Showing 48001 words to 51000 words out of 70713 words

Chapter 17 - FEERYAL BOOK2 COMPLETE

naga ke ma sai murna kike a gidan su."

cikin masifa da tafasar zuci ta ce

"Badai gidan

su ba sai dai gidan mu dan ba gidan uban Feeryal bane can."

ta juya fuu ta shige d'aki.

murmushi ya yi dan bai kawo komai a ransa ba ya cigaba da yiwa 'yar sa wasa.

Da daddare har ya yi nisa a bacci ta tashe shi, dan ita takasa baccin, sabar masifar kish

i.

ta bubbugashi tana fad'in

"Faruoq ta shi ka gaya min mene ne dalilin dayasa kake ta kawo min maganar mayyar aljanar yarinyar nan, tun a mota har a cikin gidan nan, wace munafurci kake kullawa cikin ranka."

ido ya bud'e cike da bacci ya ce

"Haba Farida a

tsohon daren nan zaki tada ni da wani magana mara kan gado, babu ko Abba'n Neezrah ma yau to me zan gaya miki, me kuma zan b'oye miki cikin raina,

dan nayi maganar kanwarki shine wani abun tashin hankali."

"Dakata Faruoq ba kanwata ba karka sake had'a ni

da ita, dan babu abun da ya had'ani da 'yar da ba'asan asalinta ba,

tsintacciyar cikin ruwa,

daga yau karka sake kawo min batun ta cikin gida har in kana son zaman lafiya a gidan nan."

janyo ta ya yi jikin sa ya ce

"To naji shike nan Sleep please bazan kar

a ba."

Farida bata iya bacci ba sabar yadda take

jin zuciyarta, kamar ana mata luguden tab'are.

Washegari da safe bayan ya fita office ta shirya ta d'au mota sai AA FIYA STREET.

tana isa b'angaren Mommy ta shige.

Mommy na ganin ta ta ce

"Ya akayi Farida

ko jiya kinyi mantuwa ne?."

ta ce "Nazo cin uwar mayyar yarinyar nan ne, jiya kwana Faruoq ya yi yana ambaton sunan ta,

zo muje Sumayya ko Ameerah ku kira min ita."

Ameerah tayi kus kamar bataji ba.

Mommy ta ce

"Ke Sumayya tashi kije ki kira mata ita, ai

kiyi mata tatas in da gobe bazata kuma bin kurwar sa cikin dare ba."

Farida ta juya ta fita Sumayya ta bita tana fad'in

"Aunty Farida da kin rabu da ita."

hararar ta tayi

bata tsaya ba sai da tafito waje ta ce

"Wuce kije ki kira min ita."

Sumayya ta wuce

sashin Aunty.

a parlour ta tadda Aunty ta ce wai Farida tana kiran Feeryal.

Aunty ta d'anyi jim sannan ta ce

"Me ya faru ta ke niman ta?."

ta ce "Ni ma ban sani ba tadai ce na kira ta."

kai ta jinjina ta ce

"Shiga tana ciki."

Sumayya ta shiga ta sameta ta

na bacci ta tasota ta d'au hijabi suka fito.

har sun kai kofa zasu fita

Aunty ta ce

"Tafad'i abin da zata fad'a ki dawo bance ki amsa ta ba."

Feeryal ta gyad'a kai kana suka fita.

Aunty ta koma ta zauna bataji ko d'arr ba dan tasan ba shegiyar da ta isa ta

sa mata hanu yanzu ta share, sai dai taji wa jikinta.

Farida na ganin su tasoma tahowa tana fad'in

"Yau nazo naci uwar ki har gida naga wanda ya tsaya miki."

ta na isowa in da take ta shako wuyan hijabin ta.

"Meye had'aki da mijina da zakisa ya koma gida

yana kawo min zancen ki,

maitar taki takai har kin fara bibiyar mijina,

me za'ayi dake da ba a san asalinki ba,

to wlh gargad'i na farko na karshe idan na sake ganin ki a inda mijina yake sai nayi miki d'anbanzan duka na b'ata fuskar da yake rud'in ki yak

e kaiki ga mazajen mutane,

shegiya mayyar banza aljanar ruwa,

nafi karfin ki wlh ba dai miji na ba."

