Showing 24001 words to 27000 words out of 70713 words

Chapter 9 - FEERYAL BOOK2 COMPLETE

fisgo ta ta fad'o kan kafar Aunty, ta rirtike ta, itama ta kankame ta gamgam tare da b'oye fuskarta jikin Aunty.

tsaki ya kuma ja badun nauyin Aunty da yake ji ba da babu abin da

zai sa yazo bare har a tsaya ana masa wannan haukar.

kwafa ya yi afili Aunty ta fahimci ransa ya b'aci, ta bugawa Feeryal tsawa

"Idan baki tsaya ba za'a barki da ciwon ki kiyi ta fama, kina hauka ne allura kawai kamar cire ran ki za'ayi haba dan Allah,

yi

hakuri Abdurrahim kayi mata."

ta d'an ja sket d'in ta kasa

Baki ya tab'e ya d'an matso ya nitsa allurar ta saman pant d'in ta.

kara ta kurma ta kai hannu ta rike nashi da ke rike da allurar ya bige hannuta bayan ya matse ruwan allurar ya zare shi a jikin

ta, yana mai dad'a gimtse fuskarsa, ya cika har wuya.

da kyar ta tsaya a ka kara mata d'aya,

"A sa mata ruwan sanyi a jikin ta."

ya fad'a a takaice.

Aunty ta d'ago ta a jikin ta ta sauka ta shige bayi da sauri.

Feeryal kukan allura har da majina.

ganin Aun

ty ta shige bayi itama ta mike da sauri ta duro a gadon.

tana d'aga kafa taji abu ya cake ta a bayan hanu.

kara ta kwalla tare da d'ago hannun tana yarfe shi.

wani kallo ya wurga mata sannan ya saki allurar dake hannunsa kasa,

"Stupid girl." ya fad'a kana

ya juya ya fice a d'akin

Aunty ta fito da sauri tana fad'in

"Feeryal lafiyar ki tun da an gama ina shike nan ko sai kin tsaya shiririta,

me ya sami hannun naki kike tallafe shi sai kace a hannun aka yi miki allurar."

Aunty ta ruko hannun nata tana cigaba

da cewa

"Um kin gani karin gardamar ki har kin ji ciwo a hannu gashi har ya d'an fidda jini, sannu zauna na sa miki towel zaki dad'a jin dad'i, jikin naki ya yi zafi sosai baki ji ya ce asa miki ruwan sanyi ba."

Feeryal bata iya magana ba sai matsar kwa

lla take.

Aunty ta taimaka mata ta cire kayan jikin ta, ta d'auko mata wani riga bes da wandon sa iya guiwa ta saka, kana ta rika jika towel tana shafa mata a jikin ta.

har sai da taji jikin ya yi sanyi kafin zuwa lokacin kuwa bacci ya d'auke ta.

Aunty t

a fita taje ta kama aiki akai-akai take shigowa dubata, sosai jikin ta ya yi sanyi ta jima sosai tana bacci..

"Ya shugaba na akwai tsoron wani mai tsanani a tare da ita, gata a kwance cikin jinya sakamakon tsoron nashi."

waziri Kutup ya yi maganar yana z

ubewa gaban sarki Aljani Matip tare da d'aura ruwan madubin ganin zahiri daga rayuwar ta bisa kafar sarki Aljani Matip.

kura mata ido ya yi sosai sannan ya ce

"Aje a wanke mata fuskarta da ruwan zuzirr, akwai bak'in yana da magauta masu neman ta sukayi jif

a ya fad'o fuskarta,

shi yasa idan tayi duba a gareshi firgici yake dirar mata,

a wancan lokacin malam Buba Mani bai san da ragowa a goshin ta ba, wan da ya gani kawai ya iya cirewa."

kasa waziri Kutup ya yi da kansa yana cewa

"A gafarce ni ya shugaba na a

mma me yasa sai a kansa take shiga wannan yanayin, ga sauran bil'adam kuma ba haka ba."

murmushi sarki Matip ya yi sannan ya ce

"Magauta bincike suke babu dare babu rana sun watsa taurarin su ta ko ina domin cikar burin su,

tauraru ya fad'a a kansa duk da

hasken shi ya disashe taurarun su amma yana tasiri a jikin sa,

shi yasa take jin hakan game da shi,

a wanke mata fuska da ruwan zuzirr na karkashin teku,

ganin da zata kuma yi masa zai kona taurarun su dake razanar da ita,

wanda yake a matsayin tarko gare

ta, za'a shafe sammanin su da suke jin sun kusa gado inda take, duk da taurarun nasu baya da kaifin tasiri a kanshi,

har yanzu lalub'e suke cikin duhu."

