Showing 18001 words to 21000 words out of 40654 words
damuwa in dai kayi Masa farin sani.
Hannu ya mika Masa Yana fadin .
"Me yake faruwa ne?na kirawo ka sau kusan biyar baka dauka ga Kuma wayoyinka a Kan ta
ble dinka? Ga mood dinka ya canza idan ba idona ne ke min gizo ba Sai naga har Dan fadawa kayi".
Murmushi ya kakaro Yana fadin"Gara da Allah yakawoka Abokina,Ina cikin wata matsala da nake Neman agaji na shawarinka dama,da bakazo ba ma dole sainazo gare
ka.
Kujera Yaja yaiwa kansa matsuguni idonsa akan Na ALH Hashim Yana fadin"to Ai gani,Allah yasa dai lafiya.
Alh Hashim yace"ai ba lafiya ba,komai baya min Dadi,ko wayoyina ma suna silent ne sbd rashin son Kara da hayaniya sbd nashiga yanayi me wuy
ar fita.
"Subhanallah,me yai zafi haka,ba dai babyn kace tazo maka da babban problem ba.?
Alh Hashim ya Shafa gefen fuskarsa Yana fadin"wato na fada komar mata ne,Wanda nake hannu dumu dumu..Nan yahau bashi labarin komai Daya wakana.
Bayan gyara z
ama da ALH Sadi yayi,kana ya murmusa yace"wannan ai abune me saukin warwara,wato kaga dai kai din yanayinka ba kowacce mace zata iya dauka ba,sbd kai din mabuqaci ne baka iya jurar yanayinka,Adan haka Karin Auren ne ya kamaceka, tunda alokacin da margayya
Haj.Aliya na Raye tana iya jimirin daukarka Amma ita Zahra kace baka Dora mata wannan Nauyin sbd yarintarta to kaga Karin Auren yakamata ayi kada Azo ana tsunduma acikin halaka.
Gyada kai Alhajin yayi Yana fadin"Yes!abinda naketa Tunani kenan,gashi ita
acan Rahama (iyabo)ta matsa da zancen Auren da nai mata Alkawari gashi Ina tsoron darun zuhra,yarinyar tana da kishi ga wayo ga gashin quma,Ina sonta Ina tausanta,shiyasa kaga nace maka ko da nake da bukatar mace arana injita kamar sau uku ko biyar to tabb
as ita sau Daya nake zuwar mata,idan Kuma na cika takura mata nace zan sake nemanta kamar sau biyu saita shiga damuwa ko ta hau kuka nikuma tausayinta nake,haka zalika Ina ganin ko idan nai Auren ma zan Kara samun Yara agaba sbd inason Inga na cika gidana
da Yara tunda gashi Allah ya fara tsayar min akan Zuhran.
Ajiyar zcy ALH Sadi yayi yawa fadin"kwarai wannan haka yake,kowa ma zai so maka Hakan,to Amma abi zuhra ahankali kar adaga mata akan zancen Karin Auren duba da quruciyarta da Kuma abinda take dau
ke dashi don ba,ason me ciki da shiga damuwa,kasan yanda zakai na Yan dabaru da rarrashi dai idan maganar Auren ta kankama Nima zanyi kokarin tura murja taje ta Bata Baki da hilata da Yan dabarun hakurkurtar da ita tunda naga Bata da matsala.
Murmushi A
LH Hashim yai Yana shafo farar kasumbarsa Yana fadin"zuhra batada kwaramniya gashi Tasamu tarbiyya daga gida,haka zalika tana da sanyi da Hali me kyau,duk da nasamu lagonta na samu ta sakko daga fushin da take Dani akan taji muryar Rahama awayata alokacin
da nake can Lagos din, Rahama ta daga wayar da Zuhra ta kira,Amma naci galaba akanta ta sakko duk da saida Nasha bakar wahala da dabaru har muka shirya saidai
har yanzun takasa sakin jiki kamar da Dani,gashi agefe guda inason intura magabatana can Lagos at
ambayomin Auren Rahama.
Alhaji Sadi ya gyara zama Yana fadin"karka damu wannan duk me saukine,Kuma me wucewa mu Alkairi da alfanun Hakan zamu kalla,tunda bamusan me Allah ya shirya atsakaninka da Rahamar ba,Dan haka Nima zanyi kokari akan ganin komai ya
tafi cikin sauki Dan ganin ba,a samu matsala ba ta kowacce fuska,yanzu dai bayaga ni dawa dawa yakamata ka Dora akan tafiyar Lagos din muje da maganar Auren sai ayi komai Dan kar aja lokaci.
