Showing 27001 words to 30000 words out of 40654 words
uku yayi ya fara lissafin 30k asati ai zam dashi dama a wata 60k ALH yake bashi idan ya hada kudinta na wata Dana watan Alhaji ai zai tashi wata Dari Nan.
Amma fa shi ya Ankarar da ita cewar tasan yanda zatai ta lalata CCTV camera
ko Kuma ta kashe ta.
Hakan kuwa tayi saita kasheta din Hankali kwance suka ringa Masha,arsu kuwa ilu me gadi na kwasar dadi ga Kuma kudi.
Abula me aikin itace ta kamasu awata Rana ana gobe Alhaji zai dawo.
Aikuwa iyabo ta tsorata sosai Dan haka sa
ida tayi yanda tayi ta kebe da Abula ta roketa akan ta rufa mata asiri kana ta Bata kudi masu yawa hartace mata tana son tayi mata wani aikin zata Kara mata kudi harma ta Bata sarkar gwal inta aikata mata aikin.
To Abular ma ba bayaba Wajen son kudi da
hangen Dala ba gammo.
Iyabo tace maganine zata Bata ta zuba abincin da Zuhra zataci...da sauri Abula taja baya dafe da kirji ido waje tace"kai nashiga uku!walh bazan iya cutar da Aunty zuhra ba,gaskiya ki sake wata hanyar Amma bazanyi abinda zai Saka na
rasa Aiki naba,ko ta mutu Allah yakamani.
Iyabo tace"ke kwantar da hankalinki ba na mutuwa bane maganin,Wanda ciki zai fita ne,Kuma Kinga in cikin ya fita ai za.a samu wani agaba,so nake kawai narigata Haihuwa agidan Nan,kin Gane?
Abula ta gyada kai t
ace"Eh nagane,to ba laifi zanyi Hakan sai gobe girkinta zai shiga sai azuba mata ana Karin safe saboda naji ladidi nacewa Alhaji zai dawo da Rana zamui masa abubuwan tarba inji Auntyn Kinga indai ba,a ana safe ba to Tare suke cin abinci in yananan.
Iyab
o tace"ba matsala kisaka mata ana safen zan Baki dubu hamsin indai komai yayi kyau.
Ckn farin ciki Abula tace"Angama uwar dakina.
Dubu 20k ta fara Bata tace na farko ne kafin zuwan hamsin.
Duk wannan abun sunyishi ne acan bayan gidan Wajen zaman h
utawa Kuma duk akan idon Ladidi Wanda Tasha mamakin wannan dadewar da sukai a kebe suna magana
Bata Jiyo me suke fada ba,Amma alamun sun nuna mata akwai wani tuggun akasa da zasu shirya Kuma dama tana Ankare da cewar sun dinke da Iyabo da Abula Dan hak
a sai Tasha Alwashin sakawa Abula ido Dan gano me suka Qulla....
Muje zuwa.
*MATAR TSOHO*..
👩🏼
🦳
👨🏻
🦳
(ta gaban goshi)
Page 15
Nabilancy Love
💘
Auntyn S and S
To akace dai karshen Tika tiki Tik! Don kuwa wannan lamarin daya
faru yai tsamari saida ran kowa ya Baci agidan.
Abula ta aikata abinda aka sakata Kuma cikin hukuncin Allah Zuhra tayi tuntube da qaddararta tasha wannan magani Don Abula tayi nasarar Saka mata acikin hadin kunun gyadar da tace ayi mata tana so.
Duk S
aka idon da ladidi ke Yi acikin sabgar Abula don ta ganota, Amma saida tsautsayin yahau kan zuhra taci guba a abinci tai ta murqususu tana ihun Neman taimako kana tana kiran sunan Allah.
Abula tasan me tayi, shashasha wacce ladidi ke mata kallon Qur!,Da
n Bata yadda da itaba duba da yadda duk ta wani nuna tsorata da makirci don kar agano da Saka hannunta ciki.
Aguje Ladidi taje ga Amarya iyabo Tana kuka take rokonta Akan ta kira megidan ta sanar masa halin da Zuhra ke ciki.
Amma mirsisi iyabo tace
wayarsa akashe ta gwda dazu yanzu kam bazata sake gwadawa ba Dan tasan Yana hanya gunda ba network Dan haka ta fice mata adaki.
