Showing 132001 words to 135000 words out of 160337 words

Chapter 45 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12398

lokacin  .

 Ahanksli bakinta  ya shiga motsi   al'amun tana son yin magana tana salati ..

 hakan ya sake gigitasu suka sake matsowa gareta , abi da bunayya suka yi saurin kasa kunnuwansu daidai bakinta dan jin abinda zata farta .......sai Kuma tayi shiru .

Yayinda da komai nata yayi sanyi ,lokacin ne muwaddat ta tsilla ihu a hankali bunayya ya sake kafe ummi da  idanunwansa  ,yaga idanun ummi sun sake rufewa haka nan bata motsi bare numfashi ,cikin hanzari  bunayya ya tashi da sauri Yana duban ummi dake Kwance ,can Kuma ya koma Jikinta ya rungumeta yayinda Kansa ke kan kirjinta abi da muwaddat  tuni kuka ya gama cin karfinta .....

Cikin lokacin kankani bunayya ya burkice Yana shafa fuskar ummi  yana magana  "ummina duniyata hakika bani da tamkarki  ,bani da mai Sona kamarki  karki min haka ummi karki had'iye zuciya ki tafi ki barni ....ki taimaki tilon d'anki bashi da kowa daga Allah sai ke ,karki min haka ..

"Abi kace  ta tashi wallahi na hakura da cikin ...,a ciresa matukar ummina zata samu kwanciyar hankali ,wallahi a zim na hakura ,"ya sake kamkameta "ummi ..!ummi !!!wallahi na hakura ki tashi "Ina son ki ummina fiyye da abi ,da muwaddat duk duniya kace mutun ta farko da nake kauna .......

*Manage plz idona kaina, Kai koina ma ciwo yake min

Mmn sudais

      MUWADDAT

     

             ~NA~

 *AYSHA  A BAGUDO*

   ~DEDICATED TO~  

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_

     _(UMMIN KADUNA )_

warning!!!

 don't read this novel  if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you   read it, is for   your own risk ......

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 38

.....cikin wani irin  birgicewa da matsanancin tashin hankalin bunayya ya soma magana cikin sambatu  "abi tashi ...taimaka ....

Ka taimakawa rayuwata abi, mu kai ummi hospital ,abi bana son na rasa ummi nah ,wallahi Ina sonta bana son na rasata ,kuskure ne abinda nayi  bazan sake ba ,wallahi nayi nadama jikinsa na kyarma yake wannan sambatun "ummi ki tashi dan Allah karki min haka ...

"Karki tafi ki bar muhammed auwal dinki ...

"Idan kika tafi duniya zata masa zafi .....

"Hakika ummi baki cancacin haka daga garemu ba ..

  Abi dake  rike da hannun ummi gam cikin nasa jikinsa ya sake d'aukar wani   kyarma yana zubda hawaye masu ciwo da rad'ad'i ... .....

Hawayen da yasan sunfi kowani hawaye ciwo da rad'ad'i arayuwarsa

 ,domin kuwa zuwa lokacin ya rigada ya gama  sadaukarwa kansa  cewar ummi ta rigasu gidan gasky ,dan haka ahankali bakinsa ke furta kalmar" Inna lillahi wa Ina ilaihi raji'un ...

"Shikenan mukarama kin tafi kin barni .......

  Jin haka yasa hankalin bunayya da muwaddat sake kololuwar tashi, a matukar firgice bunayya ke bin abi da wani irin  kallo 'kwal'kwaluwasa na juyawa ....

  can ya zabura ya mike tsaye ya soma magana cikin d'aga murya "abi me kake cewa haka ?

"Kana nufin ummin tawa ce  ta rasu ko me ?

"Impostible  abi, ka..ka daina furta haka ga ummi nah " "ta Yaya ummi  nah zata mutu  yanzu?

"Ummi ba zata mutu  yanzu ba ,lokacin mutuwar ummi nah  bai yi ba ,kwata kwata ma babu mutuwa acikin idanuwanta,idan  ba zaka taimakamin mu kaita hospital bane kawai nasani ...."Ni..ni sai  na kaita  .........

ya k'arashe maganar yana k'ok'arin kwace ummi daga hannun abi ..

Yayinda muwaddat ta kasa motsi daga inda take   ,ta dawo tamkar mutun mutumin a durkushe tana duban gangar jikin ummi da bai motsi ,koda bata san  mutuwa ba tasan tabbasss  ummi ta tafi........

