Showing 54001 words to 57000 words out of 160337 words

Chapter 19 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12534

meke damunka first kafin nasan ta inda zan fara? 

  "wallahi auwal babu abinda ke damuna sai tarin damuwa, damuwa ce ta maidani haka,  idan kaji yadda bugun zuciyata ke tafiya  sai ka sha mamaki, ya kamo hannunM.A ya d'aura a daidai saitin zuciyarsa "kaji yadda  zuciya ke bugawa? 

M. A ya lumshe kyawawan idanunsa yace"naji yaya akram amman kai kuwa tunanin me kakeyi haka? 

meye damuwarka ahalin yanzu ?

na d'auka ni za'a samu da wannan damuwar.

   girgiza kai yaya akram yayi sannan yace "damuwata tana da halaka da zamana a kasar nan auwal amman karka damu nan gaba zan sanar maka da komai ya dafa kafad'ar M.A  ya mike tsaye yashiga d'aki, M. A yayi shiru kawai yabi bayan yaya akram da kallo yana tunani wani irin damuwa ce hk ke damunsa . 

muwaddah na shiga d'akinta ta fad'a kan makeken gadonta tana fitar da numfashi  da kyar had'e da dafe saitin zuciyarta da take jin yana dokawa"wayyo Allah nah auwal ina sonka ina muradinka da dukkanin rayuwata, amman yazama dole na hakura da soyayyarka saboda nasan ummi ba zata yarda ba ....

************

kwana auwal biyar a gidan sai ga faiza tayiwa gidan diran makiya sakamakon samun labarin zuwan M.A da tayi ,wani irin mugun haushi M. A yaji lokacin daya samun labarin dawowarta dan yaso har yagama abinda ya kawo shi ya wuce basu had'u daita ba, dan duk sanda ya zo Hutu, takanas take zuwa lagos saboda shi, bare yanzu daya kawo kansa gidansu da zumar zai yi wasu kwanaki  abinda bai ta 'bayi ba , iya dadewarsa baya wuce kwana daya ko biyu shima sai idan yaya akram na kasar ne, a bangarensa sam faiza bata gabansa  dan ko fuska baya sakar mata saboda gani yake tayi bala'in rainashi da har takewa rayuwarsa shishigi, duk abinda take yana ankare daita da duk wani motsinta, da rawar jikin datake akansa har ma da yadda take son had'a jikinta danashi amman shi ko ajikinsa dan ba itace agababsa ba muwaddah yake so da muradin mallaka arayuwarsa.. 

**********

da misalin karfe takwas na dare yana zaune a parlour'n yaya akram sanye cikin wasu haddun fararen kayan bacci ,riga da gajeren wando iya cinyarsa ya lankwashe kafarsa daya ,yayinda dayar kafarsa ke mike yana karkad'ata ahankali ahankali, system ne agabansa yana duba sakonin yayinda sauran yaran da suka shigo d'akin tare tuni sun koma bangaren mumy ,ita kad'ai ce ta kasa ta tsare taki barin parlour'n, tun sanda tashigo take kallon TV ta kasa yi masa magana saboda fargaba, domin kallon fuskarsa kad'ai ya isa ya saukarwa mutun da kasalar kasa furta komai garesa  , yayinda a zahirin km kacokan hankalinta da natsuwarta suna kansa ne tana lura da duk wani motsinsa.. 

wayarsa dake gefensa ta d'auki k'ara sautin mai dadi ,faiza dake zaune a gefensa ta kai hanuta ta d'auka ta mika masa,yaki d'agowa  ya karbi wayar a hannunta har sai da wayar ta tsinke wani kiran ya sake shigowa sannan ya mika mata hannu  batare daya kalli inda take ba, yana amsar wayar ya tsura  screen din wayar ido yana kallo, sunan abokinsa nabeel ya gani yana yawo akan screen din wayar, sai daya numfasa kana ya manna wayar a kunnensa batare daya ce masa komai ba. 

bangaren   nabeel kuwa yana jin ya d'auka yace "ya'akayi ne friend nazo gida ban sa meka ba ina ka shiga ne? 

M. A ya furzar da iska daga bakinsa yace "wallahi bana nan ina ilori, but cikin satin nan zan  dawo,ahankali suka shiga hira  atakaice, sannan sukayi sallama ya katse kiran ya ajiye wayar ya cigaba da abinda yake..