"Na d'auki umurni ya shugaba na."

Waziri Kutup ya mike domin isar da umurnin da aka masa..

Sai bayan

sallar la'asar ta farka.

tana bud'e ido ta saki murmushi ganin Chuchu da Chulu a kusa da ita.

Chuchu na rike da hannunta tana share mata d'an guntun jinin da ya fito kan bayan hannunta.

mikewa ta yi ta zauna tana fad'in

"Laa Chuchu Chulu kunzo ne har kun

dawo daga tafiyar?."

suma murmushin suka mayar mata, Chulu ta ce

"Dawowar mu ke nan, muka biyo nan,

baki da lafiya kinji sauki ko mu baki magani."

"Naji sauki kaina ke min ciwo kad'an kad'an yanzu."

wani d'an karamin tandu mai murfi ta ciro, ta kwance ma

rfin ta ce

"Kawo hannun ki na zuba miki ki wanke fuskarki zaki ji kan ya dai na miki ciwo."

ta mika hannu ta tsiya ya mata har sau uku tana wanke fuskarta da shi..

fuska ta yamutsa tana

kallon hannunta dake rike a hannun Chuchu sannan ta ce

"Wannan Sahab

d'in nan ne ya caka min allura a gurin."

Chuchu ta ce

"Kina so ki rama?."

ido ta d'an waro ta ce

"Tsoro yake bani kuma duka ya ke yi fa, baku ga yadda ya yi wa su Miemie ba."

"Ki dai na tsoron shi ba ga munan ba zamu taya ki,

idan ya ce zai duke ki zamuyi

mishi irin na Mommyn shi,

kin mance tun da data tab'a dukan ki muka rike mata kafa ta kasa iya tafiya, to haka zamuyi masa shima."

Dariya ta fashe da shi tuno da abin da suka tab'a yi wa Mommy tun tana karama.

sai da dariyar ta yi tare da cewa

"To amma a

i kunce shi kun kasa iya yi masa komai, shifa mugu ne baku ga yadda ya caka min allura ba."

"Ina abin da muka baki ki sa masa a jikin san nan?."

"Yana can cikin wardrobe nifa tsoro nake ji, a ina ma zan ganshi na saka masan."

"Duk in da kika ganshi ki san

yadda zakiyi ya tab'a jikin sa, ta nan ne kad'ai zamu sami damar iya yi masa wani abu,

idan ba haka ba to mu ba zamu iya yi masa ko mai ba ba zamu iya zuwa jikin sa ba,

mun d'au ki wancan a in da kika ajiye,

amma zamu baki wani."

d'an shiru tayi tana tunan

i ta ya za a yi ta iya hakan.

"Babu abin da zai miki ki daina tsoron sa mu zamu taya ki kinji."

kai ta gyad'a.

Chulu ta mika mata wani jan ganye guda d'aya ta ce

"Idan wannan ya tab'a jikin sa zamu iya zuwa jikin sa, bai isa ya yi miki wani abu ba zamu ram

a miki."

ta karb'a tana murmushi nan take ta kudiri aniyar saka masa a jiki, duk da bata san ta in da zata fara ba.

Har kusan magariba suna tare sai da Aunty ta shigo tashinta ta tashi magariba yayi tayi wanka,

kafin su Chuchu suka tafi.

Kasancewar tana

fashin sallah,

tana fita daga wanka ta saka kaya ta fito parlour.

Aunty taji dad'in ganin yadda ta warware sosai, kamar ba ita ce jiya da d'azu abin tausayin nan ba.

Suna parlour da Aunty na sallar magriba ita kuma tana kwance tana buga game a wayarta.

