Showing 39001 words to 42000 words out of 70713 words

Chapter 14 - FEERYAL BOOK2 COMPLETE

iya kyakkyawan motsi kafin ya kyale su, yana huci kamar kububuwa.

Feeryal da kyar ta mike a galabaice ta rakub'e gefe tana kankame jikin ta da kare in da suka yayyaga kayan ta, da hannunta.

tana jan shashshekar wahala.

duk fuskanta ya y

i ja tsabar kuka.

jikin ta ya yi taya-taya duk in da suka karceta garin kokuwar tub'e ta duk ya yi ja, abin ka da farar mace.

Boturan rigar jikin sa ya b'alle ya zaro rigar a jikin sa ya rage daga shi sai dingilet.

ba tare da ya kalli inda take ba ya wurg

a mata rigar.

hannu na rawa ta d'au ka idanunta a kansa.

ya bata baya ya zaro wayarsa ya daddanna ya kara a kunnen sa.

a hankali ta saka rigar kan kayan ta da yake a yayyage,

bata saka boturan ba sai ta had'e shi ta rike da hannunta.

wayar sa ce tayi kara

ya yi picking call d'in ya kai wayar kunnen sa.

"Room 13."

ya fad'a tare da sauke wayar.

ba'ayi minti uku ba wasu maza uku suka shigo.

ya ce su kwashe su su tafi da su.

suka d'ago su suka kad'aya keyar su sukayi waje da su suka turasu cikin mota sukayi gab

a da su.

Ya taka zuwa bakin kofar room d'in ya d'au d'ankwali da gyalen ta ya wurga mata su batare da ya juyo ba ya ce

"Zaki cigaba da zama ne a gun?."

da sauri ta sauko a gadon ta biyo bayan sa tana saka gyalen a kanta ta ruko d'ankwalin a hannu, ka far

ta ba takalmi,

dan bata ma sann ta ina takalmin nata yake ba.

suna isa bakin get d'in hotel d'in.

ya bi masu gadin da mugun kallo tare da nuna musu yatsa yana girgiza shi alamun gargad'i.

ai da sauri suka sunkuyar da kawunan su.

Ya yi waje ta bisa da saur

i.

har in da ya faka motar sa, tsayuwa ya yi jikin motar yana waya.

taja ta tsaya gefe jiki a sanyaye.

wani uban ihu ta saka tayi tsalle ta matsa gefe tana yarfe hannu.

da sauri ya sauke wayar tare da juyowa yana kallon ta.

ta durkushe kasa ta rike kafarta

tana fad'in

"Wayyo kafata."

torch in wayarsa ya kunna ya d'an tako gurin.

wata katuwar bakar uwar kunama ya gani,

a dai-dai in da ta d'aga kafar nata.

ya sa kafa ya take ta da takalmin sa ya murkushe.

kana ya juya ya shige mota.

Feeryal na durkushe rike

da kafarta da ta ke jin tsananin zafi gami da rad'ad'i da da zugi.

nan da nan kafar ta had'a zufa shatin gurin da kunamar ya d'ane ta ya kunbura ya yi ja.

Hon ya danna yana hango ta ta jikin miron motar.

da kyar ta mike tana jan kafar ta yi kokarin bud'e

murfin baya taji sa a rufe. ta dawo gaba ta bud'e ta shiga.

tana zama ya figi motar.

Sai shashshaka take ja da yarfe hannu.

duk AC da ke cikin motar, bai hana gumi tsastsafo mata ba.

ta kasa zama sai juyi take kan sit.

shiko bai ko kalli in da take ba ida

nunsa a kan titi.

sai da sukayi tafiya mai nisa kafin ya gyara fakin gefen titi.

