Showing 63001 words to 66000 words out of 160337 words

Chapter 22 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12407

karyar datayi domin idan ta bari yasan bata gida kuma tana tare da al'ameen mai rabata dashi sai Allah "ban yarda ba, adaidai wannan lokacin nasan abinda kikeyi ba wanka ba ,idan kuma wanka ne ki turo min nonona nagansu nayi kewarsu .....

ya k'arasa fad'ar haka yana buso mata iskar bakinsa ta cikin wayar,take numfashi nta ,ya ne mi d'aukewa ta dafe saitin zuciyarta "Auwal zaka kasheni fa "idan na kasheki nayi rayuwa dawa ?

"Ga matan nan dayawa a duniya sai ka zaba ka durje.

"no no Sam bazasu min ba ,karki manta inda nayi karatu cikin kyawawan matan turawa Wanda yawo tsirara agurinsu bawani Abu bane duk banji daya daga cikinsu Sumin da zan iya rayuwata dasu ba ,ni kece macen Da zuciyata ta yarda ta amincewa rayuwa daita .

Ta k'arasa jikin mota taja ta tsaya tana cigaba da sauraransa gabadaya ta manta da inda take saboda yadda maganarsa ke shiga cikin jikinta da zuciyarta .

Al'ameen kuwa tafiyarta ya bashi damar yi mata tsiyaya sosai sannan ya fito ya sameta jikin motar tana waya ,bai ji komai ba aransa saboda tunaninsa ita da iyayen goyonta ne ,batare da yayi magana ba ya bud'e mato yashiga ya zauna itama ta bud'e ahankali tashiga ta zauna tana jin zai tayar da motar tayi saurin katse kiran gabadaya ,koda ta gama katse wayar batayi magana ba suka wuce .

M.A kuwa yayita k wayar taki d'auka akalla sai da yayi mata missed call biyar bata d'aga ba, sai zuciyarta dake dokawa saboda fargaba tasan tana d'auka wayarsa ta saka kanta cikin matsala,Dan zai fahimci inda take , daidai sun kai wani traffic al'ameen yace "ki d'auka mana ko kiran bashi da mahimmanci ne ?

"Sannan ma waye mai kiran ?

Yayi mata tambayar batare daya juyo ba yana taka motar saboda danja ta tsaya Kan layinsu tace "karka damu da kowaye kacigaba da tukinka kawai "

Bai ji dadin abinda tayi masa ba, dan hk ya sake wani magana ba ya maida hankalinsa kan tukin dayake ita kuma tana kallon gefen titi shi kam jifa jifa ya kan juyo ya kalleta, yanayin yadda take yin magana yana bashi sha'awa ,ta d'an juyo ahankali ta kalleshi suka had'a yayi saurin kawar da idanunsa tamkar ba ita yake kallo ba ,tacigaba da kallonsa yanayin yadda yake tukinsa taji ya burgeta saboda wannan karon Jan motar yake sannu ahankali cikin natsuwa da kwarewa da nuna ganintar tuki kowa yaga yadda yake sarrafa sitiryarin yasan ya kware da tuki ,agaskiya tukin nasa ya burgeta tunda har taji tana sha'awar itama taja mota da kanta dan dai abi ne bayason can al'amen kamar yasan abinda yake zuciyarta ai ya d'an waigo ya dubeta "kin iya mota kuwa?

Ta d'an kada kai "eh to Auwal ya fara koya min amman har yanzu hannuna bai fad'a ba "ya had'e rai dosai jin ta ambaci sunan Auwal ya cigaba "ai ina jin ko kin koyi tuki ina ganin dady'nki bazai barki kija mota ba da kanki ba, "nima ina tunanin haka shiyasa ban maida hankali wajen koyo ba .

"Amman yana da kyau ki iya koda bazaki dinga ja ba, cikin murmushi tace " zan yi kokari naga hannuna ya fad'a suka dan yi shiru ,sai dai muwaddat ta damu da yadda ya takura mata da kallo can ya sake takalota da magana "Amman tunda zaki dade agarin nan me zai hana ki dinga yawan kaiwa minal ziyara kmr yadda ta bukata?

