Showing 6001 words to 9000 words out of 40654 words

Chapter 3 - MATAR TSOHO COMPLETE

30 Sep 2026

1411

sabuwa ce ita to ya kamata saka Mata komai sabo.

Dama ya tsaida mahaifinta daga Aikin gadi na zaman gate din gidansa yasaka angyare musu gida yadawo sabo kwal,sannan a komai na kayan Aure ya gama da

su,gida an Saka mata komai sabo,sabon me gadi ya fara Aikinsa.

An fara biki haikan agidansu zuhra ranar da zatai saukar karatun Alkur,ani me girma aranar aka Daura mata Aure da Alhaji Hashim gida ya cika Danqam da dangin uba Dana uwa,sai da aka Dauro Au

renta karfe goma daidai kana aka dauki haramar zuwa wajen walimar Taron saukar da aka tsara a filin islamiyyar tasu.

Kai tsaye daga gun daurin Auren Alhaji Hashim ya zarce shi da Mukarrabansa Amarya na can cikin Dalibai bazaka iya Ganota acikinsu ba don

fuskarsu rufe take ruf!da nikaf sannan kafarsu da safuna sunsha hijab har kas!

Sai a gun karatu da aka kirata ta fito yin karatu Alhaji yaji zazzaqar muryar amaryarsa cikin suratul Bakara tana rerowa cikin nutsuwa da salon burgewa tana Jan kira,a ba ga

rgada tana kabbarewa Dalibai suma suka dauki kabbara ta koma anitse ta zauna A mazauninta

Bayan ankammala aka dawo ana Kiran Dalibai don amsar Allon zaiyana da kyautauttuka.

Akwai kyauta daga gwamnan kano Daya turo wakilinsa Wanda aka ware Dalibai m

utum biyar da sukafi kokari da tsafta da sukai karatun aka basu, zuhra itace ta farko ita aka kira ta fara karatun anware kyautarta a babbar Envelope kudi ne Naira miliyan Daya ta biyu Kuma tasamu dubu Dari biyar sai ta uku aka bata firji da Qur,Ani izifi

60 sai ta hudu tasamu keken dinki da Qur,anin Na biyar namiji ne katuwar TVn bango da Qur'ani yasamu.

Shikuwa Alh Hashim dayake gurin shi da Tawagarsa atake yai kyàutar bajinta ya Bada nashi Albishir kan cewar ya baiwa makarantar kyautar fili filoti d

aya da siminti buhu 20 da kudi naira miliyan Daya don ayi gini,malamai sunji Dadi matuqa gaya don ya futarsu kunya ya jiyarsu Dadi mara misaltuwa don dama Inda suke yin karatun Na Haya ne, rumfuna aka kakkafa.

Haka zalika kujerar makka ya bawa Shugaban

makaranta sannan yace ya bawa gwarzuwar shekarar tasu kujerar Makka itama dama zuhra ce matar tasa sai wasu agun sukaga ko don yaga tashi ce ita,Amma wasu sun San ya Saba irin wannan kyautar bajintar agun Saukar karatun indai yaje koina ne ma.

Akaita j

injina abin ana Saka masa Albarka.

Sannan malamai agun suka hau yiwa Auren zuhran fatan Alkairi da sa Albarka domin itace silar samuwar Arzikin Nasu ayau...don ta Tako sa'a Suma gashi sun fara Dandala.

Aranar zuhra ta kasance da farin ciki,abinda Alh

yai mata ba karamin faranta mata yai ba,ta kasa jurewa ta tura masa saqon godiya da fatan Alkairi

Yana Gani ya saki fara,a yana zuba murmushi tamkar tana gun,ya Maida Mata martani da kalaman soyayya.

_don ke Akai komai Sarauniya zinariya fatana All

ah ya bamu zama lafiya yasa Albarka acikin Aurenmu I love you_

Tana Gani tayi dariya kawai kunya yasa takasa tura reply Amma taji Dadi Ckn Ranta sai ta turar da wayar gefenta kawai tashiga zarafin gabanta,dama shi yakawo mata wayar ranar Daya fara zuwa

gunta.