Ya mika hannu sit d'in baya ya d'auko jaka ya bud'e,

kayayyakin aikin asibiti ne da yawa ciki.

ya bincika ya zaro wasu allurai guda biyu,

ya had'a su a Syringe d'aya kana ya

d'an dube ta fuskarsa babu wasa

"Gyara."

ya fad'a a takaice.

sautin kukan ta ta kara, gani allura a hannun sa.

sai ta shiga girgiza kai murya na rawa take fad'in

"Dan Allah kayi hakuri kar ka min."

fuska yakuma gimtsewa ya ce

"Idan baki natsu ba sai na ca

ka miki shi a baki, gyara na ce."

ai da sauri ta kai hannu ta toshe bakin ta, tana binshi da kallon tsoro hawaye na fita a idanunta.

kai ya kawar da ga kallon da take masa.

ya mika hanu yaja rigar sa da yake jikin ta gefe, kana ya d'an ruko gefen rigarta t

a baya da zip d'in sa ke bud'e.

b'ari ta soma tana shirin cire hannunta a bakin ta.

"Idan baki tsaya ba irin su goma zan miki ta ko ina."

fuskanta ta kifa jikin glass d'in kofar motar murya na rawa ta ce

"Na tsaya Allah na tsaya."

kara ta kwalla jin ya nit

sa mata allurar ta saman pant d'in ta jikin ta na b'ari.

ya zaro allurar yana jan gajeren tsaki.

ya jefar da allurar gefen titi kana ya maida jakar baya, ya gyara zaman sa yaja motar sukayi gaba.

Ta d'ago fuskarta daga jikin glass ya yi dama-dama da haway

e da zufa har da hajina.

mintuna biyar baya ta shiga sauke numfashi da ajiyan zuciya a hankali.

a sannu tarika jin zugin yana raguwa gumin da yake karyo mata ma ya daina.

A bakin get d'in wani ramb'asheshen hotel ya yi hon aka bud'e yasa hancin motar ciki

.

yana gyara parking ya wurgo mata handkerchief kan kafarta.

ta d'auka a hankali ta kai shi fuskarta,

wani daddad'an kamshi ya bi hancinta ta share fuskarta.

ya bud'e motar ya fita kana ya zaga gefen da take ya bud'e ya yi mata alama da ta sauka.

a hankali

ta zuro kafafunta da babu takalmi, ta fito ya mai da murfin ya rufe.

kana ya juya ya yi gaba ba tare da ya mata magana ba.

ganin haka tayi saurin bin bayan sa.

suna shiga cikin had'ad'd'en hotel d'in aka mika masa key.

ya amsa ya yi gaba takuma biyo sa da

sauri, zuwa kofar da taga ya tsaya yana kokarin zura makullin ciki.

yana bud'e wa ya matsa gefe ya yi mata alamar da ta shi.

jiki a sanyaye ta shige, tana shiga ya janyo mata kofar, shi kuma ya juya.

Da sauri ta waigo tana duban kofar ganin ya rufo shi y

a juya.

d'an nummafashi ta sauke hankali ta karasa ciki,

ta zauna bakin lafiyayyen gadon room d'in da yake a gyare tsaf.

sai rarraba ido take.

Fitarsa da kamar minti 20 aka turo kofar, da sauri ta d'ago.

shi ta gani rike da laida mai d'an girma a hannunsa

, ta sunkiyar da kanta kasa tana wa 'yan yatsun ta.

ya tako zuwa in da take, ya aje laidar a gefen ta kana ya juya yakuma fita yana mai janyo mata kofar.

A hankali ta gyara zamanta ta janyo laidar ta bud'e.

ganin kaya ne ciki, a sannu ta cicciro su.

doguw

ar rigar abaya ne a cikin laidar sa,

da takalmi mara tudu sosai cikin kwalinsa.

sai pant da pat duk a laidodin su sai bra shima sabo guda d'aya, da underwear,

sai turare.

kai ta sunkuyar kamar wacce take gaban sa.

ta kai mintuna biyar kafin ta iya mikewa

ta d'au laidar ta shige toilet d'in room d'in.

a gyare tsaf ko ina kwalkwal.

ta aje laidar ta tub'e yagaggun kayan kijin ta.

sai sannan taga in da jini ya b'ata bayan rigar.

wani kunya ya kamata, sai mammakewa take kamar wanda ake ganin ta.

da sauri ta d'a

go rigar sa da ya bata ta rufe jikin ta, taga shi jinin bai tab'a ba.

sassanyar numfashi ta sauke.

da kyar ta karasa cire ragowar kayan jikin ta, bra da pant da pat d'in da ya karkace garin kokuwa har jini ya sami damar b'ata mata kaya.

kana tayi wanka da

sabon sabulun da tagani a toilet d'in cikin kwalinsa.