  Wani irin  fad'uwa gabanta yayi da mugun karfi, take wani Abu ya tsarka mata tun daga kirjinta  zuwa kasan mararta ....

Cike da tashin hankali bunayya yasoma k'ok'arin ciccibar gangar jikin ummi hawayensa na diga bisa fuskarta, abi  yayi karfin halin tallafota jikinsa , shima hawaye yake, hakika wannan abu da ciwo yake ,yasan mutuwa tana kan kowani bawa da yayi eimani da Allah ,amman sam  bai ta'ba expecting mukaramarsa zata  tafi ta barshi a daidai wannan lokacin ba, ban da kalmar Inna lillahi wa Ina ilaihi raji'un babu abinda yake furtawa har suka fito daga bangaren abi ,nan ne fa binta mai aiki ta fahimci akwai damuwar dake faruwa  acikin gidan  ganin abi da bunayya suna tara tara da ummi .

 Jikinta na rawa ta k'arasa garesu tana tambayarsu "lafiya alhaji meke faruwa da hjy ?

"Me ke damunta ?

Daga abi har bunayya babu Wanda yayi k'ok'arin bata amsa, illa k'ok'arin nufar hanyar fita da suke cikin tsananin  tashin hankali..

Ita kuwa muwaddat da kyar ta soma k'ok'arin Mikewa tsaye  bisa kafafunta ,ai ko gama Mikewa batayi ba, tayi kasa luuuuuu tare da sakin wata razananniyar k'ara ta fad'i kasa sumammiya wannan k'arar data yi ne yayi sanadiyar da binta ta nufi hanyar  parlour'n cikin matsanancin tashin hankalin tana zuwa ta risketa cikin matsanancin hali take jikinta na rawa tana sallalami ta janyo sauran ruwan da aka yiwa ummi amfani dashi tashiga tsiyaya mata tana Kiran sunanta  ....

Kai tsaye inda aka  faka motar data dawo dasu daga hospital d'azu  suka nufa daita , direba na hangosu ,ya zabura ya mike ya nufo inda suke cikin sauri  ,dan ko ba'a fad'a masa ba ,yasan  babu lafiya ,domin fuskokinsu  da gangar jikinsu kad'ai ya nuna masa haka ,cikin sauri ya bud'e musu gidan baya , bunayya yayi saurin shiga yana rungumo ummi jikinsa ,abi yasanya gangar Jikinta cikin motar ya rufe,kana ya nufi gidan gaba  , gabad'aya jikinsa a sanyaye yake ,cike yake da fargaba da tashin hankali ,ya sani ya rasa mukaramarsa har abada  , ya kasa kamanta halin dayake ciki , duk yadda ake jin mutuwa Yana jinta fiyye da haka a gangar jikinsa ,zai kaita hospital ne domin bunayya ya tabbatar da bata raye ko ta fawwalawa Allah komai ........

Shi kuwa bunayya jikinsa Banda rawa babu abinda yake ,ya sake birkicewa ,sai faman   zuba sambatu yake  rike da hannu ummi ,yana jin babu wata bakar rana arayuwarsa kmr wannan ranar ,tun da yake arayuwarsa  bai ta'ba jin makamancin bugun zuciya  da tashin hankali irin wannan ba ..

ya d'auka tashin hakalin rabuwa da muwaddat  wani bangare ne na  rayuwarshi ,a she rabuwa da umminsa yafi komai tashin hankali da ciwo ...

" hakika bai san yadda rayuwarsa zata kasance nan gaba ,"shin me yasa mutuwa zatayi masa haka ?

"Karya ne wallahi umminah bazata mutu ba ya fad'a da karfi Wanda yasa direba taka motar da karfi ,shi Kuma abi yashiga goge hawaye yana sake maimaita "Inna lillahi wa Ina ilaihi raji'un.....

Cike da tashin hankali Abi yaciro wanshi yasoma neman layin d'aya daga cikin likitocin asibitin Ummi ,yana shaida musu halin da Ummi ke ciki, ikon Allah ne kawai yakai su asibitin, domin wani irin shararan gudu da driver yake tsulawa akan titi.

 wani irin mahaukacin burki me k'ara direba ya taka dai dai lokacin daya shigo haraban asibiti ,da isowarsu asibiti,sun iske bakin k'ofan emergency  cike da manyan likitoci, take likitocin suka soma k'ok'arin k'arasawa inda motar take , yayinda wasu daga cikinsu ke   turo gadon d'aukar mara lafiya ,cikin gaggawa gaba d'aya likitocin hankalinsu a tashe yake sanadiyar ganin Ummi cikin mawuyacin hali.

 cike da tashin hankali aka ciccibi Ummi aka dorata akan gadon asibiti aka fara turata  Bunayya yafito a guje , kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin matukar tashin hankali, hannu Ummi ya rike cikin nasa yana binsu gudu gudu sauri sauri ,yana gunjin kuka yana Kiran  "Ummi nah karki min haka.....

