Showing 9001 words to 12000 words out of 70713 words

Chapter 4 - FEERYAL BOOK2 COMPLETE

/>
tagabatar da su, a gurin Mommy'n ta da kawayen ta.

atake a gurin wata ha

jiya ta ce tayi wa d'anta kamun Feeryal.

Daga can in da su Ameerah ke zaune suna kallon duk abin da ke faruwa,

sun cika sunyi tab kar Ameerah taji labari.

har sai da ta gaza b'oye kishin ta ta ce

"Lallai ma Feenat mu da muka zo kan lokaci ma bata gabatar

da mu ga kowa ba, sai masu zuwan kurarren lokaci su ake wani gabatar da su kamar wasu kwamishinoni, mttsss aikin banza,

ni yanzu ma zan tafi."

A d'an gefe da su Ameerah Feenat ta sama wa su Miemie gurin zama.

suna zama wasu maza guda biyu suka dumfaro in

da suke.

cikin kasa da murya Miemie ta ce

"Feeryal ga wasu gayu fa suna zuwa nan, kalli can yadda wasu gungun gayun ma ke kallonki,

gaskiya ke me sa'a ce,

dalla ki ware jiki kiyi abu kamar wayayyiya, sai wani shan jiki kike."

"Miemie nikam mu tafi."

tafad'

a tana sunkuyar dan tana d'agowa taga idon mutane a kanta.

"Sannunku 'yammata ko zaki samin number ki?."

d'aya daga cikin samarukan da suka iso gurin su ya fad'a yana mikawa Feeryal wayarsa.

Feeryal tayi shiru batayi magana ba.

Miemie ce ta karb'a ta saka

masa lambar ta mika masa.

ya amsa tare da fad'in "Thanks."

kana suka koma gurin zaman su.

Feenat ta kawo musu drinks da d'an abin motsa baki.

Miemie ce ta ci Feeryal kam ko drink bata iya sha ba, dan gaba d'aya a takure take idon jama'a ya takura mata.

a

nata gudanar da shagalin biki.

MC ya gayyato kannen ango zuwa fili.

Feenat ta ja su Miemie, Feeryal ta make kafad'a tace suje ita kam bazata iya ba.

duk yadda Miemie tayi ta tashi fir taki.

haka suka kyaleta suka je gurin su Ameerah.

Feenat ta ce

"Ameerah

Sahla Nabila Hafsat Lailat ku zo mu shiga fili ga MC na kiran mu."

duk suka mike ban da Ameerah da ta b'ata rai.

"Ameerah ta so mana."

cewar Feenat.

ta ce

"Kuje kawai bazan shiga ba."

bata kuma mata magana ba jin MC na ta nanata kannen ango su fito, suka g

arzaya cikin fili aka sakar musu kid'a suka sunkuya tika rawa.

Feeryal sai murmushi take sakewa idanunta akan su Miemie da suke ta cashewa.

bata yi aune ba taji saukar lips d'in mutum kan kumatun ta.

dai-dai lokacin kuma hasken camara ya haske su.

a razan

e ta juyo wanda jin hakan ya bada dama wajen dai-dai tar fuskarta da tashi, nan ma hasken camara takuma haska su.

a razane ta mike tsaye tana binsa da kallon tsoro.

shigo gayan murmushi ya mata tare da kashe mata ido ya ce

"Hi baby haupa."

yaja kujerar ya

zauna yana fad'in

"Zauna mana muyi hira, nifa sonki nake ko zamuje mu sha ice cream."

da sauri tayi baya dan ba karamin tsorata da shi tayi ba.

Ameerah ta mike tsaye tare da jefa wayar ta cikin jaka, da sauri ta shige cikin filin ta ja hannunsu Sahla da

Nabila, suka fito.

suka ce yaya dai Ameerah?.

ta ce

"Ku taho mu tafi gida yanzu fa karfe goma da rabi, kafin mu isa 11 ta wuce."

tayi gaba suka biyo ta a baya suka shige mota dama direba na zaune a ciki yana jiran su sukayi gida.

Feeryal na tsaye jikin ta

na b'ari shiko yana zaune idanunsa a kanta yana latsar lips d'in sa da kanne mata ido.

