Showing 153001 words to 156000 words out of 160337 words

Chapter 52 - MUWADDAT COMPLETE

13 Jul 2025

12402

kwanciya har lokacin ,zuciyarsa taki sabawa da mutuwa  da rashin akram,  tausayin rayuwar yaransa yake ji, ko yaya Polina zataji idan labarin  mutuwarsa ta risketa?

"shi ba ma wannan ba, yaya zaiyi ya sanarwa iyayensu wannan labarin ?

"sannan yaya zai gano inda polina take ?

Yasan dai ko yaganta da wuya ta basu yaran ,Amman at least dai yasan inda jini yaya akram suke rayuwa ...

D'akin  yashiga zagaye daga baya ya soma binciken kayan yaya akram ko zai ci karo da wani abu daya danganci Addresse din polina, Amman bai ga komai ba ahankali idanunsa ya sauka akan  wayarsa dake yashe  can gefe ya k'arasa ya d'auka yana dudubawa anan yaci karo da numbobinta har guda biyu ,yasoma kira number Kira daya ta d'auka kmr zatayi kuka cikin harshen tsadadden turancinta tace "hello my everything  I have been calling your phone for five  days,  I hope  you are doing fine?

runtse idanunsa bunayya yayi sosai, cike da tausayawa sannan yace mata "yana lafiya yayi wata yar karamar tafiya ne ,Amman shi dan'uwansa ne zaizo Spain  kwanan  nan ,a ina take ya bada sako akawo mata ita da yaranta ?

"tayi shiru da kmr bazata sake yin magana ba ,sai dai taga bai dace ba, tunda gashi da number'sa ya kirata  idan bai da halaka dashi   akram ba zai bar masa wayarsa ba ,muryarta a sanyaye tace "ya sunanta acikin 'yan'nuwansa ?

Kundinbala yayi yace "Muhammed Auwal aiko ta sauke naunayen ajiyar zuciya tace "bunyaya ...?

Da acikin faricikin yake tabbas da sai ya dara saboda yadda ta kira sunansa Amman sai ya ciza lips dinsa  kawai yace "right that's my second name ,Dan haka tayi murmushin ta bashi full details dinta, ajiyar zuciya ya sauke sannan yashiga tambayarta yaranta da ainihin sunan da mahaifinsu yake kiransu dashi, nan ta sake sakankace tare da amincewa da lallai d'anuwan akram ne kuma na jini ..

*Sauran page 2 labarin muwa  ya kare , muwaddat zai yi ending a 46 ,so kuyi min hakuri da page 44 , banason ganin complete muwaddat a waje yana yawo  ,dan girman Allah kumin hakuri saboda nasan wasu daga cikinku  zasuji babu Dadi aransu,Nima  ba haka naso ba,sai dai  Ina da dalilina nayin haka*

Mmn sudais ce

page 45

.Alhamdullahi mu dat na samun kulawa matuka

daga bangaren ummi, duk abinda take so shi take mata

,sannan duk abinda ya dace mai ciki taci ko amfani dashi

shi ummi take bata

Sai da aka samu tsawon wata guda cur da rasuwar yaya

akram ,sannan bunayya ya bayyanawa su dady labarin

halin da Yaya akram ya tsinci kansa a dalilin rashin auren

days so yi suka hana , har ma da labarin yaransa dake

kasar Spain ,wannan dalilin ne yasa ya kamu da ciwon

zuciya , bai tsaya iya nan da ba har sai daya labarta

musu irin nadama da yayi da tuban da yayi kafin

mutuwar ta riskeshi

"dan haka shi ya yanke shawarar cikin satin zai Shiga

kasar ,koda kuwa baza'a bashi yaran ba, amman at

least dai yasan wani abu daya danganci akram ,mu

musan inda ahlinsa suke

Hankalin dady kusan yafi na kowa tashi a lokacin tunda

bunayya ya soma mgn yake kallonsa tamkar hoto ,ya

kasa kwakwarar motsi ,gabadaya so yake yaji

zantuttukan bunayya sun zamo tamkar a mafarki ne

suke Shiga cikin kunnuwansa, Amman yadda bunayya

din ya Shiga fito da hotuna akram da yaransa da polina

yana nuna musu ,daya daga cikin hotunan a bircth

sukayi , wasu a wuraren shakatawa wasu a gida

suna dry

cikin farinciki ,varan masu tsananin kama dashi sosai,

basu d'auko komai na polina ba sai Karin hasken fata.

da kyar dady ya samu ya dinga furta kalmar "inna lillahi

wa inna ilaihi rajiun yayinda tuni parlour'n ya kaure da

kuka ,Kowa kuka yake mumy cikin kuka tace "duk son

zuciyarka ne ya jawo haka....

