Showing 51001 words to 54000 words out of 160337 words

Chapter 18 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12435

wannan jagwal din ta xubo min eiman tayi tsagal tace "kai yaya nice jagwaal din kmr wata gwanjo?

"itace mana ko kin ta'ba ganin na yarda kin zuba min abinci? dariya suka sake kwashewa da shi adaidai lokacin da ihsan ta ajiye masa kular abinsa..

duk hirarsu tana shiga cikin kwalkwaluwar muwaddat ahankali take satar kallonsa kyakkyawa ne shima, asalin fulanin kalgo amman bai kai muhammed auwal dinta a komai ba,auwal dinta kyakkwan ne ajin farko miskilani mai kyau da haiba dogo mai matsakaitan jiki mara son hayaniya da barkwanci shi sam wannan haukan bakwarcin bata gabansa dan wani lokacin idan abi nayi sharesu yake yayita cika yana batsewa sai dai ita tabiye musu ..

ahankali jikinta ya dinga bata ita ala'meen yake satar kallo dan hk ta mike tsam ta yiwa dady sallama ta nufi d'akinta tana shiga ta sauke numfashi mai had'e da soyayyar auwal sai yanzu take sake jin wani irin kewarsa amman yazama dole ta nisanta kanta dashi domin a yadda take ji zata iya mallaka masa komai nata wanda hkn shine babban abun kunyar dazata aikata arayuwarta.

"ya rabbi have marcy on me "ka za'ba min abinda yafi dacewa da rayuwata, Allah ka sani, ina son bawanka muhammed auwal amman ummi na neman hanani mallakarsa,

" ya Allah ka fahimtar daita.. tabbas ita kanta tasan abun kunya ne gareta ace ta auri kaninta auwal amman yaya zatayi da kaddarar soyayyarsa?

ahankali ta zauna bakin abun gado tayi shiru tana tunaninsa kafin daga baya ta janyo wayarta dake kashe tana jujjuyawa kmr ta kunna sai kuma taga gara kawai ya nema ko a waya ya rasa,

Saboda jin muryarsa kawai yana saukar mata da kasala mara misaltuwa, zamewa tayi ta kwanta tana runtse idanunta gabad'aya bacci take son yi amman ta kasa runtsawa sai juyi take tare da janyo pillow ta rungume ajikinta , jiya zuwa yau kawai tashiga wani yanayi akan rashinsa ta dinga jin ina ma bata baro garin lagos ba, da yanzu suna can tare makale da juna , a yanxu da suka yi nisa da juna ta fahimci rabuwa dashi ba k'aramin tashin hankali bane gareta saboda ya rigada yayi gangar jikinta da zuciyarta mugun sabo da salonsa, cigaba juyi tayi akan katifarta tana tunaninsa.

*******

Bangaren auwal kuwa tun jiya ya kasa zama ya yashiga bangaren ummi yafi so babu adadi, haka ya dinga zariya tamkar wani mahaukaci ,yana jin kmr ya saka ihu gabadaya tunaninsa tana cikin wani hali na rashin lafiya ne yasa bai ganta ba, a ranar sam bai samu ishashen bacci ba saboda kewarta.

da misalin karfe 9:00 na washegarin ranar ya fito ya nufi bangaren ummi ,duk ya bi ya damu kwarai da gaske har wata katuwar rama yayi daman ya lafiyar kura ?

ji ya dinga yi kmr ana fixgar ransa , tun shekarajiya rabon daya saka muwaddat dinsa acikin kwayar idanunshi ,ya iske su ummi a parlour hankalinsu kwance sai sheka dariya suke suna hirar barkeanci ita da abi .

jikinsa a sanyaye ya k'araso zuwa inda suke ya rusuna ya gaishesu cike da girmamawa, suka amsa masa cikin sakin fuska, tukunnan yasamu guri ya zauna yana baza idanuwa ko zai ga sanyi idaniyansa .

abi yayi d'an murmushi sannan ya tsura masa ido yana dubansa batare daya yace masa komai ba ,

shiru ne ya ziyarci parlour'n, byn kmr minti biyu ummi ta mike da kanta ta had'o masa abun kari ,chips da soyayyen kwai da ruwan tea mai kauri , ta janyo karamin table gabansa ta ajiye da kulawa sannan ta nufi d'akinta domin k'arasa shirinta na zuwa gurin aikin.

