Showing 33001 words to 36000 words out of 40654 words

Chapter 12 - MATAR TSOHO COMPLETE

30 Sep 2026

1419

and S)

Page 18.

Wannan babban Tashin hankalin Daya Riski Ahalin ALH Hashim fadar irin halin da suka shiga ma Bata lokaci ne.

Ba karamin karfin Hali ALH Murtala yayi ba,rashin

Dan,uwa abokin shawara bagatatan akwai tashin hankali.

Shi aka fara sanarwa Wanda ba shiri ya baro gun Aikinsa,Wanda dama yanata duba lokacine Yana jiran idan Dan,uwan nashi ya iso ya bar office yaje ya Daukoshi,saiga sakon mutuwarsa Wanda bazai taba m

antawa da wannan Rana ba.

Matarsa ce kawai ta ga tashin hankalin Daya shiga,ya ringa fidda zufa yana matsar kwalla.

Suka qule adaki suna kuka na alhinin abinda yasamesu,daga karshe suka hau shirin Tasowa zuwa Nigeria Wanda suka fara nuqu nuqu na sana

rwa zuhra

Wanda alokacin tayi wanka tayi shiri na tarbar zuwan mijinta,tayi kwalliya itada yaronta sunyi fes dasu,kawai taji Hajiya Laila na sanar mata cewar ta shirya Maza inji daddyn twins zasu wuce Nigeria yanzun.

Ta tsorata sosai tahau tambayarta me

yafaru,? Amma sai Hajiya Laila tace"ke dai ki shirya Maza zamu wuce yanzun ne,nima baice min komai akai ba,Amma dai yace agidan ne ba lafiya.

Wannan Abu ya tsaya mata arai,ta ringa tambayar zcyrta shin agidansu ne ba lafiyar ko a gidan iyayanta? Ba dai

me Bata wannan amsar.

Tana shirya kayansu a luggeg tana kokarin kiran nambar mijinta Amma the phone is switch off

Gabanta ya shiga faduwa kada dai ma ko shine ba lafiya suke boye mata.

Allah sarki baiwar Allah Sam Bata kawo mutuwa yayi ba ma.

Har Allah ya kawosu gida Nigeria suka diro qlau.

Da ace ta kunna radio a shigowarsu cikin jahar da taji rasuwar tashi Dan kaf media ta dauka anata yadawa a rediyoyi da gidan Television da Facebook anata pos na hotonsa da Yi masa addua.

Ita Sam Bata

ma kunna Data ba bare tagani,suma kokarin dannewa sukai Amma fuskokinsu kana kalla kaga damuwa atattare dasu.

Gabanta ya tsananta Faduwa da suka doso cikin unguwar Wanda ta cika taf,Babu masaka tsinke da Dan Adam

Sai kallo ya koma kansu Yan zaman ma

koki.

Hajiya laila ce ta kamata suka shiga ciki Dan kanta ne yahau juya mata Dan kam da ace Boy A hannunta yake da saidai ta Yar dashi sbd gigita da tayi,tai ta zazzare idanu tana son taga ta inda Alhajinta zai billo tana Jin fargabar kada dai ace mata

shine ya rasu.

Sai zcyrta take gaya mata cewar AA saidai ko megadi ne.

To jin hajiya Laila ta riketa tana mata rada akunne akan cewar ta Nutsu ta ringa ambaton Allah.

Saifa jikinta ya saki ta sadakar.

Ai suna shiga cikin gidan Taga Hajiya Jamil

a Tayo kanta da kuka ta rumgumeta tana fadin shikenan sun rasashi,bango ya Fadi,take itama ta sulale ta Fadi kasa.

Allah yasa Murja na kusa tayi saurin tallafota ta fado jikinta tayi saurin kwance boy Bilal sai aka rufu akanta ana Shafa mata ruwa.

Ai

zuhra Bata farfado ba aranar har aka kaishi batasan inda kanta yake ba.

Bilal kuwa yaro me hakuri baccinsa kawai yake don ya gama rigimarsa Kuma can yayi shiru Yana tsotsar hannu kana saiga bacci yai awon gaba dashi.

Sun shiga tashin hankali musamma

n iyayan zuhra

Inna da take tare da ita tanata tofa mata addua.

Wata nurse ce atare da ita Wanda aka daukota danta kula da ita.

Wannan shi ake kira kana taka Allah na Nashi,karshe Raguna da Saniyar Daya Siya da hannunsa Dan Ayi hidimar suna dasu,

to dashi akai hidimar Taron mutuwarsa.