Alh Hashim Yace"To dayake Alh murtala Yana hanyar shigowa kasa
r shine da zan saita idan yazo asatin Nan kafin yakoma sai kuje da kai dashi da kawu na Rimaye saikaje ka Daukoshi.
Alh Sadi yace"To ba Matsala,ya kuwa twins dinsa sun fara wayo ko.?
Alh Hashim ya murmusa yace"Eh sunyi wayo sosai ma kuwa duk da dai y
ace ma ba tare dasu zaizo ba acan zai bar Iyalin saboda wani uzuri ne zai kawo shi Nigeria din.
Jinjina kai yayi Yana fadin"Allah sarki Dan,uwa me dadi ni ba gani ba da bani da kowa abokin shawarar gara kai ko da yake nesa kwayi ta waya tunda waccen Aut
ar taku macece dole dai shi din dashi zakai.
Alh Hashim yace"kwarai kam,itanma da muke cikin kasa Daya ai kaga nakan Dade banganta ba kamar Wanda take kololuwar nesa Rabon da tazo inda nake fa tun satin farko na zuhra agidana,ita dama kaga bari take da
yawan Yi har yanzun Allah Bai Bata haihuwa tsayyyaba bare tayi hidimar da zata ringa gani na da iyalaina agidanta.
Alh Sadi yace"Ina ruwan Hajiya Jamila itakam dai ba ruwanta bare ta samu miji mara son fice fice gashi Yana da Rufin asirinsa bare ace ko
tana tare da matsala aita ganinta akai akai,Allah dai ya Bata haihuwar itama akusa.
Alh Hashim yace "Amin.
*****. *****
A bangaren Zahra dai ta Dan saki jiki kadan da chu-chun nata Abu Daya dai takasa cire muryar iyabo acikin ranta
Duk rarrar
shin dai da akai mata ta amsa ne kawai,abinda ta iyayi shine cire zargin da zcyrta keyi akansa na hango mata da take ko Yana aikata zina da mata,tunda ya rantse mata ya Bata Baki ta nuna ta yadda dashi.
Zasusha Hira zasui soyayya zata bashi kanta Amma f
a fuska ba kamar da ba.
Duk da ya shiga takura Amma sai yake nuna mata sabuwar soyayya da tattali fiye da Da.
Saijin tai tafiyar iyayanta tazo na Umara da zasu tafi
Alhaji ya gama musu komai Wanda ita saita haihu zasuje hajji tare.
Tsabar dadi
n da taji har Baki ta bude tayi masa godiya,gashi ya gwangwajeta da sabuwar MOTA GLK da yai mata alkawarin tazo harda canza mata waya daga iphone 16 zuwa 18
Abin yai mata dadi sosai,gashi ya barta zuwa koyo tunda cikin nata Bai gama bayyana ba Kuma Ba
bu laulaye lauyen tsiyan Nan.
Farin cikinta ma da Dan,uwanta yazo gidan taringa inaka Saka inaka sauke dashi na hidima
Alh murtala yaji dadi sosai,yakira matarsa Haj Laila ya hadasu a vedio call Yana me sanarta da mata Albishir kan cewar in haihuwa t
azo Nan gun su zatazo haihu a Turai ko India dai Dan haka tayi shirin tarbar bakuwa Dan inciki ya Isa awo zata taho.
Haj.laila taji matuqar farin ciki anan tace yakamata ma sui musanyen namba su ringa chart
Take ALH Murtala din ya tura mata nambar z
uhran wacce ta karanto masa tana me jin dadin Hakan,ita dama zata fison zuwa gun Dan uwan ALH akan gun Wani abokinsa da yake raba mata Dayan biyu.itafa a son samunta ma abarta a Nigeria ta haihu abinta.
Zuhra baiwar Allah Bata San abinda ake ba,har akai
maganar Auren Iyabo da mijinta Wanda ALH Murtala da Alhaji Sadi da kawu na Rimaye da baffa Audi kawunnan Alhaji Hashim sukaje sukai komai aka tsaida wata guda Auren Iyabo da ALH tunda bazawara ce dama sun dire kudin komai sai jiran Ranar daurin Aure.....
Muje zuwa.
