Showing 12001 words to 15000 words out of 70713 words
wani bata lokaci,
ya ce yana zuwa yau gobe babansa zaizo."
kafin Fee
ryal tabata amsa Aunty tafito.
Miemie ta ce
"Yauwa Aunty dama wanine sunansa Ibrahim muka had'u da shi agun bikinan ya ce yana son Feeryal,
abokin yayan Feenat ne ya ce zaizo yau gobe kuma yaturo magabatansa anemamasa izini gurin daddy."
Aunty taware i
do ta ce
"Badai shine kuka hadu da shi ya yi mata rashin d'a'ar nan ba?."
Miemie ta ce
"A'a wlh Aunty bashi bane wannan mutumin kirkine kuma yana sonta,
abokin yayan Feenat ne ma har Mom d'in sa ya nuna mata Feeryal."
Aunty tad'anyi shiru sannan ta ce
"Amma dai yafara neman Daddy'n tukunna, in ya amince sai ya zo."
Miemie ta ce
"Ya ce zai turo babansa gobe yau zaizone kawai ya tambaye ta da kansa idan ta ce ya tura sai ya tura."
Aunty tace Allah yakaimu.
Dayamma wajen karfe 4:40 saiga kiran Ibrahim
awayan miemie yazo yana bakin gate.
Miemie tazo tasa security suka bud'e masa gate takaishi bakin sashin Aunty.
ita tashiga ta kirawo Feeryal, dakyar Feeryal tafita sai da Aunty ta ce mata taje tadawo karta dad'e.
tafito da babban hijabi tunkafin takaras
o inda yake,
ya kafe ta da ido yana fadin
"Masha'allah wallahi kamar da hijab d'inma kinfi kyau."
Feeryal takaraso a hankali ta d'an tsaya gefe da shi ta ce masa
"Inayini."
wani murmushi ya sake idanunsa a kanta.
Miemie ta ce bari tad'an basu guri tayi
falon Aunty tazauna.
Feeryal natsaye Ibrahim nata zayyane mata kalan son da yake mata shifa nan da wata d'aya yakeso ya aureta.
Feeryal dai batace kalaba sai hijabin dataja tarufe gefen fuskarta.
yaleko fuskarta yana fadin
"Bud'e mana inata magana bakic
e komiba,
kitsaramana yadda zamu gudanar da shagalin bikinmu."
jan hijabin tadayi tana murmushi tarufe fuskarta sosai.
salati sukaji abayansu ana tafa hannu.
"Innalillahi wa innailaihirraji'un! lallai kun shahara wato iskancin naki harcikin gida,
abin n
aki ya girmama har maza kika fara kawo mana su cikin gida kuna sheke ayarku,
iskancin naku har gida!."
Umma karima tayi maganar cike da hayagaga takawo hannu tad'aura abaki tana tana fad'in
"Yihuhu jama'a kuzo nakamasu, na kamasa da idona."
Ibrahim yatsa
ya yanamata kallon mamaki,
Feeryal ko gaba d'aya jikin ta ya d'au kyarma........!
KUYI HAKURI DAN ALLAH BANI DA BAKIN DA ZAN IYA BAKU HAKURI WLH SAM BANSO HAKAN TA FARU BA AKASI AKE TA SAMU KWANA BIYU,
DA DAREN NAN NASAMU NAYI WANNAN KUYI HAKURI DA SH
I DAN ALLAH
*Assalamualaikum barkanmu da wannan lokaci barkanmu da dawowa hutun Ramadan anyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ya karbi ibadun mu*
Ibrahim ya bita da kallo ganin kiri-kiri da gaske sharri take son gina musu,
ya ce
"Me kike nufi ne
wai? muna tsaye muna hira ki ce kin kama mu, kin kamamu muna me?."
da karfi ta ce
"Iskanci iskanci na kama ku da idanun nan nawa kiri-kiri ka shige cikin hijabi kana kwakularta,
munafukan Allah ta'ala asirinku ya tonu.
jama'a kuzo na kama 'yan'iska."
kan
kace me ma'aikatan da suke aiki a babban kichin sun taho gurin.
Umma Karima bata fasa kwalala ba fad'i ta ke
"Na kamasu wlh na gansu da ido na, ya makale cikin hijabin ta suna aikata masha'ar su.
