Showing 129001 words to 132000 words out of 160337 words

Chapter 44 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12397

d'ansa  farinciki .......

  haka dai taron ya watse batare da abi ya wani saki jikinsa ba, baki na barin gidan ya d'auki wayarsa ya  Kira alhaji Muhammad ya zayyane masa komai daya faru , cike da matsanancin mamaki dady ya dinga saurararsa har sanda ya dasa aya kana ya furzar da wani numfashi mai zai fi a ransa yace "kenan ala'meen haka zai yi masa ?

"da fari ya saka  shi ya zamo k'aramin mutun a gurin iyayen litafa ,yanzu Kuma yana shirin    rukujewa masa burinsa akan muwaddat ,amman babu komai zai saka masa ido yaga iya gudun ruwansa.......

********

A ranar da aka sa ranar auren muwaddat, haka nan bunayya ya yini  da zazzabi mai tsanani, zuciyarsa ta dinga tsinkewa tana harbawa  ,duk motsin da yayi sai gabansa ya fad'i,  gabad'aya zuciyarsa tayi masa nauyi da kunci, zafi kashi da kashi yake ji acikin zuciyarsa..

Gashi daman  tun daya shigo kasar cikin damuwa yake hakan ya rasa sukuni , ramar da yayi tayi yawa sosai har ta fito fili, haka  fuskarsa ta bayyana  dukkan damuwar dake zuciyarsa .

suna zaune  a gurin shakatawa shi da  abokansa, gabad'ayansu suna tsananin tausayin halin da suke ganinsa ciki , suka zabga tagumi kowane daga cikinsu  ya kasa magana.

 Nabeel  ne yayi karfin halin magana yace" m.a  ya dace ka cire wannan damuwar aranka tunda kazo kasar nan baka bar zuciyarka ta huta ba,kullun cikin tunani kake,ka shafe damuwar dake cikin zuciyarka, domin suna nuni ne da yadda ka yiwa rayuwarka kyakkyawar fahimta.

saboda a yanayi na matsayinka da wayewarka da gantanka da isarka, da wahala ace kana irin wannan tunani. domin su wad'an nan abubuwa guda uku daka mallaka kyau kudi ilimi suna sa mutun yayi kowani irin girman kai suke sa mutun,mutun  ya dinga jin kansa ishashen da babu wanda ya isa sai shi,shi ke sa mutun ya dinga jin babu abinda ya isa yazo ya dameshi saboda isarsa da takama  ..

saboda haka ina mai jan hankalinka tunanin da kakeyi a wannan lokacin yayi yawa , ka bar zuciyarka ta hutu ka yarda da kowani rin kaddara samu ko rashi..

M. A yayi tsit kansa na kasa ,ya kasa cewa komai har sai da Nabeel  yayi shiru sannan ya d'ago kai ya numfasa.

Nabeel  gabad'aya naji zantuttuka ,kuma zanyi amfani dashi, ina son ku ta yani da addua duk kwanaki nan bana jin dadin zuciyata da gangar jikina, ji nake tamkar ana zarar raina, jikina na bani akwai abinda yake faruwa gida,ko Kuma yake Shirin faruwa da rayuwata , nayi waya gida kowa na lafiya ban sani ba ko boye min suke ..

"to kayi addu'a mana shine mafuta inji cewar nabeel, "Inshaallahu duk zamu tayaka da addua amman ka saki ranka plz..

***********

tun daga lokacin da aka tsaida magana  mai karfi tsakanin al'ameen da muwaddat shikenan al'ameen ya maida lagos tamkar ilori da ogbomosho duk weekend din duniya a lagos take yi masa, ta bangaren muwaddat babu yabo babu fallasa ta kan d'an sakar masa fuska ,shi kansa al'ameen idan akace masa muwaddat bata sonshi a halin  yanzu zaice karya ne , saboda irin kulawar da take bashi idan tazo..... 

 

 wasa wasa bunaya  ya kasa samun natsuwar zuciya duk da suna waya da chatting da muwaddat kmr yadda suka saba amman duk sanda ya runtsa idanunsa sai ya kasa bacci, gashi dai kowa ta bangarensa lafiya lau yake, dan babu wanda basa waya dashi har muwaddat bai ga wata al'amun akwai wani damuwa attare daita ba yafi tunanin dai damuwar iya kansa kawai ta tsaya kullun  damuwarsa na sake karuwa ya rasa mai ke damunsa da rayuwarsa gabad'aya .