da kyar ya iya bud'e bakinsa yace "ummi . .

ta juyo ahankali tana had'e fuska tare da cewa

"kaci abinci first before anything, sannan kar naji kayi magana ka ci abinci kawai ,kai kawai ya iya d'aga mata batare da ya kalli inda abinci yake ba, saboda sam baya jin cikinsa zai iya amsar komai matukar bai san halin da muwaddat take ba.

zuciyarsa muwaddat kawai take son gani, ita kawai yake kwadayin gani yasan da zarar ya ganta zai koshi.

gabad'aya ya tattara hankalinsa zuwa kofar d'akinta yaga ko zai ga wulgawarta.

, abi ya d'ago "ya dubesa ahankali yace"ya'akayi ne bunayya ko akwai damuwa ne ?

ya juyo da kyar yace"abi....sai kuma yayi shiru "to me ma zai ce masa ..?

ganin yaki yin magana yasa abi ya mike yana kiran direbansa a waya, saboda yasan duk abinda zai fito daga bakinsa bazai wuce akan muwaddat ba .....

abi na barin parlour'n shima ya mike jikinsa na rawa ,abubuwa sun yi masa yawa ,zuwa yanzu zuciyarsa tagama samun natsuwar muwaddat tana cikin koshin lafiya kodan ganin ummi da abi cikin kwanciyar hankali da annashuwa, domin kuwa da wani abu na damunta fuskarsu kad'ai ya isa ya sheida masa ,ya koma d'akinsa ya kwanta lamo yana tunanin inda ta shige acikin gidan.

wasa wasa sai da muwaddat ta share wata guda cur a ilori ,sannan auwal yasan inda take,abakin akram kuma daman kwalkwaluwarsa ce ta bashi shawarar ya kira can yaji tunda ya tabbatarwa kansa muwaddat bata gidan domin duk inda zata boye aciki gidan dole zai kwakulota, yana gama wayar ya nufi gurin ummi tamkar wani zarare , ya isketa zaune shigowarta kenan daga asibiti tana hutawa .

ya k'arasa ya durkusa a gabanta kmr zai yi kuka "ummi nah me yasa kika aikata min haka?

" ummi zaki kasheni da kanki wallahi, at least yau tsawon wata guda kenan kina kallona ina haukan neman muwaddat ashe kinsa inda take ummi......?

"to me zan ce maka bunayya?

"me kake son nayi idan ba haka ba ?

gani nayi kana neman hargitsa min kwakwaluwa da shirina akanta "me kake tunani mutane zasu ce idan na baka aure muwaddat?

" muwaddat, auntynka ce fa ..

"yanzu misali idan an aura maka ita me zaka iya mata dan Allah dan annabi in banda tsaurin ido da rigima irin naka..?

wani far yayi da idanu zuciyar na dokawa numfashinsa da yayi kokarin d'aukewa yayi saurin dawowa dashi gangar jikinsa sannan yace "haba ummi nah ,bai kamata kece min haka ba ,ki duba lamarin da kyau, tunda nace ina sonta, ai nasan yadda zanyi daita..

"kai rufe min baki ban son shirme banza, ka daina ganin ka had'a degree dinka, ka samun aiki a hannuka yasa zakayi tunani ka isa aure .

"no no aure not yet for you now sai dai gaba ,idan kuma auren kake so kaje gaba ka nemo mata...

ya marairace muryarsa sosai tmkr mai shirin zubda hawaye sannan yace "wai ummi me yasa kike ganin kmr nayiwa muwaddat 'kankanta, Allah ummi ki daina min kallon yaro, saboda ni ba yaro bane,duk lokacin da naji kince min yaro bakinciki nake ji kmr na kashe kaina ..

wata bazawarar dariya ummi tayi "to kai din meye bunayya ?

"yaushe na haifeka ka girma?

" think har pent muwaddat ta saka maka acikin gidan nan, ta baka abinci abaki..

"ko ma dai menene ummi ai ba itace ta kawoni duniya ba.. ..

ummi tayi saurin zaro ido waje driya na neman kufce mata amman tayi sauri meidawa ta had'e rai sosai dan kar ya kawo mata wargi "ummi wallahi zan iya da ita ina tabbatar miki nan da wani lokaci zan ...

taja tsaki tace "karka nemi raina min hankali bunayya ..

