Showing 33001 words to 36000 words out of 70713 words
kwalliyar ta sosai duk wanda yagani sai ya yaba.
Tun da yamma masu kwalli da aka gayyace su suka zo.
suna ta cab'awa
kannen ango kwalliya, zuwa magriba kannen ango sun fita ras, k
amar wanda za'aje gasar kyau.
ana isha'i motoci suka fara jidan mutane zuwa filin taro.
su Hajiyan Dubai da wasu 'yan'uwan su Daddy da suka zo daga Yelwan Shendam akayi da su gidan amarya idan suka d'auko ta su wuce da ita filin taron.
Dr Imran ne tsaye a
kan sa, yana ta fama da shi ya tashi ya shirya su tafi,
antafi d'aukar amarya bai kamata ace amarya ta isa su basu isa ba, su yakamata su jira zuwan amarya.
ya ce bazaije ba idan yana da karfi yajashi ya kaishi.
ganin da gaske ba zaije ba, yafita yaje sas
hin Mommy ya sanar mata.
Mommy sun fito da kawayen ta zasu tafi, Imran yake sanar mata da abun da ya ke faruwa.
da kanta taje ta same shi,
ta ce har idan ita ta haife shi to ya tashi ya shirya,
tun bai had'u da mummunar b'acin ranta ba,
ita da tayi zaton
ma har ya tafi yana tare da amaryar sa.
badun yaso ba ya tashi ya shirya cikin wasu kaya masu shegen kyau.
suka fito suka nufi filin taron da sauran abokan sa.
Ko da Miemie ta zo suje da Feeryal ai mata kwalliya,
Aunty ta ce ita bazataje gurin bikin ba,
su tafi kawai.
Miemie kamar zatayi kuka tayi ta had'a Aunty Allah da annabi.
suna cikin haka Daddy ya shigo ya ce su tafi.
Miemie murna har da dariya
ta janyo Feeryal zuwa sashin Ammah bayan ta kira me kwalliya can.
Miemie sai mita take mata
"Ke wlh Feerya
l gaba d'ayan ki sai a hankali,
ki duba kiga kowa ya yi kwalli tun d'azu nake ta kiran ki kizo amiki kikaki zuwa,
gashi har an fara tafi su Ameerah duk sun tafi,
da nima fa na tafi jiran ki nake tayi tun d'azu,
haba dan Allah."
"Ke Ammie na ne fa ta ce baz
an je ba, dama ni ma ba wani son zuwa nake ba, ni wlh dama yanzu nayi bacci na, tun da ina off ba salla zanyi ba me zan zauna yi."
hararar ta Miemie tayi, ta ce wa me kwalliyar tayi mata da sauri dan Allah.
Simple makeup akayi mata a hakan ma da kyar ta t
saya dan cewa tayi ita bata so.
mai kwalliyar ta ce ba laifin ta bane ita kanta kwalliya ce, bata bukatar karin kwalliya.
ta saka ashoben ya zauna a jikin ta kamar dan ita aka halittasa
ta d'aura mata d'ankwalin, tare da rataya mata wani d'an siririn gyal
e.
kana ta bi jikin ta da turare.
Miemie da mai yin kwalliyar duk tsayuwa sukayi suna karewa Feeryal kallo
"Ya ilahi ya lillahi, zan iya rantsuwa tun da nake harkar yiwa mutane kwalliya ban tab'a yiwa wata kwalliya a 1time ta haska tamkar wacce na d'au Th
ree hour ana mata kwalliyar ba,
ba wani fenti nayi miki ba paudar ma sama-sama na goga, ba kwalliyar ce tayi miki kyauba ke ce kikayi wa kwalliyar kyau,
sai kace ke ce amaryar."
Miemie da ta bud'e baki sai yanzu ta rufe
"Idan da amaryar ta sami kyanta ai
da ta gode da bamusan in da rawan kanta zai tsaya ba,
yanzu ma yaya,
muje Feeryal nasan yanzu kam kowa ya watse ma saura mu."