Haka nan ta bangaren faiza taki barinsa ya huta, kullun  zata kirasahi a kalla sau goma , sai dai duk nacinta haka zata gaji ta hakura dan daidai rana d'aya bunayya bai yi tunanin  d'aukar kiranta ba, dan bai San me take nufi dashi ba ,bayan ya fito ya bayyana mata abinda ke cikin ranshi .

Ta bangaren faiza kuwa babu abinda ke dawainiya daita sai zallar shaukinsa da farincikinki burinta ya kusan cika tunda Yaya al'ameen zai zamo miji ga muwaddat tasan tabbas bunayya zai zamo mallakinta ,ta d'auki tamarar zatayi komai idan dai zai zamo miji gareta ...

 Haka nan yau cikin bacci ya mike a matukar  zumbure  yana mai  dafe daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da karfi, nan fa gumi ya rufeshi ta koina ajikinsa, ahankali "yashiga furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.. .

cikin haka kiran faiza yashigo wayarsa yana dubawa yaga itace Yaja dogon  tsarki tare da furta another matsala kawai......

 ya ajiye wayar yana gyara kwanciyarsa  ,ita kuwa jin tayi kira  ya kai sau goma sha bai da niyyar d'auka kamar koda yaushe yasa taji ranta ya 'baci  , ta dinga jin tamkar ana diga mata dalma ne akan zuciyarta ,take zuciyarta ta harzuka tasoma tunanin abinda zata masa wanda tasan babu makawa zai nemita domin Karin bayani .

Shiru yayi kawai yana tunanin matakin da zai d'auka akanta    yaji shigowar sako da kmr bazai  duba ba sai dai yayi tunanin ko muwaddat ce,dan haka  ya lalu'bo wayarsa  sakon da idanunsa suka ci karo dashi ne yasa shi tashi zaune da sauri yana sake dafe daidai saitin zuciyarsa dake harbawa har wannan lokacin , da karfi ya furta "what..?

 "When ?

 Kana ya tsurawa sako ido yana sake karantawa yana sake maimaita kalmar Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un ga abinda sakon ya kunsa"

_slm a lokacin danake rubuto maka wannan sakon ina cikin matsananci farinciki da annashuwa ,ina maka albishir da kaima zaka rasa cikar burinka daka girma dashi, yadda bazan sameka ba, haka kaima ba zaka samu damar cika burinka,  domin kuwa yau kimanin wata daya kenan  da aka saka ranar auren  aunty muwaddat da yaya al'ameen har ma da sadaki atsakani, wannan abu yayi min dadi ni faiza za'ayi to zero_

cikin wani  irin tashi hankali ya zabura ya mike yana sakin  qara tare da cewa "ba dai muwaddat dina ba, muwaddat tawa ce ni kad'ai ,duk runtse duk wuya  babu wanda ya isa ya aureta sai ni...

nan take jikinsa ya shiga rawa ,yasoma k'ok'arin kiran faiza tana kallo wayar na ruri ta saki wani shu"umin murmushi "ai nasan zaka kirani ,ni kuwa bazan d'auki kiranka ba ,kai ma kaji abinda mutane sukeji ,tana kallo wayar na cigaba da k'ara amman taki d'auka daga karshe ma ta kashe wayar gabad'aya tana dariyar mugunta .

Gajiyayi yasoma neman layin muwaddat domin jin gskyr lamari  amman shiru bata d'auka ba, gashi dai wayar tana ringing , hankalinsa yayi mugu mugun tashi yasoma ganin double, ya dafe goshinsa da hannuwansa duka yashiga bin bagon d'akin ,can ya saki k'ara mai sauti sai ga abokansa guda biyu sun shigo d'akin a matukar razane sukayo kansa suna tambayarsa  "lafiya M. A me yasameka?

yayi shiru kawai yana dubansu d'aya bayan daya tmkr wani zautacce,ya dungule hannunsa d'aya ya naushi iska Yana furta " imposble .....wani ya aure muwaddat bani ba, ya wucesu cikin  sauri ya k'arasa gaban wardrobe dinsa ya bud'e  saboda ya rasa me ya kamata ya fara yi ,akwatin kayansa ya  janyo yashiga zuba kaya yana kiran waya  "

sai lokaci suka fahimci abinda yasa ya fita haiyacinsa , suka matso kusa dashi suna tambayarsa "yanzu ina zaka haka da kake k'ok'arin had'a kaya?