"ba damuwa duk sanda na sami lokaci zan rinka zuwa "idan kin samu lokaci ko idan mai kaiki yasamu lokaci?

Jin ya jefa mata tambaya sai tace "daga ni har mai kai ni din ."amman ai ke kina da lokaci tunda ba karatu kikeyi ba kina cikin Hutu ba kuma aiki kike zuwa ba ..

"Haka ne amman ina karatu saboda wannan zango gabadaya zan rubuta jarabata ta karshe ta bashi amsar tana had'e fuska saboda ta lura hira yake son suyi ,ita kuma bata fiyye son hira dashi ba ,haka suka cigaba da tafiya yana janta da magana tana d'an sharesa har suka iso gidan tana shirin fita daga motar yace "am...aysha.

Ta waigo da sauri "kin mata kayanki ta kai ganinta ga kayan manya ledoji ne guda biyu shake da kayan ciye ciye ta d'an yi murmushi "nagode sosai amman chocolate kawai zan d'auka aciki daman kuma ita nace ina so ..

Yace "shikenan naji amman ki d'aure ki shiga dasu ko su eiman da mamana suna so ,ta d'an yatsina fuska saboda bata son kinkimar kaya tace "bari idan nashiga sai na turo su d'auka ,ta fita ta fara tafiya zata shiga cikin gidan yana zaune a motar har tashige gidan ba abinda yake banda kallon tafiyarta taku take cikin natsuwa irin na matan da suka amsa sunansu mata ,shi kansa yasan tana da mugu kyau kmr yadda mutane suke fad'a kuma ya yarda da had'uwarta da ajinta ,yasan bazata ta'ba d'aukar kayan tashiga dashi ba ,da haka da kansa ya kinkimi kayan ya bita dashi cikin gidan ya tadda kannenta zagaye daita kowa na tambayarta guraren daya kaita ,ita kuma tana cewa su bari sai ta huta ..

Al'ameen nashigowa parlour'n ya ajiye mata kayan gefenta ya tafi abunsa ta bi bayansa da kallo Wanda batasan dalilin hakan ba ,Allah sarki ta furta cikin zuciyarta tana jin rashin dadin abinda tayi masa ,tasan da Auwal ne sai dai abar kayan ,amman ko sama da kasa zasu had'e bazai d'auko mata ba ,ta ina ma girman kai da miskilancinsa zai sa ya biyota dashi "my Muhammed Auwal kenan yaro da izzan , shi Sam baya d'aukar raini ga kowa ga tsabar miskilanci Wanda yake daya daga cikin abinda yasa take naci akan kaunarsa .

Tana son Auwal tamkar yadda take son rayuwarta ,tana son shi tana son su rayyu tare muddin rai Auwal daban yake acikin maza bazata gaji da furta hakan ba....

Tunda take kallon maza bata taba ganin mai irin yanayinsa ba komai yafisu ,ba dan tana son shi ba ,sai dai tasan ummi bazata bari aurensa ba saboda kaninta ne ...

Tasan dakace auwal yayanta ne ,tasan sai inda karfin ummi ya kare amman sai ta mallakamusu juna

Mummy ta fito daga d'akinta tana fara'a "aa yan yawo kun dawo ?

Muwaddat tayi murmushin tace "Eh momy mun dawo "kece yau wata yarinya tasha yawo har ina da ina kukaje?

Mmn sudais ce....

Muwaddat page 18

October 23, 2020 Muwaddat Complete

bismillahirrahmanirrahim

page 18

Muwaddat tayi shiru tare da tsurawa kannenta fararen idanunta tana tunanin abinda zata fad'a musu har momy ta fice daga parlour'n ,aiko faiza da eiman suka dameta da tambaya,gashi ita guraren data sani kad'an ne acikin garin ilori , tana gudun kada su kureta,lumshe fararen idanunta tayi ahankali saboda tuno wasu daga cikin sunaye gurare siyaya data sani , dan haka atsanake tashiga lisafowa .

faiza taja numfashi ta fesar "ni na d'auka ma wasu mahimman gurare zai kai ki ,kawai sai ya kama yawo mail dake yanzu tunda kuka fita a shopping kuka tsaya muda muke ta jiran ku dawo ki bamu labari wuraren shakatawa daban daban ,amman yaya ala'meen bai kyauta ba, tunda yaki kai ki inda zaki sha kallo ,bayan Yasan ke din bakuwa ce ..

