Showing 66001 words to 69000 words out of 70713 words
ya dube ta da d'iyar tata da ta sunkuyar da kai y
a jinjina kai tare da fad'in
"Me kike so nace a kai bayan ke ce uwan ke ce uban, duk abin da kikaga dai-dai ne kije kiyi Hajiya Karima."
daga nan bai kuma cewa komai ba ya kwashi wayoyinsa da system d'in sa ya shige bedroom d'insa.
Mommy ta ce
"Haba Alhaj
i bai kamata ka ce haka ba, kamata ya yi ad'au mataki a kan yaron."
Umma Karima ta mike cikin d'aga murya take fad'in
"Rabu da shi Hajiya Halima,
sabo da an gama da kai an wanke an baka, waccen tambad'ad'd'iyar tsintacciyar aljanar ruwan,
ganin ta ne ba'
ayi ba kawai da daddare kabi ka d'aga hankali ko bacci bakayi ba, alhalin gurin iskancinta ta tafi sai da akaje aka d'auko ta a hotel gurin samarukan iskancinta,
sai 'yar da ka haifa wani ya sace ta yaje ya mata fyad'e kayi ko oho,
to wlh bazan yadda ba 'y
a'yana ba tumakai bane da ko wani d'an iska zai rika hawansu ya share lafiya, zakaga abin da zanyi."
ta ja hannun Saddiqa fuuu sukayi sashin Hajiya.
suna shiga ta fashe da kuka tana fad'in
"Yanzu fisabilillahi Hajiya ace ayiwa yarinyar nan fyad'e, Alhaji y
a yi ko oho sai kace zuwa da 'yar nayi gidan nan."
Hajiya ta ce
"Ke da'alla dakata Karima ki na nufin ki ce da karfi akayi mata cikin, ba maza tabi tayi yo cikin ta ba."
Umma Karima tashiga rantse-rantse ta na fad'in
"Ga Saddiqa'n ta fad'a da bakin ta ba s
aceta ya yi yaje yayi mata fyad'e ba."
Saddiqa ta kama gyad'a kai tana fad'in da karfi ya yi mata har da kukan ta.
Hajiya kuwa ta yadda har tana cewa baza'a kyale yaron ba, kuma zatayiwa abokin turawa magana ya zubar da cikin.
Umma Karima ta koma da kwarin
gwuiwa ganin hakarta ya cimma ruwa.
Washegari da safe kuwa Abdurrahim ya shigo sashin Hajiya da shirin tafiya asibiti.
Hajiya ta ce
"Yauwa abokin tuwara da ma yanzu nake shirin niman ka, ka d'auki 'yar'uwan ka kuje asibiti ka cire mata cikin nan karya g
irma ya zame mana abin gori, duk da fyad'e akayi mata amma mutane bazasuyi la'akari da hakan ba,
gara tun wuri a cire shi tun kafin a busa masa rai ayi zunubi."
wani kallo ya wurgawa Hajiya kana ya juya ya soma tafiya yana fad'in
"Ba dai ni ba ba kuma asib
iti na ba."
ya fice ya shiga mota ya bar gidan.
Aunty tashigo sashin Umma Karima ta isketa zaune ita kad'ai sai mai aikin ta da take ta mata hidima.
Umma Karima ta bita da kallon mamakin ganin ta yau a sashin ta, wanda tun ranar da aka kawo ta gidan iyaye
n ta suka kawota sashin Umma Karima tun daga ranar bata tab'a sake taka kafarta cikin sashin nata ba, duk tsawon shekarun nan sai yau.
Aunty ta nimi guri ta zauna kan kujera kana ta dubi mai aikin nata ta ce
"Bamu guri zamuyi magana."
nan da nan ta juya ta
bar gurin.