M

iemie ta shigo, ta zauna gefen ta tana fad'in

"Mara lafiyar ke nan d'azu na shigo ai kina bacci Aunty ke ce min baki da lafiya."

murmushi ta yi

"Eh amma naji sauki."

"Ba dai tsoro ne ya saki ciwo ba,ma tsoraciya kawai."

dariya kawai ta yi.

Miemie ta zaun

a sukayi ta hira har bayan sallar ishe kafin ta koma sashin su.

Siyama ce ta fad'o cikin d'akin Umma Karima, ta cire takalmi mai tsinin da ke kafarta tayi wurgi da shi.

"Ya ya mene ne hakan Siyama?."

"Aunty Karima kiyi wani abu dan Allah, ki duba fa ki g

ani lokaci kurewa ya ke dad'a yi,

auren nan fa da gaske za'ayi,

gashi duk wata hanyar da zanbi wai dan hankalin sa ya dawo kai na duk a banza,

dubeni ki gani dubi shiga ta ki gani ki ga irin had'ewa ta fa,

a haka yazo ya iske ni a sashin Mommy amma ko kal

lo ban isheshi ba,

duk yadda zanbi na janyo hankalin sa na bi amma babu wata nasara."

Umma Karima ta mike ta dafa kafad'ar ta ta ce

"Ina so ki kwantar da hankalin ki,

kar ki damu zaki mallaki Abdurrahim zaki same shi a tafin hannunki, boka yabani tabbaci

kuma yana kan aiki a kan haka,

na yadda da boka Mali nasan bazai wasa mana kasa a ido ba,

auren nan da ke za'ayi in har ina numfashi."

"Aunty Karima in har abin nan bazai yuwuba kawai ni zan tinkare sa, na fad'a masa ina son sa."

"Dalla matsa can mashirma

ciya kawai shi zai zo da kansa yace yana son ki, kuma zaki sha mamaki ki zuba ido kawai ki gani."

Da sauri Umma Karima ta d'aga hannu a kafad'ar ta tana cewa

"Tsaya ma tukun wai nikam kamar naga sonshi da gaske kika fara."

a dibirbirce Siyama ta ce

"Kamar

ya Aunty Karima ai ni so nake ayi-ayi musamu abun da muke bukata, naga jinkirin zuwan lokacin ne kawai."

"Ai ho yanzu naji batu

je ki ki cire kayan nan ki huta, ki kwantar da hankalin ki kamar tsumma a randa, kamar yanzu lokaci zaiyi ayi a wuce gurin."

S

iyama ta sauke b'oyayyen numfashi kana ta tattari takalmarta ta yi d'akin su.

Feeryal ce kwance a parlour saman doguear kujera rike da waya tana buga game.

Miemie ta shigo ta zauna gefen ta tad'a mata buka acinya tana fad'in

"Yanzu dama wayar tana hannun

ki nake ta kira kika ki d'aga wa."

"Wash Allah Miemie ta zafi fa."

"Ai dama so nake kiji zafin, ayi ta kiran ki a waya kike d'agawa, tun d'azu na tura miki abu ta Whatsapp baki ma hau online d'in ba bare ki gani,

ke kam ma ba amfanin wayar ki,

kalli kiga

ni ashoben da muka cire na kannen ango kala biyar ne, Unaisa da Umaima'n Hajiyan Dubai ne zasu taho mana dashi daga can,

duk kalolin nan ba karamin kyau zasu miki ba."

ta karb'i wayar tana duba wa

"Gaskiya sun yi kyau kam."

ta fad'a tana mika mata wayar.

Miemie ta ce

"Ai sosai ma kuwa idan muka yi waya da su zance a siyo har da ke."

"Da ni kuma to ai ni ba kanwar ango ba ce me zai sa nayi ashoben."

Miemie ta tsare ta da ido.

kai ta gyad'a tana cewa

"Eh ai Mommy ta ce shi ba yaya na ba ne kinga kuwa ni ma

ba kanwar sa bace."

"Dan ta fad'a shine me dalla kiyi abin ki, kowa zai sa ke ne bazaki saba."

