Showing 60001 words to 63000 words out of 70713 words
tawagar d'aukar amaryar nan ne ya tsaida batun tafiya makarantar ta,
sun ce babu
damuwa idan akayi auren sai ta cigaba da karatun ta,
sau biyu fa suna zuwa, ban da shi yaron da yazo yafi a kirga."
Aunty ta ce
"Hajja Umma da wurwuri haka bikin Maryam da saura wata d'aya, a dai bari idan aka yi natan sai ayi na Feeryal d'in daga baya,
n
i nafi so Feeryal ta kara girma tafi haka kafin tayi aure."
Hajja Umma ta ce
"Fatima a wannan hali da ake ciki na ko da yaushe samari suna kawo mata hari dan ma Allah yana ketar da ita, ai a aurar da ita shi yafi miki rufin asiri ke kan ki sai kin fi samin
kwanciyar hankali,
imma baza'a had'a bikin dana Maryam ba bayan bikin ayi natan kawai ya wuce,
tun da bikin Maryam d'in yazo daf, taje ta cigaba da karatun ta tana da aure ai yafi."
Aunty ta sauke numfashi tabbas idan ta aurar da ita zatafi samin nutsuwa
da kwanciyar hankali.
kullum tana cikin fargabar yawan kai mata hari da maza keyi.
ta ce
"To shike nan Hajja Umma zan fara samin Daddy da batun kafin Abban ya kirashi in yaso daga baya iyayen Sadam d'in suzo."
sukayi sallama ta kashe wayar.
Siyama bata da
wo gidan ba sai da yamma lis saurayin nata ya dawo da ita.
yana sauke ta a mota Saddiqa na fito wa.
ya zuge glass d'in motar suka had'a ido ya sakar mata murmushi, itama ta mayar masa.
ya leko yana fad'in
"Wannan fa naga kunyi kama da ita."
ya yi maganar y
ana maida kallon sa kan Siyama.
Siyama tawani narke murya tana yauki ta ce
"Saddiqa wai d'iyar Aunty ta ce, ai dole muyi kama."
Saddiqa ta karaso gurin ta dube shi da murmushi ta na cewa
"Inayini Uncle."
ido d'aya ya kashe mata sannan ya amsa gaisuwar nata
.
Siyama ta dube shi tana fad'in
"Baby sai yaushe?."
"In kin so ko anjima da daddare sai na dawo."
"Ah ka bari sai gobe."
"To Allah ya kai mu."
ya dubi Saddiqa ya ce
"To sai anjima 'yanmata."
hannu ta d'aga masa ta ce "Mu kwana lafiya."
ya ja motar sa ya y
i gaba, su kuma suka shige ciki Saddiqa tana cewa
"Aunty Simaya a ina kika samo wannan amma fa ya had'u."
Siyama ta washe baki ta ce
"Ba kad'an ba fa bamu jima da had'uwa da shi ba, kinga har maganar aure yake min,
amma duk had'uwar shi ai bai kai yayan ku
ba, badun ina da sammanin samun Abdurrahim ba da wannan zan aura."
Saddiqa tayi dariya suna shigewa parlour'n su.
Da daddare Siyama na kwance suna waya da saurayin nata, cikin hirar tasu yake tambayar ta ina mai kama da ita.
ta ce "Tana can d'akin ta."
y
a ce "Allah kuna kama fa sosai kyakkyawa kamar ki."
Siyama ta washe baki dajin dad'in an yabe ta an ce mata tana da kyau.
ta ce
"Ai haka kowa yake fad'a muna kama da ita, d'azu ai itama sai da ta tambaye ni wai a ina na samo had'ad'd'en gayen nan."
dariya
ya sake yana fad'in
"Au ki ce ita ma ta tambaye ni kamar yadda na tambaye ta yanzu."
"Eh wlh tayi maganar ka d'azu ma, ko na kaimata ku gaisa ne?."
"Aa ki barta dare ya yi kidai bani number ta ma gaisa ko ta Whatsapp ne, mai kama da baby na kyakkyawa."
Siy
ama tayi dariyar jin dad'i, ta ce
"Tom zan turo maka."
suna gama wayar ta tura mishi lambar Saddiqa.