Humaida da suke kira HUMKAM da tazo daga Maiduguri tayi mata gyara sosai na amarci don tayi Aiki sosai wajen ganin ta fito da amaryar fes! Dan haka tun da taxo ta fara bata maganin infection sbd wannan shine rigakafi na farko da yakamata ace mace

ta fara yi kafin aure duk safiya Humkam Zata dama lalle da kurkur ta zuba masa man kwakwa tasa Zuhra ta cire kayan ta ya rage daga ita sai daurin zani ta dauko wannan hadin ta shafe jikin zuhra dashi bayan ta shafe jikin sai ta Debo gaushi cikin kasko ta

debo turaren nan na magani mai suna Khairun nisa ta zuba acikin kaskon Sannan tasa zuhra ta zauna akai sai ta dauki rigar gyaran jiki ta rufe ta, amfanin wannan turare yana da yawa yana matsi yana cikowa da gaban mace yana sanya dumin hq sosai Sannan yana

maganin sanyi yar uwa shin kina amfani dashi amatsayin ki na ‘ya mace,?hhuumm ba a cewa komai dai, bayan turaren ya mutu Humkam ta dauke katon rigar da ta dorawa zuhra. Man kad’e ta dauko ta narka shi da Manshanu ta zuba garin ganyen magarya aciki da gari

n kurkur ja ta dama su ta sake zuwa ta shafawa zuhra Sannan ajikin ta sai gashi ta kuma dauko gaushi a wannan Karan Wani irin turare ta dauko zuhra na ganin shi tace “Aunty Humkam wannan fa “Zuhra wannan shi muke Kira bita zaizai turare maisa ango kukan da

di Daren farko .

Dama gyaran jiki sunkai sati da farawa, Amma tamkar Wanda sukai wata sunayi sbd yanda zuhra ta fito Shar tana kyalli fatarta kamar ta jarirai ko Ina tayi sai qamshi da Haskawa, ga tsume tsume data ringa bawa zuhran abin ba,acewa komai.

Har Qosawa zuhra tayi,baya ma naci Dana kaza da ci da kifi da ci da Nama da ci da kwai,har ginsarta sukai taji ta tsanesu.

Su gunba da su na Sha da Madara kuwa ba'a cewa komai dai.hadin 'yar gata tayi mata Wanda sai wance da wance.

Takanas dama ya

hgana da kaltume da Humkam (Humaida)da sukazo daga Meduguri zuwa wannan biki Wanda sukazo Dan yin Kara sbd sun hada jibi da inna

Haka zalika kudi suka saki don so suke zuhra ta dawo tamkar jaririya,dama ai sai kaki kudinka zakaga kyanka awannan fanni.

Acikin kawayen Amarya Khairat ce babbar kawarta Basu da nisa da ita, kama Baki tayi tana mamakin yanda tashi Daya Zuhra ta koma tamkar tsada, tana kallonta kamar kar ta daina, cikin Raha tace "Lallai in sugar daddyn Nan ya ganki yanzu nasan ba magana,

saiya saki layi ko a gaban waye kuwa".

Duka zuhra ta Kai Mata tana murmushi tace. "Wlh Baki da kirki, ita MATAR TSOHO ba ruwanta da damu kafin dare yayi nisa ma yayi barci" ta fad'a tana dariya.

'Bayani zakiyi yarinya da yaren garinku".

Tana dariya

itama.

"Wai me ki kaga nayi ne khaitar?". Dariya khairat din ta qara yi.

"To ai ke din ce kin canza,kin dawo baturiya ko ince ba India sbd fatarki tayi kyau ga sheki ga wani qamshi da kike DUK inda fa kikai to kamshin na binki Gaskiya yakamata kawata ki

hadani da Aunty Humkam dinnan taku,sbd bikina yakusa gaskiya Kuma Babu inda zanje nayi asarar kudina inba gunta ba,Dan ma naji kamar daga Maiduguri dazo Kinga tai Nisa ya kenan?

Zuhra tace"To ai zaki iya samunta anan kanon ma Kuma daga koina ana zuwa g

unta acan Maiduguri ma ana ganinta Amma intaje bata dadewa garin iyayenta ne Nan Kuma Aure take anan akwai babban shagonta acan hotoro ringroad bayan gidan man Muhibba Kuma walh bakiga yanda take da kirki ba ga iya saukar Baki ga iya gyaran amare magungun

a kuwa akwai kyau da sauki batada tsauwalawa....Khairat tace ai nagani walh abin ba a cewa komai gaskiya zan karbi nambarta sbd bikin yakusa baza.ai wata ba yakamata mu Jone da Auntyn Humkam nima zan saki kudi walh sbd ta gyareni fes don inada kishiyoyi ke

ma da Babu gaki Nan Shar tayi miki Namijin kokari kin fito fes! Ina ga ni da bani ka dai ba gaskiya bazanyi sanya ba kawata.