Cike da sanyi  jiki faiza ta matso kusa dashi zata fara damunsa da shirmenta na banza ya d'ago kansa da sauri suka had'a ido, yadda bai d'auke idanunshi cikin nata ba haka itama ta kafeshi da manya idanunta farare tas ,dan ita fara ce sol kalarsa, alama yayi mata da ido da ta bar gurin.

amman faiza ta kasa aiwatar da umarninsa saboda wani irin zazzafan soyayyarsa dake fixgarta ahankali ta lumshe idanunta tana jin wani iri sabon kaunarsa na sake shigarta cikin sananin damuwa tace " dan Allah yaya ka barni a kusa da kai mana, zamana tare da kai yana k'ara min karfin gwiwa da yaye min damuwar da nake ciki  ,ina sonka yaya ,ba tun yanzu ba kasan da haka ,ina sonka tun bansan ciwon kaina ba ,kayiwa Allah ka duba lamarina nima ,ka daina nuna min kiyayya irin haka kasancewata mace  ,ina da rauni bazan iya juriar wannan tsanar daga gareka ba ,a duk sanda kake min kallon tsana ina jin tamkar na kashe kaina ne .. ta karasa mgnr 

Idanunta suka ciciko da ruwan hawaye, "kasani ba laifina bane , nima tsintar kaina nayi cikin tafkin kaunarka Wanda nake jin bazan iya rayuwa babu kai ba ,na sha gaya maka yadda nake jin sonka a zuciyata ....

"ba sai kin tunatar dani soyayyarki ba ya katseta ta hanyar fad'a mata hk ,yacigaba da mgn a tsanake  yana kawar da fuskarsa " ina son kisan wani  abu faiza,sam  ba  kya  cikin zuciyata da duniyata gabadaya.. asalima ni yayarki muwaddat nake mutuwar so ba ke ba ,dan haka wannan yazamo karonki na karshe da zaki zo min da wannan banzar maganar,  dan bazan iya auren duk macen data fara furta kalmar tana sona ba, wannan tsarina ne ba kuma zan sauke shi ba, bare akan ke da bana sonki ...

Muryarta a matukar raunane tace 

"Nasani ,nasan baka sona amman  kayi la'akari da wasu abubuwa nima ina da ....

A matukar  tsawace ya katseta ta hanyar furta "short up there karki tozarta kanki abanza dan bazaki ta'ba samuna arayuwarki ba, and get out of this room now

,bana son sake jin komai daga bakinki , bana son sake d'aura idanuna akanki ......

babu musu ta mike sum sum   ta fice daga d'akin tana jan tsaki .

kai tsaye tana shiga part din mumy d'akin  muwaddat ta nufa tana shiga ta zauna kusa daita tana share hawaye.. muwaddat ta waigo da sauri tana dubanta hankalinta a tashe "lafiya faiza me ,yasameki kike kuka .. ?

Girgiza mata kai kawai faiza tayi tana ganin duk duniya babu mai sa'a kmrta tunda yaya bunayya ya furta ita yake son.. yin duniya muwaddat  tayi daita ta fad'a damuwarta amman faiza taki jikinta na rawa ta mike zata bar d'akin  

faiza tayi saurin riko hannuta "ina kuma zaki aunty ? 

"babu fa abinda ke damuna " wai da mumy zan kira"

faiza ta girgiza mata kai "karki kirata dan Allah mumy zata matsa min ni kuma ban san  abinda zance mata yana damuna ba,"yanzu faiza har akwai abinda zaki iya boye mana? 

"duk duniya fa mu yafi dacewa mu san damuwarki amman tunda hk kikace babu komai ta nufi bayi ta barta zaune.. 

***********

abun mamaki tunda al'ameen ya d'aura idanunsa akan muwaddat ya rasa samun kwanciyar hankali duk inda muwaddat take yana gurin yana barkwanci da kannenta Wanda kusan wannan abun nayiwa muwaddah dadi, dan duk mai son kannenta tana sonshi uwa uba yadda yake girmama iyayenta tare da mutuntasu .