Direban Ammah da Miemie ta hanashi d'aukar kowa tace ya jira su ya kaisu, shi ya d'auke su zuwa filin taron........!
Babu edi
ting
14
Tun da suka doso gurun baka jin ko mai sai sautin tashin kid'a.
motarsu na fakawa Miemie ta fito da sauri tana fad'in
"Feeryal yi sauri ana kan yi ban da mu."
ta zaga ta gefen da take ta ruko hannunta suka nufi cikin Hall d'in.
Feeryal ta rike han
nun Miemie gam ganin jama'ar gurin maza da mata gabad'aya ya tada mata hankali.
"Miemie ni kam zan zauna a moto na jira ki idan an tashi ki zo mu tafi, ga mutane fa."
"Dalla muje mutanen cinyeki zasuyi, illa iyaka ki zame musu abin kallo kamar dai yanzu da
ido ya bar kan amarya ya dawo kan mu,
ke ki natsu da'alla ki d'aga mana aji, saura ace azo ayi rawa kiki zuwa,
zo muje ta can ga gurin zama."
Da sauri ta d'ago ta hangi ango da amarya Kuraiba sai washe baki take,
angon nata kuwa na zaune fuskarnan tafi t
a kullum murtukewa da rashin annuri.
"Ido ta waro ganin in da Miemie take nuna mata,
sai sun tsaga ta sakiyar filin kafin suje gurin.
"Miemie mu zauna ata can mana."
"Ke tacan zamuje so nake a tantance kasa da sakuwa, sakanin kwalliyar mu danasu Ameerah,
d
uba kika yadda suke kallon mu,
kirika murmushin nan naki abin zai fi bada show,
ki had'a da juya wannan idanun naki, kinayi kina irin wannan tafiyar naki kamar na yanga."
Miemie ta karasa maganar da dariya..
itama dariyar tayi tana zame hannunta daga rukon
da ta mata, ta zille tayi d'aya gefen.
dole Miemie ta biyo ta.
Biki ya yi biki mawaka ana ta gwangwaje basira kowa da kalar baje basirar sa da yake,
anyi manni an zubda daloli.
Feeryal sai zuba murmushi take abun ya burge ta ba kad'an ba.
MC ya gayyaci
ango da amarya da su fito fili.
tun MC bai rufa baki ba Kuraiba ta mike,
tana yi masa alama da ya taso.
shiko fuska yadad'a had'ewa.
da sauri Mommy ta mike daga gurin zamanta ta je ta ruko hannunsa, bakin ta yakasa rufuwa
"Taso mana Abdurrahim yau fa rana
r farinciki ne, taso ka rike amaryar ka ku shiga fili."
badun kar ya dizga Mommy gaban kawayen ta ba, da babu abin da zai sa ya tashi,
karfa-karfan da akayi masa ma na zuwa gurin ya ishe sa.
ya mike ta kamo hannun amaryar ta had'a da nashi, ya zame hannuns
a ya rike iya yatsarta d'aya.
a haka suka shiga filin.
wata sassanyar waka aka sakar musu, amarya ta takarkare ta rika tikar rawa,
shiko yana tsaye abin ma haushi ya bashi ganin yadda ta dage take tikar rawa,
sai kuma wani mammannewa take a jikin shi.
Mom
my da uwar amarya Hajiya Luba da Hajiyan Dubai da kawayen su suka taso,
suka shiga b'arin kud'i a jikin su.
sai kace ganye suke wasa musu.
sai kirari ake musu, iyayen ango iyayen amarya.
Farida ma ta taso ta bud'e bakin jakanta.
Bayan su Mommy sun koma g
urin zaman su, su Amerrah ma suka taso suka shiga wasa 'yan kud'ad'en da suka zo da su a jakarsu.
Miemie ta mike tana fad'in
ai na mance Daddy ya raba mana 50-50k ga naki ma a jakata."
ta ciro d'aurin 'yan d'ari biyar-biyar sabbi tar mika mata d'aya.