Kullum gida ciki da wajensa cike da Al,ummar Annabi

Mutum ne na mutane,qungiyoyi daban daban suna zuwa gaisuwa tun daga safe har dare,wadanda yake tallafawa da wadanda ya kafasu

Islamiyyoyi ma sunzozzo gais

uwa daga gurare daban daban saboda shaharar Alhaji Hashim baki bazai Fadu ba,shi din me taimakon JAMA,A ne.

Ga 'yan TASKAR Nabilancy ma ba,a barsu abaya ba sunje gaisuwa saboda zuhra

Su Kuma 'yan group din Y@N AM@NA sunje saboda ALH Hashim ne fans dinsa

ne sosai

Sunsha kuka sosai jagabarsu da aka gaya mata fa aranar suma tayi ta farfado Shamsiyyar Sadi,farko ma Bata yadda ba sbd aranar sunyi waya ya tura mata kudi da zatai wakar suna shiyasa ta karyata tace kai badai Alhaji ne ya rasu ba saida Ruky mam

an Ayaan ta rantse mata kana ta gaskata,Ita Kuwa Likitar da yake gani Yar amanarsa Dr Bilkisu kuka harda sharb'e, karshe data Fadi ma saida aka kira me ruqiya,Jidda da Fiddausi hotoro da Fiddausi sheka sukam suma sukai saida aka Shafa musu ruwa Dan Kujerar

makka yai musu Alkawari ga Halima Yar dagwas Kuma taci burin ita zatayiwa me jego dinkin fitar suna sai abin yazo da haka aikuwa taci kuka

Acikinsu kuwa akwai wata Hajiya Dayyiba fadar irin Tashin hankalin data shiga Bata bakine sbd ita zatayi mata gy

aran jiki da dilka da qunshi murja ta daukota aranar yai mata maganar cewar in madam ta dawo zai hadasu sai tayi lissafin kudi,kai wadannan mutane fa sunci buri shiyasa kowacce ta fita haiyacin ta ta shiga damuwa suka kwana suka wuni zancen rasuwar Alhaji.

to Mukam saidai muce Allah ya Kara muku hakuri,Allah Kuma ya mantarku.

😂

Wannan Kenan!

******

Bayan sati Daya!!

Anyi sadakar bakwai,alokacin zuhra ba baka sai kunne,Bata magana har alokacin bawai kurmancewa tayi ba,kawai maganar ma ta fita aranta

sai Abu ya zama dole take Daga kai tace E ko tace A'a

Ko wayarta ma batasan inda take ba,in gaisuwa akazo mata saidai tabi mutum da kallo inkayi addua ta daga kanta da hannunta

Kowa tausayinta yake ji,alokacin da tafara jin dadin Aure alokacin aka ja

rabceta ga danyen goyo.

Tare suke kwana adaki Daya da murja,da khairat su suke tausarta suna Bata Baki dakyar take iya cin abinci sau Daya arana.

*****

Kwana goma da rasuwar iyayanta sun koma gida

Dan agidan suka tare ana karbar gaisuwa dasu,mah

aifinta suke karbar gaisuwa shi da Alhaji murtala da Alhaji sadi mijin Murja.

Khairat kuwa da ummanta suka tafi da innar zuhra ita tana Nan tare da ita.

Khairat ke rainon boy,ita ke masa wanka da lallabashi inzaiyi bacci,sannan ta ringa lura da lok

acin Shan nononsa tayi mata dolen ta bashi.

Ita Kuma murja ita ke sakata yin wanka ko tirsasawar cin abinci da gaya mata lokacin sallah da tausarta da Dada'd'an kalamai na kwantar da hankali.

Ranar da Alhaji yai sati biyu da Rasuwa aranar Rasuwar

ta zamar mata kamar sabuwa ganin kowa zai watse ya barta.

An tattaru a falon kowa Yananan harda iyayanta tana ta kuka suna tausarta.

Alhaji Murtala ya gyara zama bayan yin Addua cikin Nutsuwa yace da Zuhra"wato a farko kafin nayi zurfi cikin magana m

e muhimmancin da zan fada gareki zuhra shine in fara da Kara furta Miki da Kalmar hakuri!hakuri!hakuri Dan Allah,kowanne bawa sai an jarrabceshi fa,ke wannan itace taki jarabtar,Allah ya karbi mijinki bawai Dan baya sonki da farin ciki ba,lokacinsa ne Kuma

yayi Wanda muma Nan duk Hakan muke Jira,in kikai hakurin dai shine zaki nuna kin karbi jarabawarki hannu bibbiyu sannan Hakan ya nuna kinci jarabawarki,fatanmu Allah yasa Miki salama Zuhra,Allah Kuma ya raya mana wannan yaro Bilal....kowa agun ya amsa da

Amin.

