Showing 6001 words to 9000 words out of 70713 words

Chapter 3 - FEERYAL BOOK2 COMPLETE

haka yananan a sashin Hajiya Halima;

jeki can in baki sameshiba ki garzaya sashinsa basaina gayamikiba ko me zakiyi kinsa meyakamata kiyi,

d'an

ta zai shigo hannun mu reshe zai juya da mujiya."

Siyama tashige sashin mummy da sallama tana wani kararraya tazauna akan kujera inda ta taddasu Ameerah da Sumayya tagaida,

mummy data fito daga bedroom d'in ta.

Sumayya ta bita da kallo tana fad'in

"Ir

in wannan kwalliya haka Aunty Siyama, ina zuwa haka?."

"Kai Sumayya sai kace bana kwalli, babu inda zani."

Sumayya ta yi dariya ta ce

"Ai kwalliyar tayi kama da ta zuwa party ce."

Ameerah ta kallete ta da wutsiyar ido,

ta yamutsa fuska ta cigaba da dannan

wayarta.

Siyama ta ce

"Wai Ameerah ba magana ne?."

Ameerah ta d'an d'ago ta ce

"Sorry hankali na na wani wajen."

Siyama tayi shiru da bakin ta dan ta san halin Ameerah sarai bata kyale kowa ba.

ta gyara zaman ta

tana d'an satan kallon gun bata dai ganshiba

.

zuwa can ta mike ta fita.

Tana sako kanta zata fice daga parlour Mommy sukayi kicub'us da shi yana kokarin shigowa.

ta wani sake jiki tana wani yauki, ta narke murya

"Barka da warhaka yallab'oi, ina yini."

"Lafiya."

ya amsa a takaice

ko in da take bai k

allaba ya rab'a gefen ta ya shige cikin parlour.

wani irin lumshe idanu tayi tare da jan numfashi ta na shakar daddad'an kamshin sa.

da sauri ta bud'e idanunta, ta taune baki tana dana sanin da ta fito da ta cigaba da zama har ya shigo.

da sauri ta juyo ta

koma ciki a zaune ta ganshi gefen Mommy.

ta zo ta gaban shi ta wuce tans kad'a mazaunan ta,

ta zauna kusa da Sumayya kujeran da ke fuskantar sa,

Sumayya ta ce

"Aunty Siyama baki tafi ba ashe."

ta d'an saci kallon in da yake fatanta ya d'ago su had'a ido,

shiko baima san tana yi ba idonsa akan waya.

ta ce

"Am Sumayya dama aron wayarki zaki bani nakira tawa bansan ina na jefa ta."

Ameerah ta kalleta tana mara baki ta lura da satar kallon da take wa yayan nasu.

"Yar wahala."

ta fad'a a kasan ranta.

Sumayya

ta ce

"Ina ma wayar tawa take."

ta waiga gefe da gefen ta

"Yauwa ga shi can."

ta nuna kujerar da Abdurrahim ke zaune gefen sa wayar take,

shigowar sa Sumayya ta tashi a kujerar ta bashi gurin zama kusa da Mommy.

Sumayya na kokarin mikewa ta d'auko mata,

tarigata mikewa.

ta isa gurin ta kai hannu kamar zata d'au ka sai ta tura wayar ya da d'a matswa jikin sa.

ta saka hanu ta gogi jikin sa.

da sauri ya d'ago suka had'a ido, tawani narke murya

"Oh yihakuri waya zan d'auka."

gajeren tsaki yaja ya maida idanun

sa kan waya.

da sauri ta juya cike da farincin burin ta ya cika, tad'an lallasa wayar kana ta mikawa Sumayyar wayarta ta ce

"Naji muryar Nabila wayar tana hannunta."

ta juya da sauri ta fita cike da farin ciki.

Tana komawa sashin su ta rungume Umma Karima

tana fad'in

"Aunty Karima ya ganni na ganshi."

Umma Karima tayi makirin dariya ta ce

"An gama 'yar gari, kwantar da hankalin ki kin sami Abdurrahim a tafin hannunki."

suka wani kwashe da dariya suka tafa.

Mommy ta dubi Abdurrahim da tun shigowar sa daya

gaisheta bai kuma magana ba, sai aikin danna wayarsa ya ke.

ta ce

"Kaje kun gaisa da Kuraiba'n kuwa?."

