Showing 138001 words to 141000 words out of 160337 words

Chapter 47 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12412

ya koma ya kwanta Yana fidda

numfashi sama sama..

Mmn sudais ce

      MUWADDAT

     

             ~NA

 *AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~ 

 

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_

     _(UMMIN KADUNA )_

bismillahirrahmanirrahim

page 40

....shiru ne ya ratsa gidan  tun sanda  su  ummi suka baro parlour'n , abi dake  zaune akan kujera mai zaman mutun d'aya ya rafka uban tagumi, gabad'aya abun duniya  ya  dameshi ,ya kasa tashi  daga zaunen da yake, mafuta kawai yake nema da tunanin wanda zai tautauna matsalarsa  dashi akan bakon  lamarin daya samesu .

a qalla ya kusan minti talatin zaune agurin yana tunanin mafuta , mutun na farko da zuciyarsa  ta bashi umarnin ya nema ,shine  d'an'uwansa umar ,batare da 'bata lokaci ba, abi ya mike cikin hanzari ya  nufi  d'akinsa yasoma neman layinsa .

Bugu d'aya biyu uncle umar ya d'auki  wayar bakinsa d'auke da sallama   byn  sun gaisa ne abi  ya shiga  sanar masa   abinda dake  faruwa a gidansa , take zuciyar uncle umar ta tsaya na wunci gadi , a tsaye uncle umar yake amman bai san sanda ya Kai zaune rike da wayar ba tsabar firgici da tashin hankali , har gumi na karyo masa tsabar rud'anin da buguwar zuciyar d'aya tsinci kansa  alokaci   ,d'aya byn d'aya yake sauraron bayanan abi  "abinda ya gudar musu kenan tun farko  shiyasa ya d'auke bunayya  zuwa wata uwa duniya da sunan karatu ,amnan duk da haka basu tsira ba  ...

"Wannan wace irin maseefar rayuwa ce haka ?

"Wasu irin yara ne haka da nacin tsiya  ?

ya yiwa kansa tambayar

 yana mai  dafe gaban  gashinsa, Yana sake tuno abubuwan da idanunsa suka ci karo dashi a wancan lokacin  ,abi bai boye  masa  komai ba tun daga farko har  kan maganar zuwan  iyayen al'ameen da ummi ta tilastashi  akan lallai sai ya amshi kayan aurensu, "ni duk cikin lamarin babu abinda ke bani mamaki kmr   yadda alhji Mahmud yayi min bakan  da zance kmr bai san abinda ake ciki  ba ,kwata kwata yayi   min shiru da batun auren al'ameen da muwaddat  , haka zalika nasan dole yana da masaniyya akan zuwan iyayen yaron amman har yanzu bai ce min komai ba ....

"umar bazan boye maka ba naji haushin wannan shirun da alhj muhmud  yayi min ,saboda nasan babu yadda za'ayi ace bai san komai dake tafiya ba ,duk nayi iya tunanina ban gano ta inda ake irin haka ba, ta yaya  ma za'a ce...

"Kayi hakuri yaya ,uncle umar ya katse  shi ta hanyar fad'ar hk  "kayi mashi  uziri , ka daina  ganin laifinsa, shima wata killa yana jin yadda kake ji din ne azuciyarsa ,shiyasa bai maka maganar ba ,tunda Kai ma akaidance  yakamata ka nemeshi akan batun zuwan iyayen yaron  Koda   shi bai neme ka ba ,yanzu dai  ka fara  tuntubarshi da zance muji mai zaice ... ..

haka  suka cigaba da tautaunawa da Kuma yadda za'a bullowa a'lamarin ,inda uncle umar yace "masa zai shigo kasar da zarar ya kammala da ayyukan gabansa , zai zo ayi komai akan idanunsa ....

Yau tsawon kwanaki uku kenan da faruwa al'amarin , gabad'aya ahlin gidan basu cikin kwanciyar hankali duk wanda ka d'aura idanunka akansa katuwar ramar zaka gani a bayyane ajikinsa , al'ameen kuwa ya Kira layin muwaddat har ya gaji wayar bata shiga ,ai kuwa hankalinsa yayi kololuwar tashi ,sai daya Kira ummi ne  take ce masa wayar ce tasamu matsala amman tana gurin mai gyara, sannan ya d'an samu natsuwar zuciya,   da hakan nan ya tsinci kansa da jin cewar akwai damuwa ga wani mummunar fad'uwar gaba da yake fama dashi   ..