"Gashi kamar wayayyiya kina abu kamar na marasa waye wa, muje hotel ki tayani kwana duk abin da kike so zanyi miki, zan kuma sallame ki da 2 million,

idan baki aminta d

a ni ba zan iya using da condoms."

Jikin ta ya d'au b'ari tsoro yadad'a bayyana a gare ta.

maganar Miemie taji a bayan ta

"Feeryal wai rawan ne baki iya ba ko me."

da sauri ta waigo murya na rawa ta ce

"Miemie mu tafi gida."

mikewa ya yi yazaro kati ciki

n aljuhun sa ya aje sa kan table d'in gaban su ya ce

"Idan kin yanke kuhunci zaki iya nemana ta wannan katina ne, I'm waiting for you, kiyi shawari da kawar taki ina jiran ki ko yaushe."

ya juya ya bar gurin.

Miemie ta bi bayansa da kallo tana fad'in

"Wai

mene ne Feeryal?."

Feeryal tayi rau-rau da ido sai ga hawaye sharr, ta d'aura yatsar ta kan kumatun ta sannan ta ce

"Kiss yamin a nan sannan ya ce wai na bishi hotel."

ido Miemie ta waro ta ce

"Shine baki masa kaca-kaca ba kika tsaya kina masa kallon tsoro

,

d'an iska ina yashiga na tara masa jama'a anan awa d'an iska dukan tsiya."

"Miemie ki rabu da shi ni kam mu tafi gida kawai."

tayi maganar hawaye na ci gaba da zuba a idon ta.

"Dan Allah share hawayen ki kar kisa mutane su tsaya kallon mu, na gane shi ai

wlh sai na nemo shi,

tsaya Feenat ta zo tace mu jira ta."

Feeryal ta share hawayen ta da tafin hannunta.

Miemie sai masifa take tana d'urawa mutumin zagi.

sun b'ata lokaci a zaune kafin Feenat ta dawo gurin su.

lokacin karfe 11 saura minti 15.

suna fita

Ibrahim ya biyo su, nan suka kuma b'ata lokaci har 11 ta cika, kafin suka d'auko hanyar gida.

Su Ameerah kuwa karfe 10 da mintuna 50 dai-dai suka ido gida.

direba na gyara parking a babban parking lot suka fito.

suna tafe kowa zai wuce sashin su suka ha

ngi Abdurrahim zaune cikin wani kayataccen zagayayyen gurin da aka zagaye shi da fulawowu masu kyau da kawa,

sama d'an rumfar bukka ce mai zawaye da koyayen wuta, kasan rumfar kujeru ne.

gurin haske ne sosai kamar tsakiyar rana ba dare ba.

yana zaune lapto

p na gaban sa yana danne-danne a cikin sa.

"Kuzo nan."

yafad'a idanunsa akan laptop.

kallon junan su sukayi, kana suka janyo kafafunsu inda yake.

suka durkusa a gaban sa.

sunkai minti 5 bai ce da su komai ba kuma bai d'ago ya dube su ba, yana ta aikin lats

a laptop d'in sa.

Zuwa can ya soma magana

"Ina kuka fito har 11 na dare kuna waje?."

Suka had'a baki wajen fad'in

"Munje dinner yayan kawar mu ce."

sai a lokacin ya tsai da abin da yake ya d'ago ya dube su d'aya bayan d'aya sannan ya ce

"Da daddaren nan

sabo da rashin mafad'i ko me, ina Miemie ta ke?."

da sauri Ameerah ta ce

"Samarukansu ne suka d'auke su bamusan ina suka je ba."

"What! samarukansu ita da wa?."

ya furta yana duban su, abin ya bala'in bashi mamaki wai wad'an nan 'yan hanci wai su ke da sam

aruka.

ta ce

"Ita da Feeryal kuma da ganin su 'yan iska ne,

samarukan, sai da na ce su zo muje gida suka ki."

tana rufa baki motar su Miemie yana shigowa gidan.

duk suka bi motar da ido, su Nabila kirjinsu na dukan uku-uku Ameerah tayi karya ta janyo musu

.

ya yi shiru idanunsa akan laptop yana tuka maganar cikin ransa.

