Showing 126001 words to 129000 words out of 160337 words

Chapter 43 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12533

tana tsare shi da idanuwanta. "yakamata mu cire son zuciya acikin lamarin nan  , a zahirin gsky idan zamu bada auren muwaddat mu bawa Wanda ya girmemeta, ba wanda ta girma ba, tunda shi aure ba wasan yara bane ....

Ahankali yasoma taku had'e da Juya mata baya   ya  cikin kunar rai, yana fuskarta window d'akin..

Itama ummi cikin fushi ta bar d'akin ta nufi d'akinta ....

Ummi na barin d'akin ,abi ya d'auki wayarsa yasoma neman layin   uncle umar kaninsa  ,Kira d'aya biyu , uncle umar ya d'auka had'e da yi masa sallama"assalamu alaikum"

 daga can bangaren  abi naji ya d'auka ya amsa masa da "waalaikum Salam,   kana yace  "umar  sabuwar  matsala fa taso a gidana gabad'aya ban San yadda zanyi ba " nan  abi yashiga zayyanowa uncle umar   komai tun daga zuwan bunayya har zuwa yau din nan daya bar kasar .

Uncle umar yace  "karka damu Yaya wannan bawata matsala bace , komai zai zo da sauki inshallahu ,ka bari zan Kira ita ummi na fahimtar daita nasan zata fahimta ,"wace irin fahimtarwa zakayi mata ?

" Zaka mata bayani  komai ne, sbd lamarin fa yasoma fin karfina  ?

"to me ka gani a fad'a mata ne ?

"zan so haka gsky dan...

"No Yaya kusan fa ummi ta fika gsky ta wannan bangaren, karka biye bunayya plz ,da akwai kuruciya acikin lamarinsa,  idan ma hakan ce zata kasance abarshi zuwa gaba plz  ,tautauna suka cigaba da yi akan lamarin kafin daga baya

 sukayi , sallama .

Bunayya na sauka a kasar london  muwaddat ya soma kira amman number's dinra shiru basa shiga, dan haka ya kira na ummi,batare da 'Bata lokaci ba ,  ta d'auka suka gaishe muryarta a kausashe mai nuna al'amun  tana cikin damuwa  yace ,"umminah me ya sameki naji muryarki somehow like kina cikin damuwa ?

"Babu komai  ya ka Isa ?

Muryarsa a sanyaye ya sheida  mata ya sauka lafiya ta gayawa abi.. .. sukayi sallama, ranar dai      duka ahlin    gidan yini  sukayi cikin damuwa  ,most especial abi wanda ya fi ummi d'aukar zafi, dan ko lokacin dataje d'akinsa yaki sakar mata fuska, bare wani rawar jiki daya sabayi   akanta amman dayake tasan ta kan kayanta  haka ta dinga binsa da rarrashi da dadin baki da komai  har dai ta d'an shawo kansa suka daidaita  ..

********

tunda bunayya  ya bar kasar take cikin damuwa da tashin hankali gabad'aya ta fita haiyacinta, kallo d'aya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta da kwanciyar hankalinta, komai dai yinsa take dan kar ummi ta harbo jirginta ....

Duk wunin yau  babu inda ta leka  ko makaranta bataje ba saboda zazzabi daya rufeta, da taimakon ummi ta dawo normal , sai dai ummi haka nan take yiwa muwaddat din wani irin kallo na daban,zuciyarta nayi mata aiyane aiyane akanta  ,lokacin  datayi tunanin danganata da asibiti domin duba cikakken lafiyarta ,sukayi gari muwaddat din  tana murkususun ciwon mara ,d'aga karshe  sai ga  jini ya barke mata , wannan Abu ya kwantar da hankalinta ummi sosai ta sake bata magani da allura  , bayan kwana uku muwaddat ta d'an samu sauki dan haka  ta shirya zuwa makaranta ,ummi na ajiyeta  tashiga cikin makaranta ta isa deptment dinsu , ko minti  goma batayi ba sai gasu fatima da zainab kawayenta suka shigo , da sauri suka k'araso gurinta fatima tace "muwaddat lafiya kwana biyu baki zo makaranta ba?

muwaddat ta yatsina fuska  tace "kema kinsan duk abinda ya hanani zuwa makaranta  koda rana d'aya ne, abu ne mai mahimmancin gaske , ballantana har kwana uku.