Yaci gaba da fadin"Abinda nakeso na fara da fada biyu shine yau kowa zai koma gidansa za,a barki ke kadai bawai Dan anaso ba sai Dan yazamar mana dole yin Hakan,sannan na yanke shawarin cewar Iyayanki su dawo cikin gidan Nan su zauna atare dake s

aboda gida Naki ne Kuma yai miki girma,zamansu atare dake hakan zai kawo mk salama,da martaba da kima Dan inkin fita a takaba dole wataran zakiyi Aure ne,Kuma ba wai na Raina gidan Iyayanki ba Aa kawai naga gidan da suke ciki yai karamin da zaki zauna ki W

ala aciki tunda kin Saba zama anan,sai magana ta gaba.

Yai shiru Yana kallon Alhaji Sadi da yai Tagumi.

Gaban zuhra ya Fadi kada dai suce da Alhaji sadi za,a hadata Aure Nan gaba,Dan Akanyi Hakan,lallai kuwa da Hakan ba zai taba yiyuwa agunta ba.

Sai taji Alhaji Sadi yace"Eh!Hakan yayi sosai,Komai na Dukiya da Duk wata kadara ta Alhaji tana Nan a hade an kammaleta guri guda sai komai ya lafa za,a fitar Miki sai Kuma a fitarwa Bilal,haka zalika in zaki rike ta Bilal bazamu Hana ba,inkuma zaki bawa A

lhaji Murtala amatsayinsa na Wakilinsa arayuwa to Hakan dai duk Dede ne.

Alhaji Murtala Daddyn twins ya gyara zama Yana fadin"sai magana ta gaba da nake fargabar fadar ta,nake Kuma fatan bazakiga bakina ba.

Yaja fasali kana yace"game da Boy ne,wato K

afin rasuwar Alhaji mun tattauna dashi agame da cewar indai ba ransa aduniya to a mallakawa Hajiya Jamila kanwarsa wato Autarmu Bilal Wanda gata a zaune.

Hajiya Jamila tai kasa da kanta sbd jin Nauyin maganar da itama ya taba mata wannan alkawarin Amma

akwai Nauyi ba dadi karaba D'a da uwa fa.

Zuhra taji wani zugi cikin ranta,wani hawaye siriri ya surnano mata Amma a fuska Bata nuna komai ba tayi saurin gogewa tare da Kara rungume Boy dake jikinta Yana bacci ji take kamar ma alokacin za,a karbeshi.

A hankali sukaji tace"wannan ba wani Abu bane,ni kaina ya taba gaya min,abisa Tausaya mata da yake na rashin haihuwa da batai ba yasha Alwashin Bata duk abinda na Haifa,saigashi Allah Bai Ida nufinsa Yana Raye ba,insha Allahu zamu cika masa wannan burin,N

ayi Alkawarin inhar na Yayeshi zan batashi nasan zata iya rikeshi bisa Amana.

jikinsu yai sanyi wani tausayinta ya shigesu.

Iyayanta kuwa ta burgesu,inna tayi fahari da ita sosai wannan ya nuna tarbiyyar data Bata tayi Rana,Kuma ta yarda 'yarta me ta

wakkali da hakuri ce.

Dan haka sai Babanta ya gyara zama yace"wannan Batu ai dama bana damuwa bane,Alkawari ne akeson cikawa mamaci,kowa Nan yasan Nauyin Alkawari bare ita saukakkiya me tarbiyya Ina fahari dake yarinyar kirki karki damu,Wataran in kikai

Aure zaki iya hayayyafar gomansa ma,ke dai ki bishi da Addua kinji,Allah yayi mk Albarka.

Kowa agun yace Amin,ita Kuwa a zcy ta amsa

Murja taji ta burgeta Amma ita kam in itace ba iyawa zatai ba kam.

Khairat kuwa ma sai Taga ai abin ma yazo da za

lunci Amma dai ba yanda zasui tunda me Abu ta Aminta.

Hajiya Jamila kuwa ta kwantar da murya ta Kara tausarta kana ta nuna cewar zasu tsaya mata a komai agaba,ba,a Rabu ba ai,sannan ita kam yaro ma sai yayi wayo sosai zata karba ba ma yanzun ba sai ya I

sa sakawa a makaranta Kuma ko ta karba tayi Alkawarin ringa kawo mata shi.