*MATAR TSOHO*
👨🏻
🦳
👩🏼
🦳
( _Ta gaban goshi_)
_the romantic and love story_
❤
️
Writing by *Nabilancy Love* Auntyn S&S.
Page 12
Zuhra na gaban mirro ta gama make up a fuskarta Wanda tayi simple make up abinta fuskar ta
kara kyau ciki yasaka tayi wani fresh abinta ga Kuma jin dadi da kwanciyar hankali dama Daya Kara sawa tayi kyau ta zama on top
Jitayi an rungumeta ta baya ana Sakar mata numfashi akan kafada.
Qamshin turarensa ya bugi hancinsa Shima ya gama shirins
a knn.
Dama gidansu zai kaita zasui sallama dasu Inna da baba Dan jirginsu zai tashi asubar gobe.
Juyo da ita yayi Yana fadin"babyn love you look cute,and beautiful,wai meye sirrin ne kin Kara zama big madam fa,baya ga Ni,imarki data karu ga kyau d
a kika Kara talk me baby meye sirrin?
Tayi murmushi da kanne masa ido guda tana fadin"sirrin ai kafi kowa sani,babynka ne ya zama sila,kasan kowacce me ciki saita kasantu da Hakan bayama in ciki na karami
Ya gyada kai Yana fadin"ok I understand,are y
ou ready?
Ta gyada kai tana masa murmushi
Yace"to muje ko,so nake mu shiga S and S shopping muyi musi siyayya.
Ta mannu ajikinsa tana fadin"kai Chu-chuna baka gajiya hidimar tayi yawa fa,yaushe ne wai ka kai musu kayan abinci da komai da komai ga
Kuma kyautar kujerar makka da zasu tafi sannan Kuma ga....ya toshe mata Baki da harshensa Yana kadasu cikin bakin nata Wanda Hakan ne ya katse mata abinda zata fada.
Saida ya tsotseta tas kana ya jata suna tafiya zuwa fita a bedroom din Yana fadin"iyaye
n ki ai nawa ne baby,hidimar da nake musu ai Lada nake samu,Kuma ni yanzu da bani dasu ai su nake kallo a nawa iyayen ko ba haka ba.?
Cikin jin dadin kalamansa tace"hakane my Chu-chu Allah ya Kara arziki da Nisan kwana.
Yace "Amin babyn love'!
***
*
Ko da sukaje gidan nasu ya barta ne yace zaije wata yar unguwa yadawo,dayake lokacin byar na yamma Kuma weekend ne Yana son yaje wani guri inda tsoffin abokansu ke taruwa joint ne ayi Raha ayi zumunci masu baby suje da ita masu Shan shisha su Sha,Amma s
hikam a tsarkake yake ta wannan fannin,sabo ne kawai da aka sawa Rai.
Taji dadin Hakan na barinta kafin yadawo zuwa daren Dan tayi tsammanin ko yar shaf shaf zai mata yace su gaisa ta fito su koma.
Aikuwa da suka kebe da inna saitahau mata doguwar Na
siha Wanda jikinta yai sanyi jin Shima baba dazu yai mata agaban Alhajin Dan baba ce mata yai"Uwata akara hakuri akan Wanda ake dashi,nasan Baki da fitina gaki da hakurin jure jarrabawa,to kafin mu dawo dai Asawa Rai salama kada naji kada na gani,abi Aure
sannan ayi zaman lafiya Kinga dole saikin zama me gudun bacin rai sbd bake kadai bace,kome yasaameki ko yazo Miki ki zama me cinye kaddararki kiyi tawakkali,haka zalika baya ga mu,to Baki da sama da Alhaji Ki rikeshi dakyau Alhaji mutum ne Kuma me kaunark
i kici gaba da bin abinda yake so duk abinda yazo Miki dashi ki karba ki rikeshi da kyau Banda fushi,kinji uwata.
Ita dai ta amsa da to da Kuma godiya ga baban ba tare da fahimtar manufarsa ba
Haka itama innar tayi mata tata nasihar Amma budaddiya b
a kamar baba ba da yai mata a dunqule Kuma a rufe.