"Mommy abani breakfast."

ido ta bisa da shi sarai tasan so yake ya kawar da maganar nata.

ta ce "Ameerah je kice Shatu ta had'o masa breakfast."

"No ki

barshi."

yafad'a tare da mike wa tsaye.

Mommy ta ce

"Ai nasan dama ba ci zakayi ba shiyasa ma ban sa an kaimaka ba,

ina tayi maka magar yarinyar nan baka cewa komai."

"Banje ba."

ya fad'a a takaice

Mommy ta ce

"Amma ai yakamata ace kaje, ko da sau d'aya n

e ku gana, kafin akai sadaki."

ya zura takalman sa baiyi magana ba yafice.

Sashin Aunty ya nufa dan yasan can ne kawai zai sami abincin da zaici cikin kwanciyar hankali.

da sallama ya shigo Aunty na kokarin shiga kichin.

ta dakata ya karaso suka gaisa,

y

anayin sa ya tabbatar mata da abinda ya kawo shi,

dan tasan gadon Daddy ne ajikin sa,

shima baya cin abincin masu aiki.

Aunty tayi murmushi ta ce

"Abdurrahim ka isa dinnin bari na kawo maka breakfast."

ta wuce kichin shi kuma ya kara dinnin ya zauna kan

d'aya daga cikin kujerun dinning d'in.

ta had'o masa breakfast mai rai da lafiya ta kawo masa.

kana ta koma kichin tacigaba da ayyukan ta.

Feeryal ce kwance ke baccin ta cikin kwanciyar hankali,

kiran wayar ta dake karkashin pillow da take kai yata da i

ta.

mika tayi had'e da salati ta zura hannun ta karkashin pillow ta janyo wayar, batare da ta duba mai kiran nata ba ta kai wayar kunne idanunta a lumshe cikin muryar bacci ta ce

"Hello."

numfashi ya sauke mai sauti ya ce

"Har na cire rai da picking call d

'ina, Feeryal me yasa bakya d'aga wayata?

i miss you Feeryal ko sau d'aya ki bani dama mana,

hope kina lafiya."

shiru tayi batayi magana ba, amma ta gane mai muryar.

Major Sadam ya rumtse idanunsa yana jin sonta na zaga jini da jijiyar sa ya ce

"Please Ba

by let me know kina sona."

nan ma shiru tayi wayar tana kunnen ta.

"Feeryal." ya kira sunan ta.

a hankali ta maida idanunta ta lumshe tana saurarar sa, nanma shiru batayi magana ba.

"Kinyi min izini anjima na kira ki bayan kin gama bacci?."

a hankali ta bu

d'e idanunta cikin tsiririyar muryar ta ta ce

"Eh."

cikin matukar jin dad'in amsashi da tayi ya ce

"Yes! thank you bye."

Ta sauke wayar a kunnen ta, ta mike zaune tare da yin hamma,

har yanzu bacci ne cike tam a idanunta,

sai dai tana jin yunwa dan daren

jiya bata ci ba ta kwanta.

ta kalli agogo karfe 11 har da rabi.

ta zame blanket d'in da ke rufe a jikin ta.

ta zamo bakin gado ta mike ta nufi kofa ta fito,

daga ita sai riga da wandon bacci pink masu samtsi.

Tun daga bakin kofa ta ke fad'in

"Ammie yunwa

Ammie yunwa nake ji."

a tsakir parlour ta tsaya tayi wani dogon mika mai had'e da hamma ta saki hannayen ta sharaf tana b'ata fuska ta cuno d'an karamin bakinta gaba cikin muryar shagwab'a tashiga bubbuga kafa a kasa wan da ilahirin jikin ta matsawa suke

tana fad'in

"Ammieeeee ina cake d'ina."

ta nufi dinnin tana cigaba da kiran Ammien nata.

Aunty ta fito daga kichin da sauri ganin ta nufi dinning tana mussuke ido da hannayen ta bata ma kallon gaban ta.

Aunty ta ce

"Ke Feeryal."

cak ta tsaya bata kai ga ka

rasawa dinning d'in ba.

ta juyo tana tura baki da fad'in

"Ammie yunwa nake ji."