Feeryal ta d'au wayar ta ta cigaba da buga game d'in ta tana cewa

"Meye a ciki tun da ba tsirara zanyi yawo ba, nifa bazanyi ba karma ki sa su kawo."

Aunty da

ta fito daga kitchen tayi shiru tana sauraran su.

Miemie ta mike tana cewa

"To idan an kawo an d'in ka kar ki sa."

"Ki sa a kawo da ita zata saka ma."

cewar Aunty tana karaso wa cikin parlour'n,

Miemie ta ce tom kana ta dubi Feeryal da

ta tab'e fuska.

Tan

a cewa

"Goben zamuje gyaran gashin kuwa ni fa so nake ma ayi min kitso gashina sai karyewa yake gara naki shi baya komai,

kar gashin yagama gwaguyewa."

"Eh zamuje."

"To Allah ya kaimu."

ta fice ta koma sashin su.

Washegari da wuri Miemie ta gama shiri

ta biyo wa Feeryal suka fito bayan Aunty ta gama yi musu kashe din su dawo da wuri.

suna hanyar su na zuwa parking lot Ameerah ta hange su.

murya ta d'aga

"Ke Miemie tsaya-tsaya-tsaya."

Miemie ta juyo tana dalla mata harara dan tasan bai wuci halin nata na

rashin mutunci zatayi mata ba.

Ameerah ta karaso in da suke ta harare su sama da kasa sannan ta ce

"Da kika cewa su Unaisa su karo ashobe na mutum d'aya, ke zaki sa kala goma iri d'aya da naki da wanda za'a karon."

"Ina ruwan ki meye damuwar ki idan zan s

a duka, idan kuma ma wata zan bawa kina da matsala ne,

ko akwai sisin ki a cikin kud'in siyan kayan,

Daddy ne me bada kud'in ko ke da kika titsiye ni kina tambaya ta."

"Ai nasan bai wuce ma wannan Aljanar kika sa ba, to tunda kud'in bana uban ta bane baza

a kawo da ita ba,

ta had'a dangi da Ya Abdurrahim d'in ne da zatayi ashoben bikin sa,

to bama son gayyan sod'i, ta tsaya a matsayin ta dangin sa ne zasuyi ashoben bikin sa ba bare 'ya'yan tsintuwa ba."

Feeryal tayi murmushin takaici taja hannun Miemie ta

ce

"Muje Miemie."

Miemie ta fisge hanun tana cewa

"Ke kam kin yi asara Ameerah haka zaki kare da gori, idan kikace zakiyi min ni wlh farfasa miki baki zanyi 'yar rainin wayo."

"Miemie muje dan Allah, ki rabu da ita."

Feeryal ta fad'a tana kuma ruko ta.

Am

eerah ta waiga gefe da sauri ta isa bayan mota ta sunkuya ta d'auko magen Hajiya da ke kwance a gindin mota, ta jefawa Feeryal a jiki tana gad'in

"Munafuka idan bata rabu da ni ba ya zatayi da ni."

Wani irin uban ihu Feeryal ta kurma tare da kankame jikin

ta dake cirawa,

nan da nan kwayar idanunta suka sauya, tayi wani irin yanke jiki ta rid'u a kasa, tare da kuma kwalla kara ta zare gyale da d'ankwalin kanta ta yamusa gashin kanta.

tayi wani irin mikewa ta shako wuyan Ameerah.........!

11

Wani irin da

mka tayi wa wuyan Ameerah, tana wani irin gurnani.

idon Ameerah ya firfito, ta d'aga hanu kafafaka kamar kaza a cikin ruwa ta rike hanun Feeryal tana ja tayi-tayi ta iya b'anb'are hannunta a wuyan ta ta gagara.

ganin yadda Ameerah ta ke fafutukan niman num

fashi, da sauri Miemie ta ce

"Sake ta Feeryal yau kin nuna mata shiru shiru ba tsoro bane gudun magana ne, kyale ta mu tafi wannan ya zame mata darasi in ita mai gane wa ce,

in kuma bata gane ba gaba a kuma ankarar da ita."

da sauri Miemie ta shiga kokarin

janye ta, sai ji tayi kamar dusi take tab'awa.