Tsaye take a kitchen tana taya masu aiki ayyukan girki bisa umarnin mahaifiyarta ,domin ta koya, dan taga alamun bawani   girki ta iya ba,ranta bai so shiga kitchen din  ba, amman da yake tana shakar mahaifiyarta babu mutsu ta ware ta shiga cikinsu tana koyan nau'ikan abinci ,wani lokacin in ta takarkare tana girki har dariya abun yake bawa hjy hajara, domin ganin  bata saba ba ,dady ma da kansa yake lekawa kitchen dan yaci dariya ko yaya yaga tayi aiki sai yace "ta taho ta huta wai tagaji bazai bari ta wahala ba ,dan  yar amana ce, aiko haka za'a tasata gaba da dariya ,shi kuwa al'amen bai San tana shiga kitchen ba sai ranar da safe yashiga  neman ruwan zafi sai yaganta acikin kitchen  tana suyar dankali ,yan aiki guda biyu na zagaye daita  azumi na fere dankali yayinda ita kuma tabawa take yayyankawa dadaffen dankali tana mikawa muwaddat tana tsomawa cikin kwai tana soyawa ,abun yayi matukar bawa ala'meen mamaki domin da gani yasan muwaddat yar gata ce ta karshe ,babu yadda za'a yi asa irinta wannan aikin wahalar a gidansu yana shiga kitchen duk ma'aikatan suka gaisheshi sannan itama ta gaishe dashi daga nan ta d'auke kanta ta cigaba da aikin da take ,dan daga inda take tsaye tana hango Auwal daya zauna rashe rashe kmr wani babban mutun yana kallonta ,tun zuwanta gidan babu abinda ke had'ata da al'amen ,ban da gaisuwa asalima ko surutu yake da yaran gidan bata tsoma musu baki ciki ,ballanatana yanzu da Auwal yayi kaka gida ya kasa ya tsare wani lokacin har mamakin karfin halinsa take  yadda yake da maseefar miskilanci da girman kai da Jan aji matukar bada ita yake tare ba bazaka ta'ba jin motsin bakinsa ba,shiyasa tunda yazo gidan babu yaron da ke shiga shirginsa..

ko jiya da ana kallo a main parlour'n din gidan su Iman  da faiza suna surutu har ma da al'ameen "ya buga musu tsawa tare da cewa gabadayanku in ba ku rufe min baki ba nida ku ne masu shegen surutun tsiya ,take sukayi tsit dayake suna maseefar tsoronsa saboda tsare gida da kamewa lokacin da momy ta kawo masa abinci ya amsa ya mika mata  yace" ta kai masa shima ya  Mike zai koma part din yaya akram .

Iman ce  tayi karfin halin kyalkyalewa da dariya saboda ganin yadda yaci magani kmr bai ta'ba dariya ba, tace "haba yaya bunayya wai me yasa sai kayita wani cin magani kmr wani zaki , ka saki ranka kawai mu caskare kmr yadda yaya al'ameen yake yi damu .

Yayi mata banza ya nufi hanyar waje,  ta cigaba da magana tana jansa da wasa irin na abokan wasa, "kai kamshin abincin nan fa ya doki hancina dayawa yaya in biyoku muci tare ?

Ya juyo da sauri "karki ki kuskura in ba so kike in wurgoki daga matattakalar bene ba '"yana fita daga parlour'n suka kaure da ihu ,yayinda faiza tabi bayansa da wani irin kallo da batasan manufar hkn  ba..

ajiyar zuciya ta sauke tana sakar masa murmushi daga inda yake zaune yana aiko mata da harara, tasan duk dan yaga al'ameen ne cikin kitchen din, ta sakar masa hararar wasa itama ta dubi yaya alameen tace " am yaya kana bukatar wani abu ne ?daddar muryarta ce ta ratsa cikin kunnen ala'meen da sauri ya jiyo suka dubi juna amman sai tayi saurin d'auke idanunta saboda wani irin uwar hararar da bunayya ya banka mata yana gargadinta da idanunsa .

Al'ameen ya zuba mata ido sosai saboda maganarta tazo masa a bazata shi duk yadda yake expecting jin zazzakar muryata yanzu dayaji sai yaji ya zarta haka, saboda bawata doguwar magana suke yi ba shiyasa har lokacin bai gama tantace muryarta ba, shi dai yasan tunda yaji yana sonta yasan an jarabi rayuwarsa ..