******

muwaddat durkushe agaban ummi , har lokacin ta kasa saida hawayenta, kamar ummi itama  hawayen yaki  tsayuwa a idanunta, muryarta cike da kuka tace "ummi ki taimakeni ki taimaki rayuwata ki  zubar min da cikin nan wallahi bazan iya haihuwarsa ba ......

ummi ta numfasa tana sauke  naunayen ajiyar zuciya tace "kinsa da haka kika biyewa  kaninki  kuka aikata  abinda kuka aikata, "a shekaranjiya zuciyata  cike take fal da son zubar da cikin jikinki  amman ahalin yanzu ba zan iya ba.

" ban   ta'ba cire ciki arayuwata ba  a tun sanda na soma aiki ba kuma zan soma daga kanki ba ,haka zakiyi hakuri ki haife abinda ke cikinki , sakamakonki  kenan da zaki girba akan biyewa son zuciyarki , ni yanzu yadda zan fuskanci d'anuwana da wanna batun ne  yafi damuna ,ta k'arasa mgnr tana matso ruwan hawaye daga idanunta, nayi danasani nayi nadama mara iyaka arayuwata ,da wani ido zan dube d'anuwana na fad'a  masa wannan abun kunyar .. ?

Cike da sanyi jiki muwaddat ta mike ta nufi d'akinta tana wani irin  kuka mai ta'ba zuciya .

*******

Bunayya yayi k'ok'arin ya fahimtar da muwaddah wasu abubuwa a game da cikinsa dake jikinta  dan baya bukatar rasa shi ,domin kuwa shine karfin gwiwarsa a halin yanzu,amman  taki   bashi  wannan damar ,sai dai kallo d'aya zaka mata ka tabbatar da bata cikin natsuwa da walwala da kwanciyar hankali, duk ta fige  acikin  kwanaki had'u  kacal saboda damuwar data d'aurawa kanta ..

cikin satin  bunayya ya shirya ya tafi ilori,  da al'ameen yasoma cin karo a compand ,ko kallon inda yake zaune bai yi ba, kai tsaye part din yaya akram ya nufa, yana zaune a d'akin, yaya akram na rigingi ne yana fidda numfashi sama sama tamkar mai cutar asma  bunayya  yayi shiru gabansa na fad'uwa,   yaya  akram ya d'an gyara zamansa Yana mai  dafa kafad'arsa   yaji wani zafi ya tsara shi ya d'ago habarsa ahankali ya dube cikin kwayar idanunsa "mai ke damunka auwal?

"ka daina yawon tunani irin haka bashi da amfani "kai din cikakken likita ne kafini sanin illar tunani ga rayuwar d'an adam, idan wani abu ke damunka is better ka fad'a min ko bazaka fad'awa kowa ba "

"ni da kai mune manya yanzu acikin family duk da na girmeka nesa ba kusa ba, amman haka nake jinka kmr sa'anin juna muke.

Bunayya  ya numfasa haka nan yake jin zai iya fad'awa yaya akram damuwarsa, ahankali ya bud'e bakinsa yasoma zayyano masa duk abinda ke tsakaninsa da muwaddat tun daga farko har zuwa yanzu da cikin ya bayyana ajikinta...

"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yaya akram ya shiga furtawa yana sake maimaitawa sannan ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa shikena irin abinda ya sameni  ne ya sameka kaima "

"wannan wani irin maseefar ce haka

 iyayenmu suka yi silar jefa rayuwarmu ciki?

A matukar tsorace  bunayya yake duban yaya akram cike da matsanacin mamakin jin farucinsa " irin abinda ya sameni ne kaima ya sameka, bunayya ya maimaita yana sake duban   Yaya  akram a firgice .