Kasa na rasa d'ana a dalilin banzar ra'ayinka ,yaro ya

nuna maka aure yake so amman ka kekashe kasa kace

Sam sai ya gama karatu , ai ga irinta nan kasa an haifa

min jikoki ta hanyar zina .

kuma a wata kasa wallahi

Muhamud ka cutar dani ,ka cuceni cutar da har na mutu

bazan manta ba

'ummi ta Mike daga inda take ta isa inda mumy take

zaune ta rungume akin kuka tace "kiyi hakuri aunty

zuwaira , haka Allah ya kaddaro kowa da irin kaddara da

Allah yake masa

,ki d'auka wannan jarabawarmu ce ,sai fatan Allah ya

bamu ikon cinyeta ,kiyi hakuri gabadayanmu muyi

kuskuren, ",dole nayi kuka mukarama ,saboda nima na

biyewa son zuciyarsa ,na mance ni macece ,yanzu ina

zan samu kmr akram?

"yaushe zan haifi d'a kmr akram ?

"a koda yaushe yana k'ok'arin kyautata min da yi min

biyayya ,Allah dai ya gafarta masa yasa ya huta ,yasa

karshen walahar kenan ,Allah ka hadasshi da malaikun

rahma ,ya Allah kamar yadda kace aljanna yaya maza

suna karkashin tafin kafafun iyayensu to ni Allah

kagani na d'agawa akram tawa kafar , kasa aljannah ce

makomarsa ta k'arasa fad'in hk tana wani irin kuka

"a lokacin da maganganun mumy ke Shiga kunnuwan

dady ,ba iya kunnensa kad'ai maganar ta tsaya ba, har

zuciyarsa yake jin komai, kusan zaucewa yayi, ya dinga

sambatu "shikenan ni na kashe d'ana da kaina, tun

da'akayi mutuwar bai zubda hawaye ba ,sai na zuci

,Amman yanzu hawaye ne kwance a saman kuncinsa

gabad'aya, ya dawo abun tausayi ,wuni ranar babu

Wanda ya sakawa cikinsa komai kowa ka kalli fuskarsa

(3

ta kud'e saboda kuka

Allah sarki mumy kwana tayi ranar da zazzafan zazzabi

ajikinta ,Sam ta kasa runtsawa jin mutuwar akram take

sabuwa agareta

,dana sani kuwa tayi shi sau babu adadi ,tayi nadamar

biyewa son zuciyar mijinta ,shine duk ya janyo komai

yayi tsanani a gareta, tabbas akram yaro ne mai ladabi

da biyayya, ba zai ta'ba bijire umarninta bare na

mahaifinsa ,"danasani na amince masa a lokacin dayazo

da batun yana son yayi aure .

da yanzu ya'yansa zasu zame min sanyi idaniya a gareni

, kallonsu kad'ai zai rage min rad'adin rashinsa, bazan

sakawa ranna soyayyar ya'yansa na wata uwa duniya ba

,domin kuwa da wuya uwarsu ta bari ta gansu shikenan

bazataga jikokinta ba ?

Tayiwa kanta tamvayar,

wasu hawaye masu zafi suka zubo mata wannan

zazzabi bai hanata tashi cikin dare tayi alwala ta Shiga

sallah tana nemawa d'anta rahma gurin Allah

Akwana daya dady yayi da wannan labari ,ya dawo abun

tausayi ,Dan idan ka kalleshi sai ka tausaya masa ,Dan

kuwa yayi kuka tamkar k'aramin yaro, har wata doguwar

Rama yayi gabad'aya ya fita haiyacinsa , surutui ya koma

yi ,kallo day'a zaka masa kasan baya cikin natsuwa da

kwanciyar hankali, daman kuma dauriyar mutuwar kawai

yake Amman a yanzu komai ya dawo masa sabo, har sai

da mumy tazo tafi shi dauriya da tawakalli har ma daga

karshe ta dawo bashi baki ,ummi ma tayi iya kokarinta

dan gani ya samu natsuwa tare da bashi tabbacin za'a

zo da yaran ,dady yayi wa kansa alkwarin ba zai sake

takura ya'yansa akan karatun boko ba haka zalika

yaransa mata duk aure zaYi musu ya hutawa

rayuwarsa....