Cikin rawar murya yace "am daman ruwan zafi nake so Kofi daya muwaddat ta d'an juyo ta dubi M.A tana sakar masa laulausar murmushinta mai kashe zuciya sannan tace "okay bari a dafa maka , ta kai ganinta ga flask ta jijiga "akwai ma acikin flask bari ma na tsiyayo maka .

Girgiza mata kai kawai yayi yana murmushin jin dadin  "bar shi kawai kanwata cigaban da aikinki nagode sosai da kulawa na tsiyaya kar na tsaidake. 

Tun da yace haka bata sake cewa komai ba ,al'ameen ya tsiyayo ruwan zafi kad'an ya fita daga kitchen ita kuma tacigaba da aikinta ,daga inda take tsaye tana iya jiyo yadda M.A  ke sakin tsaki babu kaukautawa ..

Tasowa yayi ya isa bakin kofar  kitchen din ya tsaya  yana kallonta kmr zai cinyeta ,wannan shine ranar na  farko daya doshi inda hanyar kitchen yake a iya tasowarsa   ,ya cigaba da tsayuwa shiru yana agurin kallonta fuskarsa a d'aure batare dayayi yunkurin yi mata  mgn ba,gabadaya sai taga ya sake mata kwarjini  .....

Tsawon minti goma yaga tana yarfe hannunta tare da hura wani bangaren data ji digar mai , take ya lura da konewa tayi ,yasa take hura gurin idanunsa ya zaro kad"an  yana cizan gefen lips dinsa kana yace "ba dai konewa kikayi ba garin neman suna ?

Ta saki ajiye zuciya tana tsaresa da manya idanunta tace "agurin wa kuma zan nemi suna ?mai ne dai ya fallarsar min a d'an yatsa Amman bana ji zai tashi Dan bada yawa bane ya sake watsa Mata kyawawan idanunsa "wa ya fad'a miki idan  an kone fifita Gurin akeyi?

Muryata a raunane cike da shagwa'ba tace "ni barni karka k'aramin wani zafin akan Wanda nake ji ,ta k'arasa mgnrta tana  hura hanci ,a take ya bawa azumi mai aiki umarni ta amshi aikin ta k'arasa sannan ya dubeta yana jin rad'ad'i konuwarta data yi fiyye da yadda take ji "ki biyoni in ga inda kika kone bata amsa ba har ya juya .

Bayan tafiyarsa azumi tace "kai wannan yaro kamar wani sadauki ,"akwai tsare gira  ,

Azumi tace "ana magana ai idan kina jin miskili shine wannan yaron, nifa har tsoro yake bani kinga muwaddat kawo suyar na k'arasa dan kada naje nayi laifi agurinsa  "muwaddat tace dan Allah ku rabu dashi ni babu inda zanje tunda bawani kunar kirki bane ,Kune kuke jin tsoronsa   Amman ni Sam babu wannan tsoro "nifa bansa kin kone ba banda naji ya fad'a "muwaddat tace dankali naje zubawa a prepan shine man suyar ya fallatso min zafi ne ya isheni  na rasa yadda zanyi sai na hau fifita gurin da baki, shima dan yaga ina hura gurin da baki ne shiyasa ya fahimta.

tabawa tace "ai dole ya fahimta tun dazu fa ya kasa ya tsare , yana kallon yadda kike aikin  ita kuwa azumi cewa tayi "gashi kowa yagansa yaga miskili sai dai zai yi tausayi muwaddat tayi shiru bata sake magana ba saboda tasan saboda ita yazo ya kanainaiye gurin , tana jin suka cigaba da maganarsu, tana gama suyar dankali tabar musu sauran ta fito kafin ya dawo dan ba k'aramin aikinsa bane .

Azumi tace kinga wannan yaron ni har tausayin matar dazata auresa nake wallahi saboda irin wad'an nan mutane bakomai mace take musu ta Burgesu ba, duba kiga tunda yazo gidan nan  bai yarda yaci abincin da muke dafawa ba , sai na hjy kawai yake ci ko na muwaddat ko faiza datake da tsaf baya cin abincinta , "dole yaci na muwaddat bakiga al'amun ita sonta yake ba "kai haba ,bana tunanin haka ina ganin dai shakuwa ce kawai atsakaninsu "wallahi yana sonta indai baya son ta yaushe zai dinga binta a gindi gindi, duk inda take yana gurin, ita kuma sai tayita wani basawar dubi yanzu kmr bazata je kiran dayayi mata ba, amman taje, ni a yadda na lura dukkaninsu na tsananin son juna ,amman ko ba yanzu ba ki rubuta ki ajiye  wata rana hakan zai faru ,ke dai rabu da miskilin mutun in dai kikaganshi ki barshi kawai ,ta k'arasa mgnr tana sakin dariya "ni kuwa kinga miskilin mutun yana burgeni saboda ance sun fi iya soyayya da kulawa da mace "tabawa tace "ba haka bane,shi dai aure dace ne  idan ka dace shikenan ..