Zuhra tana dariya tace"yakamata kam.

*******. ***"""""

Motoci kusan ashirin ne sukazo daukar amarya kowacce MOTA tana

wace wannan a haduwa Tabbas ko Yan zuwa jere Yan,uwa da masu zuwa Dan tsegumi sun tsorata da ganin haduwar gidan da kuma irin shakiyyan hadaddun kayan da aka jera mata sbd dama kawai sunje ne Dan yin gyara da seta fasalin kayan don acan suka tararsu tunda

shi yayi komai ba kowa ya fargaba a unguwa saidai sun dawo suna Yan tseguggumin kyau da haduwar gidan suna Kuma tantatamar ba iyayanta ne zasui komai ba Dan bazasu iya Saka uban kudade su sai mata Kaya Yan waje ba tunda kowa yasan Talaucinsu.

Aranar aka

Kai Amarya mata sunata turmutsutsu da saurin shiga MOTA harda Wanda sukaje jere suna son komawa gano aljannar duniya.

Ita dai zuhra kuka kawai take ackn mayafi kukan rabuwa da gida da sabo da zama da iyaye gashi yau lokacin rabuwa yaxo abin Yana taba z

cyrta,rarrashinta da wani bari na zcyrt keyi ne ke kawo mata sauki na tuni da cewar BURIN AUREN TSOHO fa ya cika.

Saidai Kuma Da kowa ya watse sai ga zuhra ta fara shiga yanayi na tsoro sbd gidan shiru tsit sai kukan tsintsaye kawai take jiyowa danma

akwai Hasken wuta na Sola tarwai koina agdn Amma ita kanta girman gidan da yanda ake ta fadar yanda komai ya kasance sai takejin wani iri.

Tana can tsakiyar gado kanta lullube da mayafi tajiyo dirin motoci a can farfajiyar gdn take ko Gabanta ya yanke

ya fadi Ras!!! Ta tabbata dai tazama matar Alhajin, Yanzu shikenan da shi zata dawo kwana a daki Daya,a gado Daya? Ta tambayi zcyrta,labarirrikan da takanji abakin kawaye in ana hira a sch ya fado mata na yanda komai ke gudana a rayuwar Aure,na karbar bud

urci ga miji,da wahalar da ake Sha,saidai Kuma wani bari na zcyrt na mata tuni da cikar burin ta,Abinda take da buri ne fa Allah ya cika mata shi,Auren TSOHO! Kenan ta tabbata dai ta zama MATAR TSOHO tunda gata agidansa. Kawai saita tsinci kanta da yin mur

mushi tana Shafa fuska.dan ance tsoffin sunfi iya bi da mace,sunfi iya soyayya da tattali da kulawa ga rangwami a tarayyar duniyar Sex.

Hayaniyar muryoyi tajiyo a falo alamun ba shi kadai bane Dan muryoyin maza taringa ji sannan ya nufo bedroom don ya

tabbatar tana ciki, ya shigo dauke da sallama a bakinsa.

Bakinta ne kawai ya motsa sautin amsa sallamar da tai Bai fito ba ga faduwar gaban nata na Kara hauhawa.....

Muje zuwa.

*MATAR TSOHO*

👨🏻

‍

🦳

👩🏼

‍

🦳

(_Ta gaban goshi_)

~page~0

️

⃣

5

️

⃣

_The Romantic book_

💗

{ ~alove story~}

*Nabilancy luv*

💘

Auntyn S&S

____"Amarya kinsha kamshi!! Cewar Alhaji ya furta a hankali yana mata kallon qasa-qasa tare da madaukakin murmushi a fuskarsa idonsa yana kan Nata da suke

a lumshe fuskar na fitar da wani annuri, sai tayi Masa wani

irin kyau gata very smart, Banda yasan Baba me gadi baze Masa karya ba da saiya rantse wannan halittar ba'a gidansa ta rayu ba.

Ya karaso bakin gadon yana furta"Ayi hakuri da jirana,gidan ke kad

ai tsit ko?".