  "ikon Allah to me ya faru wallahi hankalinmu yayi mugun tashi har fa muna tunanin zuwa gidanku?

muwaddat ta tsuke k'aramin bakinta tace "rashin lafiya ce amman yanxu naji sauki sosai "suka had'a baki gurin mata "Allah ya sauwake sannan suka shiga duba hand out dinsu..

bayan sati biyu al'ameen ya kirata bayan sun gaisa yayita mata hira, tun tana basar dashi har da tasoma amsa shi sama sama daga karshe yace mata  yana son cikin weekend din nan "zaizo ko kar yazo?

 tace masa "babu komai kana iya zuwa ,yaji dadi  sosai .

muwaddat tana gida kasancewar weekend ce, bata zuwa makaranta tana ta harkokin gabanta sai a lokacin ta fad'awa ummi  zuwan al'ameen,ummi tace allah ya kawoshi lafiya ,ai bakiji yadda nake son yaron nan ba, irin mijin da nake miki fatar samu kenan cikakken namiji mai zati da haiba  "wannan idan kika aureshi zai ririraki saboda yana da sanyi hali .

  jikin muwaddat yayi sanyi ,da jin abinda ummi ta fad'a yayinda  lokaci lokaci gabanta na faduwa musamman idan ta tuno bunayya , duk sanda za suyi waya dashi maganarsa bata wuce ta rike shi amana ta jirasa har sanda zai dawo .... .

bayan ta gama breakfast ta shiga bayi tayi wanka,  farar hoda kawai ta shafa saboda batason kamshin man shafawarta yanzu , tashiga cikin wata hadaddiyar koriyar doguwar riga gashinta  ta jima tana gyara shi  saboda tsawonsa da tsantsi ta fashe jikinta da turare mai sanyi kamshi tare da k'ok'arin dasa digon kaunar al'ameen aranta, tunda yana neman ya zame mata karfen kafa, ta fito parlour ta d'auki litaffin karatunta tana dubawa kafin ya k'araso , bata fi minti biyar da zama ba sai ga kiransa yashigo, ta dubi ummi kawai ,itama ummi kallonta tayi tace "halan ya karaso ne ?

"bansani ba"

" to ki d'auka kiji ko ya karaso ne?

ta d'auka had'e da mikewa ta bar gurin dan bazata iya amsa waya a gaban ummi ba,byn  minti biyu ta dawo tace "ashe  wai har ya karaso ,"to maza shirya ki tafi sai ki kai shi parlour'n baki "

ahankali tabi ta cikin main parlour'n ta shiga parlour'n baki ta bud'e ta waje tare da lekawa farfajiyar gidan , aiko dashi idanunta suka soma cin karo, suka had'a ido dashi yana jingine jikin motarsa ya hard'e kafafunsa, sanye cikin wata had'ad'diyar shadda dinki jamfa idanunsa manne da  glss Yana kallonta , kusan minti goma idanunsa   na kanta ya kasa d'aukesu " ta d'an lumshe idanunta , ahankali yasoma

ta kowa  ta matsa baya kadan domin bashi hanta ,,shi kuma karasa har cikin parlour'n, ta biyoshi abaya tana nuna masa gurin zama  ya zauna idanunsa akanta  ,ahankali   ta motsa labbanta tace "ya gajiyar hanya ?

yayi murmushi yace "ai babu wata gajiya, idan ma akwaita babu ita yanzu tunda na ganki ,

tayi murmushin nan nata mai tafiyar da ruhi,  tace "to dame zaka soma   abinci ko kayan   motsa?

" tukunan dai"

 "tsiyaya min lemu kawai ya isheni ,inta kallonki , kallonki kad'ai ya isheni, ta kai hanuta ta tsiyaya masa lemu a glas cup ta mika masa ya amsa yana had'awa  da yatsun  hannunta ,take jikinta ya kama rawa ganin haka yasa ya amshi cup din ya sha kad'an ,ya ajiye tare da kiran sunanta "muwaddat kina da matsayi mai girma agurina ban ta'ba cewa ina son wata mace arayuwata ba sai ke, dan Allah ki soni koda ba zai kai kwatankwacin wanda nake miki ba ,ina rokon wannan alfarma, babban misali shine yadda na taso tun daga ilori zuwa lagos dan na ganki , ina neman yarda daga gareki zaki aureni ?

