Showing 63001 words to 66000 words out of 70713 words

Chapter 22 - FEERYAL BOOK2 COMPLETE

komai."

tayi waje tana janyo mata kofar.

A b'angaren Abdurrahim bakin cikin kiran da Dr L-cana ya yi masa akan Siyama da Umma Karima

,

an danganta shi da su da abun bakin cikin da sukaje yi yaji,

ya tattari abubuwan amfanin sa yazari makullin motar sa yabar asibitin.

yana isa gida ya gyra parking yafito ya nufi side d'in sa.

direct upstairs bedroom d'in sa ya nufa.

yana tura kofar yaj

a ya tsaya cike da mamaki yaji b'acin ransa ya karo.

masu aiki yagani guda biyu cikin d'akin,

d'aya tana d'ale a kan gadon sa tana gyarawa d'ayan kuma tana cikin bathroom d'in sa

tana wankewa.

wani uban tsaya ya buga musu, a razane duk suka taho gaban sa

suka zube.

cikin muryar b'acin rai sosai ya ce

"Waya baku damar shigo min side d'ina har ku wuce ko ina ku shigo min har cikin bedroom!?."

murya na rawa suka ce

"Mai d'akin ka ce Hajiya Kuraiba."

wani b'acin ran yakuma jin ya ziyarce sa.

cikin tsawa ya ce

"Ku fita ku b'ace min da gani! ko da wasa na sake ganin wata ta sako kafarta cikin side d'in nan ba ma d'akin nan ba, wlh sai kun raina kanku."

a zabure sukayi waje jiki na kyarma. a stairs sukayi kiliya da Kuraiba da taji dawowarsa ta shigo gefen sa.

gani

n yadda suke sauka kamar ana biyo su ta ce

"Kai wai har kun gama gyaran ko ya?."

basu iya bata amsaba sukayi waje da gudu."

da sauri ta karasa haurawa tana shiga ta gansa yana tsaye yana rage kayan jikin sa, fuskarsa babu annuri.

ta karaso tana kokarin run

gume sa ya buga mata tsawa tare da nunata da yatsa

murya cike da b'acin rai ya ce

"Waya baki ikon shigo min da wad'an can abin cikin d'aki, ke kanki albarkacin Mommy kike ci, badun haka ba na rantse baki isa ki taka kafarki cikin bedroom d'in nan ba, garg

ad'i na karshe,

kada ki sake ki sake gayyato min wasu 'yan'aiki cikin side d'innan ma gaba d'aya."

duk da taji tsoron yadda yake magana cikin fusata sosai, amma sai ta waske cike da salon bariki ta narke murya

"Haba mijin Kuraiba ai yanzu ni nake da ikon s

awa ko hanawa a cikin gida na,

wai kullun ina gidan amma wai sai Ajmaal ya shigo ya gyara maka bedroom's zuwa parlour,

shine yau na ce yabari ni zan sa masu aiki su gyara idan sun gama gyaran nawa."

wani irin mari ya d'auke ta dashi tun kan ta kaiga rufe b

akin

ta.

cikin karaji ya ce

"Bakiji me nace bane!?

masu aikin ne bana so su tab'a komai nawa, idan kika sake gigin gayyato su nan wallahi! sai kin raina kanki,

akwai kofa ta can sakanin inda kike da waje ki bud'e surika shigo miki ta can, ban yadda na ga

nsu a area'n nan ba!

fita a d'akin nan yanzun nan!!."

yakuma buga mata tsawa, ta juyo da sauri dafe da fuska tayi waje tana fad'in

"Ka mare ni Abdurrahim."

tsaki yaja ya shige bathroom.

Yana fita ya tarar da Missed call d'in Mommy a wayar sa.

yana saka k

aya ya fita ya tafi sashin Hajiya.

Hajiya na ganin sa ta ce

"Yauwa abikin turawa da ma yanzu nake kan cewa Kulu ta kira min kai,

ciwon gwuiwan nan ya sako ni gaba kwana biyu."

zama ya yi yana fad'in

"Muga kafar."

ta ja zani saman gwuiwar tana cewa

"Ka gans

hi nan zugi kamar ya kwana biyu hanani bacci yake, yanzu ko na sha na shafa maganin da ka banin nan baya dai na zugin."

yatsar sa ya d'aura kan gwuiwar yana d'an daddannashi sannan ya d'ago ya gyara zaman sa ya ce

"Za'a canza miki magani, anjima zan kawo m

iki."