Gyara zama kawai tayi Akan gadon bata iya furta masa komai ba.

Zaunawa yayi kusa da ita ya rik'o hannuwan ta da suka Sha lalle Yana Kare Mata kallo tun daga sama har qasa Yana tasbihi ga ubangijin da yayi wannan halittar.

"Zuhra..." Ya f

ad'a a Cikin Wata murya wadda ta k'asa tantance tasa ce ko wani ya kirata daban. Shiru tayi Bata amsa ba saboda gani tayi duk ya cika gabanta duk da ba wani k'iba ce dashi ba.

Mayafin ya d'an daga kadan abunda yasa tayi saurin rufe idanunta kenan Dan wan

i irin nauyinsa taji ya rufeta.

"Baby kinyi kyau har kin gaji, ya taro nasan kin gaji ko.?

Dan murmushi tayi a kunya ce tana fadin"lafiya qlau".

Yatsunta da sukasha Jan Qunshi daya Kama tun zamansa ya fara murzawa a hankali Yana fadin"tashi muje

falo ga abokanaina can sun rakoni zaku gaisa kana su sai Baki,tunda kawayen naki sun kasa zaman jira mu k'araso".

Shiya Fara Mikewa yayi gaba zuwa falon, kafin ta tashi ahankali tabi bayansa, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri Dan wlh ita tsoro ya ci

kata tun lokacin Daya rik'e hannunta jikinta ya dauki tsuma.

A falo ta Tarar da abokansa su hudu suna zazzaune.

Tayi sallama a hankali suka amsa kana ta gaidasu, ta zauna Akan 2 siter da Alhajin yake kai, idonsa akanta yana fadin"gaskiya Kusai bakin

amaryar tawa da tsada saboda ita din me tsada ce kundai ga Alama".

Wani guda akusa da kujerar da suke yai dariya yace "yo ai indai nine zansai bakin amaryar da araha zan siya tunda har nariga naji muryarta yanzun wajen gaisuwa"

Sukai dariya Baki Dayans

u saboda da zolaya ya fadi hakan,na kusa dashi yace"A Ah fa Alhaji Sadi Nagano nufinka sbd kawai Kaci burin ka Tarar da kewayenta ka Kara ne,haushin Babu ko guda sun tafi shiyasa kawai zaka Siya da saukin".

Nan ma suka sheke da dariya,kana su biyun da suk

a rage basui magana ba take suka magantu suka ce su kam sun sai bakin Amarya da Tsada don sunga mahaddaciyar Alqur,ani ce sannan tayi boko dole su darajjata. kudi suka dire a gabanta kan table bandir na Yan Dari biyar biyar na Naira dubu Dari biyar

Suna f

ad'in "gashi amarya ba yawa, Allah ya bada zaman lafiya ayi ta hakuri Kuma da Yana yin sabuwar rayuwar gidan Aure".

Ango Alhaji yayi musu godiya sosai da fara,a kwance a fuskarsa, Dan yaji dad'i sun fitar dashi kunya, duk da dama sun Saba hakan ga duk Wa

nda yai Aure za.aje masa har gida Rakiya ayi wannan Rahar ayiwa Amarya ihisani.

Har waje bakin motarsu ya rakasu yana musu godiya, sannan sukayi sallama suka tafi shi Kuma ya Dan tsaya wurin Mai gadi sukayi magana sannan ya koma ciki.

Yanda ya barta

haka ya dawo ya tarar da ita a xaunen tayi shiru tana jiran shigowarsa.

A kusa da ita ya zauna yana zame gyalen daga kanta kafin ya janyota jikinsa yana fadin "ya dai madam?ko yunwa ce acikinki,?Dan nasan hidimar biki zata iya hanawa a tsaya aci abi

nci".

Tayi murmushi tace"ba yunwa nake ji ba,kawai kewar gida nafarayi'. Ta fad'a a shagwab'e.

'Yar dariya yayi Yana Kama cheeks dinta kad'an "kewar gida Kuma?tab!lallai to kima ajiye wannan kewa,don Nan shine gidanki na gaskiya na Duniya can gidan iya

ye saidai aje da ziyara,Kuma Nan da kwana biyu ma zamu tafi honey moon sai mun zagaya kasashe biyar Dake zamu dawo".

Gabanta ya fadi Amma bata nuna komai a fuska ba.