Ta'be baki muwaddat tayi "Dan Allah ku barni na huta ,surutunku ya fara shiga cikin kwakwaluwa ",idan kin huta zaki bamu labari inji cewar eiman?

"uhm zan Baku labari eiman tace "ni gsky bazan tsaya sai kin gama Ja mana rai ba, gara na hau sama gurin yaya ala'meen din ya bani labarin inda kukaje ..

Mamaki yakama muwaddat a zuciyarta tace "wai shin wad'an nan yaran ,wasu irin yara ne masu kwakwar son jin labari haka ?

Har sai sun sa mutun yayi karya domin gabad'aya yaran gidan haka suke da son jin labarin kwakwaf idan aka d'auke ita, ita kad'ai ce tafita daban acikinsu gurin son jin labari ,itama bata sani ba kodan batayi rayuwa acikinsu bane, yasa take haka. muwaddat ta dubi eiman "Dan rashin hankali daga dawowar mutun ko hutawa bai yi ba zakije ki dameshi da shirme, baza ki bari sai ya sauko ki tambayesa ba, "to to shikenan big sister an bari na jira har yagama hutawar sai ya bani labari mai gamsarwa ba irin naki ba, muwaddat ta mike cike da sanyi jiki ta nufi hanyar d'akinta tana cewa "ke dai Allah ya shiryeki ,wannan bakin naki Allah yasa kar jamiki maseefa ...

shiru sukayi gabad'ayansu batare da kowace acikinsu tace komai ba har muwaddah ta k'arasa shigewa d'akinta ta bar su nan, zaune,yayinda a zuciyar faiza addu'a take "Allah yasa yaya ala'meen yayi tasiri a zuciyar muwadda , tunda ta lura shima sonta yake , tasan matukar suka daidai kansu, baza ta saurari M. A tunda ga dukkanin alamu bata son shi shine yake wahalar da kanshi akanta ...

Da daddare ana cin abinci a parlour'n dady ala'meen ya shigo eima ta kalleshi tana dariya "had'uwa kenan kai yaya da ganin wannan kwaliyar zance zakaje gurin aunty latifa...

aiko yana d'aga hannu ya kai mata dundu abaya "kinci gidanku keda zance zani .

aka fashe da dariya gabadaya dady yace "gaskiyar eiman mana idan ba tad'i zaka ba ina zaka a daidai wannan lokacin ?

Cikin dariya yace "dady Allah babu inda zanje ka daina kula maganar wannan tsohuwar ni da ba aure zanyi a kwanan nan ba, ina ni ina zuwa tad'i hjy zuwaira tace "kai kaga banason karyar banza da kake zuwa baka ga 'bata lokacin ba sai yanzu ya dubi ihsan "mamana jeki d'akina ki d'auko min abincina nima anan zanci dady yace "yagajiyar ku ta yawo ?

Yau dai mamana taga gari ala'meen, ya d'an razana kad'an saboda yana tsoron kar yace bai kaita koina ba ran dady ya 'baci domin ya lura dady yana matukar ji da diyarsa ....

Kafin yayi magana muwaddat tace" dady mun sha yawo nayi kallon gari sosai ta fad'i hakan dan kar yace basu je koina ba gobe ace ta sake shiryawa, faiza tayi saurin cewa "bafa koina sukaje ba, duk wayon nasu a tsiyaya suka kare muwaddat tace ",karya ne dady muje wurare da dama naga gidan sarkin garin nan da gidan gwana da dai sauransu ala'meen ya kalleta yana murmushi jin dade tare da kashe mata idonsa daya yana murmushi baki basu labarin na kaiki gidan zo ba ,ta Dan yi dariya "ok na manta ne har gidan namun daji duk munje hjy zuwaira tace ",cewa zakuyi duk kun gama zagaye gari ala'meen yace ,"gaskiya yau ayshatu tayi kallo sosai jin suna daya ambata yasa aka kwashe da dariya ,har ihsan tana neman barar da tiren da take d'auke dashi yace "wallahi da kin barar min da abinci ajiye sunan uwa zanyi agefe na nada miki na jaki, cikin dariya tace "kai yaya ala'meen banda abinka ina ka ta'ba ganin an doki uwa?