,ko tursasani dan bazan iya had'a wannan auren ba, idan kai kanka kana da hankali bazaka sawa ranka yin aure a halin yanzu ba, guda nawa kake bunayya?

duk yadda M.A yaso ya fahimtar da ummi cewar shi fa aure yake so, taki sai kawai ya tashi cikin hanzari ya koma d'akinsa ya hau shirya kayansa gudu gudu yana duba agogon hannushi cikin gaugawa yagama shirinsa tsab ya fito ya bud'e bayan motarsa ya saka jakar kayansa ya zagaya yashiga mazaunin direba ya fige motar aguje ya bar gidan..

wani irin gudu yake sharara akan titi duk wanda yaga irin gudun dayake sai yabi motar da kallo tare da tausayawa matukin mota ,aguje ya dinga wuce motaci akan titi yana cizan lip's dinsa na kasa burinsa bai wuce ya gansa agabanta ba.

koda ya isa gidan a bangaren yaya akram yayi masauki, yana zauna akan daya daga cikin kujerun dake parlour'n tare da runtse tsumammun idanunsa , d'aya byn daya yaran gida suka dinga shigowa suna gaisheshi , ya bude idanunsa da kyar yana amsa musu cikin rashin sakin fuska , cikin minti biyar kacal aka cika masa gabansa da kayan motsa baki , amman babu abinda ya fara ci ,illa ruwan lemu daya tsiyaya a glass cup yashiga kurba ahankali ahankali , shima ya sha ne kawai saboda gajiyar hanya daya dibo.

ahankali tashigo parlour'n bakinta d'auke da sallama, taja ta tsaya daga gefe can ta jingina bayanta da bango ta rungume hannuwanta bisa kirjinta tare da tsura masa fararen idanunta tana kallonsa cike da matsanancin soyayyarsa take gabanta yashiga fad'uwa sbd fargaba dan ganin ko kallon inda take tsaye bai ba ,illa kur'ban ruwan lemun daya cigaba dayi, ahankali ta bud'e bakinta "bunayya sannu da zuwa ya... ..

da sauri ya dakata daita ta hanyar daga mata "bana bukatar jin maganarki ko wani abu ..

cikin firgici da tashin hankali tashiga d'aga kafafunta zuwa inda yake "me yasa bunayya?

" dan Allah kayi hakuri wallahi ba laifina bane i don't mean to hurt you a matukar tsawace yace "nace karki min magana kada ki kulani ,kada ki karaso gareni kawai kija bakinki kiyi min shiru. ..

jikinta na rawa ta k'araso ta durkushe agabansa,har bata san sanda ta d'aura hannuwanta duka bisa cinyoyinsa tana kallon cikin kwayar idanunsa da suka rikid'e suka canza kala ,ya kawar da fuskarta gefe guda yana kallon wani bangare alamun baya son kallon fuskarta.

"dan allah muhammed auwal kayi hakuri ta kai hanuta ta juyo da fuskarsa gareta suna fuskantar juna a take zuciyoyinsu suka bugawa ,take suka soma jin wani sauyi na daban agabadaya ilahirin jikinsu wanda ke gauraye da tsantsar soyayya.

idanunta suka cicciko da ruwan hawaye muryarta a sarke tace "dan..dan Allah auwal kayi hakuri karkayi fushi dani ,ya buge mata hannuta batare dayace mata komai ba, ta sake kai hanuta jikinsa "dan Allah ka saurareni mana "

"ki kyaleni ni mana nima daina sonki tun da burinki kenan na daina sonki , dan allah ki rabu dani ,ki manta dani, ki manta da maganar na ta'ba sonki arayuwa ki.. ki mantani ya k'arasa fad'ar haka yana fidda huci mai zafi.

..dan allah kayi hakuri mana akwai maganar da idan na fad'a maka zaka saurareni bazan iya jure ciwon rabuwa da kai ba, ta karasa mgnr tana kwakwameshi ajikita tana kuka... ya fixge rigarsa data rike yana furzar da iske had'e da kawar da fuskarsa.

Tarasa yadda zatayi dashi zance zuci tasoma jikinta na rawa ......"ina kaunarka Auwal Dan Allah karka juya min baya akowani hali zan kasance tare da kai, ta maimaita hkn acikin zuciyarta yafi sau Goma ,tana mai kai hannu ta shafa kasumbar dake kwance a fuskarsa, kafin daga bisani ta riko fuskarsa sosai ta sanya kwayar idanunta dake tsiyaya ruwan hawaye acikin nasa .....aran tace ban san hka soyayyarka tayi tasiri acikin zuciyata ba, sai lokacin danayi nisa da kai ..

