Showing 120001 words to 123000 words out of 160337 words

Chapter 41 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12406

kafin abi ya dawo ya samesu hk amman ta kasa ,cikin zalaya tace "kaga malam dan Allah ka daina min irin wannan kallon, ta'be bakiyi yayi "ke da wani ido kikaga ina kallonki?

yana gama fad'ar hk ya Mike tsam ,cikin zolaya yana k'ok'arin bar part din ummi..yace " aunty ki shiryawa anjija da wuri nima zan dawo zabani na rana naci kafin umminki ta dawo ta kanainaye koina ......

Banza tayi Masa taking cewa komai har sansa ya k'arasa barin parlour'n.

muwaddat na shiga makaranta tasoma jin zazzabi sakamakon wani turaren abokiyar karantunta data shaka,gefen kanta ya sara abu kmr wasa sai gashi tana kelaya amai duk abinda tace sai data amayar dashi acikin kankani lokaci ,ta fita haiyacinta har wata yar daguwar rama tayi, tayita d'aurewa ,da taga abun na son fin karfinta ta kira number abi tace a turo mata direba bata da lafita, madadin abi ya tura mata direba kmr yadda ta buqata sai ya tura Mata bunayya, inda yake fad'a ya kula daita ta hanyar taimaka Mata , cikin kankani lokaci ya k'araso ya d'auke zuwa Gida ,tunda ta isa gida tashiga d'akinta da kyar ta kwanta bata sake fitowa ba,

Taimakon gaugauwa ya fara bata tare da maganin malaria a tunaninsa itace ke son takura Mata , tunda complain din ciwon kai take , byn ya bata magani ya kwantar daita ajikinsa Yana k'ok'arin rabata da kayan jikinta duk yadda taso ta dakatar dashi ta kasa saboda bata da kuzari ajikinta ahankali ya rabata da kayan jikinta,shima ya cire kayan jikinsa ya had'eta jikinsa yana shashshafata zafin jikinta na ratsa jikinsa , ko cikakken minti goma Basu d'auka a haka jikinta yayi sanyi ,Aiko ya birkice mata ,ta hanyar turo Mata zafafan sakoninsa masu tsayawa arai , tun tana zamewa ajikinsa ya tarairayota har ta bada kai ,suka lula duniyar soyewa , yau kam ba tayi Masa wani raki ko korafin gajiya ba, ita da kanta ma ke sake makaleshi ajikinta,tana shafosa ahankali suka cigaba da murza fatan juna batare da tunanin want ba ............

jirgin yamma ummi ta biyo ,karfe 4:00 daidai na yammaci ranar ta sauka, tana sauka number muwaddat tasoma nema kafin na kowa, sai dai wayar na ringing,amman ba'a d'auka, ta k'arasa inda tasan zata ga direbanta.

bello direbanta na ganinta ya fito da sauri daga cikin motar, yana k'ok'arin bud'e mata kofar baya had'e da gaisheta ta amsa sannan tashiga ya ja.

suna isa gidan babu wanda ta soma tambaya sai muwaddat, binta tayi mata sannu da zuwa sannan ta k'ara da cewa" dazu ta dawo daga makaranta tana d'akinta kai tsaye d'akin ummi ta nufa....

Mmn sudais

ce...



     

MUWADDAT

     

 

           ~NA~

 *AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_

     _(UMMIN KADUNA )_

~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~

warning!!!

don't read this novel  if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you   read it, is for   your own risk .....

WATTPAD @HAUESH

Page 33

..Hannu ummi ta kai jikin handle din  kofar d'akin domin bud'ewa ,taji  kofar a rufe gam ,dan haka tashinga buga kofar da karfin gaske cikin tsananin tashin hankali tana Kiran sunanta" muwaddat! Muwaddat!!

Muwaddat dake kwance a saman fad'ad'den kirjin bunayya tana baccin gajiyar sex din da sukayi  , ta zabura tai wani irin   hantsilowa  daga kan gadon cikin tsananin tashin hankali tana dafe kirjinta da duka hannuwanta tare da furta kalmar" Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un "yau mun shiga uku..ummi ta dawo...."

Wani irin shu'umin kallo bunayya ya bita dashi kana yace "mun shiga uku ,ko kin shiga uku?

Murayarta na rawa tace " duka mun shiga daga ni har  kai wallahi ...irin abinda nake gudu kenan amman ....