"Maza je ki canza kayan jikin ki sai kiyi wanka kizo."

ta juya tana yarfe hannu cike da shagwab'a ta koma d'aki.

A hankali ya tura plt d'in abincin ya mike, Aunty da ta fito d

aga kichin rike da wani had'ad'd'en kula, perpesun naman kaza ne dayaji kayan had'i na musamman acikin kular.

ta ce "Har ka gama ne Abdurrahim?."

ya ce

"Eh nagama Aunty."

"Dama na karo maka wannan ne to gashi ka tafi da shi."

ta mika masa kular ya amsa tar

e da fad'in

"Nagode."

tayi murmushi, shiko ya juya ya fita.....!

Mommyn Twins ce



Da sauri Miemie ta shigo d'akin Feeryal ta isketa kwance tana aikin ta na buga game a waya.

ta hayo gadon tana fad'in

"Yanzu dama wayar nan tana hannun ki nake ta kira ba

ki d'aga ba."

fuska ta marairaice ta ce

"Ayya Miemie wayar a nan na barta yanzu na shigo na d'auka."

"Shine kin ga kira bazaki bi kiran ba."

"Ai missed call d'in da yawa shine kawai ni ban duba ba."

"To Allah ya shirye ki watarana sai arziki ya kira ki ki

n ki d'agawa ya wuce ki."

dariya Feeryal ta yi ta ce

"Yi hakuri to, ya akayi?."

"Tun d'azu nake ta kiran ki nace miki ki shirya anjima zamuje, dinner yayar kawar mu, Safeenat Sa'id."

"Ke da su wa da su Ameerah wai? ni kam bazanje ba kuje abin ku, kitaho mi

n da tsaraba."

Miemie ta harare ta ta ce

"Ke kenan idan akace aje guri kice bazakije ba, kullum kina kunshe a gida a d'aki,

ina ruwan ki da su Ameerah a kansu zaki zauna,

yarinya tayi miki ne nagaya miki karki kuskura ki kyale ta,

barina naje na fad'awa Au

nty mun tabayi Daddy ya ce muje, idan ta ce kije kuma sai kin je."

ta zamo a gadon da sauri tayi d'akin Aunty.

Jim kad'an ta dawo ta ce

"To wlh Aunty ta ce muje, bari ma na ciro miki kayan da zaki sa kifara shiri kafin nima naje na shirya,

8 za'a fara a t

ashi 11 bikine na kowa da kowa bawai zallan 'yammata ba har da iyaye."

ido Feeryal ta ware ta ce

"Wai da ma da daddre ne bikin ma?."

"E mana kin ga yanzu za'ayi magariba ki tashi ki fara shiri, wannan kayan zaki saka."

ta aje mata wani dogon rigan dokakkiy

ar les, had'e da gyale da takalmin da zasu hau da kayan.

Miemie bata tafi ba sai da ta ga ta shige wanka.

Tana fita ta gabatar da sallar magariba da aka rigada aka kira.

kana ta zauna zaman shafa mai.

Aunty ta turo kofa ta shigo, ta karaso cikin d'akin ta

na fad'in

"Har yanzu baki gama shirin ba."

fuska ta marairai ce ta ce

"Nayi wanka fa Ammie kaya zan sa."

Aunty ta d'aga kayan da Miemie ta ciro mata dasu aje a bakin gado ta dube ta ta ce

"Ya banga bra a cikin kayan ba."

"Ammieee jiya fa nasa."

"Dan jiya a

nsa sai yau kuma baza a sa ba, oh ni naga ikon Allah,

laifin Maryam ce."

wayarta ta d'aga ta lalub'o lambar Maryam tana d'agawa ta ce

"Ya miki kyau Maryam da kika kasa gwada mata aibun rashin sa bra."

"Ayya Aunty Faty wai kullum sai an d'aura laifin a kai

na, kullum fa laifi na kike gani."

"Ai bazan fasa ganin laifin ki ba har sai randa ta koyi sawa da kanta batare da an ce tasa ba."

Aunty ta kashe wayar tana cewa

"Kullum bra ya kasan ce a jikin ki kwanciya ce kawai zaki cire sa."

baki ta turo tana marairai

ce fuska cike da shagwab'a.