Kasancewar motar Ammah ce direban ya yi kokarin wucewa sashin ta da su.

da sauri Miemie data hango su Sahla durkushe a gaban yayan nasu ta ce

"Tsaya-tsaya mu sauka anan sai ka wuce,

Feerya

l sauko muje ga su Ameerah can gurin Ya Abdurrahim."

suka sauko jiki a sanyaye kar Feeryal uwar 'yan tsoro taji labari.

a hankali suka karaso suka sunkuya kamar yadda su Ameerah sukayi.

a fusace ya d'ago ya ce

"Miemie har kinyi girman da zakibi samari a m

ota!."

ido ta waro murya na rawa ta ce

"Wlh Ya Abdurrahim babu wanda muka bi direban Ammah ne ya kaimu kuma shi ya dawo da mu."

da sauri Ameerah ta ce

"Bayan muna ganin ku da su har wani ya yi wa Feeryal kiss, daga nan kuma kuka bisu kuka tafi."

da sauri y

a kuma d'ago kansa karaf suka had'a ido da Feeryal da tsoro ke kukarin tafiya da numfashin ta.

maganar Ameerah ce ya sashi mai da dubansa gareta

"Na rantse ya mata kiss a gaban jama'a ma kuwa, ai gasu nan."

ta mika masa wayar ta,

hoton Feeryal karara wani

yana mata kiss, ga d'ayan fuskarsu daf da juna har suna gogar fuskar juna.

Miemie ta marairaice murya ta ce

"Kai Ameerah kiji tsoron Allah a'ina akayi hakan."

a fusace yad'a go wayar ya nuno musu fuskar wayar.

Feeryal tayi wani irin zabura, jiki na kyarma

.........!

Mommyn Twins ce

Wani irin sarawa kanta ya yi da sai da ta kai hannu ta dafe kan, tana girgiza kan cike da matukar tsoro.

hanjin cikin Miemie ya kad'a.

cikin fusatacciyar murya ya nuna Feeryal da hanu ya ce

"Ke tashi kibar nan!."

ya fad'a c

ikin tsawar da sai da ta zabura ta zube kasa kana ta mike da gudu ta yi hanyar sashin Aunty.

b'acin rai karara ake hangowa kan fuskarsa, ya mike a zafafe tare da d'aukar belt dake ajiye a gefensa.

yashiga nad'e shi a hannunsa yana fad'in

"Wato kun zama 'ya

n'iska kamar ku d'in nan har kun iya biyewa sa maruka, yaushe ne aka haifeku!."

Ameerah ya damko yana cewa

"Wato ke har kin iya d'aukar hoto ana bad'a la, ga kinan 'yar iska ko."

yashiga shinfid'a mata belt tana ihu sai da ya mata taya-taya kafin ya sake t

a, ya bita da naushi,

tana tsalle tana sosa in da aka zuzzuba mata bulala.

su Sahla kam tuni suka fashe da kuka tun kafin a zo kansu.

ya cafko Nabila itama ya birkita ta da duka, yana sakin ta ta zube kasa tana kuka.

haka Sahla ma.

Miemie ce dukan karshe y

adda taga yake huci yana dad'a kyara rukon betl d'in tasan yau kam zataci uban ta,

ai kuwa dukanta yafi na kowa, sai da ya mata bulala ashirin da biyar kafin ya kyaleta.

sannan ya nuna su ya ce

"Daga yau wata ta sake sa kafa ta fita a gidan nan ta gani, ku

tashi ku bani guri a nan!."

da gudu ko wannen su ya yi hanyar sashinsu.

Ganin yadda Feeryal tashigo a firgice Aunty da tun d'azu hankalinta yake tashe ganin karfe goma yayi basu dawoba.

har 11 tarinka kiran wayar Feeryal d'in saijin ringing d'in sa a d'

akinta tayi.

wayar Miemie kuwa yana shiga ba'a dagawa.

tajawota dasauri tana dad'in

"Ke Feeryal lafiya meyasa baku dawo akan lokaci ba sai yanzu, meyasa kuka zauna meyafaru naganki Hak?."

Aunty tana maganan cikin tashin hankali.

Feeryal ta kankameta ta

na kuka bata b'oyemata komai ba tafad'a mata duk abin da ya faru.

Aunty taja Numfashi cike da fargaba tace

"Yanzu ina su Miemien suke, suna gurin yayansu kenan?."

Feeryal tace Eh.