"Feeryal kyale ta sake ta haka."

tafad'a tana jan hannunta dake wuyan Ameerah, amma ko gizau hannun ta baiyi ba.

da sauri ta dube ta cike da mamakin yadda taji takasa iya b'anb'are hannunta dake wuyan Ameerah

.

da karfe ta d'ago kanta dake sunkuye gashin kanta ya rufe fuskarta.

a razane Miemie tayi baya ganin kwayar idanunta da suka sauya izuwa na ban tsoro.

Da gudu ta juya tana fad'in

"Me gadi security Feeryal Ameerah kuzo dan Allah wlh ba ita ba ce ba Feerya

l ba ce!."

gaba d'aya ta kid'ime, tayi bakin get a guje tana kiran security.

Nabila da Sahla da komai ya faru a kan idon su dan tare suke da Ameerah dama, su suka tsaya jiranta ita kuma ta karaso ciwa su Miemie mutunci.

suka juya da gudu sukayi sashin Momm

y suna fad'in

"Wayyo Allah Mommy Feeryal zata kashe Ameerah."

Mommy ta fito a hargitse dai-dai sanda Security suma suke karasowa gurin.

Aunty ma ta iso a bujajan Baba Rabi ta sanar mata da abin da ke faruwa.

Security suka bugawa Feeryal tsawa sukace

ta sa

ke ta.

ganin bata da niyyar sakin ta,

ga yadda numfashin Ameerah ke yi kamar zai bar jikin ta, suka shiga kokarin jan Feeryal da jan hannunta a wuyan ta.

amma ko gizau basu iya ko da jijjigata ba.

Mommy ta ce

"Wayyo Allah shegiya mayya zata kashe min yari

nya."

tayi kukan kura

tashiga dukan Feeryal da hanu bibbiyu ta baya tana fad'in

"Mayya sake ta kashe ta zakiyi."

wani irin sa kafa tayi ta baya ta angiza Mommy sai ga Mommy a kasa shirim, ta kawo ihu ta saka, tana dafe bayanta.

security hud'u sukayi kan Fe

eryal sukayi sukayi su iya kwace Ameerah a hannunta suka kasa.

Aunty da hankalin ta yayi mummunar tashi

ta zo ta gaban Feeryal tana fad'in

"Kuyi hakuri dan girman Allah ku sake ta na gama ku da Allah, kar ku ja mana masifa."

"Ai ita ce masifar babban anno

ba wayyo Allah mun shiga uku zata kashe 'yar gida, wayyo jama'a ku kawo mana d'auki za'ayi kisa."

Umma Karima da rahoto ya kaimata ta iso yanzu take fad'a.

ta ci gaba da fad'in

"Ku harbeta da bindiga idan bata sake ta ba, kuna gani zata kashe ta, dalla ku

kashe mara amfani."

sai kuma ta juya da gudu tayi sashin Daddy tana ihu.

Ta fad'o cikin parlour'n Daddy tana fad'in

"To Alhaji gashi can za'ayi kisa a cikin gidan ka,

ka aje gamasheka ta bunkasa tafara cire wuyan 'yan gida,

ga mayyar Aljanar 'yarnan can t

a makure wuyan Ameerah har jini na fita, ko numfashi bata yi wata kila ma ta mutu yanzu,

wani irin bala'i ne wannan ka ajiye mana a cikin gida."

Daddy ya dubi Umma Karima da take haki d'ankwalin ta a hanu ya girgiza kai,

kana ya gyaza zamansa ya d'aga kaf

arsa d'aya ya d'aura kan d'aya sannan ya dubi, Abdurrahim dake zaune a gefen sa kasan Carpet ya ce

"Abdurrahim je ka suna fad'a ka rabasu."

"Alhaji ka taso kaje ka ganewa idon ka kasheta fa zatayi."

Daddy ya d'au tsiririn gilashin sa ya saka sannan ya d

'au jarida ya bud'e yakuma gyara zamansa yasoma karantawa.

Abdurrahim ya mike ya nufi waje domin isar da umurnin da Daddy ya basa.

Umma Karima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login