Showing 159001 words to 160337 words out of 160337 words

Chapter 54 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12436

/>
' faiza tamu fa nace ta haihu ta haifi nmj ,sai kawai

taga ya sake kawar da fuskarsa wani gefen

Ta mirgina gefensa ta koma saitin fuskarsa ,ta sausauta

muryar kmr mara lafiya "amman Allah ka bani mamaki

faiza yaya al'ameen 'yan'uwanamu ne fa,idan ma baka

had'a komai da yaya al'ameen ba, faiza fa?

sister did ce uwa day'a uba daya, kaf duniya bani da

sama daita, itama haka

"ama ajiye wannan, a tunanina yarda kaga nayi haihuwar

akram , bobo , dady ,a gabanka a rashin tunanina sai

naga ko a hanya kaga mai ciki zaka tausaya mata, kayi

mata fatan alkairi ,to balle wacce ta kasance yaruwarka,

gaba fa bata da kyau "wake gaba ?

"ai ni bai isa nayi gaba dashi ba ,huld'a ce dai har abada

bana bukata dashi saboda banason yawon had'uwarku

dashi ..tayi shiru tana dubansa cike da mamaki .

Ya kamo hannuta cikin nasa yana murzawa " ya kika yi

shiru?

"to me kake son nace maka?

"to shikena Allah ya raya musu

ta janye hannuta ta tashi ta zauna ya matsota sosai kmr

zai shige jikinta ,ya rungumo kugunta daga kwance

dayake "aunty nah kada kiji haushina wallahi ina sonki ne

fiyye da komai sannan ina da matsanancin kishi akanki

bana son wasu ma su ganki bare wannan daya ga samu

yaga rashi, mutumin daya kusan kassara min rayuwa, da

ba dan Allah nasona ba da tuni na dade da mutuwa

'Ni dai zan fad'a maka gsky idan kaga dama ka d'auka

,manzo Allah s.a.w yace baya tare da duk mai raba

zumuci ,saboda haka Dan girman Allah ka saki zuciyarka

akan al'ameen, yanzu al'ameen kanwata yake aure ,bani

da wata halaka dashi byn zumunci ,kuma wallahi nayi

maka alkwari ko mutuwa kayi bazan auri wani Tsatson

aleemen ba .

Kai da kanka kasan ba sakina zakayi ba ,"ra bani, ni dai

banason ma yawon fitar nan, kina da kyau sosai har kin

fi matarsa kyau

"to sai me kasan dai babu aure tsakaninmu ?

"nasani 'ka canza dan Allah..

"Auntyna.....hannuta ta kai ta shafi gashin dake kwance a

cinyarsa "kar ka manta, nima ina sonka sannan zan

cigaba da sonka har karshen numfashina

Nice matarka ta farko ,nice matar daka soma sani diya

mace a duniya ,duk da haka nasan nan gaba zakayi

tunani kara aure ,ka auro min wata mu zauna tare ,mu

dinga sharing dinka biyu ni daita mu raba komai naka

biyu ,amman duk yadda nake jin kishinka sosai, na

hakura nake kwabar zuciyata da kishinka, nake rayuwa

da kai batare da ina tunanin hkn ba bare na d'aukeshi

nasawa zuciyata kawai saboda ina son mu zauna lafiya

da junanmu

Ko kana tunani ni bani da kishi ne "wallahi Muhammad

Auwal nafi kowa sonka a duk duniyar nan ,amman acire

ummi ka daina tunanin a yanzu zuciyata na tunanin wani

nmj byn kai ,kai kad'ai ne a zuciyata ta k'arasa mgnr tana

sakin kukan shagwa'ba dake tafe da kissa da kara

raunata zuciyar duk Wanda ya jishi "kana kallona baka

varda dani bane ?

Ya janyota jikinsa yana murmushi "stop crying my aunty

mai son girma yau kuma kece kikewa kaninki kuka ?

"ta doki kirjinsa cike da shagwa'ba 'to shikena ya isa na

yarda na amince dake dari bisa dari kiyi hkr InshaAllahu

zakiga canji ,amman sai kinyi hakuri saboda ahankali

komai zai zama normal ya tallabo fuskarta suna

fuskantar juna "kin hakura ?

Ta daga kanta "to to kiyi min murmushin nan naki mai

sanyaye min zuciya tayi murmushin had'e da kissing din

lips dinsa..

Duk da wannan mgnr datayi masa bai barta taje ba sai

ana gobe suna shima tare sukaje suka sauka a hotel,

Taron suna yayi kyau yaro yasamu sunan Ibrahim shima .

Bunayya ya canza akan yadda ya d'auki abun , most

especial daya ji sunan Wanda aka saka

Kamar dady ya kudurta a ransa, iman da ihsan suma

suna cika shekara shatakwas zai kawar dasu ya huta

,domin har lokacin bai daina jin radadin mutuwar akram

ba, kullun ya tuna yadda ya dinga masa magiya akan

yana son aure a lokacin, da zai turasa Spain hawaye ne

masu zafi suke ziraro masa ko ya yaransa suke?

ko a wani hali suke?