Kai Yaya  akram ya d'aga Masa  al'amun  haka ne, sannan yace "ka gan ni nan tun lokacin dana had'a degree dina na farko nake son nayi aure amman dady ya hana yace "lallai sai na had'a karatuna gabad'aya tukunna, haka na hakura ba dan raina yaso ba , Wanda  azahirin gsky ban hakura da bukatata ba domin zuwana Spain  muka kulla abota da wata abokiyar karatuna muka fara soyaya kamar wasa , halakarmu tayi karfi sosai har ta mallaka min kanta, ni ne d'a namjin dana soma kusantar polina, a yanxu haka in takaice maka yaranmu biyu daita mace da nmj, na barota da cikin na uku ..

shiyasa duk lokacin dana tafi banason dawowa kasar nan, gashi yanzu na kare karatu  gabad'aya, babu wata damar da zan sake koma gareta ,kuma ni a halin yanzu bazan iya rayuwa da kowace irin macen ba sai ita  ....

wannan ciwon da nake wallahi duk na rashin yarana ne da polina.. gashi ahalin  yanzu aure dady yake son nayi a cewarsa yanzu ne daidai aurena ,ni kaina yanzu  bansa yadda zanyi da rayuwata ba shiyasa yau ciwo gobe lafiya .

Bunayya ya runtse tsumammun idanunsa da suka canza kala tun soma maganar yaya akram yace "yanzu yaya akram haka zakabar  yaranka a wata kasa Kai kana rayuwa anan ?

"gasky ka koma ka taho dasu har ita polina din, yadda zasu rungume tamu kaddara da muwaddat ,haka zasu amshi taka, ai duk sune silar faruwar komai..

"kayya auwal bana jin zan iya aikata hkn, yanzu ga taka matsalar ,idan a kawo tawa abubuwa zasuyiwa iyayenmu yawa  gara dai asan yadda zamuyi da taka matsalar haka bunayya ya dawo Lagos jikinsa babu laka  ..... ..

******

Bangaren ummi da bunayya har lokacin bata sauko  daga dokin fushin datayi dashi ba ,sam taki saurararsa  ,dan ko inda take bata kaunar yazo idan ma yayi mata magana bata amsa mishi  ,sosai abi ke rarrashinta da k'ok'arin shawo kanta ta hanyar bata hakuri da nasiha da dad'dad'an kalamai masu sanyi da sanyaya zuciya  ,abi da kanshi yace" bunayya yaje ya  sake rokon umminsa yafiya bisa ga laifinsa,"Ina da tabbacin umminka zata yafe maka a halin yanzu ,duk dai kuskurenta ne , sai dai itama  nasan wasu abubuwan tana yinsu ne bisa rashin sani ,wanda ni agurin duk wannan kaddarar da take kokawa akanta ni   daidai ne .

" duk abinda zai faru gaba ni dai ka rike muwaddat amana sannan ka nemi yafiyar umminka domin ka gizgiza zuciyarta sosai   "

"abi wasu daga cikin zantuttukanka suna d'aure min Kai ,ko ma nace bana fahimtarsu sosai  "

"ba zaka fahimta ba bunayya sai nan gaba zaka fahimceni , Kuma nasan hakan zai maka dadi har ma yazamo silar farincikinka  ,maza tashi kaje ga umminka ka bata hakuri  cike da sanyi jiki ya nufi hanyar d'akinta.

 a  zaune a bakin gadonta ya isketa tayi   tagumi ,  ya shigo ahankali  yana dubanta cike da tausayawa ,ahankali ya cire hannunta da tayi

tagumin dashi ya zauna kusa da kafafunta tare da tankwashe kafafunsa idanunsa sunkuye a kasa muryarsa a raunane yasoma magana " ummina "kece kika yi silar zuwana duniya .....

Ummi  kece mutun ta farko da nake kauna duk duniya ,ummi ban aikata wannan laifin bisa ganganci ,  ko dan 'bata miki rai ba , sai bisa  kaddara  ,ummi na sha fama da ciwo da rad'ad'i soyayyar muwaddat tun ban mallaki hankalin kaina ba  , Ina jin idan na rasata arayuwata zaki iya rasani , rashinta a duniyata zai saka zuciyata tayi ciwo na har abada ,amnan duk da haka baki cancacin na cusguba miki irin haka ba,

Lokacin dana nuna Ina bukatar aure ummi a tunanina kece mutun ta farko da zaki bani goyon baya amatsayinki na uwa amman sai kikayi watse da maganata har ma kika ajiyeshi a matsayin shirme ..

 A halin yanzu ni kaina nayi nadama  ,ummi ki yafe min dan girman Allah ki daina fushi dani kiyi hakuri ki rungumeni kmr yadda kika rungumi muwaddat ,nima ki bani farinciki kamar yadda kike bata a yanzu ,dan Allah ummi ki yafe min ,nasan  na shiga hakinki na cutar dake ta hanyar kusantar muwaddat dinki ,but ki yi hakuri ki yafe min ki yafe min... ....