"Yauwa ai gara a kawo min wani, wannan gwuiwa ya sako ni gaba."

bai kuma magana ba sai wayarsa daya zaro yana daddannawa.

Hajiya ta gyara zama ta dube shi tana rike hab'a tare da fad'in

"Wai ni kam abokin turawa har yanzu banji

ana fad'in yarinyar n

an Kuraiba ta d'auki ciki ba, ko baku fad'a bane? to ai ko baku fad'a bama za'aga alamar ciki tare da ita,

akwai cikin kuwa?."

baki ya tab'e batare da ya ce komai ba.

Hajiya ta ce

"Ni halina da kai ke nan, ana ma magana kayi banza da mutane, gara ka fad'a

tun da wuri a sani a nemo maganin tsari a sunkuya bata,

dan gidan nan yanzu ya zama abun da ya zama miyagu suna son kafa sansanin su,

ban san me ke damin Abubakar ba wannan yarinyar Feeryal ba abin a zauna da ita a guri bane,

bari zanyi tattaki naje Yelwa

na karb'o mata magani a rufa idon makiya akan abun cikin,

idan ta bar gidan ba shike nan ba kowa ma ya huta, wannan karo ko ba'a gama bincike ba zata koma,

iya shegen banza kawai ina gashi nan ni ina ganin ku ina jin dad'i,

shine bazai so ganin jikokin sa

ba, idan aka barta tayi wa cikin wani abu fa tun da su dama jinnu sunfi son karnin jini,

kafin a sake samin wani ai sai an kuma yin wani watannin,

ba gara a tare ko mai tun da wuri ba, bari Abubakar zai zo ya same ni."

d'ago idon sa ya yi daga kallon waya

ya kalle, wato ita a lissafin ta ciki Kuraiba take da shi.

baki ya tab'e ya mike yana fad'in

"Da ma tana da ciki ne?."

"Yo iyashegen banza ai kai kafi kowa sani in tana da shi ko babu, kardai kuyi irin abun zamanin nan aure kusan wata 6 ai yaci ace yanzu

tana da cikin wata 5 ko shidan ma."

takalmansa ya zura ya fice

daga nan ya wuce masallaci...

Bayan wata biyu da cire cikin Siyama

Bilkisu da Saddiqa suna zaune a d'aki wanda dama su biyu d'akin su d'aya,

Rahma da Nabila suma d'akin su d'aya, Siyama nata

daban.

Saddiqa da yawu ya cika mata baki ta mike taje ta zubar a toilet ta dawo.

jim kad'an ta kuma zuwa ta zubar.

ta kuma mikewa zataje zubarwa Bilkisu ta ce

"Ke dalla kin dami mutane da tofe-tofen yawu, wai ba dama mutum ya zauna kusa da ke sai yawu,

w

ani iskancin saran da kika samu kwana biyun nan ke nan, kibi ki ishi mutane da yawu da kakarin amai."

Bilkisu bata rufa baki ba Saddiqa ta kuma mike wa da gudu ta shige toilet tashiga kakarin amai.

Bilkisu ta mike tsaye ta taho bakin kofar toilet d'in ta c

e

"Ke Saddiqa wai me ke damin ki, baki da lafiya ne bazaki fad'a a kira Family Dr ya zo ya duba ki,

ko kije ki gayawa Ya Abdurrahim ya baki magani ba."

Saddiqa ta mike tana kuma tofar da yawu.

Bilkisu ta harare ta tana kuma fad'in

"Wlh ni ni yanzu bamma ya

dda da ke ba, jiya maganar me kike sakan dare a waya,

duk da a bacci na tashi amma na fahimci akwai wani abun da kike b'oyewa."

ta juya da sauri tafita a d'akin ta nufi d'akin Umma Karima tana shiga ta ce

"Wallahi Umma ban yadda da Saddiqa ba, ki kirata k

i binciketa wlh kamar ciki take da shi, tabi ta dame ni da amai da zubda miyau."