"a da 'kan'kantarka nake yiwa amman a yanxu nasan kai ne duniyata ruhina yana tare da kai , "nayi alkwarin bazan ta'ba rabuwa da kai ba, bazan sake yin nisa da ruhinka ba ta karasa mgnr duk acikin zuciyarta tana rungumeshi gam ajikinta tana zubar da hawayen rashin bayyana masa abinda ke zuciyarta.....

kuka take sosai tana rungume dashi ajikinta tmkr za'a kwace mata shi "kayi hakuri Dan girman Allah ka daina fushi dani bazan iya jurar fushika ba.. hawayen dake boye acikin idanunsa yayi saurin maidawa domin idan yayi kuskuren bari suka sauka akan kuncinsa tabbas ya tabbata yaron datake kiransa dashi shi kuma abinda yafi tsana kenan arayuwarsa....

mmn sudais ce

MUWADDAT PAGE 15

page 15

Gabad'aya yanayinsa yayi mugu mugun tayar mata da hankali ,ta rasa yadda zata yi ta shawo kansa ya sauko daga dokin fushin da yayi da ita ,tsawon minti goma suna nan a haka suna  kallon junansu cike da matsanancin shaukin juna, batare da wani acikinsu yayi yunkurin cewa d'an'uwansa wani abu illa numfashi da suke sauke da karfin gaske ... .

ganin yayi shiru  har lokacin yaki yi mata mgn,  yasa ta bud'e bakinta da kyar tace "kayi hakuri  mana bunayya  ,kayi min magana ,zuciyata ta kasa jurar wannan fushin naka , da zan  iya ,da yanzu na barka a nan na  kama gabana....

Sanin halin miskilancinta da yayi,   yasan ba k'aramin aikinta bane ta barshi agurin ta kama gabanta, dan haka  muryarsa  na rawa yace "shi..shikenan nan.....na hakura amman karki sake barina, ta janye jikinta ta kamo fuskarsa da hannuwanta duka ta had'e fuskokinsu " bazan sake ba, saboda bazan iya rayuwa babu kanina ba ......

cike da sanyi jiki ya kamo laulausar tafin hannuta cikin nasa yana massaging ahankali ahankali yana cigaba da kallon kwayar idanunta ,tare da jin wani irin sauyi na daban a gabadaya ilahirin sansar jikinsa ,ta koina ajikinsa jike yake sharkaf da ruwan gumi tun daga samansa har kasa tsiyaya yake tsabar tashin hankalin daya tsinci kanshi , ahankali  yasoma jin wani irin sanyi me tattatre da tausayinta na ratsa jikinsa kana muryarsa ta fito ahankali tmkr mai koyon mgn yace 

"nima ina bukatarki bazan iya rayuwa babu ke ba ,shin kin  shirya rayuwa dani? 

Ya sake had'e fuskokinsu guri daya yana shakar numfashinta dake gauraye da nasa "lip's dinsa ya d'aura saman nata "nayi kewarki sosai baby .. .

"nima nayi kewarka sosai  cikin kuka ta fad'a tana Shafa fuskarsa, nayi matukar kewarka  auwal ta sake maimaita tana lumshe ido "kin yi alkwarin bazaki sake yin nisa ki barni ba.. ?

"eh na yarda "

dariya mai had'e da kuka tashiga yi masa  tana shafa fuskarsa cike da matsanancin shaukinsa,

" a gaskiyar mgn muwaddah kinyi nasara sarke zuciyata da soyayyarki , dan kuwa na kusan haukacewa akanki, kwata kwata bana bukatar na rasaki  ,wallahi idan na rasaki akwai damuwa, amman na rasa me yasa ummi take neman dakushe mana rayuwa "me yasa baby?

