Showing 12001 words to 15000 words out of 40654 words

Chapter 5 - MATAR TSOHO COMPLETE

30 Sep 2026

1414

da Kuma voice call don Shima ya Isa lafiya.

A washe gari ne dai da batajishi ba kwata kwata hankalinta ya tashi.

Bai hau online ba ga wayarsa Bata tafiya duk sai ta Wuni sakaka abinci ma kadan ta tsakura kamar mara lafiya haka ta Wuni.

Sai dare can cikin Daren ma ta fara bacci taji yakirata.

Zumbur ta tashi dama mafarkinsa take kan Yi

Aikuwa tana dagawa cikin shagwaba tahau masa kuka.

A farko hankalinsa yatashi yazaci ko batada lfy ne Amma sai yaji wai Ashe kukan na Rashin Jin Sa ne ma.

😄

Yai ta mata dariya.

Ckn shwagaba tace"wato Ka

i baka damuba Ashe da bamuji juna ba ayau.? Lallai to ngd".

Yace"No!! My love shawagabarki ce ta burgeni,ba,a taba min irin Hakan ba cikin Matan dana Aura,duk da Babu me kananan shekaru irinki,Amma ke kam ta daban ce my Zuhra,sorry nayi laifi bari na sauk

o kasa nayi kneel down ai za'a Huce ko?".

Tayi dariya tace"haba dai akan Hakan?aa walh na yafe Maka,Amma Kar asake barina irin Hakan na tsahon lokaci, duk na shiga damuwa fa nayi tumanin ko ba lafiya".

Yace "Tom madam an daina in sha Allahu, yau din

ma babban uzuri ne,nayi busy ban zauna ba,Amma baza,a sake ba kinji".

Farin ciki ne ya ziyarceta don yana Bata kulawa da girma kamar yanda take Bashi,sai aka shiga hirar soyayya da kewar da akai da juna.

Kusan kwana akai ana waya ta sake ta tsuma shi s

osai Dan saida ya Samu nutsuwa ,sai gab sallar asuba aka katse waya da aka fara hamma aka kwanta kafin lokacin sallah Dan itama dai saida tayi wankan kafin tayi sallar.

A cikin kwana na uku da tafiyar sa saiga zuhra ta kasa katabus! zazzabi ya rufeta,

ta Wuni a kwance ga amai da take ta kelayawa duk abinda takai bakinta saita amayar.

Hankalin Ladidi me aikinta ya tashi,take ta kira uwar dakinta murja ta sanar mata.

Murja ba shiri ta bazamo gidan Alh Hashim tazo taga jikin zuhran.

Ta ringa mata

sannu tana mata tambayoyi Dan azatan murja fa ciki ne ganin yanda zuhran ta d'ashe tayi Wani mugun kyau.

Wayar zuhran na ring murja takai hannu ta dauka taga Alhaji ne suka gaisa yahau ce mata meke faruwa ne yanata Kiran madam dinsa Amma wayar ba'a d'a

gawa duk hankalinsa ya tashi.

Cikin nutsuwa murjar tace "ai inaga fa a silent take,Nima me aikintace ta kirani take sanar min zuhran batajin dadi,nazo na tararta zazzabi ruf jikinta ga amai da take kelawa ba kakkautawa.

A kidime Alhaji yace"Oh God! p

lz murja ku tafi asibitin da nake zuwa,idan nace Likita yazo zai Bata mana lokaci gara kuje ayi mata taimako gaggawa plz".

Murja tace "To, kwantar da hankalinka za'ayi komai insha Allahu kamar kana Nan, na kira Alhaji ya taho zai Kai mu ma".

Nan Alha

ji Hashimi yahau mata godiya Yana ma zuhra fatan Samun sauki.

Aikuwa kafin aje asibitin ma suna kan hanya yakira yafi a qirga suna ce masa da sauki.

Alh Sadi yai tayiwa Abokinsa dariya don ya zama yaro Shima yasan da akusa ne da tuni ya taho kam.

Taimakon gaggawa sukai mata suka rufu akanta

Ga magungunan da Alh Sadi ya siyo aka Bata da allurai tuni jiki yai sauki zazzabi ya lafa.

Sai alokacin da aka sanar masa hankalinsa ya kwanta yacewa Alhaji sadi"A bani matata inji muryarta mana abokina.