"aiko za'a fara daga yau "suka saka dariya eiman tayi saurin cewa ai Kaine yaya ka ta'ba jin an kira aunty muwaddat da wannan sunan ?

Dady yace ban da abunku Dan an kira mutun da sunansa na gaskiya sai yazama abun dariya ?

Ala'meen yace "rabu dasu dady sunji sunan mai dadi ba irin nasu ba ya fad'a yana kallon inda muwaddat take zaune ,faiza ta'be bakinta kana tace "to kuma yau Dan kun fita yawo tare sai kuma kace mu sunanmu bashi da dadi sai nata ?

Dady yayi dariya" faiza baki da dama ke dai bakya rabo da tsokanar yayanki ala'meen yace "kabarni daita sai na cire mata hakora gaba in bata daina kafirin surutu nan nata ba ita da eiman "ashe mu kusan ganin hakoran 'ya gaban goshin mumy inji cewar ihsan.

"to shi yaya kullun sai ya dinga cewa surutu garemu ai duk gidan nan maganannu ne idan aka d'auke aunty muwaddat ala'meen ya zaro ido waje yana dukan bayan eiman "su waye maganannu ?

Ta Mike da sauri tana dariya wallahi kai ne oga kwata kwata a magana... Dan dai baza'a saida kai a magana ba, ni kwanan nan tunda aunty tazo gidan naji ka rage magana ta k'arasa tana kwasa da gudu ganin ya Mike aiko duk parlour'n babu Wanda bai dara ba ..

Ya koma ya zauna yana kallon inda muwaddat take domin yaga yanayin yadda fuskarta tayi babu yabo babu Fallasa tana normal kamar tun sanda yashigo, ya gyara zama sosai yana kallonta ...

Gabadaya tasha jinin jikinta sobada yadda idanunsa ke yawo ajikinta cikin haka wayarta ta d'auki k'ara ,tsam ta Mike tsaye batare da d'auki wayar ba, ta nufi hanyar d'akinta yabi bayanta da wani iri kallo mai tsuma zuciya, komai nata na burgeshi yanayin tafiyarta dirin jikinta maganarta kai komai nata yayi masa arayuwa, irin kalar mata dayake da muradi kenan ,ya dinga jin tamkar yace ta dawo ta zauna yacigaba da kallonta..

sai daya daina hangota sannan ya d'auke idanunsa akanta yana sakin naunayen ajiyar zuciya kana ya janyo kular abinci .

ihsan tace "ya dai yayana naga kana sakin numfashi?

Ya d'ago ya dubeta "ok kema ido zaki saka min kmr wancen yar banza ?

"to wallahi zan fasa miki baki kema , eiman da dawowarta kenan tace " shikenan yau za'a ganku a rana da yar gaban goshinka mu kuma abokan gaba sai mu ganku arana ...yau dai na godewa da yaya zai ture gwanatinki ",zo nan munafuka yaushe kika koyi le'be ?

Ta kwasa da gudu baza'a zo kasamu jakar duka ko ?

" gabadaya suka sa dariya har mumy da dady .

Tun kafin ta k'arasa shiga d'akin wayar ta tsinke ta zauna a bakin gado tana sauke ajiyar zuciya tana jujjuya wayar a hannuta ,ta rasa dalilinsa da yasa duk lokacin da kiransa zai shigo wayarta, take jin yanayin jikinta na sauyawa , duk sai ta dinga jin tamkar ana zarar ranta ,idan tana tare da shi kuwa , komai nata zai tsaya ya daina aiki, sabani yanzu data taso daga parlour'n duk irin kallon da ala'meen yake binta dashi Sam bata ji komai ajikinta ba, sai haushinsa taji yana shiga zuciyarya ,ko second biyar batayi da shigowa d'akin ba , wayarta ta sake d'aukar k'ara takoma ta jingina bayanta da abun gado sannan ta d'auka ", hello kanina ya kake ya gida ya tunina ya kewata?