mayafin doguwar rigarta tasa ta rufe idanunta dashi amman ta kasa amsa masa ..

dadi ya sake rufeshi domin hango nasarori acikin wannan had'uwar tasu ba kamar sauran lokutan baya ba  ,duk inda aka samu kunya to soyayya na nan, koda babu yawa al'ameen bai cika son ganin mace cikin shigarta irin wanda ke jikin muwaddat ba a yanzu, burgeshi da mace tayi shigar riga da siket  ko duk wasu kaya da zasu dame mace  jiki su fidda surarta a sarari ya kalla yadda yaga dama .

wannan kayan da suke jikin muwaddat bazasu bashi damar  ganin komai nata ba sai kyakkyawar fuskarta amman akanta yazamota shigar na matukar burgeshi komai nata yazamo da ban acikin mata kullun zaka ganta cikin abaya take amman hkn bai hana surarta bayyana .

ahankali ya taso daga mazauninsa  ya dawo daf daita ya zauna"  duk abinda yakamata na fad'a na rigada na fad'a ta bakinki kawai nake jira

tayi shiru na kusan minti biyar daga bisani ta numfasa tace "yaya al'ameen...

   ya tsura mata ido yana kallonta cike da fargaban abinda zatace, allah kadai yasan  halin da zuciyarsa ta shiga alokacin data ambaci sunansa , ta cigaba da magana cikin sanyi murya "zan fad'a maka wata magana guda daya yayi saurin katseta "dan allah idan kinsan bazata faranta min rai ba, ki bar maganar domin ni yanxu abinda zai sanyaya min rai nake bukata daga gareki idan kina sona kawai kice kina sona muwadda a wuce gurin .

tayi murmushi kawai saboda gani yadda gbdy ya rikice, yace "bakya sona ko muwaddat .. ?

"gaskiyar magana yaya al'ameen zance ace ba'a sonka ma bai taso ba ,baka d'aya daga cikin mazan da diya mace zata ki ko wace ce ita kuwa "to meyasa kike kunbiya kunbiya akaina ?

tace ba kunbiya kunbiya bane yaya al'ameen ina da dalilina mai karfi  ya saukar da kwayar idanunsa kasa yana jan numfashi da kyar "wani irin so yake mata mai zafi hk? Ya tambayi kansa.

cikin haka wayarta tashiga Kara ,ahankali ya kai ganinsa kanta daga inda yake yana iya hangon mai kiranta amman sunan kanina daya gani ne a rubuce yasa shi sauke naunauyen ajiyar zuciya "muwaddat ki bari muyi magana kune da kune umminki   da kanta ta kirani ta bani umarni zuwa, nasan tayi magana dake kafin naxo idan kinsa bakya sona ki fad'a min sai na hakura saboda banason takurawa rayuwatarki.

 "ita ba wai kalmar so bane bazata iya fad'a ba, shi din ne ba zata iya fad'awa ba, gara kawai ta amince da zata aureshi akan ya tutseyeta akan tana son shi ko bata sonshi,  bunayya nata faman  kiranta amman taki d'aukar wayar daga karshe ma  ta jawo wayar ta kasheta gabad'aya, ya sake numfasawa "to zaki aure ne na turo magabatana a saida mamaga mai karfi ..?

ya furta mata wannan kalmar yana tsareta da idanunsa, ahankali ta daga masa kai "yayi murmushi kawai "shikenan nagode yasan tabbas batason shi amman bazata iya furta masa hakan ba, koma dai yaya ne ,tunda ta amince bazai yi sanya agwiwa ba, ahankali yashiga janta da how, wata maganar ta bashi amsa wata tayi shiru da zai tafi ya tursasata sai tayi masa rakiya gurin motarsa tana tsaye ya bud'e motar ya fito da manya fararen lododi guda biyu duk shake da kayan ciye ciye, duk abinda yasan tana so sai daya siyo mata har ma da wanda bai sani ba, kudi ne dai bai bata ba, dan yasan koda ya bata bazata amsa ba..

har dare muwaddat ta kasa kunna wayarta saboda matsanacin tsoron tuhumar da  bunayya zai yi  ,yanzu idan ta kunna ya kirata mai za tace masa?