Aunty ta gyara zama ta kalli Umma Karima wanda da dama ita ma ita take kallo,
Aunty ta yi murmushi sannan ta ce
"Hajiya Karima ke nan kina cike da mamakin gani na yau a cikin parlour'n ki zaune a kan kujerar ki ko?
aje wannan mamakin ki fiskanc
e ni, kin san me ya kawo ni nazo ne na tuna miki abin da kika manta,
yau ga miyagun kalamanki sun fad'a kan d'iyar ki, 'yar da kike kira karuwa ita ta iya tsare kanta da taimakon Allah bata aikata abinda kike ta mata fata ba,
sai gashi ke mai tsoron Allah
an samo fasa gurbi cikin koyayen ki;
na dad'i ina jiran rana mai kamar tayau sabo da na mai da miki amsar kalaman ki,
amma kash banso ranar ta kasance rana mai muni irin haka ba,
wlh shine Allah nayi bakincikin abin da ya faru, bana farin ciki dan Saddiqa
tayi ciki,
sabo da itama 'yata ce tun da d'iyar mijina ne,
amma ina so ki san da cewa
shi Allah sam baya bacci, shi yasa ya nuna miki ishara idan ke mai hankali ce ki gani,
kina da wasu 'ya'yan mata rai uku bayan Saddiqa ga kuma kanwarki cikon na biyar d'i
n su;
ki kwanta kiyi nazari kiyi amfani da kwakwalwarki,
kiyi kokarin baiwa sauran tarbiyyar da zai sa su kyamaci zina,
idan kuma ke kasashshiyar uwa ce, to ki shiryawa goyon 'ya'yan gaba da fatiha,
ni da FEERYAL kainuwa ne dashen Allah."
Aunty na kaiwa na
n ta mike ta nufi kofar fita.
Umma Karima ta mulmulo ashar ta auna tana fad'in
"Karya kike Hajiya Fatima malamin ki ya yi karya, bai isa ya baki sa'an da zaki shigo min har b'angare na ki nimi ki gaya min magana ba,
ni Karima wlh zaki san da ni kikayi, mu
nafukar banza munafukar hofi,
ciki kuwa sai dai ki ganshi akan wancan tsintacciyar aljanar ruwan badai akan 'ya'ya na,
itama Saddiqa'n ma fyad'e aka mata 'yan gulma 'yan bakin ciki, ba cikin shege taje tayi ba,
cikin shege a kanku zai kare."
Aunty tayi waj
e abinta.
Umma Karima bata fasa kumfar baki ba.
kira ta shiga kwad'awa Saddiqa.
Saddiqa ta fito ta ce
"D'auko mayafinki kizo muje a burge d'an banza, baza'a haifo shi ya zame min masifa alakakai ba,
dama hauka nake na bari a haifo shi."
Saddiqa ta koma ta
fito da mayafi.
sukayi waje Umma Karima bata fasa bala'i ba.
Asibitin Dr L'cana suka je ta tura masa kud'i masu yawa, shi kuma ya sunkuya aikin sa.
yayi-yayi cikin ya fita abin mamaki ciki yaki fita,
shi kansa abin ya bashi mamaki duk kwarewa a iya cire
ciki irin nashi, sai ga wannan yana son gagarar sa.
kwaya ya cusa mata a gaban ta ya ce suje gida kwayar zaisa cikin yafita dan dole.
tun daga hanya Saddiqa ta fara wash-wash,
Umma Karima ta ce
"Ai dama nakuda zakiyi sai ki daure har ya fita."
abu sai gab
a-gaba yake har suka iso gida, Saddiqa ta shige d'aki tayi ta birgima.
kan kace me tafara fita hayyacin ta,
ihun Bilkisu ne yasa Umma Karima tasowa da sauri ta shige d'akin su.
ta tadda Saddiqa a sume, tayi ta yayyafa mata ruwa wai ko dan ta farka ina.
ba
sai ga Umma Karima tana salati da kai kawo cikin d'aki.
tayi ta kiran Daddy a waya Daddy bayama gidan yana gun meeting.
ta fita a haukace tayi sashin Hajiya tana ihun fad'in
Saddiqa zata mutu.
suka dawo da Hajiya da ta rud'e ta birkice jikarta zata mutu.
Rahma ce tayi ta kiran Daddy da layin ta kafin ya d'aga ta sa kuka tana fad'in
"Saddiqa zata mutu."
ya ce
"Rahma idan lokacin ta ne ya yi Allah ya yafe mata, dama ai shi mutuwa wajibi ne ga kowa."
ya kashe wayarsa.