Ummi  tayi shiru tare da  tsura masa idanunta tana dubansa , shi km tunda yashigo d'akinta har zuwa sanda yake zaune, ya kasa d'ago idanunsa akanta  , kallonsa ummi ta cigaba dayi  har lokacin cike da mamakinsa domin ko a mafarki bata zaci haka daga garesa ba "bata zaci zai iya kwanciya da mace a d'an shekarunsa ba har ma da dirka ciki ,sai gashi ya shata mamaki ..

Jin tayi shiru taki cewa komai  yasa ya kamo hannuta cikin nasa "kiyi hakuri ummi kice min wani abu ko zuciyata zata samu natsuwa plz.. ,wallahi fushinki bak'aramin tashin hankali bane gareni  ....

Idanunta cike da ruwan hawaye tace "bunayya me kake son nace ?

"Ai  babu abinda zance sai dai nace na gode  kwarai da gaske da abinda ka aikata mana,ni ahalin yanzu me kake tunanin zance maka ,ai  babu abinda zance sai Allah yayi ma albarka dan bazan tsine maka ba  ,ayanzu ma da ban ce jeka zaka gani ba, ga irin sakayyar da kamana....."

 Ummi  nima.... "dakata ban nemi jin komai daga gareka ba, kunya ce dai kasamu jinta a koina, ni babu abinda yafi min ciwo da damuna kamar abinda zan fad'awa mai neman aurenta...

 Bunayya ya sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da zance zuci yace "abinda zaki fad'a  masa ya wuce kice "an fasa auren dashi tunda dai bazai yiwu ayi aure da cikin wani  ba..

"yanzu dai  na  yanke shawarar zata cigaba da rainon ciki har sanda zata haife abinda ke cikinta ,sai mu Kai gidan marayu , batare da sanin kowa ba daga baya sai ayi zance aureta  da al'ameen .....

Cikin wani irin buguwar zuciya da tashin hankali ya d'ago kansa, yana zaro idanu cikin  matsanancin mamaki tare da matsowa daga zaunen da yake  zuwa gefen gadon cike da bak'inciki da son gasgata abinda yaji ya fito daga cikin bakinta , duk  a tunaninsa bai ta'ba tsamanin za'ayi masa irin haka ba ya d'auka cikin sauki zata amince a Karon kanta ..

"ka daina mamaki bunayya abinda na fad'a babu batun wasa ko mafarki ko k'arya acikinsa ,yin haka shine daidai agaremu ,kuma shine farin cikinmu, mu bar wannan sirri acikin zukatan mu  sannan har abada babu kai babu muwadda matsawar kana son kwanciyar hankalina ko tsintsiyar hannunta  ban lamunce ka sake ta'bawa ba. ....

Wani irin kallo Bunayya yayiwa Ummi wanda ni kaina nakasa tantance wani irin kallo yakewa Ummin nasa , kallon dai yafi kama da kinaneman yimin wasa da rayuwata .....

jikinsa da bakinsa rawa suke yana cigaba da duban ummi yana sauraronta kafin daga baya yasoma magana cikin zafin rai "ummi zaki sake tafka wani babban kuskure acikin rayuwarmu, muwaddah na sona fiyye da tunaniki duk wanda kuka aura mata tabbass gangar jikinta zai aura amman batu na gaskiya soyayyarta na gareni, nima kuma bangarena haka ne, zancen gaskiya Ummi idan har bani kuka aurawa Muwaddat ba to tabbas kisawa ranki miji biyu gareta domin bazan taba barinta ta zauna lafiya ba,

Ummi maganar gidan marayu dakike magana bamai yuwa bane saboda d'ana ba maraya bane gani nan ina raye duk wahala dana sha ba dare ba rana Allah ya albarkaceni da k'aru ace za'a min salalan tsiya akai gidan marayu impossible ummi don't. don't say that plz ummi .

muwadda tayi nisa acikin raina sonta baxai ta'ba barina ba, sai dai, idan bana numfashi "ya sauke  ajiyar zuciya ya cigaba da magana..

"Atakaice dai  ummi yanxu kin fi son al'ameen akaina ko...?