"plz karki bari arabamu  yasoma shashshafa sansar jikinta cikin shaukin kauna yana 'ko'karin ciro brest dinta daga cikin rigarta, tayi saurin rike hannunsa tana sauke naunauyen ajiyar zuciya "dan Allah baby karki haramta min nonuwan nan, karki haramta min jikinki, Allah ina sonsu babu abinda ke tayar min da hankali kamar naji duminsu .... ya cigaba da shafa saman kirjinta yana lumshe ido .

gabad'aya ya kashe mata jiki da salon wasaninsa kusan minti biyu suka d'auka a haka sannan ta kira sunansa cikin sanyayiyar muryarta me kashe  jiki "auwal karka manta inda muke fa. 

"shikenan ni bani da 'yancin ta'ba jikinki  akoina sai kin nemi 'bata min rai ?

"no ba haka nake nufi ba amman.. lokaci daya hawaye ya sake gangarowa bisa kuncinta wanda yasa ta katse abinda take son fad'a ,

ya kai hannunsa ya d'ago fuskarta yana  sanya kwayar idanunsa cikin nata  , yana kallo yadda lokaci daya idanuwanta suka k

rikid'e suka canza kala tsabar kuka, ahankali yace "shikenan  na bari ki bar kukan haka, dan bana son ganki kina zubar da hawaye ya fad'i hk tare da kamota ya zaunar daita agefenshi.

"muwaddah na yarda na amincewa zuciyata bazan iya rayuwa babu ke ba ina sonki fiyye da tunaninki ,amman  zan so na sake ji daga bakinki ,shin  kina sona  zaki aureni ...?

shiru tayi taki cewa dashi komai "kin amince kina son muhammed auwal zaki auresa? 

ahankali ta girgiza masa kai ala'mun a'a sannan tace "nifa bana maka soyayya irinta aure sai irinta 'yan'uwnka...

yayi murmushi kawai yana girgiza kai,   ya cigaba da mgn "ki daina jin tsoro ko fargaban nuna kina sona, ki zauna kiyi tunani sosai akan lamarinmu dake, daga ni har ke muna matsanancin son juna zance son  'yan'uwantaka kike min  ma duk bai taso ba, saboda bazan ta'ba yarda da bakya sona ba...... 

"ni dai nasan ina sonki da dukkanin rayuwata, soyayya kuma irinta aure ba wai 'yan'uwantaka ba...

" na yarda kana  matsanacin sona amman ni... ..

"amman ke fa? 

"karki yiwa kanki karya mana ,daga baya kizo ki ganni da wata ki nemi tayarwa da kanki hankali ya k'arasa mgnr yana murmushi , itama din  murmushi tayi tace "ka gwada mana wallahi babu abinda zanyi saboda Kai kanina ne ,ta yaya zanyi kishin kanina?

ta k'arasa mgnr tana jan dogon hancinsa nan suka shiga hira, bangaren M. A tsantsar soyayyar muwaddat ne ke bin dukkanin ilahirin jikinsa, yayinda ita kuma ta dinga jin wani irin abu na yawo a gabad'aya ilahirin jikinta mai kama da shocking wanda ya haddasawa kirjinta tsananta bugawa, tsawon minti talatin suna zaune suna hira suna kallon junansu jikinsu na tsuma saboda feeling's din dake kaiwa zuciyoyinsu farmaki, muryarta a matukar sanyaye tace "yakamata kaci abinci fa "karki damu ganinki kad'ai ya kosar dani, dan ma  kinki bani dama na ji dumin jikinki .....

tayi murmushi batare da tace masa komai ba 

  can kmr minti goma  sai ga yaya akram ya shigo d'akin da sallama nan ya iskesu zaune rike da hannun juna  ,tana ganin yaya akram tayi saurin zare yatsun hannunta dake cikin nasa   tare da yi masa sannu da zuwa ta mike tsaye,  ta baro bangaren zuciyarta na wani irin harbawa ta koma cikin gida shi kuwa M. A keyarsa ya d'an tsotsa ala'mun jin kunya "yaushe a garin auwal? Yaya akram ya fad'a yana ajiye jakar hannunsa. 

M.A  ya shafa sumar kansa  kana yace" ban fi awa daya da zuwa ba ,yaya jikin naka? 

"gani nan dai auwal sai godiyar  ubangiji .

M.A yace "yakamata dai kaje kaga kwararen likita . 

yaya akram yayi dariya yace "wani kwararen likita zan nema byn gashi agabana ai kai ne kwararen likitan da zai dubani  ya k'arasa mgnr yana  zama kusa dashi Yana murmushi .

murmushi M. A ya sake yi kana yace "to yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login