"Hope komai lafiya kalau ya kake gaya min yadda kayi kewata .?

Idanunsa ya runtse saboda yadda sautin muryarta tayi masa diran makiya akirjinsa....

da kyar ya samu muryarsa ta fito ",lafiya lau muwaddat Dina sai dai kin manta baki tambayi Abu daya ba ,baki tambayeni ya sha'awarki ba, kewarki kuma baki kad'ai bai isa ya bayyana hakan ba ,saboda wallahi...." ke dai ki bari kawai .."dan wallahi muwaddat kin gama da zuciyata, jiya kwana nayi ina kallon nonuwanki, dan Allah ki turo min wasu yanzu na kalla tunda baki bani jiya na kalla ba....

"kinga mu ajiye wannan mgnr , d'azu nayi miki kira yafi sau biyar baki d'auka ba ...

muryarta a matukar sanyaye tace "bana gaya maka wanka zan shiga ba"

"kar muyi haka dake muwaddat duk abinda kike fad'a min ,ban ta'ba jin ban yarda dashi ba sai yau,hkn nan jikina ya bani kin fito wani guri yau, ki gaya min gaskiya karki min karya ina kikaje?

Sanyayyen ajiyar zuciya ta sauke tana murmushin karfin hali aranta, Auwal sai dai abar shi kawai ",kin yi shiru kin barni rike da waya "to me kake son nace ?

"Kice komai ma Amman ki fad'a min gaskiyar inda kikaje .

da kyar ta fixgo magana "ni ..ni babu inda naje fa ....

"AYSHATUL MUWADDAT ya kira complete name dinta wanda take hkn ya haddasa mata sakin naunayen ajiyar zuciya ,yaushe kika koyi karya ?

"Sam Sam dabiar karya baya daga cikin dabi'unki to me yasa zaki koyi yinta ?

'"Dazu bayan nayita kiranki baki d'auka ba nakira mumy itace ta tabbatar da kun fita da wancan maganan ne mai shegen surutun tsiya ......

gabanta ne ya shiga fad'uwa, tayi shiru ta kasa cewa komai illa numfashi da take saukewa ahankali ahankali tare da runtse idanunta gam "yanxu abinda zaki min kenan muwaddah bayan sai da nace karki kuskura ki fita zuwa koina har sanda zaki dawo ,amman kika fita kinsa kuwa yadda naji alokacin da mumy ta fad'a min?

Sai lokacin tayi karfin halin cewa "to to..ni yaya kake son nayi ?

"dady ne da kansa yace ya kai ni yawo naga gari bani da damar da zanki..

"shine ni kika nemi raina min hankali ko ?

Babu komai amman karki sake binsa koina matukar kina bukatar zaman lafiyarki dani ,idan kika sake binsa yawo zamuyi fad'a wanda banga mai shiryamu ba .

Murmushi tayi "kajika da wata magana kamar wani mijina to muyi fad'a mana, ni ai bana tsoron muyi fad'a da kai, idan kasa wasa ma zan saka lambarka a daverting, sannan nayi blocking dinka a what's app naga karyar isa ..

"To kiyi a yanzu mana ai zaki iya ....ya fad'a yana Jan tsaki .

"Kana nufin nayi blocking dinka ,nayi deleting number's dinka..?

Wani dogon sakin yaja da karfin gaske batare daya sake cewa komai ba ,ya katse kiran aiko take batare da 'bata lokaci ba, ta saka number sa a darveting sannan tashiga what's app tayi blooking dinsa tana runtse idanunwata "Anya kuwa Zata iya rayuwa babu shi ?

"anya zuciyarta zata iya d'aukar wannan nauyin?

"Ba zan iya ba, tabawa kanta amsa, gabadaya tashiga damuwa gabanta ya dinga fad'awa karfa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login