Ko me ya tuna sai ya shafa keyarsa tare da kaskantar da kanshi da muryarsa yace

"Shi...shikenan  babu komai  ni ..ni.zan barta ummi  kamar yadda kika nema bazan sake  sa'bawa umarninki ba, sai dai ummi  bazan ta'ba yin aure arayuwata ba, saboda muwadda ta rigada ta tafi da duk  wasu abubuwana masu mahimmanci arayuwa.

sai abu na gaba cikina ina son abuna koda duk duniya zasu tsine min, koda zan rasa komai da kowa ku bani abuna da zara ta haifa ,kar akai min d'a gidan marayu gsky ..

Ganin yadda ya nuna son cikinsa a sarari   yasa  ummi ta zarce da  yi Masa nasiha  dan ta tsorota matuka da yanayinsa ,wasu abubuwa yake tamkar wani hamshakin magidanci  , duk abinda take fad'a sam  baya jin abinda take cewa  saboda ya tafi duniyar tunanin, tausayin kansa ne kawai ya dira masa da kuma son muwadda da yake azabtar dashi ...

Kansa na sunkunye a kasa haka zalika muryarsa na rawa yace"  ummi ki ya fe min maganar da nayi Miki a yanzu , shine abinda nake son naji daga bakinki a halin yanzu ,da kyar ummi ta bud'e baki tace "bunayya na yafe maka tun a baya dana gane kuskurena sannan a yanzu ma na yafe maka ....

wani irin sanyi dadi ne ya ziyarci zuciya da ma gangar jikinsa, duk da yana cikin damuwa da tashin hankali amman hkn bai hanashi jin farinciki ba  "na gode ummi na gode daman  nasan umminah mai yafiya ce ,ya d'aura kansa bisa cinyoyinta, ahankali ta Kai hannunta saman kanshi "Allah yayi maka albarka , sai dai bani da kwarin gwiwar fuskantar d'anuwana  ta rushe da kuka "karki damu ummi inshallahu zai fahimceki....

"Allah yasa nima ka yafe min ,nashiga hakinka nashiga rayuwarka domin nice silar komai daya faru , zance nafi son al'ameen da Kai wannan ba haka bane an ridaga an gama magana da iyayensa yanzu idan muka hanashi me kake tunanin mutanen kalgo zasu fad'a akanmu ?

"Ni dai ummi karki Kai min d'a gidan marayu ...."to yaya kake son nayi nifa banason kowa yasan da wanna batun ...

Bunayya bai samu sukuni ba tun daga ranar da abun ya faru ,sai da yayi kusan kwana goma bai nemi inda  muwadda take ba, itama bata nemi shi ba ,daman kuma yasan ba neman nasa zatayi ba, ya damu sosai har sai daya kira yaya akram ya fad'a masa abinda ummi  ta zarta ,yaya akram  yace "abinda nake so da kai kasamu natsuwa ,sannan ka kwantar da hankalinka har zuwa sanda zata haihu din, ni kuma muddin ina raye zan tsaya maka har sai ka mallake muwadda amatsayin mata.. ..maganar yaya akram ta kwantar masa da hankali har yaji natsuwa kad'an a jikinsa..

*********

bangaren muwaddat kuwa babu laifi ta d'an saki ranta ta yarda ta amincewa kaddarar data fad'a mata, sai dai duk sanda ta tuna tana d'auke da ciki ,ranta idan yayi dubu sai ya 'baci, tana kitchen tana had'a xuma da madara wanda ya zame mata kaida idan bata sha ba babu zaman lafiya .

taji bakincikinta na karuwa  a halin da take ciki ,babu abinda yake ta'ba zuciyarta da  wuce buris din da  bunayya yayi daita , haka tacigaba da aikin gabanta da kula da abubuwan da suke gabanta ,ahankali tasoma k'ok'arin fitowa daga cikin kitchen hannuta rike cup tana juya zuma  da madarar data had'a ,gabad'aya hankalin na kan zumar har miyonta na tsinkewa .

sam bata ji tsayuwarsa abakin kofar kitchen din ba, tacigaba da takowa shi kuma yashiga binta da kallo yana kare mata kallo duk da bai ga fuskarta ba hakan bai hanashi ganin kyawun da ta k'ara ba,  ta murje tayi fresh ta sake yin haske na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login