" Ummi na na tuba bazan k'arawa ba.."

" Ummi nah ki tashi karki tafi kibarni  please Ummi, yayinda ruwan hawayensa ke d'iga a saman fatar hannun ummi , kai tsaye d'akin likita akayi da ita, nan take likitoci suka rufa a kanta ,suna bata taimakon gaggawa..

Likitocin sunyi iya kokarinsu amman abun tafi karfinsu ,shi kansa bunayya ya kasa aiwatar da komai, dan kuwa kusan shi yafi su rud'ewa ,nadama dana sani babu wanda bai yi ba ,jikin likitocin yayi sanyi, suka shiga kallon juna , gabad'aya an rasa wanda zai iya fahimtar da  wad'an bayin Allah rasuwar ummi, saboda ganin halin tashin hankali da suke ciki, ba d'an ba,ba  uban ba ,kowanensu ka kalli fuskarsa kasan yana cikin tsananin tashin hankali ...

Da kyar Dr najib ya juyo Yana dubansu cike da tausayawa "alhj sai dai muyi hakuri ,dan  zuciyar madam ta daina bugawa , ta rigamu gidan gas.......

maganarsa ce ta tsaya cak sakamakon wata uwar cakuma da bunayya yayi masa, yana sakin wata irin k'ara kana jikinsa na rawa  yace  "you are very stupid Dr najib........

" ummin tawa kake cewa haka?

 "idan ka sake  furta wannan kalmar  ga umminah sai na kasheka da hannuna ...

" mamarka ce zata mutu amma ba  umminah ba, ya k'arasa fad'ar haka yana matse wuyansa da rigar jikinsa da , likitocin sukayi caaaaa akasu suna k'ok'arin kwatar wuyar Dr najib a hannu bunayya ..

 Da kyar abi yasa ya sakar masa wuyar riga ta hanyar buga masa  tsawa,"kana hauka ne bunayya ?

 "hawaye na bin kuncisa yace "abi bakaji abinda yake cewa akan umminah ba?

" wai ummina ce ta rigamu gidan gasky ,ummi nah fa .....

Mamana.... mahaifiyata ce fa....... ..

ya juyo cikin rawar jiki  ya kalli likitocin dake tsaye akanta, yace "dukkaninku baku San aikin da kuke yi ba kawai dai kuna nan ne just for nothing ,ku bar min d'akin ni zan duba mahaifiyata  amman sam ummina bata mutu ba .....

Abi ya rigada yasan d'ansa baya cikin natsuwarsa da hankalinsa, mutuwar uwarsa  tazo masa a bazata da kuma shekarunsa na kuruciya .

Jiki a sanyaye ya kamo hannunsa "muje waje bunayya "

"a'a abi babu inda zani sai nasan halin da ummina take ciki , akwai jijiya d'aya dake jikin kowani d'an adam ,abarni abani damar na dubata da kaina matukar na dubata zan......zan.........

  Sai Kuma kuka yaci karfinsa ya kasa k'arasa maganarsa ya durkushe gaban abin  "shikenan nayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyata da kaina ? Abi ya kamo shi shima kukan yake son yi

"Kayi hakuri bunayya haka Allah yaso  muje dai waje  likitoci su samu  suyi aikinsu,"abi ummina ce fa kwamce bata motsi ?

"Ka furta kalmar Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un  da kyar dai abi ya janyo shi sukayo waje  sam idan kaga bunayya bazakace shine mai shegen girman kan nan da dagawa ba abi ya rungumeta shi ajikinsa yana furta kalmar Inna lillahi wa Inna  ilaihi raji'un ,wanda sai lokacin Allah ya raimakeshi ya rika yayita yi yana zubar da hawaye ...