Dariya Alh Sadi yayi yace"to me Mata,Amma abari ta tashi a baccin data samu ko? In kuma in saka a tasheta to?".

Da sauri Alhaji Hashim yace "No!No!! Karka tasheta barta ta huta,inta Farka sai inji muryarta,Kai fa kafiya shaqiyanci Dan Allah da saika t

ashe tan?

Cikin zolayar Daya saba Alhaji sadi yace"yo ai naga ka susuce dayawa karfa ka rasa sukuni ka tsaya kayi abinda yakaika Kar ayi asarar dukiya,kasan dai indai munanan agurin zamu tsaya muga Zuhra tasamu kulawa sosai ayau, in Sha Allah fatan mu d

ai Allah ya Bata lafiya yasa abun nemane ya Samu".

Cikin jin dad'i da samun nutsuwa Alh Hashim yace "Haka ne! Nagode!! Alh Sadi naji dadi kwarai jazakumullahu khairan ,Allah ya bar zumunci,Allah ya Bata lfy...."

"Allahumma Amin,kai haba ba komai, mu

ma fa haka ake ta dawainiya da namu idan bamu nan, ka Dan Kara hakuri zuwa anjima zan kiraka idan ta farka sai kaji ya jikin nata daga bakinta ko ka Samu nutsuwa, yanzu muna jiran zasu kawo mana result na test da akai mata ne".

To!To!! Shikenan sai naji

ku..

Nan sukai sallama,murja ta ringa dariya tana cewa mijinta "Ho! Alhaji Hashim na Zuhra Kenan, nasan Kara kawai yayi maka Amma hankalinsa ba'a kwance yake ba".

Dariya kawai Alh Sadi yayi,saboda Hakan da Abokinsa yayi ya burgeshi soyayyar gaskiya k

nn.

Muje zuwa

👌🏽

*MATAR TSOHO*..

👨🏻

‍

🦳

👩🏼

‍

🦳

( _Ta gaban goshi_)

_TheRomantic love story_

💗





*Writing by*

*Nabilancy luv*

💘

(_Auntyn S & S_)

Page -8

️

⃣

____Karfe hudu da kusan rabi Zuhra ta farka dag

a dogon barcin allurar data sha, zuwa lokacin Babu zazzabin ya sauka, sai dai kasala da mutuwar jiki kawai ke damunta, Murja ce ta taso ta matso kusa da ita tana Fadin "Masha Allah jiki da sauki, sannu".

Kai kawai Zuhra ta iya gyada Mata saboda yawun Da

ya cika bakinta.

Ganin alamun zata sauko ne yasa murjar kamata ta ida saukowa.

"Toilet Zaki shiga?".

Murjar ta tambayeta, da Kan dai ta nuna Mata Alamar Eh.

Har Ciki ta rakata saboda jikin ba karfi sannan ta fito. Saida ta dauro Alwala sannan ta fito,

har murjar ta saka Mata sallaya da ajiye Mata hijabi.

Da sauri ta karaso wurinta tana Kama hannunta da murmushi a fuskarta "sannu, kiyi sallar sai kici abinci gashi Nan Yana jiranki".

Yamutsa fuska zuhrar tayi "na k'oshi fura nake so da zogale".

Baki Mu

rja ta rik'e tana dariya "kice Dan nawa ko 'yar tawa 'yan gargajiya ne".

Kalaman da suka daurewa Zuhra Kai kenan, Amma dai Bata iya cewa komai ba sai sallah data Fara a zaune, azzuhur da la'asar tayi tana idarwa ta kwanta a Nan Kan sallayar duk ta rasa me

yake Mata Dadi, ita Bata tab'a

zazzabi irin wannan ba. Murja ce ta shigo ita Zuhrar Bata San ta fita ba Saida taji sallamar Alhaji sadi, yunk'urawa Zuhra tayi ta tashi zaune.

"Sannu madam ya jikin naki"..

"Da sauki" ta amsa a hankali da muryar rashin l

afiya.

"To Allah ya k'ara sauki ya raba lafiya".

"Allahumma Amin" Murja ta fad'a da murnarta.

"Bari a Kira Alhajin tunda ta tashi daman yanzu doctor Asma'u ke fad'a min ya kirata Yana tambayarta ya jikinta".

"Dan Allah ka Bari nayi Masa Albishir din na

n da kaina".

Murja ta fad'a tana kallon Alhajin.