Kana ta d'au pat da pant da underwear duk ta saka.

ta d'au abayar ta saka batare da ta sa bra'n ba, dan dama ita ba ma'abociyar sa bra bace, na jikin ta ma dama yana ta damin ta.

kana tayi mayafi da d'

ankaalin abayan.

sannan ta feshe jikin ta da dadad'an turaren, tana yi tana lullumshe idanunta dan ba karamin dad'in kamshi ya yi mata ba.

duk kayan da ta cire ta had'a ta zuba su cikin dosbin da ta gani a cikin toilet d'in.

kana ta fito da sauran pant da

pat da bra'n da batasa d'in ba,

da kuma rigar sa.

a bakin gado ta zuba su tana zama akayi knocking jin shiru ba'a turo kofar ba ta ce a shigo.

wata ma'aikaciyar hotel ne ta shigo sanye da uniform irin na ma'aikatan hotel.

tana rike da katon tray ta karaso

tayi mata sannu sannan ta dire tray'n saman table, ta fita.

Ido ta zubawa tray'n kayan abincin yadda take jin kanta ma bata ko jin yunwa,

burinta yanzu ta ganta kusa da Ammie'n ta.

Ba'a jima ba ya shigo, ganin bata ci komai ba ya tab'e baki.

ta mike da

sauri gudun kada ya juya, gashi ya fi ta sauri bazaka fahimci saurin tafiyar sa ba sai idan kuna jerawa,

har da sassarfa sai da ta had'a d'azu kafin ta cim masa.

yadda ta miken ya baiwa jikin ta damar motsawa.

karaf idanun sa ya sauka a kanta.

da sauri ya

janye idanunsa tare da sauke shi kan gadon

"Wannan fa kin bar ma wa ko ma ki saka kafin ki fito."

ya yi maganar tare da juyawa ya fita.

a hankali tabi in da yake nunawa kan bra'n da bata sakaba.

ta kuma maida idanunta kan kirjinta

ido ta d'an waro ganin

gyalen abayar bai rufe mata kirjin duka ba,

ga kan ababen kirjin a tsaitsaye sunfi to sosai ana iya hango shatin kansu ta saman rigar.

taji matukar kunya sosai jiki a sanyaye ta d'au bra'n sai da ta koma toilet kafin ta saka ta fito.

ta kwashi sauran ka

yan ta zuba su cikin laida kana ta koma ta zauna.

Ganin shiru bata fito ba ya turo kofar, tana ganin shi ta mike da sauri ta zura takalmin wan da ya yi mata dai-dai kamar an gwada ta,tabi bayan sa.

Tun da suka shiga mota suka fara tafiya ko kyakkyar mots

i batayi ba har suka iso gida.

lokacin karfe 3 na dare.......!

17

Tun bayan wasewan 'yan kawo amarya amarya Kuraiba ta mike ta tub'e kayanta, ta fad'a bayi, ta kuma solle wanka,

ta saka wasu kaya da babu marabansu da babu, dan komai na jikin ta a na ga

ni.

ta shafa turaruka ta d'au ko jakar kayan matan ta, ta sha na sha ta cusa na cusawa, sannan ta haye gado.

tana zuba idon ganin angon nata, amma har d'aya tayi biyu ta wuce babu alamar sa.

tayi sintiri cikin d'akin har ta gaji ta kwanta, bacci ya d'auke

ta.

Tashin hankalin da Aunty ta shiga ba zai misaltuba.

Daddy yasa aka bincika gidan gaba d'aya babu ita.

bai masa ba ya zaga da kansa,

Mommy da Umma Karima suka rika mita, wai ya tada hankali akan wata da ita ba komai bace, wata kila ma tabi saurayi ne

dama ta saba.