Hajiya ta ce wa Nabila da ke kusa da ita
"Kira abokin turawa yazo yanzu kar yarinyar nan ta mutu fa."
Nabila tayi masa missed call biyar ana shida ya d'aga, ta mikawa Hajiya.
a rud'e Hajiya ke fad'in
"Abokin tuwa kazo ka ceci ran kanwarka Saddiqa zata mu."
d'ip ya kashe wayar sa.
Hajiya jin shiru
ta ciro wayar baki bud'e.
Bilkisu ce tayi tunanin kiran Family Dr su Allah ya yi taimako ba'a dad'e ba kuwa ya iso."
da kyar ya samo kanta ta farfad'o tana farkawa kuwa sai ga jini ya b'allo mata.
Umma Karima ta sauke wani uban numfashi.
Hajiya ta bud'e b
aki tana fad'in
"Yoo cikin ne zai b'are dama yake son tafiya da ita, gara ai da ka b'are da ka zauna ka zame mana abin kwatance cikin dangi."
bayan likitan yayi mata duk abin da ya kamata ya tafi, sukuma suka sunkuya gyaran in da jinin ya malala.
Bayan d
awowar Daddy da daddare Hajiya ta je da kanta ta sanar masa, cikin ya b'are.
kai ya girgiza kawai dan yasan Umma Karima ce tayi kalan nata, bawai fita ya yi na Allah ba.
Saddiqa wata guda tayi tana jinya zuwa lokacin ta ware ta sami sauki sosai...
Daddy
ne yafito daga bedroom d'in Aunty da shirin tayiya office,
Aunty na biye da shi rike da hular sa.
sai da suka zo tsakiyar parlour ya tsaya tare da duban ta.
murmushi tayi masa cikin zolaya ta ce
"Daddy wai kai bazaka tsufa bane kullum fa a haka kake baka k
ara gaba."
janyo ta ya yi yana kokarin rungume ta tayi saurin gocewa tana dariya da fad'in
"Aa Daddy a nan kuma idan Feeryal ta fito fa."
murmushi ya yi mata ya kalli kofar Feeryal ya ce
"Wannan 'yanmatan taki da alama bacci take har yanzu, a taso ta tayi
breakfast."
har ya juya zai tafi sai kuma ya kuma juyo wa murya da alamar shiga yanayin sanyin jiki ya ce
"Fad'imatu idan na dawo akwai wata maganar da nake so muyi da ke,
amma kafin nan zan tinkari Hajiya duk da zuciyana yana bugu da sauri-sauri,
har ina
jin yana min zafi, amma zan tinkare ta ahakan duk da bani da tabbacin samin nasara."
Aunty ta dubeshi cikin rauni ta ce
"Daddy mene ne kuma."
murmushi ya yi mata ganin nan da nan ta shiga damuwa ya ce
"Babu ko mai sai na dawo ai nace zamuyi magana ko, kiy
i min addu'ar samin nasara, a gurin Hajiya."
kai ta jinjina.
har gurin mota tarakashi sannan ta mika masa hularsa, direba yaja shi zuwa sashin Hajiya......!
Mommyn Twins ce
Daddy na zaune a parlour'n Hajiya bayan sun gaisa, Hajiya tayi ta kawo masa
hirarraki, yana amsata amma gaba d'aya hankalin sa na ga maganar da take cikin ransa, wanda yake tunanin tinkarar Hajiyar da shi.
Daddy ya gyara zama ya fuskanci ta da kyau ya yi karfin halin soma magana.
r"Hajiya dama wata magana nake tafe da shi, amma b
ansan da wace fuska zaki fiskanci lamarin ba,
amma Hajiya dan Allah ina so ki fahimce ni, a matsayin ki na uwa a gare ni, nasan kinfi kowa son ganin farinciki na,
yin tawassali da Allah babu abin da yafishi dad'i da samin nasara a rayuwa,
ka yadda Allah
shike da ikon yin komai a duniyar nan, duk abin da ya sami bawa da sanin ubangiji duk kuma abun da kaga ya faru da kai dama rubucacce ne cikin kaddarar ka sai dai wani yazamo sila,
shirka haramun ce babu laifin da Allah baya yafewa bawa har idan yamutu ya
na aikatashi face shirka,
haramun ne shaidar zur abin da baka da tabbaci akan sa ka tabbatar da cewa hakan ne."
da sauri Hajiya ta ce
"To Abubakar ni ban gane in da wanna batun naka ya dosa ba,
wai wa'azi kake yi min ko me?
tun kafin kazo duniya nake
jin wa'azi,
ai naga kamar shirin fita kayi katashi ka tafi Allah ya bada sa'a, wa'azi kam ai andad'e ana jin sa."
