bata kudade masu yawa yace ayi komai,mijinta kuwa ALH Sadi atamfa

yace zai Bata ta siyo ta rabawa MANYAN kawayen mejego da Kuma matan abokansu ita Kuma ta

ɗ

auki Nauyin yin manyan jakun Kuna na kwali da ake Saka hoton jariri.

A bangare guda Alhaji yasai katon Sa na miliyans of Naira yakai gidansu Zuhra yace shi za a

yanka Ranar suna sai katon Rago na radin suna shi San na hidimar da mutane zasu ci ne.

Itama khairat kawarta ta tanadi kayan Rabo na kawaye anata bangaren, Dan ALH ya shaqa mata kudi itama yace ta yiwa kawayensu mutane 20 anko da zasu Saka Ranar suna Wa

nda ta fidda kala.

Ita dai inna tanata farin ciki da mamakin wannan kudi da ake ta bajet din kashesu tabbas sunan Nan zai bada ma,ana babban farin cikinta ma da 'yarta take lafiya Itada jariri don taji muryarta.

Anata wadannan shirye shiryen dai har

lokacin komawarsa Kasar Turai yayi don burinsa kawai yaje ya taho da matarsa agabatar da Taron sunan da aka shiryeshi.tunda anyi radin sunan a babban masallacin juma.a akai aka sawa yaro mohd Bilal

Bayan sati biyu.

Ana gobe zai tafi kuwa Alhaji sun

Dade suna waya da zuhra kana suka dawo vedio call

Yaringa ce mata ta hasko masa son dinsa sosai yaga fuskarsa wai jiya yai mafarkin yanata masa dariya so yake yau yaga dariyarsa.

Tace"kai chuhchuna baifa fara dariyar ba,saidai dariyar quda in Yana b

acci,bayan a mafarki kagani.

Yace"Nikam inkun dawo zan masa wasan da zai Dara,Allah baby ko hhuumm zan bawa boy gata,zaiji dadi aduniya,na tanadar masa abubuwa dayawa na more Rayuwa ciki harda shares da zan Saka masa a wasu kamfanonin turawa akasar engl

and sbd nayi rubutu ma munfara joint dasu akan Hakan sbd Daddyn twins ma yasakawa twins shiyasa naiwa boy Sha,awa tun yanzun saboda bansan ya rayuwa zatai damu ba,wataqila ko bazanga girmansa ko Aurensa ba....kawai

saita tsinci kanta da fashewa da kuka tan

a fadin"kai Chu-chu Dan Allah ka Daina fadar haka,walh Muna sonka,ni walh bazaka mutu ka barni ba saidai ni inmutu inbarka....yai saurin tararta da fadin"Ina!Ina!! Nima bazanso ganin wannan Ranar ba walh..insha Allahu sai Bilal yaga tsufan iyayansa ma,muyi

shiru haka baby da wannan maganar saboda Bilal na da bukatarmu duka araye don Babu me iya rikon mana shi tsakani da Allah in babu dayanmu gara ma 'yar uwata datake anan ita gareni tal,aduniya Jamila munyi magana ma da ita ko ba Raina ita na Aminta ta rike

n iyalaina zan iya batasu HALAK malak sbd Bata haifaba Abar tausayi ce ko Ina Raye ni me Bata abinda na Haifa ne saboda tana da sanyin Hali kamarki batada matsala sam gashi jininmu yafi haduwa,hhuumm Baby Allah dai yadawo min daku gida lafiya,zakuga gata a

guna.

Tana share hawaye tace"Amin.

Nan yajanyo mata wata hirar da yake mata Albishir kan cewar inta dawo zataga motar Daya canza mata babbar GLK ta yayi update 2025 zata Yaba da ita fara sol aranar suna zai Bata mukullin agaban kowa.

Wani farin ci

ki taji taringa masa godiya tana masa addua.

Yaringa amsawa da Amin,Amin.

Aranar basu Rabu da wuri ta waya ba sai biyun dare sai da yaji tanata zuba Hamma ya kyaleta duk da Shima akwai bacci a idonsa Amma haka kawai yaji bayason rabuwa da ita hirar

yau tafi masa ta koyaushe Dadi ko Dan yanata gaya mata yawan kadarorinsa ne tana Saka masa Albarka.

Abin mamaki ma dataji harta fara bacci Amma ya tasheta da wayarsa wai uku tayi ta tashi tayi masa addua ko babu alwala Daren juma.a ne Akwai karbuwar Ad

dua tsakanin bawa da ubangijinsa Babu hijabi

Tace masa kawai to.sbd ita abin na chuchunta ma ya Daina Bata mamaki yanda Taga ya Kara sonta kamar Bai San ta ba wannan d'oki

Saita ta allaqa abin da zuwan baby boy ne son baby ya shafeta Ankara kaunart

a.

Bayan ta gama adduar ta kashe wayarta saita sakata a flymood sbd bacci take son tayi bazata tashi da wuri ba ma inba Bilal ne ya tasheta ba.

Kuma wani iKon Allah aranar bacci yai mata dadi ta Dade ma batai kamar irin wannan baccin ba sbd Bilal ma

ya Bata hadin kai Bai tashi ba har garin ya waye Kuma ko da yatashi ma Bai tashi da kuka ba saboda Hajiya Laila data leqo akaro na biyu Taga idonsa biyu yanata tsotsar hannu saita daukeshi kawai ta fice dashi Dan tayi masa wanka kafin mamansa ta tashi.

*****

Acan bangaren Alhaji kuwa ko da ya idar da sallar ma Wajen uku saida yakara kiran wayarta sbd yaji ko tayi adduar,Amma sai yaji switch off

Ya hakura ya ajiye wayar ya kwanta saboda Shima baccin ne a idonsa gashi jirgin 7am zai tashi.

Da gar

i ya waye kuwa sai yasami kansa da kiraye kirayen waya ya sanar musu zai tafi fa taho da matarsa anata masa fatan Alkairi.

Yakira inna yakuma kira malam baban zuhra kana yakira Amininsa Alhaji Sadi har Hajiya Jamila yakira Yar,uwarsa sannan yakira dadd

yn twins ALH murtala alokacin zasu shiga jirgi Yana me sanar masa dagowarsu alokacin.

To iKon Allah kenan ashe tafiya Bata dawowa ba!

😰

ashe bankwana mukai...kallon karshe,maganar karshe da kowa...

Jirginsu Bai gama landing a sama ba aka samu gagaruma

r matsala daga injin jirgi ya buga saiga wuta ta tashi yayinda fasinja suka shiga addua da fargaba Wanda kadanne suke da tsahon Rai aciki Amma sun jikkata wasu Kuma suka mutu da wutar ta kama jirgi ya qone Asama,cikin masu karar kwana harda ALH Hashim miji

n zuhra Allahu Akbar...!

😰

Muje zuwa ko ya zuhra zataji...to NIDAI saidai ince kwa gaya mata kafin nadawo...

😃

Amma fa yanzun labarin zai fara akwai kwarbai agaba walh.

https://chat.whatsapp.com/Fuo3XSrIYYTLrK01nb8MV9?mode=ac_t

*MATAR TSO

HO..*

👩🏼

‍

🦳

👨🏻

‍

🦳

(Sabon Salo)

Nabilancy Love

💘

(Auntyn S

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login