"Fadima Batula me halin kwarai Allah yayi Miki Albarka,ko me muka zama ko muka kasance aciki kece sila,yau gamu acikin farin ciki Rabon mu da quncin talauci na rashin Sha da ci tun Aurenki da Alhaji bam
u kasantu awannan qadamin ba,haka zalika komai namu ya canza ba ga tukunya ba baga jikin muba,yanzu muma nema ake agunmu Alhamdulullah ko Mahaifinki yanzun ya zama Dan karamin Alhaji tunda Shima ana masa sallama ya taimaka ko yayi hanyar ataimaka din,sanna
n nima yanzun a unguwa ba,a mantawa Dani aharkar biki ko wani taro sbd ansan inayi Kuma in badawa in an bukata na gudummawa kai ko adangi ana damawa Dani Kuma duk ta sanadin Aurenki ne da Alhaji me kyautatawa,Dan haka nakeson ki zama me adalci Wajen kyauta
ta masa ki rikeshi Amana tunda maraya ne duk da dai da shekarunsa Amma ayanxun ne ma yafi bukatar tattali da kulawa,sannan zan bayyana Miki abinda Baki Sani ba yake ta boye Miki sbd Yana gudun bacin ranki tunda dole ko Baki da kishi Kiji awannan lokacin d
a shakuwa ta wanzu atsakaninku kisani A yau da Alhaji yakawoki don muyi sallama na tafiyarmu to tsuntsu biyu yakeso ya jefa da dutse Daya,sbd kasa gaya Miki dayai zaiyi Aure ne yake son yakawoki gida mu mugaya Miki.... Zabura zuhra tayi tana micincina ido
tana yarfe hannuwa kamar Wanda cinnaka ya ciza.
Kamota inna tayi ta zaunarta kusa da ita tana fadin"haba Auta,haba shalelen baba da inna,meye na tada Hankalin bayan Allah ya gama Miki komai,hankali,Tunani, Nutsuwa,Arziki,samun mijin wuce sa,a,ga ilimin
Boko da addini,ga kyau da Babu wacce zatazo gidanki ta nuna tafiki,Alhaji ya yabeki sosai Kuma ya nuna mana wannan Auren da zaiyi ba don baya sonki ko ya Daina sonki xaiyiba,yace amatsayin tashi kaddarar kenan don a lokacin Daya Aureki yayi zaton ya rufe K
ofa to ashe Allah ya rubuta masa wani agaba Dan haka yace mu roka masa ke inhar Baki Aminta ba to zai hakura dan baya son bacin ranki da damuwar da zaki shiga
Rintse ido tayi tana jin zcyrta na bugawa da sauri sauri,Amma saitahau ambaton Sunan Allah ha
r inna takai Aya Bata iya cewa komai ba
Tayi lakwas ajikin inna kamar wata mage ta zama wata Abar tausayi Bata San tana da tsananin kishi har haka ba.
Amma sai inna tayi nasarar dannarta
Inna taci galaba akanta ne na yanda ta nuna mata cewa tayi
koyi da me sunanta Sayyada Nana fadima Yar Manzon mu yanda ba,a Gane bacin ranta sannan kishinta na masu ilimi take da haka zalika ta nuna kaunar miji da tattali fiye da yanda muke zato Dan Baki bazai Fadu ba,Nan dai innar taita dankwafarta akan kada ta sa
ke ta nuna ragwantaka da lusaranci akan wannan fannin tana so ma ta sake daura damba da damarar sake dabaru na rike miji da mallakeshi ta hanyar rikon Adduoi da janyo Ra,ayi ta fuskar salo salo na tarayya da biyayya kada ta Gaza a komai sannan tayi kokari
ta ringa boye bacin rai kada Kuma kishiya tazo Taga ragwancinta ta fuskar komai ta nuna mata itace gaba da ita kada tai saken da zata rainata ko da ta girme mata ne.
Ajiyar zcy zuhra taja tana me fadin"to inna naji nagode nakuma ji dadi da samun uwa tag
ari haka zalika zanyi Amfani da duk abinda kikace Shima zanyi kokarin bashi goyon baya da boye bacin Raina Allah ya bani hakuri da dangana ...sai kuka.
Innar ta Tausaya mata tasan tabbas dauriya da juriyar aka fara
😄👍🏻😊
Ta jata jikinta tana Shafa
bayanta tana fadin"daure !daure ki hadiye Allah yayi Miki Albarka,Allah Kuma ya Baki lfy ya budi ido lafiya,Allah ya Baki zurria dayyiba masu jin tausayinki kamar yanda kike me tausan iyayenki dai,goge hawayen ki kada ki tayarwa da kishiyata ko sabon mijin
a hankali suji uwarsu na kuka su kasa zaune tsaye aciki.