Daddy ya d'an yi shiru da wasi-wasi tap cikin ransa ya gyara zama yana son dai-dai nutsuwar sa, kai tsaye yasoma fad'in
"Hajiya ba haka ba
,
abin da nake tafe da shi nake son sanar miki shine,
ina so na bawa Abdulrahim auren FEERYAL, saboda wasu dalilai idan da zaki fahimceni da zan zayyano miki dalilan nawa, kuma nasan zaki bani goyon baya..."
wani irin zabura Hajiya tayi tamkar taga wan
i muhimmin mugun abin tsoratarwa.
wani irin bugawa kirjin Ajmal daya sako kai zai shigo parlour'n ya yi har sai da ya kai hannu ya dafe kirjin nasa, dake bugu dum-dum-dum!.
wani irin bakin abu yaga ya gilma masa a ido, ya juya da sauri ya koma side d'in
su.
a parlour'n kuwa Hajiya
ta mike tsaye a zabure take fad'in
"Abubakar kasan me kake fad'a kuwa! ko kunne na ne yajiyo min ba dai-dai ba?
aljanar kake son aurawa abokin turawa!
to bari kaji wlh ko bayan ba raina banyarda ka aura masa ita ba,
bama shi b
a ko wani d'a a gidan nan kai koma waye har idan da dangantaka sakani na da shi, wlh ban yarda ba ban yafe maka ba Abubakar idan ka aurawa wa wani jikana,
wannan mayyar aljanar ruwan bare jikana na fari abokin turawa!."
Daddy da yaji kamar ciwon sa zai t
ashi sabar tashin hankalin da ya shiga agurin,
dama yasan da kamar wuya Hajiya ta yadda.
ya dafe kirjinsa da ya soma yi masa zugi ya ce
"Hajiya da zaki fahimce ni ki bani dama na kawo miki dalilai na."
"Rufamin baki dalilan banza da lilan hofi,
ai baka da
wani dalilin da zaka gayamin akan auren mutum da aljana,
ai in zaka mutu babu abin da zai sa ayi auren nan, ko mutuwa zakayi sai dai ka mutu Abubakar."
Hajiya ta juya ta shige d'aki tana falle zane tana gyara d'aurawa sabar masifa.
bata karasa ciki ba tak
uma juyowa ta dawo
"Ni za'a kawowa zancen banza zancen iska,
to maza-maza kaje ka fita da yarinyar nan a gidan nan yanzu, idan kuma ba haka ba ni nafita na bar maka gidan ka,
baka zab'eta a kaina ba ai dama shi yasa ka masa kan ta zauna wai ana bincike,
a
i ita yakamata ayi bincike a kanta ba wasu ba,
to wlh idan baka kori yarinyar nan ba saina sassab'a maka."
Hajiya takama jan hanci tana cigaba da fad'in
"Dama ashe abin da yasa kaki rabata da gidan nan ke nan, Abubakar nasake fad'a maka in zaka mutu abokin
turawa bazai auri yarinyar nan ba,
yaushene ma yayi aure da za'a sake masa wani auren, kai wlh ko shekara goma ya yi da yin auren fari idan wannan aljanar yarinyar ce bazaiyi na biyu da ita ba,
tashi maza ka fita min anan ni zaka kawo wa tsiya."
Daddy ya
mike jiki ba kwari ya fita.