"Taso
muje muyi masa liki."
tayi maganar tana kokarin roko hannunta.
da sauri yati baya da hannun ta tana cewa
"Aa kyale ni je kiyi masa likin ga nawa ma duk ki had'a kiyi masa likin kawai."
"Ai baki isa ba kowa ya je ya yi masa liki ke ce bazaki je ba,
ai dai
zaki je ki taya shi farinciki, Allah sai kin je taso muje."
"Dan Miemie ni ki rabu da ni kije kiyi masa kawai ni bazani ba."
Hannunta ta figa ta janyo ta tana tirjewa Miemie tana cewa fa sai ta je.
d'an karamin bakin ta ta cuno tana bubbuga kafafunta a ka
sa tare da yarfe hannunta tana cewa
"Ni dai Miemie ki barni ni dai bazan jeba."
a haka ta janyo ta suka shige filin.
wani irin tafi gurin ya kaure da shi ji kake
rap-rap-rap.
da sauri ta tsaida buga kafa da yarfe hannun da take ta d'ago kai da sauri.
taga
mawakin yana takowa in da suke ya yin da yake ci gaba da rera salon baitin sa,
Camera ya dawo kan su.
yana zuwa in da suke ya shiga ciro kud'i a aljuhun sa yana lika mata.
aka kuma kaurewa da tafi had'e da hele..
kai ta sunkuyar a hankali ta soma yiwa a
ngo da amarya liki kamar yanda taga Miemie take musu,
amma kanta a sunkuye.
sai shigowa filin ake madadin a yi wa amarya da ango liki sai mata liki ake.
ita dai kanta a sunkuye bata yadda ta d'ago ba, tana ta lika musu kud'in hanun ta.
"Kamar ke ce amarya
r sai kike fi dacewa da angon."
da sauri ta waiga bayan ta, wata babbar mace ce tsaye tana mata liki ta baya.
murmushi matar ta sakar mata, itama tayi mata gajeren murmushi.
tana juyo wa idanunta ya yi karaf da nashi.
wani mugun kallo ya wurga mata,
da sau
ri ta zame jiki ta fice a filin ta koma gurin zaman su.
Amarya Kuraiba ta bita da ido.
wace ce ita daga fitowar ta ta cinye taron ko ita amaryar ba a yi ihun fitowar ta haka ba.
ta had'iye abu mai d'aci a wuyan ta, ta aje tambayar ta cikin ranta sai bayan
biki zata bibiyi wace ce ita,
da zata fito filin da aka tanadar domin ta har ta janyo hankalin mutane kanta.
daga an ga 'yar wata kasa sai duk a rud'e.
tayi kwafa a kasan ranta.
ta maida hankalin ta kan angon nata,
ta cigaba da shishigewa jikin sa.
Daga
in da Mommy ke zaune take ta aikawa Feeryal harara, wan da ita batama san tayi ba.
Feeryal na zama ta sauke numfashi Allah ya gani ba son shi cikin irin wannan taron take ba.
Bayan ango da amarya sun zauna aka gayyaci kannen ango.
duk yadda Miemie taso
ta tashi su shiga fili fir take, haka ta kyale ta ta je suka tika rawar su..
Duk da cikin taro ne bai hanashi busa sigarin sa ba, yana yi yana karkata baki irin na 'yan iska.
cikin muryar 'yan kwaya ya ce
"Kai dubi wata had'ad'd'iya zazzafan kayan dad'i
."
"Ai tun d'azu na lura da irin had'iye yawon da kake akanta, kai fa Jazu ba karamin maye bane amma na mata."
wani dariyar rashin mutunci ya ke ce da shi
"Ke Zuly mata abin so ne, wancan yarinyar ta tara kayan dad'i a guraren nan."
dariya tayi tana kallon
in da take
"Ba karya kam ta aje komai zam-zam amma nan gani nan bari, sakanin ka da shi kallo daga nesa."
"In dai zaki taimaka min me zai hana bazan samu ba."
"Nawa zaka biya?."
"500k."
"Seriously yanzu nake son jin su a banki na."
"Idan kika gama aikin k
i zaki jisu, kin san dai bama haka da ke."