 shi kuwa har wannan lokacin nemanta yake a ways bai samu ba, gashi yana son ya kira ummi yaji ko lfy sbd zuciyarsa bata ta'ba shiga damuwa ba irin wannan lokacin, amman Yana fargaban kiran ummi , yana kwance bisa lafiyayen gadonsa rike da waya , ac dake manne da gadonsa yana aiki kmr me ,Amman sam damuwar da yake ciki yasa bai jin aikinta ajikinsa , ya kai hannu ya danna wani abu ajikin gadon domin k'ara karfin ac d'akin, babu abinda yake  kaunar ji a halin dayake ciki kmr muryar muwaddat , domin jin muryarta kad'ai ya shafe duk muryar wata diya mace a zuciyarsa ,abin mamaki wai yau shine saboda jin murya mace  ya shiga halin tashin hankali da matsanancin damuwa," a she haka yammata da suke rud'ewa  akansa da son jin muryarsa  suke ji idan bai d'auki wayarsu ba?

a wasu lokunta ma yana sane yake kin d'aukar wayar ko ya kashe ko yasasu a derveting,   , ya kasa  runtse idanunsa gashi dai   bacci yake ji amman ina bacci yace bai san haka ba, ranar kwana zaune yayi yana neman layinta .

bangaren muwaddat tunda tayi sallar asuba ta koma ta kwanta ,sai gurin karfe goma ummi tazo ta tasheta  taci abinci  , byn ta tashi tayi wanka taci abinci ,sai ta kunna wayarta ta koma ta kwanta  .

  wuraren karfi 12:00 taji wayar ta dameta da k'ara  cikin  magagin bacci ta dauko batare da ta duba ba tace "waye............?

  shiru yayi kirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin karfi yana jin da zai iya ,da kuka kawai zai sakar mata ko ya huta da radadin dayake ji"

jin shiru yasa ta cire wayar a kunneta ta duba, sunan data gani yasa ta  dan bud'e idanunta dake lumshe sannan ta maida wayar a kunneta tace "bunayya...... ......

da kyar ya numfasa yace" ke bacci ma kike  yi ko ?

"

Ni Kuma  kika barni kwanan zaune ..

"yanzu muwaddat kin kyauta min kenan?

"me yasa bakijin tausayina for god sake?

" tun jiya ina nemanki a waya baki d'auka ba at least daga baya sai ki nemi...

 "kayi hakuri na. na.. sai kuma tayi shiru "me kika yi dayafini zama important agurinki tun fa dana dawo na rasa gane kanki da gindinki "nace kayi hakuri "zanyi hakuri ne kawai idan kin fad'a min abinda yasa baki d'auki wayata ba "

yayi shiru yana sauraronta ta numfasa "ni dai kayi hakuri kawai "saboda kinsa kin cutar dani ko?

"amman babu komai ki cigaba saboda kinga ina sonki ne ,but kisani  shi soyayyar da nake miki bazai hanani gwada kunjina akanki ba, "yazamo karo na karshe da hakan zai faru.....

 yana gama fad'ar haka ya katse kiran ta mike zaune tana dafe goshinta ..

bayan wata  uku  da

 komawar bunayya London , ala'meen zaune agaban alhaji Muhammad mahaifin muwaddat ,Yana karanto Masa bayani akan Yana son auren  muwaddat a wannan lokaci .

Alhaji Muhammud ya numfasa  kana yace  "naji dadin wannan batun naka aminu ,sai dai wani hanzari ba gudu ba muwaddat dai ....

Sai yayi shiru ya gagara karasa maganarsa  yana mai  runtse idanunsa ,kusan minti goma suna zaune a haka  sannan ya cigaba da maganarsa a tsanake "abinda zan fad'a maka Aminu  ka bar zance muwaddat saboda ina da dogon buri akanta ban tashi aurar daita yanzu ba  ,amman ga faiza nan na baka  aurenta ,ko yanzu ka tashi aure ka sanar min ,nayi maka  alkwarin zan ajiye karatunta na aura maka ita...

Shiru ne ya ziyarci parlour'n ,yayinda gumi yashiga tsatsafowa ala'meen  ta koina ajikinsa , gabad'aya jinsa ne ya nemi d'aukewa ..

