Showing 42001 words to 45000 words out of 70713 words
kaita sa
ma.
nan ta kuma gamuwa da wata kayataccen parlour.
ta tattab'a kofofin da ke cikin parlour'n taji su gam sai guda d'aya taji sa a bud'e ta tura ta shiga.
Can ta hangosa kwance saman makeken lafiyayyen gadonsa yana baccin sa cikin kwanciyar hankali.
ido ta
kura masa tare da had'iye miyau, ta shiga takowa a hankali tana jin wani dad'i cikin ranta.
komai da komai irin mikin da take mafarki.
ta haye gadon ta fad'a jikin sa ta rungume shi tana wani dad'a shigewa jikin sa.
tana shafashi tare da tura hanunta ciki
n rigar sa tana shafo kirjinsa.
A hankali ya bud'e idanunsa, ya ture ta a jikin sa.
da sauri ta kuma komawa jikin sa ta wani shagwab'e murya
"Haba mijin Kuraiba jiya ina ka shiga ka barni ni kad'ai, da kyar nayi bacci ina ta jin tsoro."
da sauri ya damke
hannunta jin in da take kokarin tura hannun nata.
ture ta a jikin sa ya dad'a yi tare da gimtse fuska,
dan ya lura da yarinyar bata da kunya.
ya mike ya shige bathroom.
bayan sa tabi da kallo tana gyara kwanciyar ta a kan gadon.
zuwa can yafito d'aure da
towel da alama wanka ya yi.
tana ganin shi ta mike taje ta rungumo shi.
tana wani nannarkewa a jikin shi.
"Haba mijin Kuraiba ban gane kana tureni a jikin ka ba, halaliya na ne fa,
wai baka mararina ne."
bai yi magana ba sai zame jikin sa da yayi yana koka
rin matsawa gefe.
takuma cakumo shi ta tura hannunta a........!
18
A kirjinshi tana shafo kan 'yan nonuwan shi, tana goga kirjinta a bayan shi.
da karfi ya ruko ta ya juyo da ita,
ya d'aga hanu zai yarfa mata mari sai kuma ya dunkule hannun.
ya nuna
mata kofa fuska ba wasa ya ce
"Fita!.
kallon sa tayi yana dad'a tsare gira, da nuna mata hanyar fita.
kukan makirci ta sake tana fad'in
"Korina kake."
sai kuma ta juya da gudu tayi waje da kukan.
tsaki yaja had'i da kwafa kana ya soma kimsawa.
kiran Dr Im
ran ne ya shigo wayar sa yana gani bai d'aga ba.
ya yi ta kira yana ji yacigaba da damuwarsa.
sai da yagama kimsawa
ya fito cikin shigar kananun kaya, sai baza kamshi yake.
Dr Imran yana daga tsaye a farfajiyar bangaren nasa ne yake kiran sa.
yana ganin
fitowar sa ya nufi parking lot d'in sa, kamar baisan da shi a gurin ba,
ya biyo bayan sa da sauri yana cewa
"Wai haka ne dan mutum ya yi aure sai ya karo wulakanci,
kana gani na ka wuce kuma tun d'azu nake kiran ka kaki d'agawa,
kawai nayi maka uzini ne da
n wata kila wani abun ne yake wakana a ciki,
amma ka fito ka ganni sai ka share kayi gaba,
wai ina ka kaisu ne kam, amma wad'an nan basu da mutunci ya akayi ne suka shigo gurin ma bayan akwai tsaro a gurin?."
"Gidan gona."
ya fad'a a takaice yana shige wa
cikin d'aya daga cikin motocin sa.
da sauri Dr Imran ya shiga d'aya gefen yana ci gaba da fad'in
"Marasa mutunci da karya kasusuwansu kayi, ta in da gobe bazasu iya kuma bin wata yarinya ba."
Wayarsa ce tayi kara dai-dai san da suke fita daga gidan ya d'
aga,
daga cikin wayar aka ce
"Oga sun fad'i in da take."
"Kuje ku d'auko ta."
ya fad'a tare da kashe wayar.
kana ya kara gudun motar.
suka d'au hanyar fita daga gari.