tabawa tace "to Allah yasa mu dace,azimi  tace "ameen. 

muwaddah na isa bangaren yaya akram taja ta tsaya tana dubansa  ganin yadda ya d'ago yana dubanta da kyawawan idanunsa yasa taji wani iri zirrrrrrr a gabadaya ilahirin ajikinta ,dan haka ta sunkuyar da kanta tana murmushi, alamun  tazo garesa yayi mata .

Tasoma takowa ahankali bai wuce  sauran taku biyu ta k'araso garesa ba  ,cikin wani irin shauki ya fixgota ta fad'o saman fad'add'en  kirjinsa ,ya matse gam ajikinsa yashiga yawo da hannuwansa duka ajikinta,da kyar ta ware idanunta tana kallon M.A da yayi mata kyawawan masauki akirjinsa, tayi saurin  lumshe idanunta saboda daddan kamshin turarensa daya bugi hancinta  "muwaddat baki San yadda kika yi  tasiri a zuciyar Auwal ba ko ?

"Tukunna ma me ye a tsakaninki da wancan sakaran dan naga yana neman kawowa rayuwata saiko? 

"Wa kenan ? Ta tambyeshi tana bud'e idanunta da suke a lumshe .

Ya kai bakinsa kan lips dinta yana yawo da harshensa sannan yace "wancan Aku kuturun mana mai shegen surutun tsiya ya k'arasa fad'in hk yana kamo lips dinta ya fara tsotsa kmr yasamu sweet tare da cigaba da yawo da hannuwansa a sansar jikinta. 

Batayi k'ok'ari  dakatar dashi ba saboda zuwa lokacin itama tanason  irin abinda yake mata, fuskarta ya had'e sosai danashi ,hancinsa na Gugan nata ,kwayar idanunsu na sarke cikin juna ,suna fuskatar juna yana tsotsan lips dinta yana busa mata hucin numfashinsa.

Ta janyo numfashi  da kyar ta fesar tana sake lumshe idanunta ,shi kuma ahankali yacigaba da tsotsa bakinta  son ranshi , ganin bakinta yasoma mata zafi yasa tasoma k'ok'arin kwace bakinta daga cikin nasa amman yaki sakar mata baki sai faman tsotsar harshenta da hakoranta yake ,da kyar ta samu ta tattaro karfi ta sanyawa jikinta, ta fixge bakinta tana sauke numfashi"wayyo Allah bakina  ciwo kmr zatayi kuka ta fad'a tana dubansa, naufashi ya fesar tare da furta wayyohlly Allah ...... yana k'ok'arin kamota zuwa jikinsa ta goce ,ya tsura mata ido kawai yana kallon yadda jikinta ya mutu kmr yadda nashi yayi ,bayan kmr second goma ya kamo hannunta yana duba inda ta kone .

Miskilanlan murmushi yayi "muwaddat manya ba dai   ragwanci ba , ba wata  kunuwa   fa kika yi ba , kawai dai raki ne irin naki  yasa kike ta faman hura gurin ,wannan ma kenan inaga kinji wannan ya kamo hannunta zai  d'aura saman joystick dinsa dake Mike.. tayi saurin kwace hannunta "banason  abinda kake min "meye na miki da baki so?

"fad'a min sai na daina ..?

"Wannan abar tun bata kai haka ba kike massaging dinta, to meye yanzu kike gudunta fi sabilillahi ?

ya k'arasa fad'ar hk yana shafo kirjinta.

Naunayen  ajiyar zuciya ta sauke tace "yanzu da lokacin baya ba daya bane Auwal, yanzu na girma na fahimci illar yin haka gareni,,shikenan na fahimta  kin amince da zarar mun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login