Ya yunkura  tamkr wani zararre  yasoma k'ok'arin barin parlour cikin tashin hankali dady ya bi bayansa da kallo ,tunda yake bai  furta abinda taji ya damesa ba sai yau..

  kai tsaye al'ameen bangarensa ya nufa kmr wani mahaukacin sabon kamu , yana shiga yashiga  Kira ummi byn ta d'auka ya zayyano mata yadda sukayi da dady ,ummi tace " Banda abunka ala'meen meye nayi  wannan zance da dady ?

"Yaya ne zai aurar da muwaddat ko mu ?

Kawai idan ka tashi ka turo magabatanka nan gurinmu ,na tashi aurar da diyata ....

da wannan  furucin yasamu karfin gwiwar ajikinsa dan haka batare da Bata lokaci ba  ya turo iyayensa zuwa ga abi domin nema masa auren muwaddat me zai yi da wata faiza shi zuciyarsa muwaddat tagani take so ba faiza ba , kafin iyayen ala'meen suzo ,ummi bak'ara min fama ta Sha da abi  ba kafin ya yarda yace" suzo"

Dady bashi da masaniya ala'meen yayi gaban kasa ya turo iyayensa ,bayan sun gaisa cikin fara'a da mutuntaka abi yayi shiru ya zubawa sarautar Allah ido  ,Banda murna  da farincikinki babu abinda iyayen ala'meen suke, amman Banda abi da yake jin kmr an d'aura Masa dutse ne bisa kirjinsa , duk safiyar ranar haka ya dinga ji fad'awar  gaba   ..

An kawo baki  abinci iri iri da abun Sha ,da kayan marmari iri daban daban daga ummi ,byn sun gama cin abinci suka soma magana akan abinda ya kawosu, Basu tafi ba sai da aka saida magana mai karfi  tsakani, inda iyayen ala'meen suka ce Nan da wata  goma cif suke son ayi biki ....

..

MUWADDAT PAGE 35

Shi dai abi duk abinda iyayen al'ameen suke tautaunawa akai na batun aure, kasa cewa komai yayi ,illa zuciyarsa dake wani irin harbawa da sauri , babu abinda yake tunani da fargaban   a halin da yake ciki facce halin da tilon d'ansa zai shiga ,yasani bunayya zai shiga matsanancin tashin hankali idan ya riski wannan labarin ,koma ya nemi zaucewa saboda shi kansa ya lura da irin mahaukaci kaunar da yake wa muwaddat

,itama Kuma muwaddat din  ya lura  tana mugu mugun sonshi  .

  gabad'aya acikin lamarin  sai yaga duk  kuskurensa ne ,da tun lokacin da  bunayya ya nuna masa yana bukatar ya aura masa muwaddat, yayi wani Abu akai da yanzu da muwaddat din  zai koma karatu a matsayin matarsa ...

  "to yanzu shi mai zai iya cewa Kuma ?

"Ya zabi son zuciyar matarsa ya hana d'ansa abinda yake kwakwar so, to idan wani Abu ya faru dashi a sadin haka wa gari ya waya ?

"Kanka ka cutar zuciyarsa ta bashi amsa da hakan ..

"Tabbass haka ne zan cuci kaina da d'ana, idan na rasashi wa zai zame min gurbinsa a wannan duniya?

Ya sake jefawa zuciyarsa wata tambayar yana duban iyayen al'ameen d'aya byn daya .

"Muwaddat ba diyar cikina bace amman ina jinta tmkr ni ne na kawota duniya ,sai duk da haka, ai gurbin ido ba Ido bane, idan na rasa d'ana, rayuwarta zata cigaba yi agidan mijinta , domin kiyayyar mace na wani d'an lokaci ne, baya tabbata muddin rai ,gara tun wuri nasan abun yi akan lamarin tun kafin abubuwa sugama rinca'be min  .

 sanyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske lokacin da yaji  iyayen al'ameen suna sake furta wata goma cif suke son a saka ranar auren ,shi kuwa inshallahu kafin lokacin zai tabbatarwa kansa   muwaddat ta zamo mallakin bunayya ne  da yarda Allah ,ba mallakin ala'meen ba , koda kuwa hakan zai zamo  sanadiyar 'batawarsa da ummi  zai gwamaci haka amman tabbas zai bawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login