Umma Karima ta zabura tare da buga kirji ta ce

"Ciki! nashiga uku ina Saddiqa'n ta ke."

ta mike a haukace tayi waje tana kwad'awa Saddiqa kira.

Saddiqa ta fito da sauri jiki a

sanyaye.

Umma Karima ta dubeta sama da kasa tana haki sannan ta ce

"Biyo ni nan maza ki bani fitsarin ki na gwada in dai ciki ne kin gama da ni Saddiqa."

Bilkisu Rahma Nabila Siyama duk suka rufa musu baya.

Kulu mai aikin Hajiya da tazo karb'awa Hajiya h

ayaki gun Umma Karima, taja ta tsaya tare da rike baki tana binsu da kallo har suka shige d'akin Umma Karima.

Umma Karima ta d'auko tsinken gwajin ciki ta mika mata d'an karamin kwantena ta sata gaba suka shiga bayi tana tsaye a kanta tayi fitsari ta bata

.

ta saka PT ciki taja ta tsaya tana fifita da d'an kwalinta.

bai mata ba ta fito parlour rike da PT, gani tayi d'akin ya kasa mata.

'ya'yan nata suka biyo ta.

wani uban ashar Umma Karima ta mulmulo ganin amsar tana da ciki sinken gwajin ya bayar.

ta sake

shi a kasa ta sa hannu akai tana fad'in

"Nashiga uku ni Karima Saddiqa kema cikin kikayi!

a ina kika samo ciki wani d'an kutumar uban ne ya miki ciki!."

Kulu ta waro ido ta juya sad'af-sad'af ta yi waje tana kama baki.

Saddiqa tayi kasa da kai jiki na ra

wa.

Umma Karima ta buga mata tsawa

"Dan uban ki ina tambayarki uban wa yamiki ciki zaki gaya min ne ko sai naci kutumar uban ki."

Saddiqa ta zabura murya na rawa ta ce

"Um..mu...."

sai kuma tayi shiru.

Umma Karima tayi kukan kura tayi kanta da sauri ta b'o

ye bayan Bilkisu tana fad'in

"Zan gaya miki Umma."

"Zo nan gaba na ki gaya min."

ta fad'a tana huci.

ta zo jiki na rawa tashiga kame-kame ta na fad'in

"Um..um..saurayin Aunty Siyama ne."

Siyama da Umma Karima suka waro ido a tare.

Umma Karima ta ce

"Au tsi

nanne tambad'ad'd'e, d'an akuya sabo da shi ya zamo bunsuru yabita ya barbare ta yakuma biyoki ke ma,

sabo da wancan karon ban d'auki mataki a kan saba, shine bari ya kuma b'ulluwa ta hanyar baya ya d'ura miki ciki ke ma,

ke Siyama d'an gidan uban waye ne

shi da yake binku yana barbarar ku,

sai na ga uban sa Wallahi."

su Nabila suka waro ido dan dama basusan da na Siyama ba.

Kulu da saurinta ta shige sashin Hajiya.

Hajiya na ganin ta babu aikan da ta mata ta ce

"Ke Kulu ina hayakin dana aike ki karb'a?."

K

ulu ta ware ido ta rike hab'a ta ce

"Hajiya wlh akwai babban matsala a gidan nan, wannan yarinya Saddiqa 'yar wajen Hajiya Karima ciki take da shi, ciki tayiyo wlh Hajiya yanzun nan aka gano tana da ciki."

Hajiya ta saka salati tana fad'in

"Wasayyawu ni ji

kar mutane hud'u Saddiqa'n ce tayiyo ciki, ciki dai acikin gidan nan,

maza kirawa min Abubakar da abokin turawa."

Kulu ta d'au wayar Hajiya ta kira lambar Daddy yana d'agawa ta mika mata.

ta karb'a ta kai kunne tana ta ce

"Abubakar kasan musifar dake faruw

a agidan nan kuwa, maza kazo yanzu ina niman ka."

ta kashe ta ce wa Kulu kira min abokin turawa.

wayarsa tayi ta ringing bai d'aga ba.

