Showing 15001 words to 18000 words out of 70713 words
nake guje miki,
hoto kawai k
ika d'auka a kaci ubanki da duka ina kuma ga kin yad'ashi wa media,
ai wlh da baki da wata mafita gun Ya Abdurrahim zai ce dama aikin ki ke nan, yad'a hotunan bad'ala;
Allah ya taimake ki."
Ameerah ta dalla mata harara tana cewa
"Ke nifa bana son munafurci
ina ruwan ki, ai na rantse bazan kyale yarinyar nan ba sai nasa an mata dukan tsiya shegiya mai idon mayu,
ai tun da aka bige ni a kan laifin ta wlh itama sai ta sha duka."
"To Allah ya taimake ki Ameerah ni dai in zaki bi ta tawa da kinyi hakuri kawai."
"Anki a bi takin Sumayya ke nifa bana son shishigi."
Sumayya ta juya ta nufi bedroom d'in su tana fad'in
"Kar ki fasa Ameerah."
cikin d'aga murya Ameerah ta ce
"Ai dama bazan fasa ba, na rantse sai ta duku."
Sumayya bata kuma bi ta kanta ba ta shige bedroo
m abinta dan tasan halin ta sarai yanzu sai ta huce fushin goge hoton da yayan nasu ya yi a kanta.
Hajiya bata nan taje ta'aziyya a yelwa, sai da tayi kwana uku kafin ta dawo,
tun bata hutaba labari ya isar mata.
ta ce wa Ajmal da ya shigo yi mata sannu
da dawowa ya kira mata Daddy.
shiko ya mike ya nufi kofar fita yana fad'in
"Kijira ya dawo mana."
"Kai Ajimi iya shege zaka kawo min, ka kira min uban ka ka ce na jira shi, gaka min iya shegen banza,
ban san me Abubakar yake nufi ba,
daga ce ta d'an zauna
na wani lokaci kafin a gama bincike,
shike nan sai ta shari gindi ta zauna har malikiyaumiddini, to bari ya dawo ya same ni zaman nata ya isa haka ta kara gaba,
nagaji da gayyar tsiya arna gun idi."
Da daddre Daddy da ya shigo gaishe ta ko zama baiyi ba
ta taresa da maganar.
ta ce gobe gobe yasata a mota ta koma inda ta fito.
da kyar Daddy ya samu ya lallab'a ta ya ce saura kiris a gama binciken ana gamawa zata koma, Hajiya ta rika bala'i haka dai ya tashi ya barta
★★★
Yau Feeryal tun da yamma take sid
e d'in su Miemie,
har bayan sallar isha, tun kan magriba taso komawa b'angaren su Miemie ta ki barinta.
har dai da sukayi sallar isha kafin suka fito ta rako ta.
suna tafe suna d'an hirar su, suka taho ta kofar b'angaren su Ajmal.
Zaraddin da tun fito wars
u a kan idon sa yana hango su ta saman bene, kafin su karaso ya yi saurin sauko wa.
suna isowa ya fito yana wage baki.
Miemie ta ce
"La Ya Zaraddin ashe kana nan, kwna biyu ina ka shiga ne bana ganin ka."
kirjinsa ya shafa yana bin Feeryal da wani irin ma
yataccen kallo ya ce
"Tafiya nayi d'azu na dawo."
murmushi Feeryal tayi tana janye idanunta daga kallon da ya ke mata cikin siririyar muryarta mai kama da mai yin shagwab'a ta ce
"Sannu da dawowa Ya Zaraddin ka dawo lafiya."
wani irin lumshe ido ya yi ya w
ani rungume hannunsa a kirjinsa da ke ji ina ma ace ta fad'o cikin sa,
komai na yarinyar ya had'u babu makusa ko kad'an.
ya karkace kai yana cigaba da aika mata irin kallon nan nasa sannan ya ce
"Daku na fara had'uwa da na shigo ku yakamata ku fara kunce j
aka ku kwashi tsaraba,
musamman ke da kikayi min barka da dawowa lafiya."
ya yi maganar idanunsa akan Feeryal.
"Oh lallai ma Ya Zaraddin d'in nan amma ai ni na fara tambayar ka banganka ba kwana biyu."