Ajmal dake tahowa ta bayansu ya ce

"Meye haka Farida wani irin abu ne wannan meye amfanin hakan."

cikin masifa fa ce

"Karabu dani Ajmal naci uban yarinay

r nan, dan wlh bata isa ba mijina yafi karfin ta."

"Kaji wani shirme dan Allah ita cewa tayi tana son mijin naki."

"Idan ta fad'a ma basai na kasheta ba, wlh mijina ya girmi ajinta 'yar da ba a san asalinta ba ma,

idan bata fita sabgar miji na ba, wlh sai

na halakata."

kai Feeryal ta sunkuyar Ajmal na kokarin jan hannun Farida da ke rike da wuyan hijabin ta wayarsa tayi kara.

ya zaro wayar a aljuhu ya kai sa kunne

daga cikin wayar ya ce

"Bawa Farida wayar."

ya zaro a kunnen sa yamika mata yana cewa

"Wai gas

hi."

sai da ta harare sa kamar ita ce gaba da shi kafin ta ce

"Inji wa nifa baza'a mareni a hanani kuka ba."

ta fizge wayar ta kai kunnenta.

Ajmal yashiga waige-waige yana son ganin daga ina yake har yasan abin da yake faruwa, yana d'aga kai ya hango sa ca

n saman upstairs na side d'in sa yana tsaye rike da Mug a hannunsa ya yin da d'aya hannunsa ke kare da waya a kunnensa.

daga cikin wayar Farida tajiyo muryar sa

"Saketa! baki da hankali ne zaki rika d'agawa mutane murya a cikin gida, oya fita ki bar gidan

nan ki koma gidan ki, kar ki kawo wa mutane haukar banza,

kisa ta tarawa mutane jama'a."

Farida ta tura baki ta mikawa Ajmal wayarsa.

ta sake ta tana cewa

"Allah ya taimake ki wlh da sai kin gane cewa mijina ba saranki bane,

mayyar aljana kawai."

ta juya

fuu ta yi gurin motarta tashige tabar gidan.

Ajmal ya dubi Feeryal da jikin ta ya yi sanyi yace

"Yi hakuri Feeryal kije abin ki."

a hankali ta juya.

tana shiga Aunty ta bita da kallo ganin jikin ta a sanyaye ta ce

"Me yasa Farida'r take niman ki?."

murya

a sanyaye ta ce

"Wai nafita sabgar mijinta wai ya koma gida yana zance na."

Aunty tayi murmushi tare da girgiza kai

ta ce "Je kiyi wanka kizo kiyi breakfast."

ta juya ta shige bedroom d'in ta.

Ji ya yi an rungume shi ta baya, Kuraiba ta manna kanta a ba

yan shi tana shafa kirjinshi.

cikin narke murya ta ce

"Mijin Kuraiba ba ko zuwa duba ya na kwana ba, kasan da ya nayi bacci kuwa,

gurin nan sai zafi yake min sai da nayita gasashi da ruwan zafi,

ka duba min zafi yake min har yanzu."

hannunta ya b'anb'are a

kirjin sa ya juyo tare da wasa mata wani kallo kana ya juya ya bar gurin.

wani uban mika ta sake tana tuna kasantuwarsu har yanzu zakinsa yaki gogewa a kwakwalwar ta,

tana ji ina ma ace ta kasance cikin hakan yanzu..

Umma Karima ce tsaye cikin d'akin ta,

rike da waya a kunnenta.

daga cikin wayar ake fad'in

"Hajiya sai yau Allah ya yi aka samo wani da kyar,

in zaki biya million 2 idan guri ya rufa zan kawo miki."

Umma Karima ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya tana fad'in

"Allah na gode maka wahalata ta

zo karshe, million 3 zan baka shima ka rike ne dai-dai komai ya dai-dai ta zan biyaka kud'in aikin ka mai soka."

"Hahaha Hajiya to na gode anjima zaki ganni."

Umma Karima ta sauke wayar tashiga tika rawa.

tana fad'in

"Sai ni Hajiya Karima bani Dubai London

bani England."

tawani shekewa da dariya

"Hahaha yanzu wasan zai soma.......!