Kulu ta ce "Bai d'aga ba Hajiya."

ba'a jima ba Daddy ya shigo da fargabar abin da Hajiya zata ce masa dan yasan maganar H

ajiya bazai wuce akan Feeryal ba.

tun kafin ya zauna ta ce

"Abubakar Saddiqa da cikin shege a cikin gidan nan, wace irin musifa ce wannan, acikin gidan ka cikin shege ya b'ullo."

da sauri Daddy da maganar ta duki kirjinsa ya kai hannu ya dafe kirji.

ya zau

na kan kujera da kyar hannunsa dafe da kirjin sa.

"Innalillahi wa innailaihirraji'un!."

kalmar data fito daga bakin Daddy ke nan.

Abdurrahim da shigowarsa ke nan yaga kiran Hajiya yana masallaci.

ya karaso da sauri ganin yanda Daddy ke dafe da kirjinsa zat

on sa ciwon sa ne ya tashi yasa Hajiya ta kira sa.

ya sunkuya gaban Daddy tare da cire hannunsa dake kirjinsa ya d'aura nasa yana fad'in

"Daddy ya kake jin kirjin ya ke maka."

ido ya rumtse ya ce

"Zafi sosai yake min Abdurrahim."

Hajiya ta ce

"Yo wad'an na

n 'ya'ya su zasu kasheka, bansan meye kake jira ace wad'annan gandan-gandan d'in 'yanmata suna zaune a gida babu aure, ba dole su d'auko magana ba,

gaba d'ayan su da an musu aure kan lokaci da yanzu 'ya'ya biyu ko uku suke da shi,

har autar tasu Nabila t

akai ta haifi d'a d'aya zuwa biyu;

to Saddiqa ta d'auko ciki sauran ma ba'a san in da hali zaiyi ba."

da karfi Abdurrahim ya d'ago ya furta

"Ciki!."

Hajiya ta ce "Kwarai kuwa cikin shege tayi, wannan irin abin kunya ace daga gidan nan ya fito."

wani irin m

ikewa ya yi damasunsa sukayi wani irin bud'ewa, b'acin rai karara ake iya hangowa kan fuskarsa.

da sauri ya juya yana taka kafafunsa a kasa, kasa tana amsa sautin takunsa

dip-dip-dip!.

ya b'allo reshen fulawa ya nufi sashin Umma Karima.

yadda ya fad'o ciki

n parlour ba 'ya'yan nata ba hatta ita kanta Umma Karima sai da ta razana..

ya yi kan su su Saddiqa da duka kan mai uwa da wabi, ba ita kad'ai ba har da su Bilkisu Rahma Nabila.

sai da itacen ta karye tayi kaca-kaca a jikinsu.

Siyama ta mike da gudu ta mas

a bayan Umma Karima dan bulalar sai da ya same ta,

ransa ya kai kololuwa wajen b'aci yayi jifa guntuwar itacen hannunsa,

ya cafko

Saddiqa yana kokarin kuncen belt d'in wandon sa.

Umma Karima ta yi saurin cewa

"Wlh in gaya maka Abdurrahim fyad'e aka mata,

fyad'e d'an iskan yaron ya yi mata bada son ranta ba."

wani mari ya d'auketa da shi sai da ta kife kasa.

ya shiga nuna su da yatsa cikin kakkausar muya yake fad'in

"Wallahi! idan kukasa bakincikin ku ya yi sanadiyyar bugawar zuciyar Daddy, na rantse dukkan

in ku sai na cire zuciyoyin ku da hannuna!."

ya yi shot da Saddiqa a yadda yake jin kansa idan yacigaba da tsayu zai iya kusan kashe ta da duka......!

Mommyn Twins ce

Abdulrahim na fita Umma Karima tayi kan 'ya'yan ta tana fad'in

"Ai kin gani Sad

diqa kin janyo muku duka dukan ku, idan badun nace masa fyad'e akayi miki ba da kinci ubanki a hannunsa,

yazama dole kema aje a cire cikin nan,

dan wlh ban shiryawa abin kunya ba,

'yan iskan yara suna ni man sa ni a bakin duniya."

a b'angaren Daddy kuwa da

kyar ya iya mikewa yana jin kirjin sa na yi masa zafi, ya lallab'a ya tafi sashin Aunty.

ganin yanayin sa Aunty ta tare shi a d'an tsorace tana fad'in

"Subhanallahi ya dai Daddy ba dai jikin ba dai?."

ta rike hannunsa ganin yana kokarin zama bakin gado, y

a zauna yana mai dad'a kankame hannunta.