A b'angaren Kuraiba tana jin fitarsa,
ta janyo wayarta ta kira number Mommy.
da fara'a
Mommy ta d'aga wayar tana cewa
"Kuraiba antashi lafiya ya gajiyan hidima ya bakunta?."
jin sheshshekan ta Mommy ta gyara zama tana kuma washe baki,
abin nesa yazo kusa gani take jiya d'an nata ya angonce.
"Aa mene ne na kukan Kuraiba ai hakuri zakiyi, sai
kin daure kinyi jarumta."
"Mommy jiyafa ko ganin sa banyi ba haka ya barni na kwana ni kad'ai inata jin tsoro,
shine yau dan naje jikin sa ya kore ni yakuma fita a gidan, bansan ina yaje ba."
murnar Mommy ya koma ciki wato abin da take zato dai ba shi ya f
aruba.
ta ce
"Kiyi hakuri bari na ne me shi."
Mommy ta kashe wayar tana amsa sallamar da Mom tayi har ta zauna lokacin tana waya.
ta ce
"Yi hakuri ina waya kika shigo ban amsa sallamar ba."
Mom ta ce
"Ai dama yanzu 'yan gaisuwan biki zasuyi ta kira ana mik
i ban gaji."
"Hm amaryar ce ma da kanta, ni bansan me ke damun Abdurrahim ba, wani irin murd'ad'd'en bahagon hali yake da shi,
ki duba kigani jiya akai maka amarya kaje ka kwana wani guri ka barta ta kwana ita kad'ai gidan da bata saba ba,
sannan ta taka t
aje in da kake ka kore ta, wani irin rayuwa ne wannan."
Mom ta gyara zama tana cewa
"Ina kuwa zai je gurin amarya yabi dare niman aljana,
to ai in baki sani ba jiya kwana ya yi yana niman wancan aljanar yarinyar da ta bi wasu 'yan iskan samaruka,
ya dawo g
idan nan jina-jina sunyi masa kaca-kaca kamar har da kariya ko gocewar kashi a hannunsa,
nace ina shi ina had'a tsafga da 'yan iska,
yabar amarya a gida yatafi niman wata banza, d'azunnan Dad d'in su yashigo yake gaya min, ya ganshi a masallaci rab'e-rab'e
Alhaji suna yi masa sannu da jiki."
Mommy ta buga kirji
"Iye kar ki gaya min wannna zancen ni ina ina ke nan akayi haka, au niman ta da jiya ake yi shine shi ya tashi ya bazama nima da sakan dare,
kai wlh Allah ya'isa sakani na da Hajiya Fatima, ta gama
da 'ya'yana maza ta gama asirce su kamar yadda tayi wa uban su."
Mommy ta d'aga waya rai b'ace tashiga kiran wayar sa, sai dai ya yi ta ring bai d'aga ba.
sai da tayi masa missed call wajen sau uku kafin ya d'aga.
"Mommy ina driving ne idan na tsaya zan ki
ra ki."
d'ip ya kashe wayar.
Mommy tayi ta bombomi uwar kawo gulmar Mom tana tayata.
A bakin get d'in gidan gona ya yi hon aka bud'e masa get.
ya na gyara parking ya fito Dr Imran ma yafito.
da sauri wasu mutane biyu suka taho in da yake suna fad'in
"Oga
anje d'auko ta ba'a dawo daga d'auko ta ba tukun."
kai ya jinjina tare da cewa
"Ina suke, kun binciko iyayen sun?."
ya yi tambayar yana tafiya ciki.
suka biyo bayan sa suna fad'in
"Suna ciki a kulle, asalin sunan sa Lukuman sunan gayun sa Zazuu shi d'an A
lhaji Wali Dollars ne, su kuma sauran zaman kansu suke babu iyayen su a garin nan,
sai dai tare suke da shi ko da yaushe."
kai ya jinjina.