 Awa uku   cur likitoci suka sake d'auka akan Ummi ,cikin hukuncin Allah sai gashi ta  farfad'o tare da sauke naunayen ajiyar zuciya  ,godiya suka shiga yiwa Allah , suna murna, sun yi farincikinki sosai domin ummi mutun ce ,akwai kirki da sanin yakamata, uwa uba sanin darajar dan adam , sam ita bata da wulakacin ,da talaka da mai kudi duk matsayi guda garesu a wajenta , rasa irinsu ba karamin hasara bane, amman idan Kiran  babban sarki  ne babu yadda za'a yi dole ta amsa Kira Kuma dole zuciya tayi hakuri .. . ...

Farkawa kawai ummi tayi ta ganta akan gadon asibiti, ta fahimci hkn ne sakamakon ganin mutun biyar   daga cikin likitocin dake aiki  akarkashinta ne tsaye bisa kanta suna Kara Mata ruwa tayi hanzarin  mikewa zaune tana raba idanu tare da tuna abinda ya haddasa Mata zuwa asibitin ,Dr saratu  dake bayanta  ta k'araso jikinta a matukar sanyaye sai dai kallo daya Tayi mata   abinda ya faru yashiga dawowa cikin 'kwalwaluwarta idanunta kamar gauta alamar tana cikin tashin hankali Kuma har lokacin idanunta Basu daina zubar hawaye ba, ta fasa ta razananniyar k'ara tare da fizge hannuta daga rikon da Dr Salim  yayi  Mata ta kamkame saratu  ajikinta tana kuka magana take son yi amman ganin likitocin yasa ta kasa furta komai sai kuka " to me ma zata ce ?

"Duk abinda zata fad'a a yanzu tamkar ta tonawa kanta asiri ne, dan hk ta cigaba da kukanta Dr saratu na shafa bayanta , Dr saratu ta kamkameta  tana rarrashinta  alamar tayi shiru ..

.

" ki kwantar da hankalinki mukarama inshallahu komai zai daidaita ganin kamar akwai wani sirri na musamman  dake bakin ummi yasa likitocin suka fice daya bayan d'aya suka bar d'akin Dr saratu ta kwantar daita "ki kwantar da hankali koma meye ki damunki ki fallawa Allah .....

Ki yawaita furta Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un ,zuciyarki na matukar bukata hutu a halin yanzu ummi ta runtse idanunta gam ..

Likitoci na  k'ok'arin fitowa  abi ya fad'a d'akin  shi kuwa bunayya da sauri  ya bi bayan d'aya daga cikin likitocin yana tambayarsa ,yanayin jikin umminsa ,suna tafiya doctor  na yi Masa bayani ,har suka shiga cikin office dinsa, ya dan juyo yana dafa  kafadar bunayya "ka kwantar da hankalinka inshallahu zata samu sauki, ka dinga had'awa da addua zamuyi mata allurar  yanzu  dan ta samu relief, bunayya yayi jugun hawaye na kwarara akan kuncinsa , da kyar yayi karfin halin  juyawa batare da ya cewa likitan  komai ba, ya bar office din  kai  tsaye d'akin d'a'a kwantar da ummi ya nufa ,yana shiga ta bud'e idanunta tana ganin shine, ta d'auke kanta zuwa wani bangare tare  da cewa "kace masa kar ya k'araso gareni banason ganinsa ,ya  bar d'akin nan bana son ganina acikin idanuna , karaf maganarta ta shiga cikin kunnuwanshi .

tun kafin  Wanda  aka bawa sakon ya fad'a masa , ya tsaya daga inda yake yana duban ummi da har lokacin kuka take ..

"Ummi ....

Ba..bana son jin komai daga bakinka  ta k'arasa maganar tana sauke numfashi da kyar "

Hannu abi ya d'aga masa al'amun ya tafi kawa ..

Ahankali ya juya jikinsa a matukar sanyaye  ya fice ya nufi harabar hospital  din yana jin wani irin kuna acikin zuciyarsa , kai tsaye bayan mota ya bud'e ya shiga ya zauna yana jin wani irin bakinciki ,batare da bata lokacin ba direba ya yiwa motar key ,suka bar hospital, zaune kawai yake a bayan motar amman shi kad'ai yasan abinda yake ji ,shi kad'ai zai iya misalta halin tashin hankali da yake ciki.

 da fari baiyi tunani zai  damu a dalilin cikin jikin muwaddat ba domin ganinsa haka shine sakamakon masu  hali irin na iyayensa ,sai yanzu ya fahimci   abun ba haka bane,  suna shigowa gidan ,ya nufi part din umm domin ganin halin da muwaddah take ciki ,can karshen gadon ummi  ya iske kwance tana jujjuya Kai had'e da rike kasan mararta ,ya k'arasa gareta da sauri  yana k'ok'arin kamota jikinsa  ta goce "karka ta 'bani ... kana ta yunkura ta mike tsaye ta soma tafiya.