Hajiya ko cewa tayi, yaje ya kwanta kar ya yadda ya tada hankalin sa har ciwon sa ya tashi a kanta, dan bata da asara

ita Hajiyar ce da da asara.

A daren Daddy ya baza jami'an tsaro.

dan su tunanin su mai tawagar d'aukar amarya ne ya turo mu

tanen sa suka d'auke ta.

a b'angaren Ammah ma ita da Miemie Abbie basuyi bacci ba, fargaba da tunanin halin da Feeryal d'in take ciki ya hanasu rumtsawa.

Abbie da Ammah suka sako Miemie gaba da wayarta da sukayi hoto da yarinyar da suka tafi da Feeryal.

s

ukaje sashin Aunty.

Daddy ya ce a daren nan kuwa zai bada binciken yarinyar, duk suka d'ungumo sukayi waje.

Abdurrahim na gyara parking Feeryal ta kai hannu tana kokarin bud'e motar

maganar sa ta jiyo

"Ina ke aljana ce me ya hana ki iya kare kanki?."

da

sauri ta waigo ya tsare ta da ido.

yana nad'e bandaji a hannunsa, daya d'an ji rauni garin dukan su, yana d'an fidda jini.

a hankali ta sunkiyar da kanta,

ta bud'e kofar ta fita.

ta na tsaye sai da yagama wayar da yake kafin ya fito, ya yi gaba ta bi bayan

sa.

gidan shiru babu motsin kowa sai security dake bakin get.

da sauri ta d'aga kafa ta biyo shi da sassarfa jin kukan magen Hajiya da ga sashin ta.

dai-dai san da su Daddy suke fitowa.

ganin su tare cikin hanzari suka nufo su.

Daddy yana fad'in

"Abdurrah

im tun d'azu da na neme ka security suka ce min ka fita,

nayi ta kiran ka in sanar maka abun da ke faruwa baka d'aga ba,

a ina ka samo ta."

Daddy ya yi maganar dai-dai san da suke karasowa.

Feeryal ta sa gudu ta rungume Aunty, tare da fashewa da kuka.

Aunt

y ta rungume ta gam-gam tana fad'in

"Feeryal ina kika shiga, nayi zaton wad'an can mutanen ne suka kuma d'auke ki,

mene ne me ya same ki!?."

Miemie ma ta rungume ta ta baya.

baki ya tab'e ganin yadda take wani kukan shagwab'a.

Ya cewa Daddy

"Wayar da kak

e kira tana gida ne Daddy da d'aya wayar na fita."

"Kai alhamdulillah duk hankalin mu ya tashi, mun d'auka mutanen nan ne suka kuma d'auke ta,

amma dai babu wata matsala ko, a ina suka tsaya ne haka ko can gidan surukanka ne aka wuce da su?

to kukan na men

e ne kuma Feeryal ai mun godewa Allah tun da abin da muke zato bai faruba."

kuma tab'e baki ya yi yana shirin barin gurin.

Da sauri Daddy ya ce

"Me ya same ka a hannu haka."

kowa ya maida hankalin sa kan sa, Feeryal ta saki Aunty ta tsaya itama ta kallon

sa,

jiki a sanyaye dan tasan garin ceton ta ne yaji ciwon.

"Ba wata matsala ba ce Daddy."

ya fad'a a takaice

Abbie ya ruko hannun nashi yana cewa

"Kamar jini ne ke fita babu wata matsala kace?."

"Eh ba komai Abbieh."

ya fad'a yana wuce wa ya nufi side d'

in sa.

Feeryal tabi bayan sa da kallo murya a sanyaye ta ke fad'in

"Ina ga garin dukan su ne yaji ciwo."

da sauri kowa ya dawo da hankalin sa kanta.

Daddy ya ce

"Garin dukan su wa?."

rau-rau tayi da ido sai ga hawaye sharr,

murya na rawa take fad'in

"Wasu

ne wasu ne."

sai kuma ta fashe da kuka.

da sauri Aunty ta ruko ta hankali tashe sai yanzu ta lura da kayan jikinta wasu ne daban ba ashobin bikin sa ba.