Mommy da Mom akusan tare suka iso gurin 'ya'yan su sun kaimu
su rahoto.
sai tafa hannu suke da sallalami.
Ammah da mai aikin ta ta sanar mata da abin da ke faruwa ta fito abujajan.
Ibrahim na tsaye ya cika da mamaki matuka.
Mom ta rike hab'a tana sallalami, da fad'in
"Ai dama akwan a tashi in dai halin mutum ne sai
asirinsa ya tonu,
a had'asu da karnuka da security su rakasu da duka 'yan'iska tambad'ad'd'u, zaku kawo mana iskanci har cikin gida."
cewar Mom tana aika wa Ibrahim da Feeryal banzan kallo.
Ammah data karaso gurin tayi saurin cewa
"A'a baza'ayi haka ba z
o ka wuce katafi abinka kaji bawan Allah."
Mommy ta ce
"Kamar ya zakice ya tafi Hajiya Safiyyah ai yazama dole su karb'i hukun ci dukkan su shi da wacce ta jajub'o sa."
Ammah ta girgiza kai ta ce
"Ashsha ai ni banga shaidar da ke nuni da abin da ake zargi
ba,
mutum d'aya bai wadatar da bada shaida kan zina ba,
a cikin ku akwai wannda ta gani da idon ta bayan Hajiya Karima?."
Ammah tayi tambayar tana tsaresu da ido.
duk ma'aikatan suka girgiza kai, Ammah ta ce
"To kaje abin ka kaji,
dan kuma Hajiya Halima d
a Hajiya Nafisat kusan a tare muka iso nan da su,
babu wanda acinin mu zai bada shaidar abin da ake zargi, dan ita zargin zina sai ana da kwararan shaidu guda uku wad'an da suka gani da ido."
Ibrahim yaja kafarsa yana girgiza kai yama kasa iya cewa komai,
tsabar mamakin matar,
ya shige motarsa ya bar gidan baya ko ganin gabansa.
Gaba d'aya gurin ya kacame da hayani Mommy da Umma Karima da Mom, sai bala'i suke suna fad'in
yarinyar da kowa yasan ita 'yar'iska ce a filin Allah cikin bainin jama'a take iskanc
i, har ana d'aukarta hoto da video waye bai san 'yar iska bace.
Aciki kuwa TV da yake a kunne ne ya hana Aunty da Miemie jin abinda yake faruwa da wuri,
sai da hayaniyar ya kara yawa kafin suka jiyo hayaniyar sosai.
da sauri suka nufo waje.
Aunty ta tsay
a cike da mamaki tana jin abinda yake faruwa cikin b'acin rai sosai ta dubi Feeryal dake tsaye ta toshe bakin ta da hijabi tana hawaye ta ce
"Ke Feeryal da gaske kin aikata abin da suke fad'a?."
da sauri ta girgiza kai murya na rawa hawaye na zuba ta ce
"A
'a Ammie."
hannun Feeryal Aunty ta janyo ta dawo da ita kusa da ita sannan ta dubi Umma Karima ta ce
"Hajiya Karima kin dai ji da kunnen ki ta ce bata aikata ba, to kuwa tabbas bata aikatan ba,
ki tsaya a matsayin ki kada ki sake shiga lamarin ta bai shaf
e ki ba."
"Iye lallai ma kuwa ba shakka! irin ga waliyyiyar nan wacce bata fad'an karya daga ta fad'i magana gaskiya ce,
tana aikata iskanci kiri-kiri a kamata dan ta ce batayi ba shike nan ya zauna a kan bata yin ba."
Aunty tayi saurin katse ta
"Ni na yar
da da d'iyata idan da ta aikata nasan bazata tab'a yi min karya ba zata fad'a min,
dan haka bata aika ta ba,
kowa ya kama gabansa kubar min kofar side!."
Nan da nan ma'aikatan kowa ya kama gabansa.