Tashi yayi ya kamo hannuwanta duka biyu ya mik'ar da ita ya nufi bedroom dinsa da ita

sabanin Wanda suka fito dazu. A bakin gadonsa ya zaunar da ita Yana fadin "Ina zuwa". Ya fice daga dakin, tana zaune tsuru ya dawo da wata Leda a hannunsa da plate da cups.

"Oya baby sauko kici abinci kada ki fara hora min kanki da yunwa".

Batai masa mu

su ba ta sauko kasa bayan ya matsar da table suka bararraje Akan Kafet ya janyo ledar Daya shigo da ita.

Manyan yoghurt jarka biyu ya Ciro tare da Naman kaji guda biyu sai qunshin tsire da Kuma ice cream.

Ya Mike yakai jarka guda ta youghort din fir

ji da tare da ice cream biyu ya karo Cup daya ya dawo Gabanta ya tsiyaya ya Mika mata ta karba ta kafa Kai ta fara Sha sanyin da dadin na ratsa mata Zuciya ta lumshe idanu an Dade ba.a hadu ba

😁

Ya ringa yago naman yana bata abaki a kunyace ta ringa ka

rba taba ci.

Saida yaga ya ciyarta ta qoshi ta ture masa hannu sannan ya hau ci da kansa.

Da gaske Taga Alhaji yana nuna mata soyayya ba kunya, ita mamaki yake Bata idan ta tuna lokacin da yaje wurinta yanda ya ringa had'e fuskarta Ashe Shima guda ne

.

Bayan sunyi sallar gdy ga Allah bedroom din da aka Kaita suka koma, da sukaje kwanciya yace mata lallai rigar bacci yakeson tasaka masa bazai yadda ta kwana da kaya me Nauyi ajikinta ba. Diri diri tayi ta rasa me zatayi, rigar ta d'auka irin transferenc

e din Nan ce wadda da ita da Babu duk daya. Jujjuyata ta shiga yi ta rasa ta inda zata Fara cire kayanta Yana zaune.

"Dan Allah ka tashi Zan cire kayana".

Ta fad'a a hankali cikin murya Mai cike da sarewa da sallamawa.

Kofar toilet ya nuna Mata Alamar t

a shiga ta cire, shi Kuma ya kishingida a Kan fito ya basar da ita.

Cikin azama ta fad'a toilet din ta cire kayan jikinta ta zura rigar, Sai Kuma tayi turus ganin yanda ilahirin halittarta ta bayyana muraran, gefen bahon wanka ta zauna ta zuba tagumi, Jin

shirun tayi yawa yasa Alhaji tashi tsam ya nufi toilet din, a zaune ya sameta da sauri ya karasa wurinta Yana Fadin "what happened Baby".

Firgigit tayi tana kallonsa da idanunta da sallar tsoro ya bayyana, dan har ga Allah bataji shigowarsa ba.

Jikinta

yake kallo yanda fatarta ke shining ne Ya burgeshi ta dauke masa hankali matuk'a.

Ga Yan nonuwanta car! Atsaye masu kan tasa cikin Yar b'iqil din rigar bacci me hannun Bra,iya cibiya ta tsaya ga Shara Shara sannan ga kokon bra ajikinta Kuma yai CAS! Ak

an kirjin nata.

Kanta yasha gyara an daure dogon gashinta cikin Ribbon. Bai San lokacin Daya Isa gareta ba duk ya susuce, qamshi takeyi na wasu hade haden turaren qamshi da Humkam ta hada matasu.

"Hannunta ya riko Idanunsa kur a Kan kirjinta.

"Let's g

o" abinda ya iya fada kenan.

Adduarta Ckn zuci Allah yasa Alhaji kar yai mata komai ayau sbd jikinta ko Ina ciwo yake mata ga uwa uba tsoron abinda zaije yazo.

Kan gadon ya nufa da ita Yana nuna Mata ta kwanta, cikin serious dinsa.

Shima kwanciyar ya

yi daga shi sai short niker ajikinsa da Yar Best farare Shima qamshin Yakeyi gashi yasha magunguna da abokansa suka bashi shaqiyyan Kawai

😅

Ai Yana kwanciya kusa da ita ta shi zulumi da D'ar! d'ar!! Ta qudundune jikinta, ganin haka Nan take ya janyota

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login