Aunty ta ciro mata underwear da pant da bra.

ta ce

"Taso maza ki saka."

tana tsaye ta saka ta tayata ta karasa shirin.

da kanta tayi mata d'aurin d'an kwalli,

Feeryal na zaune gaban mirror Aunty tad'au sarkar da 'yan kunne na g

old ta saka mata,

man lips kad'ai ta saka ko pauda babu a fuskarta.

amma kyawunta ya dad'a bayyana a gareta ya d'are wacce akayi awa 3 ana mata makeup.

Aunty ta tsaya tana kare mata kallo sai fad'in

"Tabarakallah masha'allah."

ta ke.

ta mika mata gyale ta

yafa, ta gyara mata zaman gyalen, kana ta miko mata takalmin da Miemie ta d'auko mata, baya da tudu sosai ta zura a kyawawan fararen kafafunta.

ta fesa mata turare masu sanyin kamshi.

Aunty ta dubeta cike da farinciki ta ce

"Miqe na ganki d'iyar albarka."

ta miqe tsaye tana dariya.

Aunty tayi mata hoto da wayarta tana ta yaba kyawun ta.

Miemie ta shigo da sauri tana fad'in

"Allah dai yasa kin gama Feeryal."

ido Miemie ta waro ta ja ta tsaya tana kare mata kallo baki bud'e.

ta ce

"Kin ganki kuwa kamar ke ce

amaryar."

Feeryal ta saki sassanyar murmurshi.

Miemie ta janyo hannunta ta ce

"Taho mu tafi mu ake jira.

"Miemie kada ku wuce karfe 10, ko ba'a tashiba ku dawo gida, kuma ku kula sosai dan Allah kada ku biyewa samaruka marasa d'a'an nan,

wai tukun na ma da

gaske Daddy shi ya ce kuje."

cewar Aunty tana tsare Miemie da ido.

Miemie ta ce

"Allah Aunty shi ya ce muje tun da safe muka tambaye shi, ai ya ce ma zai je gurin d'aurin auren d'azu bayan sallar azahar wai Abba'n Feenat ya gayyace sa."

Aunty ta jijjiga

kai dan tasan Alhaji Sa'id mahaifin Safeenat, da suke kira da Feenat suna d'an huld'a da Daddy.

ta ce "To shike nan sai kun dawo ku kula sosai dan Allah a fita kuma da addu'a."

suka ce to.

Suna fita suka hangi su Ameerah a jikin mota, da wasu kawayen su b

iyo.

Sahla ta tab'a Ameerah ta ce

"Kalli can ki ga wacce Miemie ta d'au ko."

Nabila ta ce

"Kan uba wa zata bi, lallai ma Miemie nan shine har da wani gayyato ta."

Ameerah ko tun kafin su karasu take aika musu harara.

kawayen nasu kuwa baki suka bud'e suna

kallon Feeryal tare da fad'in

"Wow."

Ameerah ta dad'a b'ata rai har suka karaso in da suke.

ta ja dogon tsaki ta harari Feeryal sama da kasa sannan ta ce

"Ke Miemie wai ya za'ayi ki d'auko wannan kice zata bimu."

"Ina ruwan ki akan ki zata tafi."

cewar

Miemie tana yi mata kallon sama da kasa.

Ameerah ta wani dalla musu harara ta ce

"To wlh ba a motar mu ba, ki dai san motar da zaki sata."

Nabila ta ce

"Gaya mata dai dan wannan motar ubanmu ne ya siya ba uban wata ba."

Miemie ta ce

"Ina dai babu wacce ta

siyi motar a cikin ku,

to ai alhamdulillahi sai ku bari sai ko wacce acikin ku ta siya da kud'in ta kafin tayi gadara da shi,

na rantse dan dai kawai motar nan bazata d'auke mu bane dukan mu da wlh in mutuwa zakuyi sai ta shiga,

mttss zo muje Feeryal direb

an Ammah ya kaimu, daga nan ku had'iye motar a cikin ku,

in kuma ba haka ba to wlh duk randa fita ta kama mu sai ta shiga, in zaku mutu sai dai ku mutu."

taja Feeryal sukayi sashin Ammah.

