Showing 18001 words to 21000 words out of 70713 words
/>
ke lekashi take yi ai na ganta da ido na."
Ameerah tayi maganar cikin hayagaga.
Miemie ta ce
"To meye a jikin saurayin naki da za'a leka shi,
ana ta ce miki kiyi hakuri kina ta wani d'agawa mutane murya to ta kalla kiyi abin da zakiyi,
dalla wuce mu tafi,
Feeryal tayi abin da zatayi."
"To idan zan mata abun da zan matan zaki hana ne,
kema bakifi karfin na had'a da ke ba bana son shishigi."
Miemie ta dalla mata harara ta ce
"Kar ki yadda kice zakiyi min ehe ni ba Feeryal bace kul in gaya miki,
kisan wad'an
da kike wa rainin wayon ki, kar ki yadda kice zakiyi min,
dalla wuce mu tafi kin tsa tana gaya miki magana har kina bata hakuri."
taja nannu Feeryal fuuu suka kara gaba bata fasa mitar ba.
"Ki ci gaba da tsayu kowa yarika cin tuwo a kanki yana wanke kwan
on, idan Ameerah ta gane kina tsoron ta to kin shiga uku bakisan wannan shegiyar bace, kin tsaya kina wani bata hakuri baki gaggaya mata magana ba, ita da saurayin nata."
"To me zan ce mata Miemie jiran ki fa nake wlh ni ba leken saurayin ta nake ba."
"Da
lla ni ki daina min wannan maganar kayan haushin, kar kiyi baki ki iya rama waba, Ameerah da kike gani rashin mutuncinta ya wuce duk in da kike zato."
shuru tayi bata ce komai ba.
Kamar ko da yaushe Umma Karima ce zaune gaban bokanta, babu d'ankwali bab
u takalmi.
a gaban su wata tukunyar kasko ce tana tafarfasa ita kad'ai tamkar yana kan garwashin wuta.
boka Mali ya leka cikin tukunyar
cikin kazamyacciyar muryarsa ya kece da dariya
"Hahaha aiki na kan wakana sai dai har yanzu kin kasa samo cikon na uku
har yanzu aikin ki bai cika ba,
bazaki tab'a samun yadda kike so ba har sai kin jefa duka ukun cikin tukunyar nan."
cikin damuwa Umma Karima ta ce
"Boka duk yadda zanyi nayi na kasa samu babu wata hanyar da za'a bi a cikita min aiki na in yaso sai na biya
kawai."
Sandar tsafin sa ya buga kasa yayi wasu surkullensa kana ya zaro wata laya ya ce ya jefata cikin tukunyar nan,
wani irin kumfa had'e da bakin hayaki fuuu ya taso cikin tukunyar.
ya ce
"Duk sanda layar nan ta gama narkewa har idan baki samo cikon
na ukun ba to aikin ki ya lalace, sai dai a fara daga farko."
da sauri ta ce
"A'a boka hakan bazama ta faruba ko ta halin kaka zan nemo bazan bari aikin shekara da shekaru ya tashi a banza ba."
"Hahaha kin yi tunani mai kyau maza ki tashi ki bazama nima."
Umma Karima ta mike a bujajan tayi waje bayan ta zazzage masa bakin jaka.......!
8
Mommy ne zaune a bedroom d'in ta rike da waya a kunnen ta, tana fad'in
"Ki bata hakuri Hajiya Luba halin Abdurrahim sai a hankali, ko ni nan hakuri da shi nake dole sai
tayi hakuri,
har zuwa san da zata shigo gidan sa bazata tab'a samin yadda take so da shi ba, dan shi wani irin mutum ne baud'ad'd'e,
san da suka kasance a tare ai ita mace ce tasan yadda zata bi ta karkato da hankalin sa gare ta."
Hajiya Luba ta ce
"Amma
dai babu dad'i haka ace an bada sadakin ka ko sau d'aya saurayin bai tab'a zuwa ba,
kullum a cikin karya take wa kawayenta baya kasar ne, har wasu sun fara gane wa."