"Baka da matsala."
ta fad'a tana mike wa, ta nufi in da su Feeryal suke zaune.
Kujerar da ke fuskantar Feeryal ta ja ta zauna da murmushi kan fuskarta tana fad'in
"Sannun ku dai sister's to ya bikin?."
"Gashi ana
kan yi."
cewar Miemie."
zama budurwar mai suna Zuly ta gyara idanunta a kan Feeryal ta ce
"Tun daga can na ke ta hango ki, na ce yau daren nan tawa ce nayi samuwar kawa,
sunana Zuly."
ta karashe maganar da miko mata hannu.
ido Feeryal ta bita da shi batar
e da ta miko nata hanun ba, sai murmushin da tayi mata.
Zuly ta dubi Miemie ta marairaice murya.
"Kawar tamu bata magana ne dan Allah kice ta ce min wani abu mana."
Miemie ta tab'e baki
"Da alama dai yanzu ta kurmance."
"Hahaha amma anyi kyakkyar kurma ana
n to a haka nake son ki da kawa,
kin ga ke ma kin zama kawata tun da ke kawar kawata ce,
ni suna na Zuly ke fa."
maganar ta bawa Feeryal dariya.
tad'an dare.
Hannu Miemie ta mika mata kamar yadda itama ta mata tana cewa
"Ni kuma Miemie ita kuma Feeryal."
"Wow nice names, amma ku kannen ango ne ko naganku da ankon kannen ango?."
Miemie ta ce
"Eh mu kannen sa ne."
sosai ta dage tayi ta zuba musu hira, Miemie uwar 'yan surutu tana taya ta.
har Feeryal tad'an saki jiki tana d'an sa baki cikin hirar.
Karfe 12
dai-dai aka tashi, motoci suka soma jidar mutane suna maida su gida.
tuni ango ya shige nashi motar ya yi gida batare da yajira komai ba,
dan dama ya yi yinkurin tafiya har sau biyu Mommy ce ke hanashi.
aka kwashi amarya da kawayen ta aka tafi da su A.A F
IYA STREET.
Su Miemie sukayi waje gurin nasu motar.
har gurin motar Zuly ta biyo su,
suna kokarin shiga mota,
ta ce
"Dan Allah ku d'an jira ni na duba na gani ko motar da nazo ciki ta tafi,
dama kai amarya zanyi sai na biku kawai."
ta juya da sauri suna t
saye suna jiran ta jikin mota.
Can ta nufa in da mutane suke tsastsaye da ala ma jiran mota suke.
da sauri ta karaso gurin ta ce
"Sannun ku mota kuke jira?."
suka ce Eh.
ta ce "Ga mota can babu kowa cikin ta, ku karasa mana ku shiga."
ai ko da sauri suka
nufi in da ta nuna musu, ita kuma ta yi saurin isa gurin
abokin harkallar ta sukayi magana kana ta juyo da sauri, gurin su Miemie.
mutanen da ta ce misu ga mota can suna zuwa kuwa suka kama d'uruwa cikin mota.
Miemie ta ce
"Aa ya ya haka ya da shiga mana
mota?."
suka ce gidan amarya zasu kuma ance musu wannan motar gidan amarya ce.
Feeryal ta ce
"Miemie rabu da su su shiga kamar zai d'au ke mu ai motar."
tun kan ta rufa baki suka shige.
Miemie ta shiga gaba tana cewa
"To ai sai ki zo ki shiga nan mu had'u
mu makuru."
tayi maganar tana hura hanci.
murmushi Feeryal tayi ta shiga ta zauna gefen ta tana kokarin rufe murfin motar,
Zuly ta karaso gurin tayi saurin rike murfin
"Ah me zan gani haka wariyar launin fata za'a gwada min, mota ta cika ni ina kasa,
to ai
kuwa sai dai ke ki fito, mu nima wata motar,
yauwa gama mota can sauko dan Allah muje mu shiga can, ba girman ku bane zama a matse alhalin daga gidan A.A FIYA kuka fito, yaho muje can motar."
ta janyo hannun Feeryal ta fito ta maida marfin ta rufa tana fa
d'in
"Allah ya tsare gamu a bayan ku muma sai mun iso."
direba ya ja motar suka fice daga harabar Hall d'in.