Can cikin gidan gonar suka shige in da suka kulle su cikin wani d'aki mai duhu.
suka bud'e mishi ya shiga.
suka biyo
bayan shi, wutan cikin gurin suka kunna tare da bud'e tagogi.
gurin ya bada haske sosai.
suna d'ad'd'aure, duk an tub'e su gajerun wanduna ne kawai a jikin su.
sunyi mugun galabaita suka d'ago kawunan su, sai numfashin wahala suke saukewa.
ya tako gaban s
u ya janyo kujera ya zauna.
yana kare musu kallo.
sai kuma ya mike yana cewa
"Jaq miko min sandar can basu duku ba gaskiya."
zabura suka yi suna cewa
"Dan Allah kayi hakuri Yaya wlh mun duku, bazamu sake ba."
murmushi Dr Imran ya yi sunji wuya har da kiran
sa Yaya.
Da sauri Jaq ya d'auko ya mika masa.
sai da ya kewaye su da sanduna uku-uku duka rika ihu kafin ya jefar da sandar.
kana ya sunkuya ya bud'e wata jakar da ya shigo da ita yana fad'in
"Da alama bayi muku kaciya ba zo ku tub'e min su."
Zazuu ya
mirgina kai gefe cikin muryar galabaita ya ce
"Wlh ammana ni tun ina jariri ma aka min."
aska ya ciro yana gyara rikonsa ya matso gaban sa
"Sabon kaciya zan maka idan ka warke zaka tantance, wata gona ya kamata ka rika shiga."
yana gama fad'i ya cafko maz
akutan sa da karfi ya murd'e.
wani uban ihu ya sake jiki na kakkarwa.
sai da ya tabbatar da ya azabtu kafin ya sake shi, ya kawo bakin sa saitin kunnen sa ya rad'a masa
"Har yanzu bai kosa ba idan na kara ganin kabi wata sai na cire shi gaba d'aya."
kai ya
shiga gyad'awa a matukar tsorace zufa na karyo masa.
Sauran suka birkice ganin ya d'ago yana kallon su.
wad'an da suka kamo Zuly suka hankad'o ta ciki.
suna cewa
"Ga ta nan Oga mun kamo ta, sunan ta Zulaihat, inkiya Zuly 'yar Kano ce zaman kanta take a
nan."
ya juya yana binta da kallon kyama gami da tsana,
wai mace ce wannan ta banzatar da kanta ta tsunduma harkar iskanci da shaye-shaye.
ya tako gaban ta a zafafe yashiga d'auke ta da maruka da hannayen sa biyu ta ko wani gefen fuskarta.
a gigice ta zube
kasa sabo da wani irin masifaffen jiri sai take ji kamar ana jonata da wutan lantarki ne.
Cikin fusatacciyar murya ya ce
"Ku kamata ku d'aure ta kuyi mata aski."
nan da nan suka rirtiketa sukayi mata d'aurin goro.
Jaq ya aske mata kai tas har yana walkiy
a.
ya janyo kujera ya zauna a gabanta ya kuma d'auketa da mari d'aya sai da gefen bakin ta ya fashe.
cikin tafasar zuciya ya ce
"Yanzu ke baki ji kunya ba, wai ke a hakan mace ce! sam baki dace da mace ba, da shashashshun maza irin wad'an can kika dace,
sh
iyasa nasa a miki aski!
da ke ake had'a baki ake cin zarafin 'yan'uwanki mata ke baki ji kunya ba!."
ya karashe maganar tare da naushin kujerar da take kai a d'aure, tayi baya ta bugu da jikin garo.
ya mike a fusace ya tako gaban ta cikin kakkausar murya y
a ce
"Kar ki sake na sake ganin ki a garin nan, ki koma gidan iyayenki ki samu miji kiyi aure, kina ji ko!!."
ya karashi maganar cikin karaji sosai.
ta zabura tana gyad'a kai ba kakkautawa, jiki na kyarma.
Ya juya ya dubi su Jaq ya ce
"Ku sake su, kuyi m
ata bukin Airplane ku bata 10 million yau d'in nan tabar ganin nan, kar ki sake nasake jin labarin ki a garin nan,
su kuma a sasu a taxi zuwa gida."
yana kaiwa nan ya juya Dr Imran yabi bayan sa.
yana biye da shi yana ta kallon shi kamar bai tab'a sanin sa
ba.
shifa mamaki yake bashi baka tab'a gani alkiblarsa.
har suka shiga mota suka bar gidan gonar bai fasa kallon sa ba.