 "wata uwar

Harara ya zabga Mata Wanda yasa take ta had'iye abinda take son furtawa ,  k'ok'arin d'aukar wondansa yayi ya saka hankalinsa a kwance ,  ya kai hannunsa ya janyo farar rigarsa dake yashe kasa  ya rataya a wuyansa " madam please open the door for me...."

"What ta furta a kid'eme tana girgiza masa kai?

"dan girman Allah karka min haka bunayya, ba..banason ummi ta ganmu tare  ......" ka rufa mana  asiri bunayya ,ta kamo a hannuwansa cikin rud'ewa da matsanancin tashin hankali ,jikinta na sake d'aukar rawa sakamako sake Kira sunanta  da ummi tai "muwaddat zo ki bud'e min kofar ,ko jikin ne yayi tsanani ?

Bata amsa illa jikinta daya kama rawa tmkr mazari "zo ..zo muje ka fita ta window tayi hanyar window d'akin dashi ....

Da sauri ya fixge hannuwansa dake cikin nata  yana nuna kirjinsa da yatsan hannunsa " ni ne zan fita ta window ko wa?

tayi saurin d'aga masa kai al'amun "eh"

 "Dan  Allah ka rufin mana asiri  ni da kai  ,ban ta'ba sanin haka  tashin hankali  irin wannan yake ba sai yau  ,kwata kwata na manta cewar yau ummi zata dawo ....... ta k'arasa mgn hawaye na gangarowa bisa kuncinta.

 "ka rufa min asiri bunayya ,"ka taimaki rayuwata ka rufa min asiri bunayya!!tana mgnr tana kuka tana jujjuya Masa hannuwanta tmkr wata k'aramar yarinya , bakinta na rawa tana k'ok'arin kai gwiwowinta kasa ..

 ya kai hannunsa ya kamota jikinsa zai rungumeta, ta yi saurin gocewa tana kuka "to  yanzu me kike son nayi ,ni dai gsky bazan iya fita ta window ba  Allah ya sani , Koda kuwa hkn bashi da wata illa ,bare Yana da ?

"Yanzu haka kina sake

  ' bata lokaci ne ,har sai  kinsa ummin ta fahimci wani abu, ki bud'e kofar kawai ta ganmu ,ba sai na fad'a Mata cewar Abi ne yace na taimaka na duba lafiyar ki ba.....

 "ni..ni..dai a'a ,ummi nada saurin fahimta abu, hanyar bayi ta nufa dashi tana kuka "muje bathroom dan Allah karka a'a .. suna shiga suka tsaya cirko cirko suna duban juna ,shi kam bunayya ko dar bai ji ajikinsa  ba ,asalima tsumammun idanunsa ya tsura mata  yana  k'ok'arin rungumeta a ajikinsa, "muwaddat ki natsu plz duk   kin wani rud'e ,ki samo  mana mafuta , ummi fa zata iya shigowa nan  is better ta ganni a bedroom dinki akan nan  ....

ba tace dashi komai ba, illa hawaye data cigaba da zubarwa tana k'ok'arin barin jikinsa kafin kace me jikinta ya sake d'aukar zafi  ,hankalinta a matukar tashe  ta fito daga cikin bayin tana kulle kofar tare da Murd'a  key ta zare , jikin na rawa ta shiga gyara gadon dan gabad'aya ya  hargitse a wasaninsu , ta janyo doguwar rigarta ta Sanya , ta nufi kofar d'akinta wanda zuwa lokacin har ummi ta juya da niyyar zagayowa ta dubata ta window ,tana gama bud'e kofar ummi ta juyo da wani irin  sauri ...

Lumshe idanuwanta tai tana saisaita natsuwarra kana ta juya   ahankali  tana dafe kanta da take jin yana Sara Mata tmkr zai cire tsabar tashin hankali ,fad'awa tai  kan gado tana fidda numfashi sama sama ta sake sanyawa jikinka natsuwa  .