Ameerah ta ce da kawayen nasu

"Dalla kuzo mu tafi muna b'ata lokaci

n mu anan."

Hafsat d'aya daga cikin kawayen nasu ta ce

"Haba da kun bari ta shiga nan ai, ni wlh tagama tafiya da ni kamar na kwana ina kallon ta,

sai kace ba 'yar'uwar ku ba kuke hantarar ta haka."

Ameerah ta yamutsa fuska ta ce

"Wa wannan aljanar babu ab

in da ya had'a mu da ita, 'yar tsintuwa ce ba dangin mu ba."

"Ko ni ma tayi min kyau bari mu isa muyi musanyar number na sata a friend list d'ina, wannan ka shiga da ita cikin kawaye ai girmanka sai ya karu."

cewar d'aya kawar tasu Laila.

bakin ciki kamar

ya kashe Ameerah anyi abin da ta tsana wato yabon wata bayan ita,

sai taji ta dad'a tsanar Feeryal.

har suka isa tana jan tsaki da yin kwafa.

Motar su ta riga nasu Miemie isowa.

Feenat ta tare su da murna tana mu su oyoyo, ta jasu ta kai su gurin zaman da

ta tanadarmu su.

ta cike su da kayan motsa baki

Zaman su da kamar 20min motar su Miemie ya iso. suna shigowa Hall d'in kallo ya dawo kansu.

Feenat ta mike da gudu tazo ta rungume su,

Feenat dama ita tasan Feeryal sau biyu suna had'uwa da ita idan tazo gu

rin su Miemie.

ta ce

"Kai Feeryal gaskiya naji dad'i ganin ki taho muje ku gaisa da su Mommy da ango da amarya.

taja hannun Feeryal Miemie ta biyo su tana cewa

"Au ita kad'ai ma kakaji dad'in zuwan ta to mu bari mu koma."

sukayi dariya.

dai dai sanda suka

karaso zasu ratsa ta tsakiyar filin.

MC ya canza wata zazzafar waka,

bai sai kaji gurin ya amsa da hele ba.

ya yin da camara ya saito su yana ta kashe musu hotuna masu d'aukar video suma suna yi.

Feeryal kunya kamar ta nitse kasa, Miemie da Feenat kuwa sa

i wani fankama sukeyi.

suka janyota cikin takama, ita ko da kyar take iya d'aga kafarta har suka iso gurin zaman ango da amarya.

Feenat cikin rawar kafa ta ke fad'in

"Feeryal Miemie ga ango Ya Mujahid ga amaryar tamu Aunty Nuwaira,

Ya Mujahid kawaye na ne

wannan Feeryal wannan Miemie."

ta nuna ko wannen su.

Mujahid ya fad'ad'a murmushin sa ya ce

"Mun gode da ziyartar taya mu murna."

"Bayan naku sai namu da ita wlh ni naga mata."

maganar abokin ango ke nan Ibrahim daya taso daga gurin zaman sa.

yana d'aya d

aga cikin mazajen da suka kasa control d'in kansu da ganin ta har sai da ya iso gare ta.

Mujahid ya yi dariya ya ce

"Allah aboki na."

"Insha'allahu kuwa akwai Mom d'ina anan bari na kirata tazo shaida ga surukarta nan."

Feeryal dai kasa tayi da kanta.

suna

kokarin barin gurin suka jiyo magana a bayan su.

"Ina surukar tawa take, wacece haka ta birkita min lissafin my son?."

Feeryal takuma yin kasa da kai.

Mom in Ibrahim ta leko fuskarta tana fad'in

"Ah lallai ba shakka dole ka rud'e insha'allahu kuwa ka samo

mata, Feenat kawarki ce ko daga ina ta taho?."

kai Feenat ta gyad'a tana murmushi, ta ce

"Daga gidan Alhaji Abubakar Fiya."

"Masha'allah zamu dangana da gidan kuwa domin a bamu ita."

Ibrahim ya kankame hannun Mom d'in sa ya ce

"Mom dan Allah yau aje."

ta

dunguri goshin sa ta ce

"Ba yau ba kam sai gobe."

Feeryal kam takasa cewa komai kanta na kasa tana wasa da 'yan yatsunta su Miemie nata dariya.

Feenat ta ja su zuwa gurin su Mommyn ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login