Dagowa zuhra tayi tana kallon innar tana murmusawa hawaye na bin kuncinta Dan maganar innar ta Bata dariya.
Tana goge hawaye tace"au inna dama in uwa na cikin tashin hankali Hakan na shafar jar
iri aciki?
Cikin dabara da wayo na iyaye sai inna tace"kwarai kuwa,idan damuwa ma taiwa uwa yawa shine zakiga yaro yazo duniya awani iri gilmi gilmin Nan,ayita wahala yaro kiga shi ba me hankali ba shi ba mahaukaci ba dai,Dan haka kiyita kokarin jure ko
mai ki turar da damuwa gefe ko Dan abinda ke cikinki tunda Dan fari ne gun Alhaji har gunki ma bazamuso yazo ahakan ba,Sam ba,ason me ciki da damuwa kinji
Ta hau gyada kai tana fadin"insha Allahu na ajiyeta anan ma kuwa,Allah yakaramin juriyar shikuma
Allah ya bashi iKon yin adalci atsakaninmu.
Innar ta karbe da "Amin.
To ko da yazo daukarta Bai iya shigowa ckn gidan ba waya yai mata Yana cewar ta fito Yana kofar gida zasu wuce
Dayake sunyi sallama shi dasu innar ya cikasu dama da kudin guzur
insu Dan canjin kudin saudiyya yai musu wadatacce kana ya basu na Nigeria ma awadace haka zalika ya hadasu da drivern da zaizo ya daukesu yakaisu filin jirgi da sassafen,daga can danginsa ma na kauye ya debi wasu tsoffin nashi ya basu kujerar umarar mata b
iyu Maza uku shiyasa dangi suke yinsa ga taimako.
da suka
ɗ
auki hanya suna tafiya shiru tai masa bayaga sannu da dawowa da tai masa kafin su taso.
Shima ya fuskanci taji maganar Aurensa Dan ta kasa kallonsa ma Amma fuskarta ba yabo ba fallasa dai.
Har wani shakkarta ya fara ji,bayason ayi masa boren Nan mata me sakashi a taskun takura.
Shiyasa dama yai mata wannan daurin damarar na hadata da iyayanta yasan ita me biyayyace Kuma da alamar yaci galaba.
Yakai hannu ya kunna wakar vedio acikin
motar ta soyyayace Amma irin ta Neman yafiya dinnan awakar dai jarumin ya durqusa ne gaban matarsa Yana fadin ta yafe masa laifinsa na Karin Aure da zaiyi indai Bata amince ba zai hkr kawai ita Kuma jarumar sai wani fuffusga takeyi tana Shan qamshi ana ta
shakara.
Zuhra sau Daya data kalla saita dauke kanta tana jin wani iri cikin ranta,ita da zai kashe ma Hakan zaifi mata Dan saitaga kamar ma ya Raina mata wayo knn irin da gayya dinnan to kuwa saidai yayi shi kadai ita yanzun ta babynta na ciki take.
Alhaji yaga ana masa Shan qamshi an karo Aji
😅
sai ya rage volume yace"madam love ya kikai shiru ko akwai wani abun ne.?
Ta juyo tana kallonsa harda kakaro murmushi tace"bubu komai my Chu-chu me ka gani?
Yai saurin girgiza kai Yana fadin"ah Banga ko
mai ba,bana son shirun ne kawai.
Haushi taji cikin ranta Amma sai tace masa"to ko wakar kakeson naita bi ne ?
Kamar yai dariya Kuma sai ya fasa yace"Nop! Bawai haka ba,dayake nasaba aita min Hira me dadi ne sannan Kuma aringa min shagwabar Nan da nak
eso.
Tace"hhuummm!! Kawai
Ganin haka yahau wasi wasin ko dai innar Bata gaya mata ba ne.to ai Kuma sunce zasui mata maganar cikin lallami to da alamun dai ta lallamun.
Da sukaje gida ya ringa Nan Nan da ita
Rawar jikinsa ma haushinsa taji gan
in zaiyi amarya kenan zai sake Bata wata sabuwar kulawar zatai maganinsa ita Kuma nata kulawar datake bashi zata tsayar dayi masa komai cak! Zata barwa amaryar Taga iya gudun ruwansu.
Da suna kwance cikin bargo bayan dawowa daga duniyar Dadi ya shige ji
kinta