"Karki damu Hajiya Luba ke dai a saka bikin nan kawai daga zaran anyi ba shike nan ba,
bar
i alhaji ya dawo zan masa maganar ya turo aje a sa rana, ayi bikin nan da wuri kawai, kudai kuci gaba da shiri nima ina kai za'a kawo muku lefe satin aure."
"To yanzu naji batu Hajiya Halima ga d'iyar taki ma wai na bata ku gaisa."
Mommy ta washe baki
"Ah
bawa surukar tawa mu gaisa."
Hajiya Luba ta mikawa Kuraiba da ke kwance a jikinta waya tana fad'in
"Ga Mommy'n naku kullum in muna waya kiyi ta ce nabata ku gaisa kamar baki da wayar kiran ta ku gaisa."
Mommy ta yi dariya
"Yar albarka ya kike ya shirye-s
hirye."
"Lafiya lau Mommy muna kai."
"Yauwa madalla kiyi ta hakuri da Abdurrahim lokaci na zuwa."
"Mommy ko na kirashi baya d'aga wayar."
"Kar ki damu Kuraiba daga zaran kunyi aure duk wannan matsalolin sun kare, kinji ko."
ta ce to.
"Yauwa to sai anjima."
Mommy ta kashe wayar.
Kuraiba ta gyara kwanciyar ta jikin uwar tata.
Hajiya Luba ta ce
"To kinji da kunnen ki Hajiya Halima ba karamin kaunarki take ba,
zaki kuma sami d'anta yadda kike so cikin ruwan sanyi."
"Momma ina son Abdurrahim burina kawai na mall
ake shi, nadad'e ina mafarkin samin miji kamarshi,
kyakkyawa kakkarfan namiji a tsaye mai kud'i."
Hajiya Luba ta yi dariya tana cewa
"Kud'i kam akwai shi dan kuwa su kud'i gadarsa sukayi, jinin kud'i ne a jikin su yake malala,
kwantar da hankalin ki kamar
kin sami Abdurrahim kin gama."
Kuraiba tayi wani murmushi tana hasasho kasantuwar su da shi..
Nan da nan Mommy ta sunduma cikin soma shirin auren Abdurrahim da Kuraiba,
a gefe guda kuwa Umma Karima ma na nata shirin dan kuwa ta lashi takwabi sai kanwarta
Siyama ta auri Abdurrahim dan tanan ne kawai zata dad'a samin cikar burin ta.
bokan ta ya bata wasu lakanin suna nan suna ta aikin shaye-shaye da shafe-shafen magani.
Feeryal da Miemie ce zaune a cikin keb'ab'b'en gurin hutawa dake gefe da sashin Ammah,
wanda yake a matsayin mallakin sashin,
kamar yadda ko wani sashi na gidan yake da irin gurin.
an zagaye fulawowi kujeru na zagaye a cikin sa gurin hutawa ne na musamman da aka kawata shi da furanni.
Miemie ta bud'e baki da hanci tana kallon Siyama da ta do
shi hanyar part d'in Abdurrahim.
ganin yadda tayi da baki Feeryal ta saki murmushi mai sauti tana fad'in
"Meye hakan Miemie?."
Miemie ta yamutsa fuska tare da cewa
"Dubi waccan 'yar wahalar shegiya jibeta ba gaba ba baya ba nono ba d'uwawu,
gatanan tsanga
rgar tana tafiya tana wani karairaya jiki kamar an d'aurawa muciya zane,
me Ya Abdurrahim zaiyi da ita,
shi da ya yi rayuwa cikin turawa da larabawa,
har garama Kuraiba tana da d'an cika ita ma d'in dai ba wani fasalin kirki ne da ita ba,
Mommy ce kawai
ta masa dole sai ta had'a shi da 'yar kawar ta,
shiyasa Hajiya ma ta ce yaje can Yelwan Shendam ya nimi mata akwai kyawawan mata a gurin,
Mommy ce ta ki da Yelwa zamuje mu sha biki,
da kinje garin kakanmu kin gani garin fa akwai dad'i."
Da sauri Feeryal
ta waiga inda Miemie take nuna mata Siyama,
tana daf da shiga part d'in sa.
hab'a Feeryal ta rike ta ce
"Ke Miemie ki raba ni da niman magana ni dai bani da karfe idan ta jiki sai dai na gudu na barki."