Su ummi basu dawo Lagos ba sai bayan da akram yayi

wata biyu ,lokacin cikin muwaddat ya Shiga wata na

takwas ,tun da suka dawo muwaddat bata sanya

bunayya a idanunta ba, yana can yana fama cikucukun

Shiga kasar Spain , sai data samu tsayin wata daya

sannan ya zo mata da labarin tafiyarsa ,zuwa kasar span

, shi da yaya alameen acikin satin tabbas taji dadin

kwarai da gaske ,sannan taji rashin jin dadin kartazo ta

haihuwa baya nan, sai dai ta nuna bata damu ba sosai ,

saboda gudun kar ya gane ya rusa tafiyar ,yace har sai

byn ta haihu ,ita kuma abinda ba zata so kenan yaya

ba,yaya akram ya wuce komai agurinta ,yafi komai a

rayuwarta ,sanin inda yaransa har uku suke shine

farincikinta

Yau tsawon kwana Goma da tafiyar bunayya amman ko

sau daya basuyi waya dashi ba ,tashiga damuwa sosai

har damuwarta ta fito fili, kullun ummi na kwantar mata

da hankali Wanda hakan ya rage mata tsananin tunanin

rashinsa kusa daita ,hakan ba karamin dadi yakewa

muwaddat ba gani yadda ummi ta sake maidaita yar

gata ,bata aikin komai kayan data Cire sai dai a wanke

Wanda zata sakawa jikinta ma sai dai ta gansu ,komai

ummi ce ,shi yasa kullun take jin ummi ta zarce matsayin

uwa gareta, ta zame mata komai na rayuwarta ,yanzu da

ta gudu tabi uwa duniya a wannan ranar yaya rayuwar

zatayi ?

'Allah nagode maka da ka arzurta ni da samun uwa kmr

ummi ,allah ka ja da ranta, ka kara Mata Nissan kwana

,samun irin su da wuya a wannan lokacin...

Tana kwance a d'akin ummi saboda gyaran d'akin da

zaayi ,karar wayar dake gefen gadon ummi ce ta tasheta

daga baccin daya soma d'aukarta mai dadi ,cikin tsaki da

yatsina fuska ta d'auki wayar ta manna a kunneta tare da

fad'a "Assalamu alaikum "daga can bangaren aka amsa

mata da waalaikas salam ,tana jin sautin sanyayyiyar

muryar tasan sanyi idaniyanta, burin zuciyarta tsayayen

namiji abun tikaho, nmjin dake shirin tafiyar da rayuwarta

da komai nata, Muhammed Auwal kenan cikin



sanyayyiyar

muryarsa yace "na tasheki a bacci ko ?

Bari na kashe kar NASA ki Haifa min yaro mai manne

n

ido tunda NASA shima baby bacci zai yi, ya fad'a cikin

farinciki "Kamar kasani har ma da yankakken kunne tayi

maganar cikin muryar shagwa'ba "sorry lov

e

banyi zaton

kina bacci ba, ganin rana ce a fuwa zuciyata, ya baby nah

ki fad'a baby kar yayi fushi yanzu ummansa zata koma

bacci yayi hakuri inzo inganshi da kunnuwansa da

idanuwansa ,suka sa dariya ,"kai bunayya bakagajiya da

soyayya wallahi ,ya bakunta da fatar kunyi nasara?

Baki ai sun kusan dawo wa ,to dai da dan nasara zance

,domin dai an sanar mata da komai tayi kukanta ta

hakura, batun zuwa da yaran ne kam babu sauki, wannan

sai dai zuwa wani lokaci idan sun girma kenan..

Ni dai zanyi k'ok'arin ziyartasu akoda yaushe, saboda su

sani su shaku dani, shine kawai hanya mafi sauki da

zanyi domin sadasu da sauran yan'uwa dan bakiga

macen ba muwaddat wallahi kmr kece kika haifeta ,sak

kamarku day'a sauran mazan kuma yaya akram Allah dai

ya jikansa "ameen tayi mgnr tana goge hawayenta "ba

kuka zakiyi ba muwaddat mu godewa Allah ,dayasa ta

fahimcemu, bata takaryata cewar ba yaransa bane da

me zamuyi ?

Muna nan dawowa cikin satin nan, nafi son ki Haifa min

baby nah ina nan ,ina son ganin haihuwarki ,naji ihun

first nit dinki zanso naji na haihuwa, shi Kuma kowa za'a

Kira?