Aunty tatsaya shiru kana taja hannunta suka shiga d'aki.

Tana fad'in

"S

hiyasa tunfarko banso tafiyan nan nakuba,

samari 'yan bana d'ayan nan basu da tabbas,

shiyasa kullum magana ta baiwuce ki kula ba,

Feeryal Allah ya yi miki baiwar zubin halittar da ba kasake za'a barki ki rika yawo ba,

fitar nan sam bana son shi sai ya zam

a dole."

Aunty ta rika fad'a Feeryal da har lokacin tsoro bai gama sake ta ba,

sai sharar kwalla take.

sai kuma Aunty ta shiga rarrashin ta,

kana ta taimaka mata ta cire kayan jikinta ta shiga bandaki tayi wanka tafito.

tagabarta da sallahn isha tasa kay

an bacci ta haye gado takwanta,

tare da sunkulewa guri guda tana rarraba ido cikin tsoro.

har lokacin Aunty nacikin d'a kin tasata tayi addu'ar bacci kafinnan tafita .

Takai zamani guda batayi bacci ba tana sake-sake a ranta sai chan bacci barawo ya sami

damar yin awon gaba da ita.

Nabila ta shige sashin su a guje tana mussuke jikin ta inda ta sha bulalu.

Umma Karima ta zabura da sauri tana fad'in

"Ke lafiya yaya haka?."

Nabila ta zube gefen ta tana cewa

"Ya Abdurrahim ne ya bige mu."

"Duka kuma a laifin

me?."

Umma Karima tayi tambayar tana yamutsa fuska.

Nabila ta gyara zama ta shiga fesa mata labarin abin da ya faru karya da gaskiya.

Umma Karima ta ware ido tare da buga kirji ta ce

"Ita da laifi ku da duka! jar'uba har ta iya tsotsar bakin namiji a cik

in bainin nasi,

baiyi kasa-kasa da ita ya farfasawa shegiya baki, muga bakin da zata tsotsi bakin wani namijin da shi ba,

ai wannan yarinyar tajima tana iskanci tun tana kankanuwar, tafiyarta Abujan da taje ma iskanci take acan ai munsan komai,

gashinan a

sirinta na kan tonuwa kad'an ma ke nan, in Allah ya yarda asirinta yarika tonuwa ke nan,

sai tabar gidan nan,

ai abin da yasa Abdurrahim ya koreta ba zai iya yiwa kazanta hukunci ba,

ai sai dai ku tsaftatattun kannen sa,

ta ya zaiyi yayiwa 'yar'iska hukunc

i, hukuncin ta ke nan kora gidan ma gaba d'aya zata bari,

yanzu kam alkadarin ki Fatima ya karye daga zaran Abdurrahim ya ce ta bar gidan nan dole zata bari,

hahahaha."

ta karasa maganar da shekewa da dariya tana tafa cinya.

Washegari kuwa Umma karima ha

r da kiran Ameerah ta zo ta nuna mata hoton.

Umma Karima ta rike baki ta ware ido kan wayar tana fad'in

"Tabd'i jam lallai yarinyar nan cikakkiyar 'yar'iska ce asirinta yarika tonuwa ke nan."

Sai da rana kafin Miemie tashigo sashin su Feeryal.

a falo ta

tadda Aunty da Feeryal d'in zaune,

ta zauna tare da gaida Aunty,

ta amsa tana cewa

"Kunyi rashin hankali Miemie da kukakai goma awajen taron nan,

watakilama shiyasa maza suka bibiyeku,

da kundawo kan lokaci da duk hakan bai faruba,

Allah dai yatsare yas

a yayanku baimuku komai ba dai?."

Miemie taja rigarta tagwada wa Aunty shatin bulala Aunty tawaro ido tace

"Subhanallah abin da ake guje muku ke nan Miemie yanzu ina amfanin sa, sam fitar dare ba na d'iya mace bace, Allah shikyauta gaskiya ku rika kiyayew

a."

Feeryal kaman zatayi kuka ganin shatin bulala a jikin Miemie.

ta ce "Wayyo sannu Miemie dan Allah kiyi hakuri ."

Miemie tayi kwafa ta ce

"Wallahi bazan kyale Ameerah ba,

ba ita ta iya munafurciba dukda tare aka bige mu."