"Allah sarki rayuwa Allah ya jikanka Ibrahim allah yasa

aljanna ce makomarka bazan gushe gurin yi maka addua

ba...

cikin wannan halin mumy tashigo ta samesa "ko bata

tambayesa ba tasan kukan dayake wanda itama har

lokacin tana jin zafin mutuwar d'anta fiyye dashi, kasa

zama tayi ta fice daga d'akin wasu daga cikin yaran

aikinsa masu hankali ya bawa rensu eiman .

Bangarensu bunayya da muwaddat kuwa duk karshen

shekaran duniya sai sun fita yawon bud'e ido ,wannan

karon dai yawon bud'e ido , daga nan su kaiwa su

muhmud ziyara Wanda hakan ya sake jawo shakuwa

mai karfi atsakaninsu , yawo yayi dadi kmr koda yaushe

da suka ba dawo da tsaraba , dan yanxu ma gata

kwance tana lauyayin wani sabon ciki Wanda yanxu ya

Shiga wata na uku a jikinta

Bayan shekara Goma

Bunayya ya k'ara girma sosai ya zama cikakken

magidanci mai tsananin kyau da d'aukar hankali Dan a

lokacin ko cewa akayi bai yi aure ba zaka yarda itama

muwaddat duk da yaranta biyar yanzu, amman har

lokacin jikinta a kame yake ,Sam bata bar jikinta ya

lalace kmr yadda wasu matan keyi ba, haihuwa daya biyu

kaga sun dawo wani kala

,yaran yaya akram muhmud Wanda ya kasance babba ya

,yaran yaya akram muhmud Wanda ya kasance babba ya

ziyaracisu a wannan shekarar , yan'uwa sunyi murna

sosai ,barin dady da momy sukayi tasawa bunayya

albarka ,domin shi yayi tsayin daka a cikin lamarin ban

da shi sai dai rayuwarsu takare akan d'ansu nada wasu

ya'ya a wata uwa duniya, amman ba zasu gansu ba

Allah mai yadda yaso yanzu ya'yan muwaddat takwas a

yanzu maza bakwai mace day'a wace taci sunan ummi

suna kiranta da mufeedah ,kusan awa day'a kenan data

tasa mufeedah gaba tana kallonta had'e da tunanin

rayuwa

Har kusan karfe takwas na dar kwance take tana

tunanin sakamakon bakin da b nayya yayi daga London

abokan karatunsa ne...

Ta kasa runtsa idanunta saboda rashin maigidanta kusa

daita, sai wajen 12:00 yashigo ya sameta kwance ya

karaso gareta inda take kwance ya sunkuyo ya sunbacci

goshinta 'Yaya dai aunty nah ?

tayi murmushi Dan Allah ka daina ce min aunty nan idan

ba haka kaima zaka dawo yaya

"kice min mana ai zan fi son hk..taso ki gaya min

damuwarki kinyi shiru kina faman tunani ,azo a gaya min

tunanin wa ake yi .

Ta Dan juya kad'an ta kama hannunsa cikin nata tana

massaging ahankali ahankali sannan ta yunkura ta Mike

ta d'auki mufeedah ta kaita d'akin baccinsu, ta dawo

Wanda lokacin har yashiga wanka ,itama sauya kaya tayi

Ta kasa runtsa idanunta saboda rashin maigidanta kusa

daita, sai wajen 12:00 yashigo ya sameta kwance ya

karaso gareta inda take kwance ya sunkuyo ya sunbacci

goshinta 'Yaya dai aunty nah ?

tayi murmushi Dan Allah ka daina ce min aunty nan idan

ba haka kaima zaka dawo yaya

"kice min mana ai zan fi sonh aso ki gaya min

damuwarki kinyi shiru kin

n tunani ,azo a gaya min

tunanin wa ake yi .

Ta Dan juya kad'an ta kama hannunsa cikin nata tana

massaging ahankali ahankali sannan ta yunkura ta Mike

ta d'auki mufeedah ta kaita d'akin baccinsu, ta dawo

Wanda lokacin har yashiga wanka ,itama sauya kaya tayi

zuwa na bacci tabi lafiyar gado bayan ya fito ya shirya ya

kwanta abayanta ya juyo daita suna fuskantar juna "gaya

min damuwarki ta shige jikinsa" bani damuwar komai

,tunaninka ne kawai ke dawainiyya da ruhina ,bayan shi

tunanin mai zanyi bayan na godewa Allah daya azirtani

da samu adalin miji tamkarka fatana har aljannah mu

kasance tare .

Alhamdullahi Alhamdullahi Alhamdullahi nan muka kawo

karshen labarin muwaddat abinda nayi daidai Allah ya

bani lada kuskuren dake ciki kuma Allah ya fe min

Subahanaka allahumma ashadu allaila a illahah

astagfiruka wa'atubu ilaik

Mmn sudais ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login