21

Guri na rufawa kamar yadda mutumin da sukayi waya da Umma Karima yace zaizo kuwa sai gashi yazo.

a parking lot d'in ta ya tsaya tafito ta sameshi.

ya mika mata wata bakar

laida yana fad'in

"Ga sakon ki Hajiya na d'auki kasada sosai amma na shafe duk wata shaida."

har hannunta na b'ari ta karb'i laidar tana cewa

"Kai sannun ka da aiki kayi namijin kokari da kai za'aci arziki saboda kayi rawar gani wajen ganin an samo arzikin

,

yanzu ga wannan miliyan ukun ne, kaje ka sha shayi da su kayi murna lokacin arzikin ka yayi."

ta mika masa jaka mai d'auke da kud'ad'en da ta shirya ciki.

ya karb'a da murna yana fad'in

"Lallai kuwa godiya nake Hajiya, ai muna fadarki muci arziki mu bart

a a inda take."

har ya shiga motar sa bai fasa zuba mata godiya ba, yana fita tashiga kwad'awa Liti direban ta kira.

ya shigo cikin hanzari yana amsa kiran nata.

ta ce

"D'auko makullin mota da sauri fita zamuyi yanzu."

"Ina kuma zamuje Hajiya da magriban n

an?."

"D'auko da'alla a hanya kayi min wannan tambayar."

ta shige mota da sauri tana rungume laidar da kyau a jiikinta.

sai da suka haura titi kafin ya dubeta yana cewa

"Hajiya ina muka dosa ko tafiya zamuyi ta yi kawai?."

ta ce "Dajin Mali zamuje kara gud

un motar yi sauri hanzarta."

"Hajiya ba dai kud'i kika d'auka a laidar nan zaki kai masa ba, ni fa dama ina da bukatar wasu kud'ad'e sabo da na kwan biyu ban yi aike gida ba."

"Ni matsala ta da kai ke nan, kullum baka da damuwa sai na kud'i, ko an baka sai

ka kuma niman su, ka aje bukatar kud'in nan naka yanzu sai an gama komai tukun,

Allah na tuba idan aiki ya kammala meye kud'i kuma ai sai dai ka bawa wasu,

kai dai yi sauri mu isa."

Liti ya kara gudun motar yana cewa

"Wai gara in fad'a miki da wuri ne kar

ki kwashi kud'ad'en duka ki kai masa mu mu rasa."

Karfe 7 da rabi suka isa saboda gudun da motar take.

Umma Karima ta sauko a motar guri ya rufa yayi duhu, babu tsoron Allah bare tsoron dukun dajin bare tsoron wani mugun dabba mai cutarwa.

zuciyarta ya k

ekashe muradin ta kawai take hangowa a gabanta.

ta kunna hasken wayarta ga kuma hasken fitilar mota.

jiki na rawa na son cikan muradinta, sai kakabe laidar take a jikinta.

ta cire mayafi ta kunce d'ankwali ta cire takalmi, ta d'uru cikin duhuwar kogonnan,

zuciya a kekashe babu d'igon tsoro bare imani.

"Gafara dai boka yau gani tafe da babban guzuri, nasamo cikon na uku."

wani irin hargitsastsen dariya kogon ya kaure da shi

"Hahahaha kinyi nazari da lissafi mai kyau, saura kiris laya ta gama narkewa jeki sa

nya shi cikin tukunya."

da sauri ta isa gaban tukunyar kaskon tajefa laidar ciki.

wani irin hargitsewa gurin ya yi da wani irin sauti mai ban tsoro,

tukunyar ta kama tafasa tana dafuwa tamkar wutar zuga,

wani kumfa ya taso fuuu yana bin jikin tukunyar yana

gangara zuwa cikin wani rami mai zurfin gaske da ba'a iya hango karshen sa.

jikin Umma Karima na rawa, idanunta a kan tukunyar, har kumfar tagama sauka tas tukunyar ta shafe kamar babu abinda ya tab'a zama cikin ta.

kazamtacciyar dariyar nan ya kuma kece

wa da shi yana fad'in

"Aiki ya kammala ikon ki ya soma."

zubewa gaban shi tayi tashiga karanto mishi ayoyin godiya.

ya ce "Tashi kije gaki ga duniya kin samu."

jiki na kyarma ta mike tafito daga kogon ta kwashi kayakin ta, tashige mota bakin ta yaki rufuwa

.