Koda Aunty ta sami Daddy da batun da Hajja Umma tayi mata kan Major Sadam, yanzu ya matsa yana so inda so shine samu a had'a bikin su dana abokin sa Ins
pector Nasir.
Daddy ya yi shuru sannan ya ce ace
su dakata tukun ba yanzu ba...
Kullum Umma Karima a cikin tunani take na yadda zata bi ta idda samin nasara a karo na gaba ta ke.
har in tana bukatar samin nasara kuwa ya zama dole Feeryal tabar gidan,
ta
nan ne kad'ai idan tayi jifan ta zai fad'o kan wanda take so batare da an tsare shi ba.
sai dai wannan karo tana bukatar taimako dan ta lura a yanzu dole sai ta sami mai tallafa mata kafin ta idda kudirin ta.
da sauri ta mike ta d'au mayafi tayi sashin Mo
mmy.
a parlour ta tadda Mommy ita da su Ameerah.
Mommy na ganin ta tasan wani labarin ta kawo mata, ta jata sukayi cikin d'aki.
a bakin gado duk suka zauna, Mommy ta dubeta ta ce
"Ya dai Hajiya Karima akwai labari ke nan."
Umma Karima ta gyara zama cikin d
abara da kwarewa a iya makirci take fad'in
"Yanzu Hajiya Halima haka zamu zuba ido mucigaba da kallon matar nan,
da wannan aljanar ruwan da ta kawo mana ita gida, ta zame mana fitina alakakai,
to bari kiji ina mai maganin da na kawo shi rannan ya duba Alh
ajin nan,
ya ce yarinyar ba karamar matsafiya bace, aiki tayi da tsafin ta har ta kore shi a gidan,
yanzu haka ya ce idan bamusan yadda mukayi muka fitar da ita a cikin gidan nan ba,to wlh mu sai ta fidda mu kaf a kan 'ya'yan mu."
Mommy ta dafe kirji ta ce
"To yanzu meye mafita Hajiya Karima, wannan hasabibiyar yarinyar ya zamuyi da ita?."
"Mafita d'aya mud'agawa Alhaji hankali mu tada bori cikin gidan nan, mu zuga Hajiya musa ta tasa shi ya kore ta,
in ba haka ba fa ina mai tabbatar miki muzata kora cikin
gidan nan,
kuma duk shirin Hajiya Fatima ce makirarriya ta kwantar da kai ta had'a mu da gamasheka, tana sarar mu ta kasa."
Mommy ta ce
"Amma fa Hajiya Karima idan muka ce zamu d'aga hankali da yawa kinsan halin Alhaji karshe ya ce, zamuyi a bakin auren mu
,
ni kinsan fa saura biyu ne sakanin mu ya guntule d'ayan tuntuni,
gara ke ma bai tab'a yi mi ko d'aya ba,
ni ina ganin kawai mubi a sannu mu sami Hajiya mu tuna mata ai dama ya ce,
idan aka gama bincike ne akan wanda suka sace ta mai tawagar d'aukar amary
ar nan,
zata koma can Abuja, mu tuna mata da wannan batun dan naga kwana biyu tayi shiru, kuma nasan har da ciwon Alhajin ne ma yasa tayin shiru,
tun da ya sami sauki zance ya kare tasashi ya koreta ta koma can in da akayi gayyar ta."
Umma Karima ta d'any
i shiru bataso haka ba, taso Mommy ta d'auki zugarta kamar yanda kullum take sata akan keken b'era.
ta ce "To shikenan hakan ma za'a sami nasara, bari zan sami Hajiyar nasan yadda za'ayi."
nan ta cigaba da kisawa Mommy yadda zasuyi kafin ta koma sashin ta.
..
Shirye-shiryen bikin Maryam da Inspector Nasir yana ta matsowa,
duk abun da aka sawa rana komi daren dad'ewa zai iso.
ana saura sati d'aya bikin Aunty da Feeryal suna zaune a parlour kiran Maryam video call ya shigo wayar Aunty.