"Wlh wannan had'eta zanye na kalmashe 'yar banza, ai
ke kin shiga uku da shegen tsoro ina abin jin tsoro a jikin waccan shamuwar mttss."
taja dogon tsaki.
Feeryal ta girgiza kai tana fad'in
"Ni dai babu ruwa na."
"Dalla ta shi mu je ki rakani na amshi book d'i na gurin Sumayya,
banson kayan haushin nan naki
."
Feeryal ta mike tana dariya.
Suka fito daga cikin gurin Miemie tana fad'in
"Book d'in nan shi ke tayani hira da daddare idan bamuyi waya da Murad ba,
Sumayya daga aro ta rike taki bani, kullum sai tace zata kawo min gara naje na amshi kayana,
yau Murad
ya yi tafiya book d'in ne zai taya ni hira."
"Wani irin book ne haka, mene ne a cikin sa?."
"Love story ne gobe zan baki ya kwana a gurin ki ko zaki shiga layi, dan naga ke sai an d'auraki a network kafin ki dawo saiti,
jiya ma da wani abokin Ya Faisal ya
ganki a sashin Ammah sai da ya tambaye ni ke,
kawai na watsar da lamarin ne dan nasan ke d'in sai a hankali."
baki Feeryal ta tab'e dan tana ganin soyayya duk shirme ne da kuma b'atawa kai lokaci.
Suna shiga cikin side d'in Mommy Feeryal ta tsaya a farfa
jiya bata yadda ta shiga ciki ba.
ta ce wa Miemie taje ta dawo tana jiran ta dan bata mance gargad'in Mommy kan shigo mata sashin ta ba.
Da sauri Ajmal ya turo karamar kofar da ke jikin get d'in side d'in ya shigo.
Feeryal ta waiga suka had'a ido ya sakar
mata murmushi.
itama takaitaccen murmushi ta mayar masa tare da sunkiyar da kanta.
ya karaso in da take yana fad'in
"A'a Feeryal ya kika tsaya a nan baki shiga ba."
"Miemie nake jira ta shiga yanzu zata fito mu tafi."
agogon hannunsa ya duba kana ya dube
ta ya ce
"Yauwa dan Allah shiga ki cewa Ameerah wai taje in ji Ya Abdurrahim,
sauri nake yi ana jira na a office."
da sauri ta d'ago suka had'a ido sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta,
jiki a sanyaye ta ja kafarta, da fargabar abin da zai biyo baya ida
n ta shiga, tana kuma jin nauyin ta ce masa bazata iya shiga ba.
Tayi taku d'aya zuwa uku ya kira sunan ta
"Feeryal."
cak ta ja ta tsaya tare da waigawa bata bari sun had'a ido ba kanta a kasa.
numfashi ya furzar kana ya ce
"Ina so muyi wata magana yaushe
kike da lokaci, nazo na same ki a side Aunty."
Shiru tayi tana wasa da bakin gyalen ta.
"Jeki sai na dawo."
ya fad'a tare da juyawa da sauri ya tafi.
Takai minti 5 tsaye a bakin kofar tana tunanin shiga daga bisani ta tura kofar ta shiga da sallama a ha
nkali.
Mommy ce zaune ita kad'ai a parlour tana ganin Feeryal ta ware ido.
"Ke me ya kawo ki nan?."
ta fad'a tana dad'a ware ido a kanta.
Feeryal taja ta tsaya jiki na kyarma.
"Ke kutumar uban ki nace uban me ya kawo ki sashin nan, au anturo ki ki barbad'a
wani barbad'en naku ne ko,
zo nan."
Mommy ta fad'a cikin tsawa.
Feeryal ta zabura ta shiga takowa in da take ta tsaya gefen ta.
tsawa takuma buga mata
"Miko min maganin da ta turo ki ki barbad'a min, ki koma ki ce mata malamin ta ya fad'i."
kai Feeryal ta
girgiza cike da tsoro ta ce
"Ba.ba..babu komai dama um Ya wannan ne um Ya wannan."
gaba d'aya ta mance sunan shi da taji Ajmal ya fad'a da kuma yadda Miemie take kiran sa da shi. sai fad'in Ya wannan ta ke.