"Kai janye idanunka ka a kaina."
ya yi maganar idanun sa a kan titi.
"AA wai dama kasan ina kallon ka ne,
nifa wallahi wani lokaci tsor
o-tsoro kake bani,
idan kayi wani abun sai naga kamar canzaka ake, sai na kasa gani wanne ne asalin wanne ne ake kawo shi jikin ka."
hararar shi ya yi da wutsiyar ido yana cigaba da driving d'insa.
Suna isa gida sashin Mommy ya nufa Dr Imran ya biyo shi
.
kasan cewar da ba'i a sashin nata ta kofar baya ya shiga, ya shige bedroom d'in nata.
Mommy na zaune da wasu 'yan'uwan ta suna ganin shi suka mike suka fita bayan sun gama masa kirarin ango.
Dr Imran ya zauna kan kujera yana gaisheta da yi mata ya gajin
biki.
tun kan ya zauna Mommy ta soma masifa
"Wai me ke damun ka ne Abdurrahim, a kawo maka amarya jiya ka tsallaka cikin dare kafita kabar ta cikin d'aki,
wai kaje niman wata mayyar aljana;
ka barta ta kwana ita kad'ai a wannan makeken gida,
tayi hakuri da
haka ta aje alkunyar mu ta mata ta tashi da kanta taje in da kake ka zazzageta ka kore ta, kaki saurarar ta,
anya Abdurrahim ka kiyayi fushina fa ka guji fushina akanka fa,
na ce maka bakai ba aljanar yarinyar can babu wani taimako sakanin kai da ita,
kai
kasan wace ce ita kuwa yarinyar nan ba karamar hatsabibiya bace,
ban yarda ba ban yarda kasake taimakon ta ba, ka barta ta tafi duk in da zataje,
wad'an da sukayi lamanin ta suje su nemo ta;
matarka kuma bana son sake jin makamancin haka,
jiya da kyar t
ayi bacci saboda tsoro kar ka sake barinta ita kad'ai,
akan wancan banzar yarinyar zaka sallaka kabar matarka cikin d'aki;
kar na sake jin wannan nagaya maka ke nan."
ya mike tare da nufar kofa yana cewa
"Tun da tana tsoro, ta koma gida mana idan ta daina
tsoron sai ta dawo."
"Ai ko baka isa ba dan ba'a tab'a haka ba, kar ka sake ka wasa min kasa a ido ka sani shiga kunyar kawaye."
Ganin ya yi waje Imran ya bisa da sauri cike da mamakin lamarin.
suna fita waje Imran ya ce
"Lallai wannan yarinyar 'yar sosai
ce, auren jiya-jiya shine har an fara kai kara,
karan ma akan miji bai saurare ki ba,
to kai ma ka saurare ta mana me kake jira, da bazaka more angonci ba, kaje ka kwashi gara kawai mutumi na."
wani kallo ya wurga mishi.
Imran ya tsaya yana cewa
"Ni bazan
ma shiga ba daga nan zan tsaya,
kai nifa tsoron yarinyar nan nakeji,
kanaji Hajiya rannan ta ce da zakuna ta bisu,
ga Mommy ma tana ce bakasan waye ita ba,
to ni bari na koma daga nan, ban shirya had'uwa da damisai ba,bazanje ayi attack d'ina ba."
Ya juy
a da sauri Abdurrahim yaja tsaki.
Yana shiga bedroom d'in sa ya rage kayan jikin sa ya wuce bathroom.
ya yi wanka ya fito, ya shirya cikin wando 3qtr da singilet.