Aunty na d'agawa Marya
m ta turo baki tana fad'in
"Aunty Faty wai sai yaushe ne zaku zo ne kam, biki saura sati d'aya ai yau ya kamata kuzo."
Aunty ta ce
"To mara kunyar amarya mai kiran a zo bikin ta."
dariya duk sukayi Feeryal na dariya ta ce
"Aunty Maryam an gama d'inkamin a
shobe na kuwa?."
"Ke da Sadam yazo ya karb'i naki wai zai kai da kansa a d'inka miki,
jiya ma suna nan yayi ta kiran wayar ki baki d'aga ba."
shiru Feeryal tayi sarai taga kiran shi jiya, bata d'auka ba, yau da safe ma sai da ya mata missed call yakai biya
r bata d'aga ba.
maganar Maryam taji tana fad'in
"Ai bakiga d'inkin da yasa akayi miki ba ya nuna min hoton su a waya."
murmushi kawai tayi tana kwantar da kanta a kafad'ar Aunty.
Aunty ta bita da ido tana son karantar yanayin ta.
"Aunty Faty dan Allah ku
taso gobe."
Maryam tayi maganar tana marairaice murya.
Aunty ta ce
"Sai ana gobe d'aurin aure zan shigo, ni kad'ai Daddy ya ce zan zo banda Feeryal,
ya ce har yanzu ba'a gama bincike ba,
shigowarta Abuja yana da hasari yanzu."
da sauri Feeryal ta d'ago mu
rya kamar zatayi kuka ta ce
"Ayya Ammie ni dai zanje."
"Aa Feeryal ki bari tukun komai yagama dai-dai ta, idan natafi ana gobe kwana biyu kawai zanyi na dawo."
"Ayya yanzu Aunty Faty banda ita ke nan a zuwa, wlh ni har naji auren ma yafita min a rai."
Mary
am ta fad'a kamar itama zatayi kuka.
Aunty ta kashe wayar ganin duk suna son caza mata kwakwalwa.
Feeryal har da kuka ita ala dole sai ta bita.
da kyar Aunty tayi ta rarrashi har sai da Daddy ya shigo ya taya ta.
ya ce tayi hakuri itama zataje saura kiris
a kammala bincike...
Ana goge d'aurin auren kuwa, Aunty ta gama shirinta tsaf zatabi jirgin karfe 9 na safiya.
yau Feeryal ko baccin safiya bata koma ba, tana nan tana bori ita sai tabi Ammie'n ta.
tun a daren jiya Miemie tazo ta kwashi wasu kayan ta tana
ta murna dan a sashin su zata zauna kafin Aunty ta dawo.
ai kuwa da sassafe ta zo side d'in Aunty.
karfe 8 dai-dai Daddy ya ce Aunty ta fita direba ya kai ta saboda karfe 9 jirginsu zata d'aga.
a tare suka fito Feeryal kayan bacci ne a jikinta ta d'aura
hijabi iya gwuiwa a kan kayan baccin, tana tafiya tana sharar kwalla.
Miemie na d'auke da d'an madaidaicin akwatin Aunty.
a can tsakiyar farfajiyar gidan mota ke jiran ta.
Daddy na zaune a bayan motar Abdurrahim na tsaye a jikin kofar gefen da Daddy yake
.
tun kafin su karaso direba ya yi saurin bud'e wa Aunty d'aya gefen, suka karaso Aunty na kokarin shiga motar Feeryal ta saki kukan shagwab'a tana bubbuga kafa kasa tare da yarfe hannayen ta,
cikin muryar ta mai sanyi take fad'in
"Ammie ni dai zan biki."
Daddy ya ce
"Aa Feeryal ina mun gama wannan maganar tun jiya,
kiyi hakuri idan komai ya dai-dai zakije ai,
yanzu kam babu halin ki shiga Abuja gaskiya,
kiyi hakuri kinji."
bayan hannun ta takai tana share hawaye tana jan shashsheka, wasu hawayen suna zuba.
Ammah da ta karaso gurin yanzu tayi karamar dariya tana fad'in
"Aa Feeryal wai duk kukan rabuwa da Ammie'n naki ne haka, to ayi hakuri."