Mommy ta ce
"Da kyau mana bakuyi sammanin asirin
ku zai tonu ba, dole ki rika kame-kame, hatsabibiya bakar ashana sai naci uwar ki a nan kafin naje na sami wacce ta turo kin."
"Abdurrahim."
taji an rad'a mata a kunnen ta, ido ta rumtse ta had'iye miyau da kyar, muryar Chuchu tajiyo a kunnen ta tana rad'
a mata sunan nashi, kana ta bud'e ido da sauri ta ce
"Ya Abdurrahim ne ya ke kiran Ameerah."
kirji Mommy ta buga ta ce
"Waye yayan naki nashiga uku!
to bari kiji in gaya miki kar ki sake nasake jin kin dangana min d'a da yayanki dan shi ba yayun aljanu ban
e,
kar ki sake nasake jin kin kira min d'a da yaya shi ba yayanki bane,
kije can ki nimi yayan ki, kul nasake jin kin kira shi da yaya sai na dirza bakinki ya yi jini,
wuce ki bani guri shegiya mayyar aljana."
Su Miemie da suke d'aki da su Ameerah har su
na rige-rigen fitowa suga wacce Mommy take wa bala'i.
Miemie ta tsaya sororo tagama mancewa tare suke da ita tana jiranta a waje.
jiki na b'ari Feeryal ta nufi kofa sakamakon kuma buga mata tsawa da Mommy tayi, gaba d'aya ta birkice har tana karo.
Sumayya
tayi saurin cewa
"Gurin Miemie kika zo gata nan fa."
bata ko waiga ba tuni tayi waje jiki na rawa Feeryal bakaramin tsoron tsawa da fad'a take ba nan da nan yake birkitata ta fice hayyacin ta.
Ameerah ta buga dogon tsaki
"Mssttt na rantse na tsani yarinya
r nan bansan me yasa Daddy yaki koran ta ba."
Miemie ta bita da sauri Feeryal bata tsaya ba sai da ta fice a farfajiyar side d'in gaba d'aya.
ta tsaya tana maida numfashi kamar wacce tayi tsere.
Miemie ta karaso da sauri murya a raunace ta na fad'in
"Yi h
akuri Feeryal kin gaji da jirana ne kika shigo ko, ai dama tafiya kikayi abinki baki shiga musu side ba bare ayi miki rashin mutunci,
wlh na mance kina jirana kiyi hakuri dan Allah."
Feeryal ta maida hawayen da suka ciko mata ido sannan ta ce
"Ya Ajmal ne
ya ce naje na kira Ameerah wai wannan na kiran ta, shine fa na je."
"Waye wannan kuma Feeryal?."
"Um wai waye sunan shi ma wannan babban yayannan naku mana wai waye ma sunan shi, am Sahab."
"Sahab kuma bamu da wani yaya mai suna Sahab, Ya Abdurrahim ke na
n ."
"Eh shi, mamansa ta ce kar na sake ce masa yaya shi ba yayana bane,
dama nima ban san shi ba."
da sauri Miemie ta ruko hannun ta ta ce
"Kibar maganar taho muje kiyi hakuri kinji."
ta janyo ta suka yi gaba.
Shirye shiryen bikin Abdurrahim da Kuraiba
yana dad'a kankama, musamman a gurin iyayen su mata Mommy da kuma Hajiya Luba, a d'ya gefen har da Alhaji Jibiril wato mahaifin Kuraiba,
dan yana matukar farin cikin had'a zuri'a da baban family sanannen family irin family'n A.A FIYA.
Daddy ya ba Mommy is
asshan kud'en da zai isa yin lefe,
a b'angaren sa baya nuna farin ciki ko akasin sa game da auren.
da farko shima yaso d'an nasa yaje gida can Yelwan Shendam ya nimi mata, amma da Mommy ta buga kasa ta kekashe ita tayi masa mata sai ya kyale ta, tun da ita
uwa ce ita ma tana da hakki a kan sa,
sannan kuma ya d'an yaba da gidan da matar ta fito.