Miemie tayi maganar tana d'aga kiran Ammah da ya shig
o wayarta.
"To Ammah."
ta fad'a tana sauke wayar.
ta dubi Feeryal tana fad'in
"Ki karasa bari naje na bawa Ammah ATM d'in ta zata aiki direba kuma ni na aje mata shi wai bata gani ba, ina zuwa yanzu."
Feeryal ta gyad'a kai.
Miemie ta juya da sauri.
Feerya
l ta d'aga kafa tana kokarin barin gurin,
da sauri Zaraddin ya ce
"Ah ina kuma zakije tun baki karb'i tsarabar ki ba,
ai kin cancanci tsaraba mai tsoka ke da kikayi min fatan na dawo lafiya ai dole na saka miki, taho muje ki karb'i tsaraba sai kinso ki sam
ma Miemie."
ya juya ya shige kofar dide d'in su, sannan ya juyo ya ce
"Zo mana zo muje ki karb'a."
ya yi maganar yana gwada mata hanya.
a hankali ta d'aga kafarta da zummar biyo shi.
wata mota da ta shigo gidan yanzu fitilar motar ta hasko mata ido.
da sau
ri ta kai hannunta biyu ta kare fuskata,dan har jijiyar idanunta sai da ya amsa sakamakon hasken nan.
Tsawon sakanni 20 wutar motar bata janye a kanta ba.
da sauri ta matsa gefe tare da janye hannayen ta kan fuskarta, sai a sannan ta sami damar iya bud'e
idanunta.
abin da ya bata mamaki motar tana tsaye batayi gaba ba ba'a kuma kashe wutar motar ba.
maganar Miemie ta juyo a bayan ta
"Feeryal muje gashi har na dawo."
Miemie tayi gaba Feeryal ta biyo ta, da sauri Miemie ta d'an dawo da baya ta ruko hannun F
eeryal ta ce "Motar Ya Abdurrahim ce wannan zo mubi ta can.......!
*Babu editing a karanta da hakuri*
Miemie ta janyo hannunta suka bi gefe.
yana zaune cikin motar ya jingina bayan sa jikin sit idanunsa akan waya yana latsawa.
kallo d'aya tayi masa t
ayi saurin janye idanunta sakamakon jin wani irin mummumar fad'uwar gaba,
sau uku ke nan tun da take gidan ta tab'a ganin sa, had'uwarsu ta farko a sashin Hajiya da yake tambayar ta wai ita aljana ce ko,
sai kuma ranar da sukaje dinner sukayi dare, sai ku
ma yau.
ganin da tayi masa sau uku duk abu guda take ji mummynar fad'uwar gaba mai had'e da tsoro.
duk da ba su yake kallo ba idanunsa na kan wayar hannunsa, amma gaba d'aya ta rud'e ganin irin dukan da ya yi wa su Miemie ya dad'a kara mata tsoron sa.
da k
arfi ta damke hannun Miemie ta kara saurin ta.
Suna shiga parlour Aunty ta wani sauke numfashi mai sauti.
Miemie ta dube ta ta ce
"Ya dai Feeryal?."
kai ta girgiza tare da kakalo murmushi.
A parlour suka tadda Aunty da Daddy zaune suna kallo tare da d'a
n tab'a hira.
suka karaso suka gaishe su, Daddy ya dubi Miemie ya ce
"Mamana mutumiyar taki taci abinci kuwa?."
Aunty ta ce
"Wani abincin cake da yogurt ba tana da abincin da ya wuce su ne."
kai Feeryal ta langwab'e ta ce
"Naci tuwo fa Daddy ko Miemie."
Mi
emie tayi murmushi ta ce
"Taci Daddy tare ma muka ci."
"Yauwa ko ke fa gara dai a rika had'awa da mai nauyin, idan iska ya taso kinyi nauyi bazai iya kada ke ba."
cewar Daddy cikin zolaya.
dariya duk sukayi.
Daddy ya mike ya nufi bedroom ya na cewa
"To sa
i da safen ku."
zama sukayi suka bud'e sabon hira, har wajen karfe goma kafin Miemie ta yi musu sallama ta tafi.