Ummin ta k'araso da sauri zuwa  inda take  kwance ,ta tsura mata ido tana kare mata kallo, saboda doguwar ramar data ga tayi, ahankali idanunta ya sauka akan  kirjinta gabanta yayi wani irin  mugu mugun fadawa kafin daga bisani  ya shiga dokawa , kirjinta taga  yayi wani irin mahaukacin  cikowa  , yayi mata hake hake ,numfashinta na sauka ahankali ,girgiza kai tashigayi tana kawar da abinda taji ya tsarga Mata acikin zuciyarta "a taanake tashiga kallon d'akin still zuciyarta na dokawa Wanda ta rasa abinda yasa hk  hk Nan take jin tsinkewar zuciyar ...

Jikinta a sanyaye ta samu guri a gefen katifa ta  zauna ta d'aga kan muwaddat ta meida kan cinyarta, taji zafin da jikinta yayi ,ya ratsata ,ta dafa goshinta tana kiran sunanta ahankali "muwaddat dina...... ...Sannu "

"shi yasa hankali yaki kwamciya  a duk wuni yau ,ashe baby nah bata da lafiya"

muwaddat ta bud'e idanunta da kyar tana duban ummi sannan ta kirkiro murmushin  dole tana mikewa da kyar ,ummi tace "kiyi kwanciyarki ma ,ina da ina ke miki ciwo?

"ko kanki ke ciwo ta fad'i hakan, saboda tasan tana da yawon ciwon kai, muwaddat dake atsorace  ta rasa mai zatace Mata , kawai ta d'aga  mata, saboda ita alokacin babu abinda ke damunta sai tsananin tsoron dake tattare daita .

 jikin ummi na rawa tace "okay bari naje na kawo miki magani  ki Sha ,wannan zafin  jikin naki ya wuce

 kaida, ta ajiye kanta akan pillow ta nufi kofar fita cikin sauri ,kai tsaye ummi hanyar  d'akinta ta nufa .

 cikin wani sauri muwaddat ta zabura ta mike, jikinta na rawa ta bud'e kofar  bayi ta janyo hannusa ,suka fito tare dashi tana rokonsa  ya fita kafin ummin ta dawo amman kememe bunayya yace "bai zuwa koina , aiko ta d'aura duka hannuwanta bisa kanta ta rushe  da wani irin kuka mai ta'ba zuciya  ....

Naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske yace "Kinga fa wannan shirmen da kike yi Allah shin zai saka ummi ta fahimci wani abu ,ki natsu ki kwantar da hankali ...ta d'ago da sauri  tana kallonsa  da idanuwanta da suka gama canza kala tsabar tashin hankali..

   Ummi kuwa nashiga d'akinta  ta nufi dorowarta dake ajiye magunguna ta d'auko mganin zazzabi da Maleria ta dawo d'akin muwaddat cikin sauri .. turus tayi tana binsu da wani irin kallo mai cike da tambayoyi iri iri .

Muryarsa a kasalance yace" ummi   sannun da zuwa,"yauwa Daman kana cikin gidan ne ko yanzu ka shigo ?

Bayan keyarsa ya tsutsa Yana duban muwaddat dake k'ok'arin runtse  idanuwanta,kana  ta rufe fuskarta da hannuwanta yace "yanzu nashigo "

"Okay to d'an bamu guri zanyiwa baby allura ..lumshe idanunsa yayi  yana shafa sumar kansa ,sannan ya soma k'ok'arin ficewa daga d'akin,magani ummi ta'bata  had'e da yi mata allura  still zuciyarta na cikin taskon Dan har lokacin ummi Bata daina jin fad'awar gaba ba, kwantar daita tayi ,tana sake  jero Mata sannu ,kusan minti goma ummi na tare da ita kafin daga bisani ta fito ta sake nufar dakinta .

Ummi na fita daga d'akin ta mike  zaune tana d'aga hannuwanta duka sama ta shiga yiwa Allah godiya ,daya rufa Mata asiri ,aranta tayi alkwarin babu ita babu bunayya har karshen ratuwarta, ita dashi sai dai kallon kallo bazata sake barin ya kusanci inda take ba ,tunda yafi kaunar ganinta cikin tashin hankali  ,kafin  wani  lokaci  zazzabi jikinta ya sauka, ta dawo normal sai dai yanayin jikinta da take jin shi wani iri kmr banata ba komai a sanyaye take yinsa gashi  bata jin dadi bakinta komai taci kmr zata amayar ...