Ammah ta dubi Aunty ta ce
"Har kun fito ashe to Allah ya kiyaye hanya, a dawo lafiya."
Aunty ta amsa da amin-amin.
ka
na Ammah ta d'an rusuna ta gaida Daddy cikin girmamawa.
Aunty ta shige mota tana fad'in
"Yanmatan Ammie kwana uku fa kawai zanyi na dawo, a daina wannan kukan dan Allah."
Feeryal hanci takuma ja tana goge ido da bayan hannu.
direba ya yi wa motar ke Daddy
ya dubi Abdurrahim yana cewa
"Ka duba yuwuwar dacewar sayar masa da duka gonakin audugar 30 wad'an da ba'a sasu a jadawalin kai su company ba, na gaya masa kai ba manomi bane likita ne bansan me yasa yake son sako ka cikin lamarin ba,
ko da yake ya ce min
wai kafini sanin harkar noma, na ce wane kai tun kan a haife ka nake noma, in ya ce fed'e mutane a d'inke to na yadda."
murmushin gefen baki ya yi tare da rufe masa murfin gefen sa.
Aunty ta gyara zama tana fad'in
"Daddy ka had'a kanka da shi shifa d'an za
mani ne."
cikin yin kasa da murya Daddy ya ce
"To bayan ina da ke 'yar zamani ai nima nazama d'an zamanin ke nan."
murmushi ta yi shima ya mayar mata.
kana yacewa direba yaja su tafi, dan shi zai rakata airport d'in da kansa.
Feeryal takuma yin rau-rau da
ido sai ga hawaye sharr san da taga motar su Aunty yana shirin fita daga gidan.
Amma ta ce
"Taho muje Feeryal yi hakuri mana kinji, kin san matsalar da yasa baza'aje da ke ba, badun son kare ki daga 'yan ta'addan can ba ai da dake za'aje."
Ammah ta yi gab
a.
Miemie ta ruko hannunta ta ce
"Muje Feeryal."
a hankali ta soma d'aga kafarta tana waigen baya in da take hango fitar motar su Aunty.
gajeren tsaki yaja idanunsa a kan waya.
zura wayar dake rike a hannun nasa ya yi cikin aljuhun jallabiyar jikin sa.
ka
na ya zura hannayensa duka cikin aljuhun,
har suka zo daf da shi zasu gotashi Feeryal bata fasa waigen ba.
ya saka mata kafa ta fad'i tim a kasa.
kara ta sake tare da fad'in
"Wayyo Ammie na, wayyo kafata."
ta rike gwuiwa tana yarfe hannu kwalla na zuba.
da
sauri Miemie ta sunkuya tana yi mata sannu dan bata lura da abin da ke faruwa ba.
Ammah ta juyo da sauri ta dawo in da suke tana fad'in
"Sannu Feeryal fad'uwa kikayi ne garin yaya?."
shiko gefe yabi ya wuce cikin garden ya yi zamansa.
Ammah da Miemie suk
a tallafo ta suwa sashin su tana tafiya tana yarfe hannu...
Kwanan Aunty biyu a ran na uku ta juyo dan hankalin ta na gida gun Feeryal, duk da tasan Ammah zata kula mata da ita.
Siyama ce ta fito daga d'aki ta wuce dinning ta bud'e kular abinci zata d'i
ba.
da sauri ta toshe hancinta ta juya da gudu ta koma d'aki, ta wuce bayi tashiga kela amai.
Umma Karima da ke zaune a parlour ta bi bayanta da kallo.
zuwa can ta fito tana yamutsa fuska.
Umma Karima ta ce
"Ya dai Siyama me ya faru kamar amai naji kike yi
?."
fuska ta dad'a yamusawa ta ce
"Wannan matar Sukai na ce ta dai na cika wad'an na Spices d'in cikin abinci amma bataji ba, wari suke min da zaran na zo ci sai naji zuciya ta na shi."
ido Umma Karima ta ware ta ce
"Siyama kar dai zargina ya kasance gaski
ya, gaba d'aya yanayin ki ya koma irin na masu ciki,kwana biyun nan."
kame-kame ta shiga yi tana fad'in
"Ci..ci...ciki kuma Aunty Karima a'a kam ni kam bani da komai."