"Muje ko ga motar can."
suka jera zuwa gurin motar.
ta bud'e gidan baya,
maza biyu ne a zaune a ciki sai kuma d'aya a mazaunin direba, ta shiga t
a masa can ta mannu da mazan sosai, ta ce
"Shigo mu lallab'a, ko kuma kai fita kar mu tseta sosai."
wan da yake jikin kofar ta can ya sauka ya koma gefen mai zaman banza.
kana Feeryal ta shiga jiki a d'an sanyaye dan bata tab'a shiga mota da maza irin haka
ba.
Babu wan da ya yi magana a cikin su har suka fice.
sunyi tafiyar da baifi na mintuna biyar ba motar ta tsaya.
na mijin da ke gefen Zuly ya bud'e motar ya fita, itama ta sauka, shi ya dawo cikin motar ya rufe kofar.
ta zago ta gefen da Feeryal ta ke t
a d'aga mata hannu
"Bye bye 'yanmata sai mun sake had'uwa."
da sauri Feeryal ta dube ta cikin rashin fahimta.
ita ko ta juya tana cigaba da d'aga mata hanu, ta shige wani motar da yanzu ya karaso gurin.
tana shiga aka figi motar da gudu.
wani irin juyowa t
ayi jin an......!
15
An wani rungumo ta, ido ta waro cike da matukar tsoro.
ya dad'a wani cacumo ta yana fa d'in
"Wayyo kai kaji jiki kamar auduga,
ja motar nan da sauri mu karasa ko mai zai iya faruwa a nan, nazo har wuya fa."
ya ja motar suka shari
wata kwana, tuni cikin ta ya d'ura ruwa sai musu-musu take tana tutture shi.
ta fashe da kuka da ihun niman taimako.
a bakin get d'in wani hotel suka yi hon,
a ka bud'e suka shige ciki.
d'aya na mijin da ke zaune a gaban mota ya miko masa key dai-dai san d
a suka gyara parking.
ya ce
"Room 13 shine d'akin ku asha dad'i lafiya oga."
wani dariya ya sake hahaha. yana shafa fuskar Feeryal da yayi dama-dama da hawaye.
"Yi shiru mana zazzafa wannan irin kuka haka sai kace yanka ki zanyi, kayan dad'i kawai zan bak
i, kuma ke zake fad'i farashin ki da kanki, ba kyauta zan more kayan alatun nan ba,
muje ki fad'i nawa zan biya."
ya bud'e motar ya fito kana ya miko mata hannu ya ce
"Zo muje ko 'yammata."
da sauri ta matsa baya tana girgiza kai, hawaye na zuba.
ya mika h
anu ya janyo ta ya fito da ita tana tirjewa, had'e da ihu.
Babu kowa harabar hotel d'in guri ya yi shiru, sai masu gadin hotel d'in su biyu.
ihu sosai take tana fad'in a taimake ta.
amma masu gadin sai dariya suke suna fad'in
"Kai Zazuu kabi a hankali fa
sabuwar hannu ce wannan da gani."
ganin zata bashi matsal sai kawai ya ciccib'e ta ya yi ciki da ita.
a bakin kofar room 13 ya direta ya rike ta gam da d'aya hannun sa, d'ayan kuma ya zura key'n ya bud'e kofar kana ya tura ta ciki shima ya shige ya zare ke
y'n ya maida shi ta ciki ya kulle kofar.
Sosai Feeryal ke kuka kamar zata shid'e,
ta shiga magiya da rokon sa
"Dan Allah kayi hakuri kar kayi min komai, wlh ni bana son kud'in ka bana so dan Allah dan Allah."
ta kuma rushewa da kuka sosai.
Shiko wani iri
n murmushi yake sakewa yana tako wa in da take,
baya ta