Dubai Mommy ta tafi suka had'e da Hajiyan Dubai bayan sun had'a akwatuna set biyu suka wuce Egypt suka had'a set uku kafin ta biyo girgi da kayan ta dawo.
sashin Ha
jiya aka jibge kayan, 'yan'uwa da abokan arziki ana ta zuwa gani, anata yaba kyau da tarin yawa da tsada irin na kayan.
Feeryal da ta fito daga bathroom d'aure da towel, ta isa gaban wardrobe da sauri ta bud'e gefen da su pant da pat d'in ta suke.
ido ta
d'an waro tuno da pat d'in ta ya kare ga period d'in ta ya zo.
dafe goshi tayi tana fad'in
"Wayyo na mance ashe ya kare."
sai kuma ta rufe wardrobe d'in tayi waje tana fad'in
"Ammie Ammie."
a sakiyar parlour suka had'e da Aunty da kiran nata yasata fitowa
daga kitchen.
"Ya akayi ne Feeryal mene ne da irin wannan kiran?."
baki ta turo tare da langwab'ar da kai cikin muryar shagwab'a ta ce
"Ammie pat d'ina ya kare."
ido Aunty ta waro gaba d'aya ta mance da tame d'in period d'in ta ya yi, dan ko wani tame ta
na zuwa duba pant da pat nata,
tagama mancewa da wancan watan pat d'in zai kare bazai kai wannan watan ba.
ta ce
"Subhanallah na gama mantawa ne amma bari Baba Rabi yanzu ta fita taje ta siyo miki, jira yanzu za'a kawo miki."
Aunty ta juya da sauri ta koma
kitchen in da suke aiki da Baba Rabi.
ita kuma ta juya ta koma d'aki.
Ta kasa zama sai sintirin shiga bayi take tana wanke shi da ruwa,
sam bata son jini ya b'ata mata jiki ko kad'an,
a rana takanyi amfani da pat kusan goma dan duk san da zataje fisari
to fa sai ta canza pat.
gaba d'aya ta damu tana jin ta kamar a kan kaya take,
da sauri ta d'au hijabi ta zura kan towel d'in jikin ta,
ta fita da sauri ta nufi sashin su Miemie.
A parlour ta tadda Ammah ita da Faisal.
ta gaishesu tare da tambayar Ammah Mie
mie,
Ammah ta ce
"Tana sashin Hajiya."
"Wayyo Allah."
ta fad'a a kasan ranta a fili kuwa cewa ta yi
"Ammah bari na d'auki abu a d'akin Miemie."
Ammah ta yi murmushi tana cewa
"Ke da d'akin ku har sai kin fad'a zaki shige shi."
itama murmushi tayi.
Faisal
kuwa cewa ya yi
"Kar dai Miemie ta koya miki halin gulmar nan nata."
nan ma murmushi tayi ta wuce d'akin.
wardrobe d'in ta ta bud'e ta bincika ko zataga pat tagama dube-duben ta bata gani ba,
abin haushin ma ga wayar ta a kan gado bata tafi da shi ba bare
ta karb'i wayar Ammah ta kirata da shi tun da itama bata fito da wayar ta ba.
kamar zatayi kuka ta fito.
Amma ta ce
"Kin sami abin ko ta canza masa gurin ajiya, kin san halin ta da iya b'oye abu kamar me."
d'an jim tayi tana jin nauyin ta ce ga abin da ta
ke nima ga Faisal a gurin, sai kuma ta girgiza kai ta ce
"Zanje na dawo kafin ta dawo."
Ammah ta ce
"Ko zakije ki kirata acan tazo ta baki, Miemie idan ta sami hira ba dawowan yanzu ba, bare anje ganin kayan lefe."
Feeryal tayi shiru bata isa taje sashin H
ajiya ba kam.
maganar Amma ta kuma ji
"Kije ki kirata Miemie fa bazata dawo yanzu ba."
a hankali ta juya ta fita, kamar kwai ya fashe mata a ciki a haka ta isa kofar Hajiya.
ganin tsayuwa bazai ficceta ba