***********

da daddare yaya al'ameen ya kirata sai da ya soma had'ata da 'yan'uwanta  suka gaisa sannan suka shiga hira , wanda duk hirar shine ke yinsa amman ita daga uhm sai uhmm, ba wani abu yake fad'a mata mai Dadi ba  ,illa sake jadadda mata yadda tayi tasiri arayuwarsa, jinsa kawai take saboda gabad'aya zantuttusa sun isheta ,koma tace haushi suke bata ,km  amatsayin shime ta d'aukesu, tana zaune ummi tashigo parlour'n cikin shiga ta alfarma duk yadda ta d'an manyata hakan baya hanata yiwa mai gidan kwaliyya ,bare anyi kwana biyu ba a had'u ba ta fad'i hakan a zuciyarta , tana gani shigowar ummi ta katse kiran,tana duban ummi .

bayan ummi ta samu guri ta zauna ,ta d'an dubi muwaddat, "ke da waye a waya?

"yaya al'ameen ne ta fad'a mata atakaice, ummi ta kai hannu ta amshi wayar tana dubawa sunansa ta gani sannan tashiga bincikar wayar babu komai na aibu aciki dan haka ta mika mata wayar .

"ya jikinki naki yanzu hope you are feeling better ?

ta d'aga mata kai ahankali ,sannan tashiga  janta da hira tana

bata labarin yadda bikin minna ya kasance"baby muwaddat idan kikaga yadda binki fadila ya k'awatu abun sai ya burgeki , sai naji ina ma bikinki ake yi ,amarya da ango sun sha kyau har sun gaji , kema dai zuwa yanzu yakamata  musan mai kike ciki da al'ameen, yaron nan na da kirki da hankali matuka ,uwa uba yana da natsuwa sannan ya had'a Master's dinsa zaku dace da juna, dan irin miijn da nake miki fatan samu kenan arayuwarki ,wanda nasan kema shine irin zabinki dogon namji kyawawa mai haiba ko ba hk ba?

muwaddat ta had'e rai sosai  tana turo baki, ummi ta cigaba "amman ke sai naga kmr  kina basarwa  a duk sanda aka yi miki maganarsa,ke kowa yazo kice bai yi miki ba gashi wannan shekarar zaki kare karatunki, zan so ki saida miji , da zarar kin gama karatunki  musha biki "gaskiya ina sonki da al'ameen sosai sai dai bazan matsa miki ba, idan kinji baki sonshi shikenan sai a bashi hakuri shima kmr sauran ...

 muwaddat tayi shiru kawai tana sauraron ummi har tagama maganarta.

ummi ta du'beta sosai tana nazarinta kafin daga baya tace "kinyi shiru  shima bazaki auresa ba ko?

 kin fi son kiyita ganina ina yawon zuwa bikin mutane, ni kar azo nawa?

muwaddat ta girgiza mata kai kawai ala'mun a'a amman a cikin xuciyarta cewa tai lokacin da nake son aure ba'a min ba ,sai yanzu za'a dameni to ni banason Yaya al'ameen .....

Kmr ummi tasan abinda ke zuciyarta tace "nifa bazan Miki auren dole ba sai Wanda kike so zan baki ,idan baki son shi abar zancesa kawai  ,amman  idan kin  amince kin yarda da auri al'ameen nasan kowa zai ji dadin wannan had'in.

a kasan zuciyarta kuwa cewa tayi "ni auwal fa nake so ummi bawani Yaya al'ameen ba ...,da zaki aura min shi da kin gama min komai ,da na samun duk wani  jin dadi duniya ,"auwal  shine cikar burina da kwanciyar hankalina, duk wani wanda zaki so na aura ,bazai ta'ba kai min kmr auwal ba......., banason yaya al'ameen din nan wallahi..amman ummi kina neman takura rayuwarmu  ..

"tunanin me kikeyi mueaddat kinyi shiru kina jina ?

 ahankali ta bud'e bakinta tace "babu komai ummi,  tunda kin amince dashi, kin yarda na auresa ,naji na amince zan auresa kawai  amman ina son ki min alfamar d'aya ummi?

ummi ta fad'ad'a murmushinta tana murna saboda jin dadi tace "wacce irin alfarma ce wannan mamana?