Liti ya kunna motar su ka soma fita daga dajin.

ganin yanda yau ta fito cikin mashahuriyar farinci daga gurin bokan nata ya ce

"Hajjaju an samo wata nasarar kenan."

baki ta dad'a washewa ta ce

"Nasara mai girman gaske ma kuwa, kai dai yi sauri mu isa gid

a kawai."

karfe tara ya kawo su gida, Umma Karima ta shige gida tana jin kanta da girma.

Da misalin karfe goma na dare Daddy na zaune yana dube-dube cikin computer.

Mommy na zaune a gegen sa dan yau ita ce da shi.

da sauri ya kai hannu ya dafe kansa tare

da fad'in

"Innalillahi wa innailaihirraji'un."

ya rike kansa da karfe

yana jin wani irin sarawa da kan sa keyi had'e da jiri da gilmawar bakin duhu.

addu'a yarika karantowa duk wacce tazo masa baki.

Mommy ta mike tana masa fifita da fad'in

"Alhaji me ya f

aru?."

yakai tsawon minti goma a haka da taimakon Allah da addu'a yarikajin sassaucin abin da yake ji.

har ya iya janye hannunsa a kan da yake ji kamar an d'aura masa wani katon abu mai matukar nauyi.

kallon Mommy ya yi dake tsaye tana masa fifita, numfash

i ya ja da kyar yana tuna da Fad'imatu'n sa ce da da addu'a zata taimaka masa ba fifita ba.

ido ya rumtse yana jin girman ta cikin zuciyarsa, lallai mace mai ilimi garkuwa ce cikin gida.

Da kyar ya iya mikewa ya dawo bakin gado ya zauna, yana cigaba da a

mbaton sunan Allah.

har yakai bayan sa ga katifa bai fasa ambaton Allah ba,

yana ji kamar ana kafa masa kusosi cikin sassar jiki musan kansa da yake jin sa kamar zai rabe gida biyu sabar nauyi.

yakai awa guda idanunsa a rumtse bawai ko dun ya yi bacci ba.

Mommy kuwa ganin ya yi suru da addu'o'in da yake a fili, tuni ta d'ale gado tashiga sauke minshari.

sai wajen karfe biyu kafin ya samu bacci marad dad'i ya d'auke shi mai cike da tarin wahala.

kamar yadda ya saba munanan mafarkai masu cike da rud'ani da fi

rgici yanzu ma haka ya soma, sai dai na yau ya girmi na sauran lokutan.

Wasu halittu ne masu ban tsoro suke binsa zasu kamashi abaya gudu yake basa samin nasarar kamashi,

yau kam duk iya gudun sa sai da suka cimmasa.

suka d'ad'd'aure shi da igiyar wuta,

j

ikin wani katon itaciya wacce kasan ta, rami ce mai zurfin gaske wuta yana ci ba kakkautawa.

ga mashi gami da kifiyoyi a hannunsu suna ihu mai firgitarwa da haniniyar zasu kashe shi.

ga igiyar wutan tana shiga jikinsa tana cin namar jikin sa.

wad'annan d

odannin halittun kuwa,

sun d'aga wata kifiyar wuta suna daf da caka masa.

ya zabura tare da yin salati ya mike zaune jiki na kyarma.

ya had'a zufa sharaf hatta tafin kafarsa zufa yake.

hannu ya kai ya dafe kirjin sa da yake ji kamar zasa fito.

kallon gef

en sa ya yi yaga Mommy na kwance tana sharar baccin ta.

da kyar ya mike yana jin jiri na d'ibansa ya fad'a bayi ya yi al'wa ya fito.

ya shinfid'a sallaya yasoma gabatar da sallah a daddafe.

har wajen karfe hud'u ya sallame ya kwanta kan sallaya bacci na d'

aukar sa yakuma yin wannan mafarkin.

kiran salla ce ta taimake shi wajen farkawa daga mummunar mafarkin nan.

ranar Daddy bai iya fita masallaci ba a gida ya yi salla.