Da kyar take takawa  ta fito tana layi hakan yasa ya biyo bayanta da sauri  yana Kiran sunanta  "muwaddat Ina zaki cikin wannan hali ?

Ta juya ahankali domin fad'a Masa bakar magana jiri ya kwasheta tayi kasa zata fad'i   cikin rud'ewa ya kamota jikinsa ya d'auke  cak dan ganin jini a bin kafafunta  , part dinsa yayi daita , da kyar ya samu jinin daya soma bin cinyoyinta ya tsaya amman ya Sha wuya sosai, yanzu wani irin son cikin ne ya dawo masa sabo fil  ....

Allurar bacci yayi mata domin tasamu natsuwar zuciya, amman ta burkice masa tana zuba masa ruwan bala'i  ..

Duk yadda yayi k'ok'arin ya shawo kanta ta  fahimceshi  amman abin yafi karfinsa, sai faman had'ashi  da Allah take ya rabata da ciki ,gabad'aya ya sake shiga rudu  ..

yana kallonta ta fice daga bangarensa shima ya biyo bayanta anan suka ci  karo da idanun baba mai gadi kallo daya yayi masu ya kawar da kansa yana Allah wadai da masu hali irin su   "da al'amun uwarsu bata da lafiya, amman hakan bai saka sun hakura da juna ba, wannan wace irin maseefa ce haka?

 yayi maganar a kasan ransa " ko yake zuwa yanzu ya daina ganin laifin su sakacin iyayensu ne ..

Binta  bunayya ya shiga yi   har ya karaso inda take bai tsaya wata wata ba ya d'auketa  ya sabata a kafad'arsa yayi  d'akinta daita ,ya kwantar  yana mata sannu , sannan  ya  koma cikin part dinsa, har kusan magariba yana d'akinsa kwance bai tashi ba tunani Kashi da Kashi ke dawainiyya dashi, jifa jifa ya kan Kiran abi ya tambayi  yanayin jikin ummi ,sannan haka ya dinga zariya tsakanin part dinsa zuwa na ummi domin duba lafiyar muwaddat..

Karfe biyun dare muwaddat ta farka daga baccin daya d'auke ta ,yana  zaune  akusa daita ya zuba mata ido, hannushi cikin nata jin motsin datayi ne yasa ya gane ta farka da sauri ya mike yana Kiran sunanta muwaddat, sai ma ta rufe idanunta wasu zafafa hawaye na zubo Mata babu irin maganar da bai mata ba amman ta shareshi band'aki ya shiga ya had'a mata ruwan mai d'an dumi zuwa yayi zai d'auketa duk da Jikinta babu kwari sai data fixge tana zabga masa uwar harara "bana son jin hannunka ajikina na tsaneka ka rabu dani ..

Kuka ne yaci karfinta, jin kukan  nan yake har cikin zuciyarsa ya kasa ce mata komai "

Can kusan minti goma yace "plz muwaddat kina bukatar kulawa da taimakona a daidai wannan lokacin ..

"Banason ko wani iri taimako ne daga gareka ka barni na mutu na huta da wannan bakinci ," komawa tayi tayi kwanciyarta, har kusan asuba yana fama daita tana jin  Fitarsa matsalaci ....

Koda ya dawo ma kusa daita ya tsaya ,ban da hawaye babu abinda idanuwanta ke zubarwa cikin sanyayyiyar muryarsa yace "Dan Allah muwaddat na rokeki ki bar kukan nan haka kada yayi miki illa  "

"Yaya kuke son nayi, gaki tashin hankali gurinki  ,ga matsalar ummi ,Ina bukatar kowane daga ciknku arayuwata ,bana son ba rasaki "kiyi hakuri muwaddat  ki d'auka kaddararmu ce tazo haka ...

Gefe ta juyar da kanta "ka rabani  cikin Nan ni banaso .......

Shiru yayi kawai had'e da kafeta da tsumammun idanunsa ,yau tazo Masa da abubuwa dayawa tashin hankali da rudani   , gabad'aya duniya ta cakud'e mashi waje d'aya ba ta bangarenta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login