Kuka sosai ladidi ke Yi na tausan uwar dakinta
A ido dai Abula ta tsorata sosai Amma ckn zcyrta tana tunanin Mafita da Kuma
kudin data samu agun uwar dakinta iyabo.
Ladidi tayi dabarar kiran murja d wayar zuhra ta sanarta.
Ai take murjan t dauko mota ta taho gidan zuhra a sukwane,Allah ne kadai yakawota lafiya.
Murja ce ta kaita Asibiti aka Bata taimakon gaggawa.
All
ah yataimaki zuhra Babu abinda yasami yaron cikin nata,sai ita data Sha wahala Dan har suma tayi
Saida zuhra ta farfado ta samu sannan murja ta dawo ckn hankalinta dama tanata yiwa zuhra addua ne,wayarta a silent take tana zaune tsuru tana tunanin kada
dai Yar mutane ta mutu ko Kuma ace anrasa abinda aka Dade ana nema,ALH Hashim kawai take Tausaya Dan kam tashin hankalin da zai shiga bazai Fadu ba.
Saida akace mata zuhra tasamu hartayi bacci komai is normal Now,shine fa ta samu damar dauko wayarta da
ke cikin MOTA Dan ta kir ALH Sadi mijinta saita tarar da tarin missed calls
Da bakin nambobi data mijin nata
Shi tafara kira Yana dagawa yace mata ai gasu Nan ma da ALH Hashim Dan ya iso gari ya jikin zuhran?
Murja tayi musu albishir kan cewar ai
tasamu ma,baby ma lafiyarsa qlau.
Dayake a handsfree yasaka alokacin idon ALH Hashim akansa sai Yaja ajiyar zuciya dayaji bayanan murja.
Saida suka iso cikin asibitin ne ma suka San me yafaru Dan likitan yai musu bayanin cewar zuhra fa guba ce Tasha
a abin Sha.
Alh Hashim ya tada Hankalinsa Yana fitar da zufa Yana fadin"impossible!!walh sai na
ɗ
auki mataki me karfi,guba! Acikin gidana?!tabbas kashe min mata da abinda ke cikinta akai niyya Kuma walh ko waye yai Hakan bazan barshiba.ransa abace yake
fadin hkn
Likitan ya bashi shawarar akan ya Saka ido sosai kam Dan Agaba kar akara gigin Hakan sbd gubar me karfi ce Dan ma Allah yayi da sauran Numfashinta agaba ne,sannan da taimakon kawota da akai da wuri asibiti da saita cutar dasu duka da Ankara w
asu awanninma tabbas da bazasui escafe ba.
Agaba yasaka zuhra dake kwance kan gadon masu jiyya fuskarta tayi fuyet, Yana ta kallonta cike da tausayinta na yanda take karbar gashi a samuwar cikin Nan,
Yanata share zufa da hawaye hannunta na rike cikin
nasa.
Murja ta gamsu da son da yake mata,tana jinjina jarumtarsa ai da mijinta ne ma kuka zaita riskawa duk girmansa Amma baya da juriya.
Alh Hashim yace"ka kwantar da hankalinka kabi komai a sannu kayi bincike cikin lumana sbd dole a ckn masu Aikin
gidanka za,a samu Wanda aka hada Baki dashi akai Hakan.
Alh Hashim ya gyada kai yace"ba matsala ai CCTV camera zata nuna komai.
******
Da aka sallamota murja tana gunta har dare kana oganta yazo ya tafi da ita.
Zuhra jiki ba kwari ciwon cikin ya
lafa Alhajinta yanata Nan Nan da ita,iyabo ganin idonsa yasa tazo ta dubata hr dakinta
Iyabo bataso Hakan ba,taso ace cikin ya lalace gashi ta biya Abula kudin aikinta,tasan in zata sake sakata wani aikin agaba saita sake biya tunda wannan hak'anta Bai
cimma ruwa ba Kuma bazata hkr ba.
Ganin Alhaji baice komai akan maganar ba iyabo ta kwantar da hankali aranar don taci burin idan asirin Abula ya Toni tace ba ruwanta aciki in sunanta,inkuma ya Kori Bula Tasha Alwashin dawo da ita cikin kissarta da ban
hkrn da zatai masa.
Saidai batasan Alhajin lamfo yai musu ba,abin Yana cin ransa
Da safe kawai taji kiran bazata daga Alhaji kan cewar Maza tazo dakinta ta Kuma taho da Yan Aikin gidan su Abula da Ladidi Yana son ganinsu.