Dariya yayi Yana Fadin "Kika sani ko an rigaki fad'a Masa tunda ya Kira doctor Asma'un".

Ita dai Zuhra shiru tayi Dan kalaman da suke fad'a tana buk'atar ayi Mata fashin bak'insu, duk da taje Ghano Amma

dai a fito Mata a mutum sak mana.

Kiransa Alhaji Sadin ya Fara murjar na lafe a jikinsa ko kunyar Zuhra bataji.

Yana d'agawa ya Fara fad'ar "Alhaji Yaya ta tashin ne?".

"Haba yallabai ai ka amsa min sallamar da nayi ko?"

"Sorry wlh duk na rasa nutsuwa

ta ne tun dazu na kasa aikin komai jina nakeyi tamkar nayi fiffike na ganni a asibitin".

"To kwantar da hankalinka ta tashi, Kuma jiki Alhamdulillahi ga madam tace na Bata wayar".

Da d'oki ta karbi wayar tana Fadin " yallabai Albishirinka, madam na dauke

da Babynka Wata Daya da kwana goma".

Wani Abu yaji ya tsirga masa tun daga kansa har tafin kafarsa, Dan wani abune da Bai taba kawo shi a kusa ba, take a Nan ya sauko daga Kan chair din yayi sujudush shukur ga ubangiji ta gdy. Yana Fadin "Masha Allah! A

lhamdulillahi, lallai kin cancanci goron Albishir kuwa ki turo min account number dinki, sannan nayi Miki alkawarin idan Mace aka samu kin samu takwara, bani amaryar tawa naji ya jikin nata".

Godiya Murja ta shiga zuba Masa tasan kakarta ta Yanke saqa tu

nda tasan Babu had'i Alhaji Hashim yafi duk 'yan click din nasu kudi nesa ba kusa ba Kuma ya fisu shekaru kawai dai business ya hada su har Aminci ya shiga tsakaninsu.

Tana Bata wayar suka fice daga dakin Dan ta Samu sararin yi Masa magana tunda da alama

tana Jin nauyin Alh Sadin.

Cikin madaukakin farin Ciki ya Fara fad'ar "Babyna ya jikin naki Ashe kina dauke da Alkhairi irin wannan na tsallake ki na shiga duniya neman kudi, sorry gani Nan cikin week end din Nan in Sha Allah sauran na karasa online, yanz

u me yake Miki ciwo my princess?".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta bude bakinta cikin kasalalliyar murya tace "ba komai kawai dai bana Jin dad'in jikina ne".

"Ok kiyi hakuri haka Yana yin yake yanzu kinci abinci?".

Kaita girgiza kamar yana ganinta kafin

tace "bazan iya cin abincin ba na fadawa Aunty murja a kawo min fura da zogale su Zan iya ci".

Bai Dade Yana wayar ba ya kyaleta saboda Yana yin jikinta.

Bayan sun Gama wayar lamo Zuhra tayi tana ayyana Wai ita ce da cikin haihuwa irin na mata, itama z

ata Zama uwa, wani farin Ciki ne ya rufeta sai taji ita ta warke ma.

Ba'a fi minti goma ba da Gama wayarsu Murja ta shigo Wata yarinya 'yar budurwa na biye da ita da basket a hannunta da kayan abinci da jug da cups a Ciki, a Kan bedside locker din gadon

ta ajiye tana gaishe da Zuhrar tare da dubata.

"To Mrs Hashim tashi ga favorite din naki nan, fatan mu dai Allah yasa idan an cin ya zauna".

"Amin". Zuhrar ta fad'a a hankali.

Alhamdulillahi taci Babu laifi Kuma cikin ikon Allah ya zauna.

Sai dare b

ayan an Kara yi Mata allura saboda akwai maleria a jikinta, aka salkame ta, daga yamma zuwa dare Alh Hashim ya Kira wayar Zuhra yafi sau goma, yana tambayarta me kike so?me zakici? Yaya Ina yake Miki ciwo? Haka yake ta faman tarairayarta, ita har tausayins

a ya Fara kamata duk ya kasa samun nutsuwa.

Alh Sadin da Kansa ya tuko motar suka kawo zuhra gida, yayi Mata fatan samun lafiya, har bedroom dinta na k'asa Aunty Murja ta rakata da ledar maganinta saida ta had'a Mata ruwan wanka sannan tayi Mata sallama s

ai gobe zata dawo.