Umma Karima tayi shewa tare da tafa hanu tana fad'in
"Ah
ayyeee rass. ke har kina da bakin fad'ar wannan maganar yarinyar da gata nan cikin hoto kiri-kiri tana rungume da wani katoton gardin d'an iska,
a cikin bainin nasi kowa ya gani babu wanda bai sani ba,
an dai ji kunya wlh, an aje katuwar 'yar'iska a gida a
na son ta b'ata mana yara"
Aunty ta yi saurin katse ta
"Ki iya bakin ki Hajiya Karima kar ki kuskura ki wuce gona da iri, zakiyi nadamar bakaken kalaman ki."
Mommy ta watsawa Aunty kallon banza tana cewa
"Bafa zai yuwu ba yazama dole ayi zama da Alhaji da
n wlh bazamu zauna da 'yar iska ta gurb'ata mana rayuwar 'ya'ya ba, Ameerah Sumayya wuce mujen ku bari Alhajin ya dawo."
Mom ma ta kad'aga keyar Sahla bayan ta gama fad'an miyagun maganganun ta.
Umma Karima ta dubi Aunty tana fad'in
"Hajiya Fatima alkadari
n ki na daf da karyewa, dan bazamu bar tsintacciyar agola cikin 'ya'yan gida ta koya musu iskanci ba, na fad'a na kara fad'a,
kiyi abin da zakiyi."
Siyama ta yamutsa fuska ganin kamar tana son yin magana Miemie ta dalla mata harara.
Umma Karima ta kad'a ke
yar nata iyalan
Bilkisu Rahma Saddiqa Nabila Siyama suna gaba tana bayan su.
Ammah tabi bayan su da kallo kana ta girgiza kai tana fad'in
"Agwagwa ke nan 'ya'yan ki nagaba kina baya, mugun abu yabi dare cikin duhu Allah shi kyauta,
kiyi hakuri Feeryal, Ha
jiya Fatima sai dai ayi ta hakuri dan wad'an nan mutanen halin su sai su."
Aunty ta ce "Mugun nufin su ya kare a kan su, insha'allah abin da suke son gani kuwa bazasu gani ba,
haka zasu kare da kai kawo."
ta ja hanun Feeryal suka shige ciki Miemie ta biyo
bayan su, Ammah kuma ta koma sashinta tana mai mamakin hali irin na Umma Karima da su Mommy masu shaidan zur.
Ibrahim a hargitse ya isa gida, yana dai-dai ta parking ya fita da sauri ya nufi sashin Mom d'in sa.
ganin yadda ya fad'o cikin parlour da sau
ri ta tare shi tana fad'in
"Son lafiya me ya faru mene ne!?."
a binka da d'an gatan da bai saba shiga damuwa ba ya labarta mata abinda ke faruwa cikin matukar damuwa.
Mom d'in sa ta waro ido ta ce
"Wlh karya ne bazai yiwuba dole a wanke zargin da aka maka
a gaban kotu, daga zuwa niman aure dan baza'a baka ba sai a bika da mummunar kazafi,
to wlh bazan lamunta ba sai mun d'au mataki."
ta d'aga waya ta kira lambar Dad d'in sa ta sanar masa abin da ke faruwa.
baya kasar amma yace sabo da faruwar haka zai dawo,
dan ya ce bazai lamunce wulakanci da tozarci kan d'ansa d'aya tilo ba.
amma da jin ko a wani gida lamarin ya faru ya ce
bazai dawo ba amma zai nimi Alhaji Abubakar d'in da kansa,
dan yana ganin mutuncinsa dan yasan shi mutum ne mai mutunci.
nan da nan y
a nimi Daddy a waya, Daddy yana hanyar dawowa gida daga office kiran Dad d'in Ibrahim ya shigo wayarsa.
Umma Karima najin shigowar Daddy, ta nufi sashin Mommy da sauri, tana shiga ta isketa a parlour tun kafin ta karaso take fad'in
"Hajiya Halima taso maz
a muje naji shigowar Alhaji kafin wancan makiran matar can tasa,
ta rigamu zuwa ta je ta kitsa masa makirci yahau ya zauna a kai,
gara a yi ta ta kare yau 'yar nan ta bar gidan nan,
badun Hajiya bata gari ba, ai da anyi ruwa an d'auke."
"Ai kuwa maza muje
dan ni tun da nake ban tab'a ganin makirarriya irin Hajiya Fatima ba,
tagama da Alhaji gaba d'aya wlh ji nake kamar ta mutu na huta."