Feeryal ma ta mike dan bacci ne cike a idanunta ta shige bedroom d'in ta.
Aunty ta je ta kulle kofar parlour kana ta dawo ta kashe TV sannan ta
rage wutan parlour ta shige d'aki.
Ta taras da Daddy ya yi nisa a baccin sa, ta rage kayan jikinta ta sa na bacci kana ta shige bayi ta d'auri al'wala ta fito ta haye gadon itama ta kwanta gefen sa bayan tayi addu'a.
wani irin zabura Daddy ya yi ya mike
zaune tare da fad'in
"Innailaihirraji'un!."
ya dafe kirjinsa jikinsa na cirawa.
a razane Aunty ta mike ta ruko shi tana fad'in
"Subhanallahi ya ya dai Daddy me ya faru bakayi addu'a bane ka kwanta."
kai ya girguza mata yana sauke numfarfashi tare da share
gumin da ya karyo masa.
gaba d'aya Aunty ta rud'e a 'yan kwanakin nan ta lura a duk sanda ya kwanta haka zai farka a birkice.
tsawon shekaru ashirin da d'ori bayan auren su ya yi ta fama da irin wannan matsalar wacce damuwar haka takai ga tab'a masa lafiya
r zuciya,
a wancan lokacin bayan auren su da wata biyar yasoma irin wannan mummunar mafarkin,
sai da ya shari shekaru goma yana fama da matsalar,
da taimakon Allah da taimakon addu'o'in da Aunty take tayashi yasami sassaucin lamarin,
damuwa da irin wahala
r da yake sha idan ya kwanta bacci,
ta kai ga tab'a masa lafiyar zuciya, da har gobe yake shan magani.
sai gashiga a 'yan kwanakin nan abun ya dawo yanzu ba bu dare babu rana daga zaran ya kwanta bacci zai farka a firgice.
Ganin yadda gaba d'aya hankalin
Aunty ya tashi, a hankali ya kwantar da kansa jikin kafad'ar ta yana sauke numfashi.
cikin shiga damuwa sosai Aunty ta ce
"Daddy tashi kayi al'wala muyi sallah babu abin da yafi karfin Allah babu abin da zai faru da yardar Allah."
Tarika karfafashi har
ya mike yaje ya d'auro al'wala,
yafito ya taras har ta shinfid'a musu sallaya ta sa hijabi tana tsaye tana jiran sa.
shi ya jasu sallar suna idarwa taje ta d'auko musu Alkur'ani.
sun jima sosai suna karatu cikin suratul BAQARA, sai da ta tabbatar da nusu
wa tare da shi,
har yana karatun yana gyangyad'i,
ta gyara ta mike kafafunta ta ce
"Kwanta Daddy."
ya mike kan sallayar yayi pillow da kafarta.
a hankali take karatun cikin kasa da murya tana yi tana shafa kansa, nan da nan bacci ya yi gaba da shi.
ya yi b
acci abadan kafin itama ta soma lumshe ido. ta rufe kur'anin kana ta jingina bayan da jikin gado a haka bacci ya d'auketa a zaune.
Har sai kusan asuba ya farka ya ganta zaune tana bacci.
kauna da tausayin ta suka dad'a shigarsa, ya mike ya ciccib'eta ya d
'aurata a kan gado,
yana ajeta ta bud'e ido.
murmushi tayi masa cikin muryar bacci ta ce
"Daddy ashe da sauran ka har yanzu tun da ka iya d'aukata."
kumatun ta ya ja ya na fad'in
"Tun da ina da ke kam tsufa bata isa ta matso ni ba."
murmushi tayi masa ta g
yara kwanciyar ta.
shiko ya shige bayi ya d'auro al'wala,
yafito ya haye sallaya yasoma gudanar da nafilfili.
sai da aka kira sallar asuba kafin ya tashe ta shikuma ya wuce masallaci.
Aunty na idar da sallah ta je ta tada Feeryal kafin ta koma tacigaba da
adhkar.
Feeryal ko bayan ta idar da salla da karatun alkur'ani tayi kamar yanda kullum Aunty ke umurtar ta da tayi, tana shafa addu'a ta haye gado ta koma baccin ta.
ba ita ta farka ba sai wuraren karfe 11 da rabi.