Suka sa dariya gabad'aya "bunayya kenan har kasa na

harareka a waya "kai kai to ina dawo kuwa sai na biya

kudin harara da kudin da bazasu kirgu ba tasan irin

kudin da yake nufi ,dan haka ta'ajiye wayar kawai

Yau ta kama ranar dawowarsa tun asuba ummi tasoma

shirya masa abinda zasu ci idan sun sauka ,ita kuwa

muwa at tayi wan ata gyara ji inta ta awo turarru a

tabi jikinta dashi domin shirin tarbo mijin abun har yaso

yabawa ummi mamaki ashe datayi k'ok'arin aurar da

muwaddat ga wani , tabbas da tayi kuskure ,maganar

abi daya ce da zasu bi junansu ,yanxu ma da basu tare

ba, suke bare bare, ina ga sun koma gidansu , kusan

tafisu matsuwa tana gama shiryawa tashige cikin

Bargon ummi tare da kashe fitila d'akin ta kwanta wani

bacci mai dadi ne ya d'auketa

Karfe takwas da rabi na safe taji tashin sautin muryarsa

a daf da shigowa d'akin ummi tayi saurin juyawa kofar

baya a dole bacci takeyi .

Tana jin shigowarsa har da mayar da kofar ya rufe da key

a zuciyarta tayi dariya shi kuwa har wani sanda yake wai

kar motsinsa ya tadata ahankali ya haye gadon ya zauna

daidai inda ta mayar da fuskarta .

Take zuciyarta tashiga dokawa ta dinga kokuwa da

numfashinsa, lokacin dataji ya sumbaci lips dinta ,ya

gangaro zuwa cikinta shima yayi masa kiss tare da Dan

shafawa alamun ko yana cikin koshin lfy ,sai lokacin ta

bud'e idanunta Dan kar ya zarce daga hkn, dan tasan

hali, ita dai kam sai dai tabawa wani labarinsa ,ahankali

ta tashi zaune tana yatsina fuska ,ya matso kusa daita

sosai 'Sannu na tasheki ko ?

Kafin tace wani abu ya rungumeta ajikinsa yana murnar

ganinta da kyar ta samu tarabata da jikinsa ya kamo

yatsun hannuta ",ya baby nah ?

Ni na isa, ayi min afuwa ya kike kin tashi lfy?

Lafiya lau ya kuka baro min yarana fatan duk suna cikin

koshin lfy?

"Alhamdullahi duk suna lafiya kmr mu barosu har

airport suka rakomu su da mamansu abun tausayi .

Yana maganar yana shafa fuskarta zuwa cikinta cikin

minti ashirin tasoma jin bakon alamari na maganarsa da

ta canza salo zuwa wasanin daita, ta soma

Biye masa sukayi Amman acikin minti talatin taji

bunayya na neman canja akalar wasa ,hakan yasa ta

nuna masa alamar ba'a wasa biyu alokaci daya a kare

lafiya ,amman take ya nuna mata shi mai iya wasa kala

hudu ne a lokaci day'a, amman wannann wasan shima

bazai iya ba adaidai wannan lokacin burinsa bai wuce ta

haihu su tare a gidansu ba, ta tsura masa ido tana jin

yadda soyayyarsa ta dawo mata sabuwa fil ta kai bakinta

ta sumbaci fuskarsa," ina sonka mijina, kmr ta tsira

masa allura yayi wani firgigib ya cakumota ya kwantar

ajikinsa 'bunayya wai meye hk ?

Sone aunty nah

Bai barta haka ba sai daya auratayya daita ,iya murzuwa

ta murzu a hannunsa .

Wuraren misalin karfe tara na safe taji jikinta yan

a

mata

ciwo iri iri' Amman hakan bai hanata hirarta da ummi ba'

da binta mai aiki ba' hkn kuma bata sanarwa da kowa ba

har ta Mike tashige dakin ummi ta kwanta Cikin baccin

Clwon mara a, al sa onu u a uguntaya ama ara

da wani juyi ,baccin da bata koma ba kenan

Cikin minti Goma sai gata a tsaye ciwo yayi tsanani

wauta irintata, sai ta kwanta Amman ciwo ya gagara

zama bare kwanciya

cikin haka marata tayi wani irin Murd'awa ta saki wata

razananniyar kara sai ga ummi tashigo a guje kmr zata

fad'i tana ganinta tasan abun yazo.

ta fita da sauri tsawon minti biyar suka shigo tare da

bunayya, lokacin har faya ta fashe Sam ummi batasan ya

biyota ba ",me haka bunayya ?