Umma Karima ta mike zumbur ta ce
"Haba Siyama nasan jiya fa nasan yau, to me zaki b'oye
min ma tukun,
wani irin hauka ne ya kaiki barin ciki ya shige ki, wannan d'an iskan dake zuwa babu dare babu narar nan shine ya miki ko?,
na shiga uku ni Karima zaki lika mana abun fad'a."
da sauri ta d'au wayarta ta kira lambar Family Dr su, yana d'agawa
ta ce
"Duk abin da kake kabari ka zo, ina niman ka."
ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya wlh bana ma garin nayi tafi sai jibi zan dawo."
Umma Karima ta kashe wayar da sauri bata jira ya gama maganar nashi ba.
ta ce
"D'auko mayafin ki da sauri kizo muje, yau cikin n
an bazai kwana a jikin ki ba,
kafin wani ya ankara an cire d'an banza,
ina zan iya ina fama da wani damuwar wani damuwar ya kuma kunno kai,
akwai wani arnen likita gurin shi yanzu zamuje yanzu ba sai anjima ba."
ta shige d'aki da sauri itama ta d'au mayaf
in ta suka fito.
tun kafin su karaso parking lot take kwad'awa direba kira, ta ce ya taho da makullin mota da sauri.
suka shige mota tayi masa kwatancen asibitin da zai kaisu,
wani private hospital ne.
suna isa ta janyo ta da sauri sukayi cikin asibitin.
bayan an bud'e musu Folder aka turasu ofishin likita.
suna zama Umma Karima ta soma kora masa bayani jiki na rawa, ta ce ko nawa ne ita zata biya bata so cikin ya kwana a jikin ta. ya caja su 500k batare da b'ata lokaci ba tayi masa transfer zuwa account d
'in sa.
kud'in suna shigo masa ya mike ya ce yana zuwa.
ya fita.
Abdurrahim na zaune cikin office d'in sa sako ya shigo wayar sa.
ko da ya d'auka ya bud'e, hoton Umma Karima da Siyama ya gani.
yana kokarin aje wayar kira ya shigo.
sunan Dr L-cana ya bayya
n a screen d'in wayarsa.
kamar bazai d'aga ba har wayar takusa yankewa kafin ya d'aga.
daga cikin wayar Dr L-cana ya ce
"Hello AA How far, how you are there."
ya ce "Fine."
Dr L-cana cikin harshen sa da bai gama sayawa ba ya ce
"Wannan kamar matar Daddy'n
ka ne na gane fuskarta, d'ayan ce dai ban gane ta ba sai dai naga sunyi kama ko daughter ta ce,
abortion suka zo ayi wa yarinyar,
nayi wani tunani nace bari na sanar maka,
kar azo a sami damuwa, shin nayi mata?."
a zafafe ya ce
"Then, So what! meye nawa d
a zaka kirani kana gaya min, It is not my.concerned, I don't have problem,
damuwar su ce wannan,
so please Don't call me again;
ko ma meye ku kara ta."
ya kashe wayarsa yana jan dogon tsaki.........!
Mommy'n Twins ce
Ganin ya kashe wayar Dr L-cana y
a d'aga kafad'a tun da ya yi ko oho da maganar shiko yana ganin kud'i bazai barsu ba, komai ya faru ma daga baya ne.
ya koma ciki yasata ta tube ta haye gado.
ya had'o kayan aikin sa batare da b'ata lokaci ba ya burge cikin. ya bata magunguna suka nufo gid
a.
suna isa gida Umma Karima ta jata d'aki ta sunkiya mata bala'i.
"So kike ki samu a bakin mutanen gidan nan, badun na ankara da wuri ba ai da zance ya kwab'e,
idan mutane suka sani har ya shiga kunnen Abdurrahim ai shike nan kuma, sai mun nimi yadda zamu
yi mu rufa bakin sa,
kar ki kara irin wannan ganganci;
ki cigaba da shan magani ki warke ko su Bilkisu kar ki bari su gane