Ba karamin faduwar gaba t
a riska ba.
Alokacin da suka shigo dakin nashi zuhra na gefensa kan 3 siter tana Shan malt shikuma Yana bare mata ayaba.
Ladidi da Abula suka zazzauna akasan kafet kusa da center table
Yayinda matar gida amarya iyabo ta zauna akan 2 siter dake fa
cing dinsu
Bayan shiru na Dan wani lokaci Alhaji ya dauki remote ya rage karar tv kana yai gyaran murya yace"inason kowa ya Bude kunnensa dakyau zanyi maganganu masu MUHIMMANCI da Jan kunne tare da wata tuhuma Wanda inhar nagano da Saka hannun wani ack
nku akan yanda aka sakawa matata guba a abinci Dan Tasha ta mutu itada yaron cikinta to walh hukunci ne me karfi zai biyo baya Dan saina daure mutum ko waye acikinku.
Gaban iyabo ya Fadi cikinta ya kurda.
Ta maje tana aikawa da Zuhra harara ta kasan
idanunta.
Alhaji yace"Kuna sane da cewar jiya matata zuhra ta shiga wani Hali na yanda Tasha kunu ashe da guba aciki ko.?
Duk suka dago kai suka Kalli zuhra ladidi tana Al,ajab.
Yayinda fargaba ta cika Abula.
Ita Kuma iyabo haushin Kalmar dayac
e matata ta cikata taji kamar ta shaqo zuhran taita duka.
Alhaji yace"bawai zan tambayi waye ya aikata ba,kawai dai zan kunna CCTV camera ne muga Wanda ya aikata Hakan tunda in muka tsaya tambayar waye yayi ba samu zamui ba,Dan haka ba zamu tsaya batawa
kanmu lokaci ba,tunda kaf cikin gidannan an jona connection na cctv camerar data karsashin kasa data bayyane Wanda inma ta bayyane batayi to ta kasan zata bamu abinda muke nema,kunga inma wanine yazo daga waje yai wannan Aika Aikar sai muganshi mukuma kiy
aye wajen yin mu,Amala dashi bayan ya karbi hukunci knn.
Wani duummmm!da gaban iyabo ya bada saida zuhra taso ganota Dan ido tahau zarewa harda dafe kirji.
UnExpected Taga ALH yatashi ya kunna wata Na'ura Yana fadin"daga kowanne kewaye na lungu da sa
qon gidannan zaku gani tun daga na farkon watannan da wancen watan in Muna bukata zan Kamo saboda tsaro,kai ko lalata naurar waje kota falo akai to ta nan dakina zata dauko komai Kuma ta ajiyemin Dan haka kowanne ya Bude maganansa da kyau.
Yana gama yin
shiru sai ga babbar TVNsa dake falon Daya hada ta kunun harta fara Aiki
Kuma abinda t fara haskowa shine tarayyar me gadi da Iyabo sun kebe suna magana ya karbi kudi ahannunta kana ga Ranar da yashiga dakinta cikin dare aranar Alhaji baya gari,ga Kuma
Wanda ita tafara shigar masa.
Sai aka hau kallon kallo da ita da Alhajin Dan basu zata ba.
Zuhra ta Tsura mata idanu tana tuhumarta.
Iyabo ba Baki sai masifar fargaba ganin Na'ura ta dauko mata boyayyen sirrinta lallai yau kashinta ya gama bushewa a
she ALH ya hada komai adakinsa lallai ba,a ja da me kudi fa.
Shikuma Alhaji mamaki ya cika dashi Ashe cutarsa akeyi Bai saniba,lallai shi yayi wannan tsaron ne saboda Yan ta,Adda macuta na waje ashe zata farai masa amfani da macuta na ckn gida
Allah
yaita godewa Yana fadin"Alhamdulillah,Allah nagode maka Daka nunamin ha'intata da akeyi acikin gidana
Ya Kalli iyabo yace"Rahama me nake gani! Me gadi!me kukeyi dashi,me Kuma zakiyi da Mai gadina tirrr! Ya dafe kansa Yana jin kamar ya kashe Amma akwai
abinda yakeso ganin agaba.
Tiryan tiryan camera taita nunin short short vedio na kasantuwar kullum na shige da ficen mutanen gida daga falo waje kicin da kewaye da lungu na gidan.