Aunty tayi kokarin zame hannunta tana fad'in

"Daddy bakasha magani ba ko bari na d'auko maka kasha."

ya dad'a rike hannunta tare da girgiza mata kai ya ce

"Barshi Fad'imatu dan ko na sha ma babu amfanin da zai min."

jikin ta ya yi sanyi sosai ta ce

"Daddy dan Allah kar ka bani tsoro, me kake ji yanzu, ya kirjin ya ke maka."

"Zafi sosai yake min Fad'imatu sai ina ji kamar zafin yafi na baya."

kallon sa ta ke cikin tsoro "Fad'imatu."

ya kira sunan ta murya a sanyaye ta

gyad'a masa kai alamun tana jinsa.

hannunta ya dad'a rikewa gam kana ya soma magana

"A cikin gida na ni Abubakar Fiya, aka samu mai yin ciki a waje a cikin 'ya'yana,

Fad'imatu ina jin zafi sosai cikin zuciya ta."

wani irin waro ido Aunty tayi kirjinta ya

buga da karfi ta ce

"Daddy wacce irin magana ce wannan maraddad'in ji!?."

kai ya gyad'a mata ya ce

"Tabbas Saddiqa tayi ciki a waje Fad'imatu har haka na gaza a gida na?

me mutane zasuce a kaina."

Aunty ta dad'a jin gaban ta ya tsinke jikin ta ya yi sanyi

matuka,

taji rashin dad'in abun ba kad'an ba,

duk da mugun hali irin na uwar Saddiqa bazatayi fatan ace d'iyarta ta kasance cikin wannan halin ba,

jiki a sanyaye ta ce

"Daddy baka gaza ba masu taimako ne aka sami sakaki daga wajen su, uwa ita ke taimakon u

ba wajen yiwa 'ya'ya tarbiyya, a yayin da uba ya fita nima,

kayi hakuri Daddy jarabawa ce babu wanda yafi karfin kaddara,

mutane zasu fahimceka dan sun san cewa kai tsayayyen uba ne;

ka rungumi kaddara mai imani ne ake jarabtar shi ta ko wacce hanya,

shin

Daddy ka mance imanin mutum bazai cika ba har sai ya gaskata ya kuma yarda da wad'annan abubuwa guda shida,

yadda da ALLAH d'aya ne kayi imani da shi, da mala'ikunsa da duk littattafan da ya saukar, da duk manzannin da ya aiko,

da ranar karshe wato ranar

kiyama,

da KADDARA mai kyau ko mara kyau;

Daddy kaddarar mu ce bazamu tab'a ketare masa ba, kayi hakuri dan Allah Daddy ka barwa Allah ko mai kaji Daddy."

ta zauna gefen sa ta cigaba da kwantar masa da hankali,

wanda cikin kankanin lokaci yaji nutsuwa tare

da shi.

A cikin gidan kuwa labari ya soma yawo kamar dai yadda idan abu ya faru ake kai kawo da shi.

sai dai wannna karo masu yawo da zance kasa-kasa sukeyi dan yau abin maganar daga tushin uwar kai kawo ya fito, wato Umma Karima.

tarika sakaye wa tana c

ewa ai fyad'e aka mata.

a ranar da abun ya faru da daddare Umma Karima tasa Saddiqa gaba suka ce sashin Daddy.

yana zaune a parlour yana kallon labarai a TV.

Mommy na zaune a gefe san yau ita ke da Daddy.

Umma Karima ta zauna saman kujerar da ke fuskantar

sa, Saddiqa ta zauna a kasa.

Umma Karima ta marairaice murya dake nuni da zallar shiga matukar damuwa ta ce

"Alhaji yanzu fisabilillahi kaji abin da ya faru, amma baka zo kaji taya hakan ya faru ba,

shike nan za'a zuba ido a gyale yaron da ya keta mata ha

ddi ya mata fyad'e ke nan, baza'a d'auki wani mataki ba,

ko d'an gidan uban waye baza'a tura hukuma suje su kamo sa ba,

shiru za'ayi da batun ke nan abu tun safe kayi shiru bakace ko mai ba har dare."

Daddy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login