"ki fad'a min shi, ni kuma nayi miki alkwarin zan yi miki shi muddin bai fi karfina ba, idan bani dashi zan nemoshi matukar akwai shi acikin duniyar nan..

muwaddat ta numfasa ta runtse idanunta saboda d'acin abinda zata fad'a sannan tace "  duk abinda za'a yi na aurena da yaya al'ameen har zuwa lokacin  da komai za'a kankama ,  inason ayi shi a boye cikin sirri  ummi...

 "ta yaya kike tunanin za'a yi maganar aure cikin sirri ?"  waye bakyason yasan zakiyi aure?

muwaddat tayi shiru taki magana har sai da ummi ta sake maimaitawa, sannan tace"auwal .....

"ummi  banason bunayya ya sani saboda banason yashiga damuwa "bakyason yasani saboda bakyason yashiga damuwa ?

ummi ta sake maimaitawa tana dubanta .

"bakyason yasani ko kema kina son kaninki kmr yadda yake naci ..?

 har zatace eh sai kuma tayi saurin girgiza mata kai ,"banason shi ummi amman kuma bazan so na gansa cikin damuwa ba ,ta k'arasa mgnr hawaye na ciccikowa a kwarnin  idanunta "ummi  tsakanina da Allah banason yaya al'ameen amman tunda kin yarda da natsuwa da nagartarshi wallahi na amincewa zan aurensa ...

,nasan zan so shi daga baya....amman a halin  yanzu gsky banason shi...

ummi tayi saurin kamo hannuta tace "anya kuwa yarinyar nan lafiyarki kalau?

"Anya kuwa muwaddat baki da aljannu kowa kice baki so ..?

" tun tasowarki kike samun masoya amman kowa yazo sai kin kawo aibunsa"

 "nifa bani da komai ummi kawai dai banasonsu ne ta k'arasa mgnr hawayen da take k'ok'arin makalewa suka samu nasarar zubowa..

"ummi tace ashsha abun har da kuka?

" to abar zance al'ameen din kawai tunda shima baki son shi, ta d'ago kanta tana duban ummi "a'a ummi ni nace na amince wallahi zan auresa, kuma zanso shi saboda   shima bashi da makusar da zan kisa.. ..

"to shikenan  kukan ya isa haka Allah yayi miki albarka zan fad'awa abi sai ayi masa magana ya turo magabatansa .

"zance   bunayya kuma ki ajiyeshi a gefe ,banason ki damu kanki saboda shi, shiyasa nake Allah Allah ya  koma ,kuma nasan kafin ya dawo anyi komai angama, muwaddat bunayya ba sa'an aurenki bane,  koda kina sonshi bazan bari ki auri kaninki ba azo Yana baki ciwon kai , bare baki sonshi , idan kuma kinsa kema kina sonshi ne sai ki fad'a min?

Jikinta na rawa ta  girgiza mata kai , tana jin yadda bugun zuciyarta ke tsananta, ina ma zata iya fitowa ta fad'a wa ummi wallahi da tayi, domin babu wanda ya dace daita sai d'anta  Muhammed auwal ...

sun rabu da ummi tana cikin damuwa mara misaltuwa, gabad'aya komai ya tsaya mata ta dinga jin kmr ana k'ok'arin rabata da rayuwarta ne ,amman haka ta dinga d'aurewa saboda kar ummi ta fahimci maganar ce ta haifar mata da damuwa  ...

Tunda asirinsu yaso tunowa muwadda ta kiyayi kanta dashi ta daina sakar Masa fuska bugu da Kari Kuma  zance al'ameen da kullun ummi take damunta dashi ,yasa take sake nisanta kanta dashi.

abu fa kamar wasa zazzabi dare ya saka muwaddat  gaba kullun daren da zazzabi take kwana, ga amai kmr zata amayar da hanjin cikinta ,

 yau dai  bunayya ya kawo mata ziyara sbd ya kasa hakuri  , yanayin jikinta yayi matukar firgitashi  ,har ya mike zai koma part dinsa ya d'auko kayan aikinsa Dan ya  dubata, sai kuma ya kasa barinta ya koma ya kwanta a bayanta ya  zagaye kugunta da dukka hannunwansa da zumar washegari zai dubata special ya gano takaimai mai matsalarta

**********

washegari bayan ya tabbatar da ummi tana gurin duba percent dinta, ya had'a ruwan  allurar da zai yi mata ya nufi makarantasu, ya kirata a waya tun daga nesa ya hangota tana taku

anatse tana yauki kamar batason taka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login