Ta Jima a toilet din tana gasa jikinta sannan ta fito dai dai Kiran waya Yana shigowa wayar zuhra number Babanta ta gani, ji tayi gabanta ya Fadi "Na shige su badai fada musu ina da cikin yayi ba" ta fada a hankali, harta katse Bata sam

u kwarin gwiwar d'auka ba, wani Kiran ne ya sake shigowa number din inna ta gani sai taji Dan dama- dama gara innar.

D'aga Kiran tayi tare da sallama. Tana fadin "Inna Ina yini? Ina wanka Kiran Baba ya shigo kafin na Kira Kuma naki Kiran ya shigo"

"Eh w

lh yanzu Mai gidan naki ya Kira malam ya fad'a Masa a sibiti kuka wuni Baki Jin dad'in jikinki".

Jan numfashi tayi tana hamdala ga Ubangiji da bataji innar tayi Mata zancen cikin ba.

"Eh wlh Inna nice nace kada a fad'a muku tunda zazzabi ne kawai".

"K

ai Amma Bakiyi wayo ba, ko banzo ba ai na turo Harira tazo ku zauna kamar Baki da gata! A kul hakan ta qara faruwa ai ita lalura ta Kori komai, ya jikin naki? Ga malam ma yace a duba ki".

Cikin kasala zuhra ta amsa "Da sauki Inna".

"To Allah ya qara lafi

ya, da safe in Sha Allah zamu shigo da Harira muga jikin naki".

Cikin murnar Jin Inna zatazo gidan zuhra ta Fara murna kamar ba Mai ciwo ba.

Washe gari a Nan murja ta wuni su Inna ma sunzo sai lokacin Inna taga dakin, tayi murna ta Sanya Alkhairi da

Albarka, zuhra kamar ta goya Inna murja ma sai Nan Nan take dasu an kawo musu abinci kusan kala hudu Wanda zuhrar tasa Ladidi tayi tun da Dan hantsi, da kyar innar taci Saida Aminiyarta Harira ta matsa mata, Basu dad'e ba suka tafi.

Suna hanya ne Harira t

a dubi Inna "nifa Ina ganin wata Kama a jikin 'yar tawa ko Baki gani ba?".

'yar dariya innar tayi "na gani ai tun jiya Mai abun ya fad'awa malam kinsan su maza ba ruwansu da kunya, nice dai ban nuna Mata mun sani ba saboda nasan halinta sai tayi Mana kau

ra ta daina zuwa ko ta takura Kanta Amma a haka sai ta Ware har ya Kai lokacin da ze bayyana Kansa".

Kai kawai Harirar ke jinjinawa har Inna ta Kai aya.

"Masha Allah! Allah ya raba lafiya, ai d'iyar tawa badai kunya ba"

"Allahumma Amin".

Da wannan hira

r suka k'arasa gida.

** ** **

Tunda gari ya waye Alh Hashim Bai zauna ba, har dare Yana ta faman Kai kawo, so yake yayi minimizing na lokacin ya Gama komai Dan da gaske hankalinsa yayi 9ja Kuma.

Sai dare ya Samu zarafin kiranta tun Wanda yayi da

safe, saidai Kuma Kash!ya Kira yakai sau goma Amma amsar Daya ce ake fada Masa _"the customer you're calling is not answering,"_ abinda ya d'aga Masa hankali,domin duk numbers din Daya Kira Bata shiga a Nigeria din, daga baya tata din na daina shiga tayi

yaji ta switch off.

Fad'ar tashin hankalin Daya shiga baze misaltu ba abubuwan da yawa yake ayyanawa yanda yaga Rana haka yaga dare duk da banbancin lokaci a tsakani.

A cikin Daren ya Gama Yanke hukuncin dole yabar kasar, online ya nemi visa very luckily

kuwa ya Samu Amma ta Lagos ze sauka, Babu ja ya Amince ai yasan ko a mota ya karasa Dan gani yake kamar za'a kwatanta irin na Hajiya Azeeza ya rasa Babyn tasa su duka yanzu ma.