Bayan tayi wanka ta shirya cikin doguwa
r rigar atamfa da ta amshi jikin ta.
ta fito ta wuce dinning ta tarar da Aunty a gun ta tanadar mata abin kaunar ta wato cake da yogurt.
ta bayan kujerar Aunty ta zo ta kwantar da kanta gefen kafad'ar ta cikin siririyar muryarta ta ce
"Ina kwana Ammie na."
Aunty ta shafa gefen fuskarta ta ce
"Lafiya lau 'yammatan Ammie antashi lafiya ya lalaci,
a rage lalacin nan gobe ke zakiyi mana breakfast idan Allah ya kaimu, yau ma tare zamu shiga kitchen anjima."
"To Ammie."
ta fad'a tana mikewa a jikin ta taja kujera
ta zauna.
Kamar yadda Aunty ta ce da rana tare suka shiga kitchen da Feeryal.
Sosai Aunty ta dage wajen koyawa Feeryal nau'ikan girki kala-kala, bata yadda ta barta kara zube kamar yadda wasu masu kud'in suke yi wa 'ya'yan su ba,
komai sai dai masu aiki
suyi ba dai 'ya'yan su ba, suna ganin wai hakan gata ne da yawa sai sunyi aure suke had'uwa da kalu bale daban-daban a gidan auren.
duk da Aunty d'iyar masu kud'i ce bata taso cikin tarbiyyar irin wad'an can 'ya'yan masu kud'in ba.
shiyasa ta zage damtse
wajen koyawa Feeryal abubuwa da dama da suka shafi cikin gida.
yawan zama da Miemie takeyi a sashin itama ta karu da wasu abubuwa da dama.
Aunty ce zaune a parlour tana video call da Hajja Umma.
jiya aka sami nasarar zakulo mutum biyu daga cikin tawagar
'yan d'aukar amarya, da hukuma suke ta kan bincike a kansu har yanzu.
Aunty tace
"Amma dai Hajja Umma babu wata matsala ko?
ni fa tun da naji ance an kuma kama wasu 'yan gidan sa duk a tsoro nake,
kar sauran da suke a b'oye suce zasu fito d'aukar fansa."
Hajja Umma ta ce
"A'a babu komai insha'allah, wannan yaro Sadam Abokin Nasir Allah dai ya saka miki, yaron akwai kokari jiyan nan kusan da shi muka wuni a gidan nan da jami'an su, da daddare ya turo jami'an su biyu da folisawa biyu da Nasir ya turo
har mu
ka waye gari yau da su,
har yanzu ma suna nan,
amma naji Alhaji yana cewa anan zasu cigaba da zama har zuwa a kare bincike."
Aunty ta sauke numfashi tare da cewa
"To Allah ya dad'a tsarewa."
"Amin ya Allah, wai ni kam ina kishiya take ne banji d'uriyar ta
ba."
"Tana d'aki ai bata san muna waya da ke ba da kin ganta."
Aunty ta d'aga murya ta wala mata kira,
ta fito da sauri tana amsa kiran
"Taho ga Hajja Umma tana niman ki."
da sassarfa ta karaso inda Aunty take ta zauna gefen ta tare da kwantar da kanta a
jikin ta, ido ta waro ta ce
"La Hajja Umma shine tun d'azu baki neme ni ba ko."
"A'a nunar gwanda bagashi na nemo ki ba yanzu,
kwana biyu da ban gankiba sai naga kin dad'a kumbura, kazar turai jikin nan ya dad'a komawa tumatur sharaf."
baki Feeryal ta turo
ta ce
"Ba Abba ya ce ya ce ki dai na fad'a min ba, ke da shi,
Ammie na kashe ki kira min mijin ta muyi hira."
"A waya kawai zaki ganshi ni kuma ina tare da shi a nan."
"Ai baki sani ba Hajja Umma kullum sai yabi jirgi yazo gurina,
ke kina can kina ta kan
cewa masu aiki,
kuyi kaza kuyi kaza, kar ku saka gishiri da yawa a abincin almajiran nan fa ku sa musu magi ya ji."
dariya duk suka fashe da shi.