Aunty ta ce

"Kiyi hakuri ka

r kice zakuyi fad'a da ita tunda itama anbigeta, ki rabu da ita kawai, ku dai kurika kiyaye abin da zai janyo muku laifi."

Miemie sai kwafa take tana cize lips.

Aunty tayi kitchen tana saka lamarin aranta sam bataji dad'i ba da Abdurrahim bai hadasu da Fe

eryal ya musu hukunci dukan su ba,

tun da in laifin ne tare sukayi,

ya ware kannensa kenan yamusu hukunci?.

ta girgiza kai kawai tana shigewa kitchen.

"Ke Ameerah kada kiyi gigin cewa zaki yad'a hoton nan a Media dan wlh idan kika kuskura Ya Abdurrahim

ya ci karo da shi sunan ki sorry, sai ya yi miki kabarin da ba sallah,

jiya ma ke nan ya yi miki dukan d'aukar hoton bare kuma kin yad'a shi wa duniya,

zai ce dama kin saba yad'a hotunan batsa wlh mukam babu ruwan mu."

cewar Sahla da suke tare da su Ameer

ah a parlour'n Mommy.

Nabila ta ce

"Gaskiya nima dai ban bada goyon baya ba, kibari Ameerah mu aje hoton nan zai zame mana makami nan gaba, ai shegiya banso Ya Abdurrahim ya barta ta ba, da ya mata shegin duka 'yar iska yanzu kam mun gama da ita babu wanda

zai zo gurin ta,

in yazo kuwa sai ya gani."

Sumayya ta rike hab'a ta ce

"Hm wlh Ameerah kibi ahankali ku rabu lafiya da Ya Abdurrahim,

ina dukan da ya miki akan d'aukar hoton ne shine zaki ce zaki yad'ashi wa duniya, idan fa kika kuma shiga hannunsa bazak

i ga da kyau ba."

Ameerah ta ja tsaki

"Mttss ai na rantse da Allah yadda aka bige ni sai an bige ta, wulakantaccen duka ma kuwa,

da wayarta zanyi sending hoton wa duniya kowa ma yagani ta yadda kowa zai d'auka ita d'in ce ke tallen kanta wa duniya."

Sumayy

a ta gorgiza kai ta ce

"Ameerah nadai gaya miki kibi a sannu, idan ta kwab'e miki bazakiga da kyau ba."

Ameerah ta mike tana hararar Sumayya ta wuce d'aki,

cike da shan alwashin sai ta aikata.

Bayan kwana uku da faruwar haka da sauri Miemie ta shigo sas

hin Auny.

A parlour ta tadda Feeryal ita kad'ai tana zaune tana kallo a TV.

Miemie ta zauna kusa da ita tabuge cinyar

ta tana fad'in

"ke Ibrahim yakirani fa tund'azu,

ya d'agamin hankali shiyasa ma nazo amma tun d'azu ina kwance ne banyi niyyar zuwa gu

rin ki ba,

tun da ke tsoro ya hanaki fitowa kizo in da nake, matsoraciya kawai,

sai aka ce miki kuma shi Ya Abdurrahim d'in duka yake haka kawai babu dalili,

kuma ma ai dukan da ya min ni nasan har da naki ya had'a dan duka na yafi na kowa tun da tare muke

da ke,

tare Ameerah ta kulla mana sharri."

Feeryal ta marairaice fuska batayi magana ba sai narai-narai da ido take suna kokarin kawo kwalla.

Miemie ta ce

"Bari na kirashi dan ya ce yayi ta kiran ki baki d'aga wayan sa, nace kad'an daga aikin ki."

tana

kokarin kiranshi Feeryal ta ce

"Ni dai Miemie da kin barshi to mezanmishi."

Miemie ta ce

"Ke dallah wannan had'add'an gayen,

kuma yace zai zo na ce wallahi yazo."

Feeryal taware ido ta ce

"Wallahi babu ruwana Miemie yazo ina baburuwana."

Miemie ta ce



"Ke wlh dad'ina dake tsoro, da har dake aka buga

ranar da ban san ya zakiyi ba nasan har fitsari sai kinyi tsabar tsoro,

ke wallahi Ibrahim dagaske yakeyi ya ce aure yake son yi babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login