Ko kulata baiyi ba ya ykarasa da sauri gurin da

muwaddat take durkushe tana ciza lebe babu kunya

bunayya ya kamota yana shafa gashin kanta zuwa

bayanta " sannu kuwa yayi mata yafi sau Goma sha

gabadaya amatsayinsa na likita kasa aiwatar da komai

yayi ,ummi tace tashi ka fita waje kabarta taji da Abu

daya

da kyar ya bar d'akin ya Shiga kai kawo atsakanin d'akin

da parlour'n Amman har lokacin shiru babu labari aiko

ya sake shigowa yayi zaman Durshan agabanta, ita kuwa

tuni ta manta da sha'aninsa ,har ma da ummi sai kiran

sunan Allah take ,da yan adduo,i ummi ta fita cikin sauri

ta sake dawowa da sauri tana bashi umarni ya fita ,shi

kuma sai magiya yake mata kada a barta ta mutu ,ummi

ki taimaka mata mana , mata dayawa gurin haihuwa

suke mutuwa .

"dan Allah ki taimaka karta mutu kalle yadda take shan

wahala muje hospital "ko hospital din mukaje iya abinda

zan iya mata kennan, yanxu ta soma nakudar fa sai zuwa

nan da awa biyu zata haihuwa "inna lillahi wa inna ilaihi

rajiun ya furta awa biyu ummi ?

'Ta Dan daga masa kai kawai ,ai awa biyu tazo ta wuce

shiru da tafiya tayi tafiya ta Dan bud'e idanunta sai

ganin bunayya tayi zaune a gefen gado yanata faman

goge hawaye

Muwaddat bata haihu ba ai data gama shan wahala,

zuwa lokacin hatta ummi hankalinta ya tashi ,shinkuwa

bunayya ma ya daina kuka ya zuba mata ido yana jiran

yaji ance ta mutu domin ya sadaukar da mutuwa zatayi .

Wuni zirrrr tayi durkushe tana abu daya Sai karfe Goman

dare ta haifo yaronta nmj , acikin jinin da take tsugunne

bunayya ya rarrafo ya rungumeta ajikinsa, yana mata

sannu ,ya dinga furta sannu har sai da ummi ta rufe

masa baki saboda yawon sannun dayake mata sannan

ta d'auki yaron tayi bayi dashi.

Da bunayya duk akayi aikin jini, sai da aka gama gyarata

tsab ya ganta lafiya sannan yake tambayar ummi abinda

aka Haifa ummi ta d'auko masa yaron ta mika masa .

"Gsky Muhammed Auwal bashi da kunya ,lokacin da ya

d'auki yaron sai ya soma murmushi yana cewa "aunty

muwa kalleshi kiga da wa yayi kama dani ne ko?

Ummi tace "oho ni yasu wannan yaron na rasa ina

kasamo wannan rashin kunyar ,oya tashi maza ka bar

d'akin nan, 'haba ummi karki min haka mana Dan Allah

,ke daya kamata ki tayani dubawa da wa yayi kama

shine zaki koreni ",ungo nan jairin mara kunya kawai ,da

ubanka yayi kama ,maza tashi ka fitar min a d'aki

bunayya ya saki murmushi sannan ya tashi ya fita

Yana fita yashiga sheidawa abokansa zance haihuwar

da'akayi masa, yana murna, sannan ya d'aura a duniya,

saboda jin haihuwar yake tamkar amasa albishiri da

gidan aljanna.

,cikin awa daya kira suka dinga shigowa wayoyinsa da

sakonni ,duk Wanda ya kira yayi masa barka sai kaji

yana masawa da ameen ameen ,abunsa har ya daina

ba wa ummi mamaki

Da daddare ummi da mai binta mai aiki ,suna zaune a

parlour'n suna hirarsu ,ita kuwa muwaddat tana d'akinta

ta tasa jaririnta gaba ta tsura masa idanu tana kallon

kyautar da Allah yayi mata Wanda ko da wasa bata ta'ba

tunanin zata iya samun ba

soyayyar yaron ne ke fixgarta ,ta sauke ajiyar zuciya, ta

Dan gyara zaman domin kara gyarawa yaronta kwanciya

ahankali yashigo d'akin ya zauna akan kujera ya kura

mata ido yana kallonta 'ke ma kina son baby ko ....?

Tayi murmushi kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login