"Nigeria ya basu amsa atakaice ....."plz M. A.. ..

"don't dont say anything to me dan ba fahimtarku zanyi ba, sai sai..  .. yayi shiru tare da  cilla da wayar bai gama jin mai ake fad'a masa acikin wayar  ba .......

"haba M. A kayi hakuri mana kasanyawa zuciyarka natsuwa ,karka tafi cikin wannan  tashin hankali ,Dan girman Allah ka bari zuwa ..."NO bazan bari ba sadik yayi maganar yana d'aga murya  ,Ni zata yiwa wannan wulakacin  saboda taga ina sonta ?

"wallahi sai na bar kasar nan, kuma a yau idan ba haka ba zan haukacemuku ,zan na tashi hankali kowa yau a gidan dan haka kusan yadda zan bar kasar nan  .....

sai sai na ....ya kasa k'arasawa ya dunkule hannunsa ya bangon d'akin   yana furzar da numfashi mai zafi ..

Sadik ya rungume shi ajikinsa "plz m.a kayi hakuri zamu San yadda za'ayi ka bar kasar but at least kasanyawa zuciyarka natsuwa.. numfashi kawai yake ja Yana saukewa tamkar mai cutar asma yana girgiza kai ..shi kawai yasan halin tashin hankali dayake ciki .

nabeel najin yadda sadik ke fama dashi gurin bashi hakuri amman yaki ,yasa   ya  d'auki wayarsa dake yashe da har lokacin ba'a katse Kiran  ba ,cigabasa wayar ,inda yake tambayar  "ko akwai jirgi mai zuwa nigeria ayau din ?

daga can bangaren aka bashi amsa da akwai amman sai gobe karfe shida zai tashi na safe. "okay ka mana booking ya fad'a atakaice cikin tashi hankali ,sannan ya dawo ga bunayya ya tsura masa Ido Yana kallonsa ,duk ya wani  firgice , gabad'aya ya  rasa wani irin so bunayya yake wa muwaddat ,tun haduwarsu yasan da zaman muwaddat ,itace macen data hana mata dayawa samun gurbi acikin zuciyarsa ,duk macen daza tace tana son shi sai ya kusheta yace "muwaddat dinsa tafita kaza , ranar dai babu wanda ya runtsa acikinsu , Allah Allah suka  dinga yi gari ya waye ya bar kasar..

Washegari tun asubar fari ya bar kasar london zuwa Nigeria ..

mmn sudais

      MUWADDAT

     

             ~NA~

 *AYSHA  A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~  

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_

     _(UMMIN KADUNA )_

warning!!!

 don't read this novel  if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you   read it, is for   your own risk ......

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 37

...tun da muwaddat taji sautin muryarsa yana furta kalmar  "abi ummi ku daina wahalar da kanku ciki na ne..  ... zuciyarta ta tsaya cak ta daina aiki na wunci gadi....

 kafin daga baya zuciyarta ta soma bugawa da karfin gaske,maganarsa ba'a iya kunnenta  kad'ai suka samu nasarar  tsayawa ba har ma da gangar jikinta da koina take jin saukar furucinsa  tamkar saukar aradu ....

yi tayi  kmr ta kwasa da gudu ta bar parlour'n domin tsira daga wannan taskon  tashin hankalin data tsinci kanta  mai tattare da abun kunya , amman babu halin aikata hakan  sakamakon gabobi  Jikinta da take jin tamkar ba'a gangar Jikinta suke ba   , ahankali jikinta ya sake d'aukar rawa kamar mazari, hawayen idanunta suka tsananta gangarowa bisa kuncinta , da kyar  ta juyo inda  ummi da abi wad'an da sukayi mutuwar zaune agurin suka dawo tamkar matattu suna duban bunayya ,mamaki ne ko kuwa dimuwa ce tasa me su alokacin, ita dai bata sani ba, dan tashin hankalin da take ciki ya ninka nasu.....

Cikin tsananin matsanancin tashin ahankali bakinta ya cigaba da maimaita kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun jikinta na wani irin kyarma  .

wannan kalmar da muwaddat ke maimaitawa a fili itace ta dawo da ummi da abi cikin hankalinsu  suka shiga kallon  ita kanta muwaddat din, kallo kuma irin na tsantsar mamaki da al'ajabi da tashin hankalin.