A b'angare Ajmal kuwa d'akin sa ya shige ya kulle kansa ciki.
ya kafa kansa jikin garu-bango yana jin wani irin azaba cikin ransa.
yarika dukan jikin garu-bango yana fad'in
"Why Why why! ya akayi nayi nauyin baki ne, ni nake so
n FEERYAL Daddy ba Ya Abdulrahim ba."
ido ya rumtse da karfi tare da buga kanta a jikin bongo, sai kuma ya zame kasa ya zauna ya mike kafafunsa, ya jingina bayansa da jikin garu yana juya kai hannunsa na dafe da gefen zuciyar sa, ya yin da idanunsa ke a ru
mtse.
Daddy kuwa yana fita ya shiga mota direba yakai shi office sai dai me yakasa zama office d'in ya fito yasa direba ya maida shi gida.
Aunty ta mike tsaye da sauri ganin Daddy ya ya shigo bedroom d'in ta.
ta ce
"Daddy ba dai mantuwa kayi ba, naga ka d
awo da wuri."
zama ya yi yana cewa
"Zauna Fad'imatu muyi magana."
Aunty ta zauna tana kallon shi da alamun soma shiga fargaba.
"Fad'imatu."
Daddy ya kira sunanta.
"Na'am Daddy."
ta amsa zuciyar ta na d'an harbawa.
"Jiya magabatan wannan yaro mai son Feery
al Major Sadam sunzo, nasa akayi musu masauki a masaukin ba'i na cikin company;
sunzo nima masa auren ta sannan sun taho da shirin su sunaso a yanka musu sadaki, da sa rana duk a jiyan, dan suna tafe da kud'i idan aka yanka sadaki subiya nan take, a samusu
ranar da bazai wuce wata guda ba.
sai dai ni na ce musu nayi mata miji tuntuni,
kuma a halin da ake ciki zan aurar da ita wa mijin da nayi mata nan da kwanaki kad'an,
Fad'imatu na sami Hajiya da ma nasan ba lallai ne ta aminta da abun da naje mata da shi
ba,
ina da yakinin bani kad'ai ba kowa zai amfana da abinda nake son aiwatar wa."
Aunty ta jinjina kai kamar ko da yaushe acikin yadda da maigidan nata take ta ce
"Insha'allahu duk abin da kake son aiwatarwa alkhairi ne,
amma mene ne shi d'in Daddy?."
num
fashi ya sauke sannan ya ce
"Zan aurawa Abdulrahim Feeryal hakan ne kawai zai kaini ga tsira daga farmakin da ake kawo min cikin bacci, wanda bansan ta ina ne yake zuwa ba."
zumbur Aunty ta mike tana girgiza kai da fad'in
"Aa Daddy dan Allah kar ka soma, d
an Allah kar kabar maganar nan ta fita na roke ka, kaje ka sami Hajiya ka ce mata dama fad'a kawai kayi ba zartarwa zakayi ba;
Daddy ka rufa min asiri ya zanyi da rayuwa ta a cikin gidan nan idan wannan maganar ta fita,
ya zanyi da Hajiya da Hajiya Halima
da sauran 'yan gidan nan, Daddy so kake na tattara na tafi ko, dani da Feeryal d'in duka,
dan Allah Daddy kar ka sake wannan maganar, Feeryal kam ma tana da wanda zata aura Major Sadam, ka bashi auren ta kawai."
"Fad'imatu zauna dan Allah."
Daddy ya fad'a
yana ruko hannunta.
kai ta girgiza ta ce
"Aa Daddy tsoro nake ji dan Allah ka janye batun nan."
"Ke ma ashe bazaki saurare ni kiji dalilai na ba,
Fad'imatu kaf duniya babu wanda yake fahimtata sama da ke, kin fi kowa sanin damuwa na, zauna dan Allah."
jiki
a sanyaye ta koma in da ta tashi.
ya dube ta da kyau kana ya soma magana
"Na jima ina tunanin wanda zan zab'awa Feeryal a matsayin abokin rayuwarta, tun lokacin da ta fara tasowa,
nake yi mata fatan nagartaccen miji, wanda zai kula da ita yaji kan lamuran
ta,
a daren da aka rasa Feeryal ranar auren Abdulrahim,
yasa kafa yafita nemo ta batare da wani ya sani ba, yaje ya kwato ta a hannun wad'an da suka so b'ata mata rayuwa,
lokacin da ya dawowa da ita gidan nan tun a ranar naji shine ya dace da