Ajiyar zcy zuhra ta saki a bayyane tace"Allah ya jikan Alhaji.

Kafataninsu suka Amsa da Amin.

To Taron ya watse bayan an Kara rufe taro da addua Wanda Dukiya suka danqa w

ata dayawa ahannunta da wasu kadarorin, kana Alhaji Murtala zai tafi da wasu Dan yatayata adanawa, Dan awashe gari zai koma shi da iyalinsa England.

Bataso khairat ta tafi ba Dan ba yanda zatayi ne sbd An fara maganar Za,a kawo kudin Aurenta ne shiyasa

ta koma gida Amma kam tanajin Dadin zamansu tare tunda umman khairat bazatace ta dawo gida ba sai in itace tai niyya

To zama fa yadawo da iyayanta gidan suka dawo tare,oh lamarin Allah kenan,saiga baba me gadi yadawo babban gida

Zuhra ta Bude masa b

abban shago a kasuwar kwari Yana saida yadika da shaddoji har yaran shago ya samu.

Baba ya fara shigowa gari fa Shima shigarsa yake ba raini.

Boy koyaushe na tare da inna sunyi sabo yaron ya fara wayo.

Suna zaune ne cikin kwanciyar hankali da Jin

dadi

Har me Aiki suka tsayar uwani takanzo tayi wanke wanke tayi girki ta tafi.

Motocin Alhaji na cikin gidan guda uku kowacce ta Nan a ma,ajiyarta sai tata da take fake a gefe guda a parking space din duk anrufesu da tintek.

Yawan tunane tunanen

da take yasa duk ta rame,ga yawan mafarkan Mijinta da takeyi an nuna matashi awani guri me korama ko lambu ko a guri me sanyi da qamshin dadi

Takan yawai sadaka da kyauta da taimako ga marashi duk saboda Allah ya isar masa ladan.

Farin cikinta ma Ya

n,uwansa suna sonta ko yaushe takan amsa kira daga waninsu.

Daga kasar waje basu yar da itaba,Hajiya Laila suna tare a online Always

Shima Alhaji Murtala yakan kira yaji ko akwai wani abun ko in yashigo kanon yazo mata takanas su gaisa.

Hajiya Ja

mila kuwa sukanyi waya,bataso tazo ta tsinka mata zcy ta zaci ko tazo ne sbd boy.

Shiyasa ta gwammace ta kirata su gaisa su taba hirarsu kawai.

Murja ce ta Bata shawarar ta koma makaranta kawai Hakan zai rage mata zaman kadaici ko Kuma ta fara busine

ss online.

Makarantar dai tayi na,am tace me zata nema a kasuwancin kudi ne dai Kuma akwai su sunyi hannun Riga da Talauci

Karatu kuwa dama burinta kenan,Shima yataba ce mata zataci gaba inta Haifa masa Yara uku ko biyar to ashe bazaiganiba.

Lo

w sch ta nema ta shiga so take ta Karanci Aikin Lauya.

Cikin Ikon Allah Kuma tana farawa taji hankalinta ya kwanta da sch din

Ta fara sakewa karatu ya fara shigarta inna take barwa Boy Wanda alokacin shekararsa biyu Wajen wata hudu da yayensa kena

n yaro yataso da kuzari ga wayo gashi very beautiful kamar Dan larabawa har wata wushiryace take atsakanin hakwaransa da suka fito na sama.

Ita kanta kyan yaron har tsoro yake Bata intana kallonsa,takanji inama Dad dinsa na duniya da yaga gata sosai,gas

hi a kullum tana jin kamar lokacin Rabuwarsu ya kusa gani take ko yaushe zata iya ganin Hajiya Jamila tazo karbar shi.

Yanda tayi Alkawarin Bata da son cikawar Alkawarin Margayi ai dole ma ta Bata shi.

Shiyasa ma Bata Saka damuwar rabuwa dashi aranta

ba,tasan Allah zai Bata zuria agaba madadinsa Kuma duk a inda yake dai yananan amatsayin Yaronta ai,Dan kamar riko zaije wani Wajen bawai kyautar har Abada bane tunda inhar ya girma sai inda ya zaba,Dan dai wani Sa,ilin in akai sabo rabuwar dakyar take yi

wuwa ne ita Kuma takan hangi Kirkin Hajiya Jamila

Karatunsu ya fara mikawa alokacin bikin khairat yazo Dan Kara bikin akai sbd tana son tagama NCE dinta sbd suna gab da shiga NCE two lokacin Bikin yazo

Yanzu kuwa sungama biki ya rage saura sati biyu

suka fara zirga zirgar zuwa kasuwa da gyaran jiki itada zuhra Wanda a dole zuhran take binta sbd inta dawo a sch take biyawa ta

É—

auki khairat din su tafi sai yamma suyo gida.