  "da gaske ne  abinda kunnuwansu  suka ji ya fito daga bakin  tilo  d'ansu ko kuwa karya ne ?

ummi ta tsaida kallonta akan bunayya sosai tana son ya karyata mata abinda taji ya fito daga cikin bakinsa cewar karyar ne ba gaskiya bane....

amman sai taga yayi shiru yaki cewa komai illa wayarsa daya rike gam kmr za'a kwace daga hannunsa , yayinda a bad'ini kuwa ba za  iya misalta kalar tashin hankali da shi kansa yake ciki ba...

da kyar ummi ta had'iye abinda taji ya tsaya mata a makoshi  ta kira sunansa cikin wata irin murya wacce bai ta'ba sanin umminsa dashi ba "bunayya ......

cikin jikin muwaddat kai kayi shi ko kuwa kunnawanmu ne suka jiyo mana sa'banin  haka?

 A sukwane ya d'ago kansa ahankali zuciyarsa na wani irin bugawa da karfin gaske  ya tsurawa umminsa da hawaye suka gagara tsayawa akwarnin  idanunta ido yana kallonta , kafin daga baya ya d'an lumshe tsumammun idanunsa   ya bud'esu fesss akanta ya janyo numfashi da kyar ya fitar hankali, sannan yace "eh ummi cikina ne kuma ina son abuna plz ku bar min shi......

" inna lillahi wa inna ilaihi rajiun  shi yayi nasarar katsewa bunayya  hanzarinsa.

    "cikinka ne kuma kana son abunka ,abar maka shi bunayya?

Ummi ta furta haka tana kuka ,ya d'aga mata kai ala'mun eh, ai ko ta sake rushewa da wani sabon kuka.....

kuka ummi take sosai tamkar ranta zai fita tana dafe da kirjinta da take jin tamkar zuciyarta zatayo waje.

 "wace irin bakar rana ce yau gareni ?

"Meke Shirin faruwa da rayuwata data ahlina ?

"Ya  Allah kasa zantuttukan bunayya  su kasance cikin mafarki nake jiyo su ?

"Allah Allah  kasa karya  ne ,karka nuna wannan bakar ranar acikin rayuwata "me zancewa duniya ........ ?

"Me duniya zata fad'a akaina ?

"Idan wannan abu ya kasance gaskiya ya ..ya ..ta kasa k'arasa zancen zucin da take sai ta kama  haki  tana fidda numfashi sama sama ......

    shi kuwa abi gabad'aya kasa magana yayi yana cigaba da kallon bunayya cike da matsanancin mamakin karfin hali irin nasa  "wato dai sune suke masa kallon yaro k'arami wanda bai isa aure ba,a she shi tuni  ya zarta inda suka ajiye matsayinsa?

"lallai yaran  zamanin yanzu sai dai abarsu kawai ......

 har lokacin abi ya kasa cire mamakin wannan a'lamarin acikin zuciyarsa   ,wai muhammed auwal d'ansa d'an shekara 22 ne  yayi  muwaddat ciki, to a ina akayi wannan cikin....... ?

 kwalkwaluwarsa tashiga caji da tunanin inda akayi ciki suna cikin gidan batare da sun sani ba.

Bunayya ya mike tsaye ahankali ya isa gaban ummi  ya durkusa bisa gwiwowinsa yace "dan Allah ummi karkice zaki cire cikin  nan wallahil azim ciki na ne ajikin muwaddat, kuma ina son kayana .....

 tassss !tasssss!! tassss!!! Kake jin  ta d'auke shi da wasu gigitattun maruka har guda uku ajere tana haki  "ka min Shiru .... d'an iskan yaro mara d'a'a  idan ka sake furta  wannan kalmar agabana  sai na tsi....

" kul...... ....abi yayi saurin katseta ta hanyar fad'ar haka , "baki ta'ba masa mummunar  furuci  ba a tsawon rayuwarsa kin dai ga abinda ya faru yanzu .....

"baki ta'ba furta wata kalmar banza garesa ba kinga aika aikan da ya aikatamana , hakuri zamu taru muyi gabad'aya tunda haka  kaddarar tazo mana, amman batu na tsinewa ko zagi duk bai taso ba.