******

Da wannan tunanin da zullumin ya daure ya dauki jarida Yana karatun

dole Dan kallon da yakeyi ma ya fice masa arai,matsalarsa da rashin jin dadinsa kowa wayarsa akashe fa kamar hadin Baki,hatta wayar ALH Sadi ma akashe yajita,Yana zaune dai ya rasa sukuni news paper dayake karantawa ya ajiyeta a gefe sannan ya cire glass

din medical dake fuskarsa ya kashe Tvn falon Yana da niyyar zuwa ya kwanta tara saura na agogon can

Ya Mike kenan yaji wayarsa na ruri

Da sauri yakai hannu kan table da take zai daga da doki Yana tunanin ko Babynsa ce

Sai yai diris ganin me kiran

Rahma ce (iyabo)wata tsohuwar budurwarsa dake cikin garin Lagos Wanda ta Mayance masa, ada baya daga wayarta shiyasa ta sarara masa yanzun Kuma data kira ko me zata gaya masa a Daren Nan

Yaja tsaki Bai dagaba,saida ta kira akaro na biyu ya dauka Yana f

adin"Madam Rahama ya akai ne?

Taja ajiyar zcy tana fadin"ranka ya Dade kwana dayawa,fatan kana lafiya.

Yace"lafiya qlau,me yafaru adaren Nan haka? Shi mamakin da yake kenan har yanzu tana ajiye da numbers dinsa har international din tunda da layinsa

na Dubai ta kirawo shi.

Tayi dariya tace"to ai Alhaji naga Daren Bai tsala sosai ba,gashi ko Tara batai ba fa,ta fada da rubabbiyar hausarta ta yarabawa.

Yace"to yayi,bana kasar ne fa ,Kuma nayi busy dayawa"

'Na sani ai da number Dinka na Nan U.A.E

din na karawo ka, kasan ku Hausawa Kuna cewa "Mai son Dan tsuntsu shi yake binsa da jifa,nakira na Nigeria naji taqi shiga,Oh! har yanzu busyn Bai ragu ba kenan?".

Cikin k'agara yace"saima k'aruwa yayi,kinsan nayi Aure fa".

Cikin bugawar kirji tace"w

hen? Yaushe kenan,lallai to Allah ya sanya Alkairi,fatan zaka shigo mana Lagos a kwana kusa?

Ya nisa kana yace"Eh to Ina tunanin next mouth ma zamu shigo wata semener zantaboki inmunzo.

Cikin jin dadi tace"kai Amman naji dadi Allah ya kaimu".

Yace

"Amin" ckn gundura ya ajiye wayar,yasan ta Lagos dinma zai sauka kawai bazai fada mata ba,sbd yasanta da naci da magiya zata takura tace yataimaka yatsaya mata tunda Yana qaruwa da ita na soyayyarta da kulawar da take bashi inyaje Lagos Bata da lokacin ko

wa sai nashi,cancakas take tarewa a hotel din Daya sauka har saiya tafi,Amma itama ai tana jiquwa da nera.shikam yanzun ba komai ke gabansa ba sai Babynsa so yake yaje su gaisa da gudan jinin Daya Bata ajiya gara yaje ya ingantashi.

Ita Kuwa Rahama iya

bo tana dire wayar ta hau kaiwa wayar kiss kamar ta Sami bakin Alhajin tana fadin "wow! Dole natashi na Kara aiki akan Wanda nakeyi akanka Alhaji,da baka daga wayata,yanzu na samo bakin zaren,yanzu Kuma kace zakazo to tabbas saina saka anyi min aikin D'ank

adafi wanda zan rike maka wuyan da bazaka tafi ba sai kayi maganar Aure na inkazo....

Muje zuwa.

*MATAR TSOHO*

👨🏻

‍

🦳

👩🏼

‍

🦳

(Ta gaban goshi)

Writing by *Nabilancy luv*

💘

(Auntyn S & S)

💋

❤

️

The love and romantic story

💋

❤

️

Page -9

______ K'arfe hudun asuba da mintuna zuhra ta farka, Shima fitsari ne ya tasheta, ita Kanta tasan tayi barci Amma ta danganta hakan da alluran barcin da akai mata a asibiti da magungunan baccin da Tasha ko sune Basu gama sakinta ba, toil

et ta shiga tayi uzirinta ta dauro Alwala ta fito.

Alhamdulillahi a tsaye tayi sallolinta na nafila tana zaune tana Addu'oin ta aka Fara tada sallar assalatu ta tashi tayi tata sallar, anan ta zauna har kusan shida da rabi sannan ta tashi ta koma Kan gado

tana hamma wayarta ta gani can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login