Saida akazo lamarin kicin gaban Abula ya Fadi sbd camera fa ta fara n
unin haduwarta da Iyabo acan Wajen shakatawar gidan da suka fara qulla dill din Wanda ladidi ta gansu ta rasa fahimtar abinda suke qullawa sai gashi Allah ya fahimtarta ayau.
Yanda ta Bata wani Abu a yar kwalba har Ranar jiya da Abular tai Amfani da mag
anin ckn kwalbar gashi Nan ta zuba acikin cooler na kunu da suka dama ta kai kan dining table tana wani action na rashin gaskiya da harda yin leqe ko wani zai taho kana ta zuba ta boye kwalbar cikin breziyya ta koma kicin da sandarta tana ta wasu Yan dube
dube.
Abula taji wata zufa me kauri tana yanko mata,ji take kamar kasa ta Bude ta shige don kunya shikenan aikinta yazo karshe Iyabo ta cuceta kudin data Bata bazai amfana mata komai ba.
Take nadama ta shigeta saita durqushe gaban Alhaji tahau kuka t
ana Neman yafiya tana tonawa kanta asiri tana fadin iyabo ce tasata Amma tayi nadama.
Iyabo ma ba gaskiya sai tahau zufa tana qifqifta idanu ba baka sai kunne to me zatace?! Laifi biyu gareta fa ai tasan itama yau dai kam Alhaji ba yafiya sai hukunci.
Zuhra ta cika da mamaki lallai mutum mugun icce ne.
Alh ya kasa furta komai Dan mamaki,Bai gama da mamakin abinda Mai gadi da Iyabo sukai masa sai ga wannan.
Ya Kalli ladidi yace"ke Yar Albarka amintacciyar Matata tashi Maza kije kitasomin me gadi ag
aba.
Jim kadan saiga ladidi sun shigo da me gadi ya shigo ckn sanyin jiki da fargaba atare dashi.
Me gadi ya sunkui da kai alamun rashin gaskiya.
Alhaji yace dashi"Ilu ka haince ni Kaci Amanata,ashe akwai wani qulli da kukeyi kaida Rahama agidanna
n bansaniba,gaya min yaushe kuka fara mu,Amala da ita?
Cikin mika kai ba gaddama ilu yace"ALH na tuba ayimin aikin gafara tsautsayi ne da son zcy walh ita ta rinjayeni akan Naira dubu goma kullum da take bani Wanda gashi yau Bata amfanamin komai ba,walh
...
Alh ya katseshi da fadin"cewa nayi yaushe kuka fara ha'intata?ko saina nuna maka a majigi ka gani? To Kasani akwai komai a ajiye ackn CCTV camera da take dakina da Kuma ta karkashin kasa inma ta waje Bata Yi ko zaka gani insaka maka.
Alh ya dauko
remote zai sake dawo masa dashi baya.
Da sauri ilu ya rike hannun ALH Yana fadin"ban karyata ba Alhaji,natuba nabi Allah walh nasan na aikata aikin Dana sani
Ayau nayi nadama Wanda bana Jin Allah zai yafe min sbd ka bani yadda kuma kana fita hakkina Da
n Allah k yafe min...ALH yace"to kaje na yafe maka Amma daga yau ka bar Aiki Dani na sallameka kaje kacigaba da yiwa Rahama aiki,itama na sauwaqe mata Aurena dake kanta,ke Abula ki bita Maza.
Iyabo sai kuka haka Abula haka Shima ilun.
Alh ya Daka mus
u tsawa yace masa su fice masa a falo daga yau ya Daina yadda da kowa.
Hatta ladidi dake gefe cike da tsoron lamarin ya kalleta yace"ladidi zan Baki kudi me tsoka kije kija jari in Aurenki yazo ki sanarmin zan mk komai na kayan daki da Uba keyi a sakamako
n rikon amanarki da kaunar matata dakikeyi,Amma ki zauna agida babu batun Kara aiki damu ba Dan komai ba sai don gidan zai zama ba kowa don ackn satin Nan zanyiwa zuhra visar fita waje zata koma gidan Dan uwana acan zata haihu inta dawo intana da Ra,ayin s
ake zama da me Aiki to zamu nemoki,inkuma zatai komai da kanta to.
Ladidi ta durqusa tana masa godiya ta tashi ta fita.