Anci burin yin gayu a biki Dan ta manta yaushe Rabon tayi kwalliya ma Amma ta

nason ta Dan D'ana ayi da ita tunda yanzu lokacin capacity ne inbakayi ban guri.

Ta kashe kudi sosai har amaryar saida ta kama Baki tace"Ah zuhra! Hardasu gyaran jiki da biyan kudin make up tunkafin zuwan lokacin!ah lallai inaga Wani gwarzon ne zai bayy

ana.

Zuhra ta harareta alokacin suna tafe ne ta karya kwana zata shigar da motarta layinsu tace da khairat din"Hhuumm Allah ya yafe Miki khairat! Saboda kawai kaina zanyi kinji,kara'i zan danyi ba wai Dan kowa ba,Wanda bana ma fatan kowa yazo kinji,bafa

zanyi Aure akusa ba ko mijin ma yazo sai ya Jira,ba wani namiji dake gabana,ke Banga ma Wanda zai burgeni ba walh,haka kawai Ina zaman zaman a jam,iyyar Zaman lafiya ki daina mini wani batun namiji,In kuwa ba haka ba walh sai in fasa.

Khairat tace"an

shigesu me zaki fasa?

Zuhra tace"komai ma.

Sai Kuma sukai dariya atare alokacin da tayi parking a kofar gidansu khairat din tana fadin"oya amarsu fita kiyi gida nima inyi gidanmu,agaida ango inyazo,sannan agaidamin umma,Kuma kicewa Yaya Ma,aru gobe a

je a debo kujerun na biya kudin sungama dazu carpenter din ke gayamin ta whasApp na manta zanturo mk ma kigani saina koma gida.

Khairat ta dubeta da wani farin ciki tana fadin"Kai kawata jazakallahu khairan,gaskiya kin gama min komai walh,gudummawar kuj

eru ai ba kowa ba walh,Allah ya biyaki da Aljanna.

Zuhra ta rufe idanu tare da lunshesu tana fadin"Amin, meye na godiyar,kin manta agidanku nake samu inci in koshi kenan ada,kin manta har garin tuwo ana bamu agidanku kenan ada,kin manta....da sauri khai

rat tace"ba tone tone da tunano da nace kiyi ba,rayuwar Nan ta shige Allah ya Kara mana Rufin asiri,ki gaida inna.

Ta fito ta rufe murfin motar tana daga mata hannu.

Zuhra ta murmusa tana hangen gidansu na Da Wanda suka saida tana yin ribas tana koka

rin barin layin

Yayinda wasu tsoffi a majalissa suka hau daga mata hannu sbd sun ganeta abokan babantane.

Da sauri ta faka ta fito taje ta durqusa ta gaidasu kana ta basu rafar Yan dubu na Dubu 20 su hudu ne dama

Aikuwa sukaita shi mata Albarka.

*****

An fara biki inna agidansu khairat ta tare duk inda tayi M.Bilal Yana tare da ita sunyi mugun sabo,Wanda zuhra ita take tausayawa ma randa duk akazo tafiya dashi sbd shaquwarsu.

Ranar kamu aka shirya yin event na cocktail da kamu gurin

da aka kama din Ango ya biya me tsada ne yayi bajinta ba duk kai ba sbd Yana da abokai Yan karya Shima Dan gayu da son Nuna fafa

Amarya da kawayenta kuwa ansha ashobe me tsada haka ango da abokai ma anyi shiga ta top Wanda sukai shigar Yan gayu duk iri

Daya har takalma da agogonsu,sunsha glass

Da amarya da Ango kuwa suka fito anyi Watsin nera Abokai akaita likin 'yan dubu dubu.

Aka dawo kan kawaye ana musu kirari Amma tsit kakeji

MC yasamu abinda yakeso ya fara wasa amarya yaga ba kawar da ta

fito Dan fitarta kunya kamar yanda ango abokai suka fitarshi

Ita zuhra idon mutane ne bataso Amma tana son fita sbd ajakarta harda dollars ma ga sabbin Nairas

MC yaringa cewa a lasifika"Amarya kiyi hakuri Baki da goshi kamar ango,da alamar kawaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login