"Hm kyale munafukar can taurin rai gare ta amma ajuri zuwa rafi saura kiris tulu ya tarwatse."
cewar Umma Karima tana jinj
ina kai.
suka fita suka nufi sashin Daddy.
Daddy na zaune a parlour'n sa dan da ya shigo a parlour ya zauna bai shige ciki ba.
har suka shigo suka sami guri suka sauna bai d'ago ba yana abinda yake yi.
suka had'a baki sukayi masa sannu da dawo wa, ya am
sa, batare da ya d'ago ba.
Umma Karima ta d'an tab'a Mommy tayi mata alamar ta fara magana.
Mommy ta gyara zama tare da fad'in
"Alhaji mun zo gurin ka ne, yanzu fisabilillahi Kai kaji ka amince 'ya'yan ka su zamo tambad'ad'd'u ta sanadiyyar 'yar da ba'a sa
n asalinta ba ma,
bafa zai yuwu ba yazama dole a kawo karshen lamarin,
iskancin yarinyar nan ya tashi a waje ya dawo har cikin gida kana sane kayi shiru,
bari Hajiya ta dawo dan wlh mu bazamu zuba ido muna gani tarika shigo mana da 'yan'iska cikin gida,
g
a 'ya'yan mu mata suna cikin gidan ba."
Umma Karima ta ce
"Ato gaya masa dai,
yarinya tasan ta rika kawo 'yan'iska cikin gida suna iskanci ai abin nata ya girmama ya kai makura,
da idanuna na gansu a tsaye a bakin get d'in sashin Hajiya Fatima, ya shige
cikin hijabinta suna shagalin su,
ni tun da nake ban tab'a ganin tambad'ad'd'iya irin aljanar yarinyar can ba."
Daddy ya d'ago yana dubansu rai b'ace,
ya nuna Umma Karima tare da fad'in
"Sai da nayi sammanin daga gurin ki maganar nan zai fito, da Alhaji
Shitu Abdu ya sanar min,
ke Hajiya Karima ki kiyaye ni wai me ke damun ki ne kam Hajiya Karima?
kin san waye Alhaji Shitu Abdu kuwa?
to bari kiji taken sa mai kud'in shari'a, ba'a tab'a takasa a share lafiya sai ya yi shari'a da koma waye,
me ya kaiki shig
a lamarin sa ina ruwanki;
badun yana ganin mutuncina ba da yanzu kinji sammaci daga kotu,
idan kiyi wa Fad'imatu kin share, ko ince ni tunda Feeryal a gurina take nine ubanta,
to Alhaji Shitu Abdu bazai jure tozarta masa d'a ba,
ki dawo hankalin ki nagaya
miki ke nan!."
Daddy ya mike rai b'ace ya kwashi wayoyin sa ya nufi bedroom yana cigaba da fad'a.
Umma Karima ta d'a murya ta nad'e taburman kunyarta da bori
"Eh da ma ai zaka ce haka tun da ni mai jinin kule ne, yazo ya yi sammaci na mana muzuba mugani
da ni da shi wazai fad'i a shari'ar,
in shi mai kud'in shari'a ne ni mai bakin kare kai ne,
haka kawai ga gaskiya muraran a nimi rufa gaskiya da bayan hanu."
ta mike fuu ta bar parlour'n.
ta bar Mommy nan zaune dan dama ita ce da Daddy.
Koda Umma Karima t
a fito zata koma sashin ta can ta hango,
motar Abdurrahim da shigowar sa ke nan yana kokarin gyara parking a babban parking lot.
ta karaso, dai-dai sanda ya fito daga motar ya maida marfin motar ya rufe,
waya na rike a hannunsa yana kokarin tura kira.
ta c
e
"Sannu da dawowa Abdurrahim ya aikin dai."
"Alhamdulillah."
ya fad'a a takai ce yana kokarin barin gurin.