Mommy na idar da sallar ta taja kafarta ta koma side d'in ta, babu gaisuwa bare tambayar

sa ya yakwana da jikin nasa.

Daddy na zaune har wani lokaci a kan sallaya dare d'aya ya jijjiga har ya fara fita a hayyacin sa.

ya mike da kyar ya nufi sashin Aunty.

Aunty na zaune parlour tana saurarar karatun alkur'ani a TV ya shigo.

duban sa tayi tana

sakar masa murmushi,

shima murmushin karfin hali ya yi mata.

ta ce "Yanzu nake shirin zuwa sashin ka naga har wannan lokacin baka shigo ba, na ce ko lafiya."

murmushin yakuma yi mata yawuce bedroom d'in ta.

ta mike ta biyo bayansa, taga ya haye gado ya kwa

nta.

rike baki tayi

"Daddy kazo ka kwanta kuma bafa a nan kake ba."

tayi maganar tana karasowa bakin gadon, ta zauna tana dubansa cikin kulawa.

da d'an mamaki ta ware ido a kanshi ganin yadda fuskarsa ta zabge kamar dai mara lafiya.

hannun sa ta ruko tana

fad'in

"Ya ya dai Daddy me ke faruwa ne baka da lafiya ne?."

tayi maganar cikin nuna damuwa sosai.

hannunta ya kankame yana gyad'a mata kain.

gaba d'aya ta damu ta ce

"Me ya same ka Daddy ba dai ciwon ka ba, sannu kaji yanzu ina ne ke maka ciwo, Abdurrahi

m ya sani kuwa? bari na kirashi ya zo ya duba ka."

ido ya rumtse kana ya bud'e ya ce

"Banyi bacci ba jiya Fad'imatu ina jin kirjina da kaina kamar zasu fashe."

"Subhanallahi sannu Daddy, kuma kasha maganin ka kuwa, ko dai kwana biyu baka sha ne? bari na d'

auko maka na nan kasha sai na kira Abdurrahim."

ido ya rumtse yana jin yadda kai da kirjin suke masa.

ta mike da sauri taje ta d'auko maganin sa datake ajiyewa a gon ta wanda idan yana gurinta da kanta take basa yake sha.

ta had'o da gorar ruwa tazo ta bas

hi ya sha.

ta mike tana fad'in

"Bari na d'auko waya nakira Abdurrahim."

ya ce

"Barshi tukunna Fad'imatu idan bai lafa ba zuwa anjima sai a kirashi."

kai ta gyad'a cike da matukar tausaya masa.

ta gyara zamanta gefen sa tana ta yi masa sannu.

ta bud'e tafin

hannunta tana karanto addu'o'i ta tofa ta shafa masa a kai d'in zuwa jirjin sa.

a hankali ya lumshe idanunsa yana jin nutsuwa na shigarsa, duk da yana jin ciwon amma yaji matukar jin dad'in nutsuwar da ya samu wanda jiya zuwa yau da safiya bai samu ba.

a

hankali a hankali bacci ya tafi da shi.

ganin yasamu bacci Aunty ta tafi kichin domin ta shirya masa abincin da ta san yafi so idan ya tashi ya ci.

ita da Feeryal da Baba Rabi ne a kichin.

Feeryal na taimaka mata da wasu abubuwan in da Baba Rabi kuma ke ta

aikin gogewa da wanke duk in da yab'aci da duk abin da akayi amfani da shi aka aje zata d'auka ta wanke ta goge sannan ta maida shi gurin zamansa.

Suna kammalawa Aunty ta d'auko lafiyayyen girkin da tayiwa Daddy,

Feeryal kuma ta d'auko nasu shima kayatac

cen breakfast da abinda tafi muradi wato cake d'in da ta had'a da kanta, da yoghurt mai sanyi.

ta fito ta haura da shi dinning.

Aunty na shiga ta hango Daddy jikin sa na b'ari ya had'a gumi sharkaf, idanunsa kuma a rufe.

da sauri ta dire tray'n abincin ha

nnunta kasa, da sauri mai kama da gudu ta hayo gadon ta rirrikeshi tana jijjigashi da kiran sunan sa

"Daddy Daddy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login