Aunty ta ce
"Au haka Hajja Umman take fad'a."
kai ta gyad'a tana dariya ta ce
"Kullum sai Abba ya shigo yace
ta zauna ta huta ta barsu su suyi aikin, yana fita zata tashi taje bata zama tarika kai kawo ke nan, bata ko gajiya,
ai shiyasa Abba ya ce yafi so na ma, ita kullum bata hutu gata da masu aiki."
dariya Aunty tayi tana dungurin kanta.
Maryam da ta shigo ta
tadda suna wayan ta leko cikin wayar Feeryal ta washe baki
"Aunty Maryam ina kika je ne?."
"Gidan su Haulat yanzu kuwa muke hiran ki da ita, tana tambaya ta yaushe zaki dawo."
"Ai nakusa dawowa, sai dai bana so na rabu da Ammie na ne."
tayi maganar tana d
ad'a kwanciya jikin Aunty.
"To ai sai ku dawo tare da Ammie'n naki."
cewar Maryam tana mata hararar wasa.
Wayar ta da ke rike a hannunta ne ya yi kara,
ganin Miemie ce ke kiran nata yasata d'agawa.
"Hello Miemie."
daga cikin wayar Miemie ta ce
"Feeryal y
i sauri kizo kiji wani magana."
"Wacce magar Miemie?."
jin shiru yasata ciro wayar a kunne taga har ma ta kashe kiran.
ganin Aunty sun kama wani hirar da Hajja Umma sai ta fice zuwa sashin su Miemie.
Har ta kusa rabin isa sashin nasu kiran Miemie ya kuma
shigowa wayar ta.
"Yauwa Feeryal tsaya ma kawai bazan zo."
"Ai gashi na fito ma bari na karaso."
"To tsaya-tsaya ma kawai bari ni na fito."
Miemie ta fad'a tare da katse kiran.
Feeryal ta sauke numfashi tana fad'in
"Oh Miemie."
Gefe ta matsa ta jikin wasu
dogayen bishiyoyin fula da suke jere a gurin, tana jiran fitowar ta.
maganar da taji ta cikin bishoyoyin ne yasata juyawa da sauri ta d'an leko ta sakankanin flaws d'in.
karaf suka had'a ido da Ameerah da ke zaune da saurayin ta suna hira kan kujerun da s
uke cikin gurin.
saurayin ya mike da alama sun gama hirar zai tafi.
da sauri ta d'an matsa baya.
Tana tsaye har motar saurayin ya fita a gidan.
a razane ta waigo jin an buga kafad'ar ta ta baya.
Ameerah ta bita da kallon sama da kasa ta ce
"To sannu bak
ar munafuka, wacce munafurcin ne yakawo ki nan kika zo kina leka min saurayi,
Allah ya toni asirin ki saurayi na kike lekawa."
murya a sanyaye Feeryal ta ce
"Kiyi hakuri wlh bansan kuna nan ba, kuma ni ba lekensa nake yi ba."
"Karya kike yi leka shi kike y
i ai ina kallon ki,
sai kin fad'a min uban da yasa kike lekashi, ko naci uban ki da duka anan, dama ina da cikin ki."
"Allah Ameerah ni ba leken sa nake ba, ban ma san kune a gurin ba."
Miemie da ke tahoto ta bud'e baki tana kallon yadda Ameerah ke d'agaw
a Feeryal murya ita ko sai magiya da kwantar da kai take kamar zatayi kuka.
da sauri ta karaso gurin ta na fad'in
"Ya ya akayi wai mene ne?."
da sauri cikin tsiwa Ameerah ta ce
"Kamata nayi tana leka min saurayi."
Feeryal tayi narai-narai da ido ta ce
"All
ah ba leken sa nake ba magana naji na leka bansa su bane."
Miemie ta ce
"To lallai saboda Feeryal d'in ta rasa aikin yi sai ta tsaya leken saurayi kamar wacce ta rasa samari,
ta ce ba leka miki saurayi tayi ba ai sai kiyi hakuri ki rabu da ita."
"Karya ta