Umma Karima tayi saurin fad'in
"Da ma yanzu nake shirin kiranka idan na koma ciki,
na ce da kai idan ka dawo kazo ina niman ka."
bai yi magana ba
sai kiran da ya katse yana son jin abin da ke tafe da ita.
ganin hakan ya sata fad'in
"Abdurrahim ace kana cikin gidan nan, abubuwa da yawa suna ta faruwa a matsayin ka na babba a gida, kana ji baka d'au wani mataki ba,
a kaf gidan nan fa daga alhaji sai
kai,
ko kannensa Alhaji Sulaiman da alhaji Tukur sai dai su biyo bayan ka su jira umurnin ka,
dan kaine Alhaji karami.
amma ace sanannen gida kamar wannan a aje tukururuwar karuwa aciki tana d'ebo 'yan'iska tana shigo wa da su har cikin gidan nan,
ba'a tak
a mata burki ba;
ai ko dan gudun gurb'acewar kannen ka zakayi wani abu, kafin ta kai ga lalata musu rayuwarsu suma,
wannan yarinyar da Hajiya Fatima ta tsinto annoba ce a gidan nan,
sam ba yar arziki bace irin tambad'ad'd'un aljanun nan ne,
haka shekaran j
iyan can ta ja su Ameerah ta kaisu gurin party, haka ta tsaya a bainin nasi tana rungume rungume da maza,
ga video a wayan Ameerah kowa ya gani iskanci muraran,
yau har gida abokin iskancin nata ya biyo ta,
aka kamasu hanu da hanu,
haba ina amfanin sa abi
n nata ya yi yawa."
"To ni meye matsala ta da hakan Hajiya Karima?
ki sanarwa Aunty'n da ta kawo ta mana, inaga zai fi."
ya yi maganar yana picking na call d'in da ya shigo wayar sa,
ya kai wayar kunne ya fice a parking lot d'in.
Umma Karima ta bi bayan
sa da mugun kallo a fili ta ke fad'in
"Wannan d'an iskan yaro har gobe bazai canza halinsa ba,
in banda tsabar rashin daraja,
ni da na zauna shekara da shekaru da uban sa da Hajiya Karima ya ke kirana, sai wancan juyar yake kira da Aunty,
a sannu duk zaku
dawo karkashin ikona kai da uban naka."
tayi kwafa a fili, ta juya ta nufi b'angaren ta.
Har ya d'au hanyar sashin sa sai kuma ya juya ya nufi b'angaren Mommy.
a bakin kofar parlour ya tsaya, su Ameerah da Sumayya suna zaune cikin parlour'n ko wannen su d
a waya a hannunsa suna chatting.
suna ganin sa kowa ya shiga taitayin sa, duk suka aje wayoyon suka shiga gaishesa.
batare da ya amsa gaisuwar tasu ba ya dubi Ameerah fuska a murtuke ya ce
"D'auko wayar ki ki zo nan!."
da sauri ta mike ta d'au wayar ta tak
o gabansa kirjinta na dukan tara-tara
hannun ta na rawa ta mika masa.
ya amsa tare da kuma tamke fuska ya daddana zuwa can ya d'ago tare da nuna mata screen d'in wayar ya ce
"Uwar me kika ajiye sa kike yi da shi a wayar baki goge ba?."
da sauri tayi kasa d
a kanta tashiga kame-kame dan irin kallon da yake jifan ta da shi tasan babu ko shakka zata iya samin tsarabar duka.
da sauri ta ce
"Dama..dama.ban..bansan yana nan ba nayi zaton na goge tun ranar."
wani mugun kallo ya wurga mata ta kuma shiga taitayin ta
da kyau.
ya mai da idanunsa kan wayar kana ya d'ago ya ce
"Ina video yake?."
da sauri ta d'ago ya tsare ta da ido, baki na b'ari ta ce
"Babu wani video hoto ne kawai."
ganin yadda ya tsare ta da ido murya na rawa ta soma rantse-rantse
"Wlh Ya Abdurrahim iy
a hoto ne kawai na rantse da Allah babu video kuma ka duba ka gani ma."
bai kuma magana ba sai idon da ya tsare ta da shi.
cikin dakika guda ya karanto iya gaskiyar take gaya masa.
wayar ya wurga mata kad'an ya fad'i kasa tayi saurin taro sa,
ya nuna ta da
yatsa tare da kad'a yatsar yana mai taune gefen lips d'in sa alamun gargad'i,
kana ya juya ya fita.
Sumayya da ke zaune cikin ta ya d'ura ruwa.
tana ganin fitarsa ta mike da sauri ta na fad'in
"Ina ga irin ta ina kinga abinda