"Irin abinda nake hangowa kennan agareki mukarama kika mutsutsuke idanunki kika biyewa son zuciyarki yanzu wa gari ya waya ?

"Tabbass idan bunayya na da laifi namu laifin ya zarta nasa "

"Yaran nan suna son junansu sosai fiyye da tunaninki ,amman kika ce Sam ba haka muwaddat bata son shi yanzu ai Kinga karshen kiyayya  tun da ga sakamakon nan ta haifar ,tun tuni na zubda makaman yakina akan lamarin sabida ba'a jayayya akan irin wannan lamari 'a'a bunayya yaro ne bazan bashi diyata ba this and that ya k'arasa maganar yana  furzar da iska tare da buga abun kujera yana zabgawa bunayya wani irin mugun kallo .....

Bunayya wanda idanunsa suka rikid'e sukayi ja tsabar tashin hankali da yake ciki ya mike ya   nufi gurin abi ,"abi kayi hakuri dan Allah karka karawa ummina damuwa akan wanda take ciki "yi min shiru wa ya jawo ?

"Ai suk wanda ya sai rariya yasan zatayi zuba "Kai Kuma da yake ..sai yayi  kawai yana sake furzar da iska mai zafi  ...

"Kuyi hakuri amnan  tun tasowata nake son muwaddat Kuma da aure ,na cire kawaici da kunyarku amatsayinku na iyayena na bayyana muku abinda ke raina da burina amman kuka ki ,ni dai  dan girman Allah ku bar min ci.....

Wani sabon mari yaji daga bayansa wanda yasa take ya had'iye abinda zai furta "shine akace ka mata ciki dan iska ?

"Nasani muwaddat ba zata ta'ba aikata hakan ba wallahi sai dai idan tursasa kayi .

"kayi Mata dole dan kawai  kaga karshena ko bunayya ?

" Nasan kayi haka ne dan ka kuntata min  amman sai numfashinta ya d'auke sakamakon hakin d'aya rufeta tayi kasa luuuuuuu  zata Fad'i, bunayya yayi saurin tarota jikinsa Yana jijigata ,take hankalin abi da muwaddat ya sake tashi suka yo kanta atare suna Kiran sunanta  muwaddat na kuka ta durkusa kusa da ummi ta kamo hannuta hawaye na bin kuncinta ...

 "ummi..!ummin....!!"ya rabbi   dan girman  Allah ummi karki mutu ki barmu  a duniyar Nan ,idan wani Abu ya sameki a dalilin abinda na aikata bazan ta'ba ya fewa kaina ........

Abi yasoma k'ok'arin amsarta daga hannunsa amman furrrrrr bunayya yaki sai Kiran sunanta yake cikin tsananin  tashin hankalin .

Cike da matsanancin tashin hankali abi yace "wa. water .....  wani irin zabura muwaddat tayi ta nufi hanyar inda  firdge din abi yake, ta bud'e ta  d'auko ruwa mai tsanyi tun kafin ta k'araso  ta soma k'ok'arin bud'e robar ruwan  tana gama k'arasowa ta  shiga tsiyayawa ummi tana wani irin  kuka ..

 gabad'aya sun gigice sun rud'e sun fita haiyacinsu kallo d'aya zakayi musu kasan cewa suna cikin tsananin damuwa ,  duniya da abinda ke cikinta sun taro sun   cakud'e musu  guri d'aya , barin muwaddat da ke jin  rayuwata ita   da babu duk d'aya ,addua kawai take a halin da take ciki  Allah ya d'auki ranta a lokacin ta huta ,da kyar numfashin ummi ya dawo gangar jikinta.

 tayi atishawa tare da  sauke naunayen ajiyar zuciya Jikinta na wani irin  rawa  take suka shiga rigerigen yi mata sannu suna sauke numfashi "sorry



ummina dan Allah karki tsine min bisa  kuskurena ......

ummi ta  bud'e idanuwanta da kyar hawaye na tsiyaya daga kwarnin idunta  tashiga kallonsu d'aya bayan d'aya  tana girgiza Kai kana ta runtse idanunta gam  tana jin yadda dukkanin su ke jero mata sannu amman banda bakinciki babu abinda ke dawainiya daita da zuciyarta  "me zatayi da wani sunnunsu "an rigada an  cuceta an cuci rayuwar diyarta.. bunayya take kallo ta kawar da kanta tana hawaye su bunayya da muwaddat suma kuka suke har wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login