Aunty da hawaye ya fara zuba mata tashiga girgizata tana fad'in

"Feeryal su waye ne niman gudu da ke

sukayi, da niman yi miki fyad'e ko."

kai ta shiga gyad'awa hawaye na zuba.

Aunty ta kankame ta tana cewa

"Allah bazai tab'a baiwa masu mugun nufi a kan ki dama ba, tun kina karamar ki ake bibiyar son ganin an ruguza darajar ki,

Allah bazai basu sa'a ba."

"Insha'allahu kuwa."

cewar Ammah tana bubbuga kafad'ar ta.

Jikin kowa ya yi sanyi Daddy yabi bayan Abdurrahim da kallo da yake shigewa side d'in sa.

ya yi murmushi tare da girgiza kai

"Abdurrahim ke nan da zurfin ciki wato baya son fad'a gudun kada hanka

li ya tashi."

ya kuma girgiza kai, sannan ya ce kowa yaje ya kwanta ad'an tab'a bacci dan yanzu gari zai waye.

Su Abbieh sukayi musu sai da safe suka wuce sashinsu.

suma suka shige ciki.

Daddy ya wuce bedroom d'in Aunty.

in da Aunty ta ja Feeryal zuwa bed

room d'in ta, dan ta lura har yanzu akwai tsoro tare da ita ba lallai ne ta iya bacci ita kad'ai ba.

kamar yadda bata saba b'oyewa Ammie'n nata komai ba ta labarta mata duk abin da ya faru a daren.

Aunty ta ce sai an nemo yarinyar nan an hukuntata da bata

da kishin jinsinta tana d'iya mace.

Washegari a masallaci bayan an idar da sallah Daddy da Abbie suke tambayar Abdurrahim ya hanun nasa.

ya ce ba ko mai ya warke.

Daddy ya dube shi cikin kulawa ya ce

"Jinyar jiya a ce yau ya warke."

"Ba wata matsala ba ce

da sauki Daddy."

"Yauwa to dai da saukin zakace."

Daddy ya fad'a ya juya yana amsa gaisuwar da ma'aikatan gidan suke yi masa.

Dad daya zuba kunnuwan sa gurin su ya ce

"Wai rauni yaji a hannun nasa ne?."

Abbie ya ce

"Eh jiya ke nan da aka nimi yarinyar na

n Feeryal, ashe wasu 'yan iskan yara ne b'ata gari suka d'au ke ta,

garin kwato ta ne yaji raunin."

Dad ya kama baki yana cewa

"Amma dai ba kariya ba dai ko?."

Abbie ya ce

"Aa haba ba kariya bane d'an jin ciwo ne kawai."

"To Allah ya sauwaka."

cewar Dad ya

zame jiki ya yi cikin gida.

Daddy da Abbie suka fito da Abdurrahim suna takowa cikin gida, Daddy ya dube shi yana cewa

"Ya'yan su wane ne a garin nan, shin ka binciko iyayen su?."

"Ban kai ga sanin iyayen su ba amma yau zan sani, dan suna hannuna."

kai D

addy ya jinjina.

Abbie ya ce

"Ya kamata kam a binciko iyayen su dan sunyi rashin d'a a."

Yana shiga side d'in sa ya wuce bathroom ya wasa ruwa kana ya fito ya haye gado.

ba da jimawa ba bacci ya yi gaba da shi.

A b'angaren Kuraiba kuwa, tayi mamakin har

wayewan gari wajen karfe 10 batagan shi.

batayi zaton abun da ya yi mata tana gidan su haka zai mata idan ta shigo gidan sa ba.

tayi zaton zaiyi d'okin ta a matsinta na amarya da ko wani ango yake d'oki a daren farkon su.

bayan tayi wanka tayi kwalliya ta

fito, tana karewa kayataccen sashin nata kallo.

kana ta nufi kofar da take tunanin wata kila ya kasance d'akin sa.

tana tura kofar taga hanya ce ta bi hanyar ya kai ta har izuwa wani kayataccen parlour.

a hankali ta nufi stairs tana takawa har ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login