Suma kowanne yatashi yafita sum sum.
Zuhra saida ta hadawa ladidi Sha Tara ta arziki da suturunta da sukai mata kadan da kudi i
ta kama tace da debi kayan Amfani na kicin sbd karsu lalace in gidan ba kowa har kayan abincin.aikuwa ladidi murna kamar ta mace.
Yanda me gadi da Abula suka bar gidan cike da nadama haka iyabo aranar ta hade karanta ta koma Lagos Babu wata riba atare d
a ita sai ribar saki da Alhaji yai mata.
Amma taci Alwashin fa saita Kara maka masa asirin da zai dawo Lagos bikonta afujajan in zuhra ta bar kasar....
To fa muje zuwa.
*MATAR TSOHO..*
👩🏼
🦳
👨🏻
🦳
(ta gaban goshi)
_a romantic and love
story_
❤
️
🩷
❤
️
🩷
Writing by Nabilancy Love
💘
Auntyn S and S
Page 16
To faruwar wannan lamarin sai ya Kara tsorata Alhaji yaji matan sun fice masa arai sbd mugun halin wasu,yaji duk duniya zai hakura yakarasa rayuwarsa da matarsa zuhra gudun s
ake faruwar Wani abun gareshi in yace zaita kare Karen Auren,shikam bazai iya da balain mata ba kala kala,kada ma wataran yai gamdakatar din haduwa da wacce zata karsa.
Hohoho mata sun koyar da Alhaji Hashim wai Dan ma ba da yawa yai ba
😂
iya Yar yaraba
wa ce ta tashi kansa,yo dama Ai Auren Asiri ba inda yake zuwa.
Akan wannan gab'ar zuhra Taga tsagwaron kauna gun mijinta,Motsi intayi sai ya zabura ya tambayeta ko lafiya,? Haka zalika zai sakata agaba da tambayar Ina ke mata ciwo,?me zai mata?me takeso
? Ga yawon shakatawa da
yake kaita in dare yayi Kuma afita yawon motsa jiki saboda lokacin cikin yashiga wata na bakwai ladidi amintacciyarta ta koma gidansu ta bar Aiki Amma fa sun cikata da kudi don taja jari
Iyayanta koyaushe abinta suke da Adduar s
amun waraka intazo haihuwa.ffffAaAf
Haka zalika itama takan Hana idonta bacci ta tashi sallar cikin dare tayi nafilfunta tayiwa kanta addua tayiwa iyayenta da mijinta.
To ahaka dai Rayuwa nata tafiyar mata cikin kwanciyar hankali alokacin Yana kaita wa
ni private hospital tana ganin likita suna mata awo kafin idan Takusa haihuwa ya kaita kasar Wajen da zata haihu acan.
Anyi mata scanning anga Namiji ne Kuma lafiyayye dashi.
A yanayin yanda yake da yawan motsi acikin tayi zaton ko twins ne ma.
Ba
yan sun dawo sun baje a falon tana zaune ajikinsa tana ta faman masa shagwaba wai cikin Nauyi ita kam kawai ayi mata CS acireshi tun yanzun.
Yayi dariya tare da Shafa kumatunta yace"haba babyn kauna,me yasa zaki zama raguwa ne,ki daure lokaci qalilan ya r
age Miki,nikam banason a yanka mini ke,Kuma Nafison ayi Miki komai a England ai.
Ta zobaro Baki cike da shagwabarta datake mata balain Kyau tace "kai Chu-chuna Allah Dan bakasan yanda nakeji bane.
Ya Kara mannata da jikinsa yace"nikuwa nakeji,ko baki
san tare dake muke laulayi da rainon cikin bane.?
Batasan lokacin data Dara ba tace"lallai ma shiyasa ashe naga munayin karba karba da cikin.
Shima dariya yayi yace"kinsan Allah da anayin Hakan kinsan zanyi ai,Kuma duk da CS din yanzun ya zama na zam
ani ba kamar na baya ba da ake yanka mace yanzun abin yazo da sauki nikam Nafison ki haihu da Kanki babyn kauna Hakan yafi sau dubu,kinsan da ace inason CS da tuni na biya kudi me tsoka tunda nafiki dokin son ganin Son.
Tace"to wanne sunan Kuma za,a Sak
a masa tunda abaya kace in macece za,a Saka mata Amina sunan mom Allah