Kuraiba tanajin dawowan sa, tayi sauri-sauri ta shiga tayi wanka ta d'au wani yalolon riga i
ya cinya ta saka, sannan ta fesa turare.
ta fito ta nufi b'angaren sa.
tana shiga parlour'n sa dai-dai da yana sauka daga stairs kenan.
tana wani taku cikin yauki ta karaso shima ya karasa sauka kenan, ta rungumo shi tana fad'in
"Mijin Kuraiba tun d'azu na
ke jiranka, ina katafi ka barni,
ga abinci can masu aiki sun kawo, yana wancan dinning d'in, yunwa nake ji nakasa iya cin komai bakanan, taho muje mu ci."
zame jikin sa ya yi ya karasa parlour ya zauna.
ta taho ta d'ale kan cinyarsa ta sakalo wuyansa, tar
e da kai bakin ta kan.......!
19
Kan bakin shi tana kokarin kissing lips d'in shi.
ido ya ware kan fuskarta ya yi saurin kai hannun sa ya ture fuskar nata yana wasa mata wani kallo.
shgwab'e murya tayi tana wani bankaro kirjinta da kusan rabin sa a w
aje suke ta ce
"I'm sorry, I really love you
shi yasa nake zuwa gare ka,
You are very handsome, komai naka is so cute,
ka daina kori na ajikin ka bazanje jikin wani ba, kai ne miji na,
be with rne please.
cikin side d'in can tsoro ya ke bani,
ni fa ban s
aba zama ni kad'ai ba."
tana maganar rana tafiya da hannunta daga wuyan sa zuwa kirjin sa."
"It's okay tashi."
ya fad'a yana kokarin ture ta.
jikin shi ta shige ta manna nonuwan ta sosai a jikin shi tana wani dad'a narke wa.
da karfi ya cirota tana kokarin
kuma komawa jikin sa,
ya d'auke ta da marin da sai da ta zube kan kujera,
ya mike tsaye.
ta saki jikin ta sharaf tare da ware kafafun ta.
yadda ta zube ta ware kafafunta hatta pant d'in ta sai da ya bayyana ana hango shatin pussy d'in ta.
cikin tsawa ya
ce da ita
"Stand up and get out!
idan kika sake shigo min nan sai ranki ya b'aci, tashi na ce!."
ta zabura ta mike ya kuma nuna mata hanya da hannu yana dad'a gimtse fuska.
ba shiri ta bi hanyar.
tsaki yaja ya d'au wayoyin sa yafita.
Cikin garden yaje ya
zauna
ya d'au d'ya daga cikin wayoyin sa ya kira number Ajmal.
Ajmal ya d'aga da sallama ya ce
"Je ka karb'o min Breakfast gurin Aunty."
Ajmal ya ce to.
ya fito daga b'angaren su ya nufi b'angaren Aunty.
Aunty na kichin tana shirin d'aura girkin rana, jin
sallamar Ajmal ta fito.
bayan ya gaishe ta ya sanar mata da sakon yayan nasu.
Aunty ta isa dinning ta had'a masa nau'in abinci kala uku da Sudan tea daya fi so.
tana mamakin har yanzu bai karya ba,
tasan bazai tab'a cin abincin masu aiki ba in zai wuni,
tu
n lokutan baya da Mommy tayi mata rashin mutunci akan samasa abincin da take, wai tana sa masa magani ciki duk ta mallake mata 'ya'ya mazanta,
kar taje ta samusu guba suci su mutu.
shari'a har gaban Hajiya.
daga nan ta rage samasa abinci har yazo ma yabar
kasar.
daya dawonnan kuma idan ba shi ya aika ba bata sa a kai masa,
gudun abin da zai je ya dawo sakanin ta da Mommy.
Ajmal na tsaye idanun sa a kan kofar Feeryal.
Aunty ta taho ta mika masa tray'n data shirya kayan breakfast d'in ya karb'a yana cewa
"Au
nty wai ina Feeryal tun da na shigo ban ganta ba."
"Tana ciki tana bacci ne, bata jima da shiga ba tasha magani kanta na ciwo."
"Subhanallah Allah ya sawaka."
ya fita yana waigen kofar nata.
Ya iso garden ya aje tray'n saman table d'in gabansa.
yana shiri
n tafiya ya jiyo muryarsa yana fad'in
"Me ya hanaka gyaran d'akin yau?."
da sauri Ajmal ya dube shi,
har yau d'in ma bai sami 'yanci daga bautar side d'in nasa ba,
ai shi tun da akayi auren nan