Showing 36001 words to 39000 words out of 70713 words

Chapter 13 - FEERYAL BOOK2 COMPLETE

shiga ja tana girgiza kai.

har ta garu da jikin gado,

hankad'a ta ya yi a kan gadon ya hayo kanta, yashiga shafa gefen fuskarta

"Oh zazzafa ki natsu mana, ni fa ba d'an yankan kai bane,

ni kawai mai b

ada gudumawa ne agaggauce;

baki tab'a sanin dad'in abin bane, ko kin hange sa a wando ne ya tsorata ki,

ki nutsu mu more juna gaskiya zan sha zaki kamar zuma,

ta ina zamu fara ko kin bani zab'i."

yana maganar yana tafiya da hannunsa jikin ta.

Ido ta rumts

e da karfi tana bige-bige da shure-shure, had'i da kururuwa, jikin ta na kyarma.

"Ki dai na wannan ihun babu wan da zai jiki a nan, ko an ji ma babu mai zuwa taimakon ki,

ke dai ki baje kawai mu more."

ya mike a jikin ta tare da rungumota ya matseta a jiki

n sa ya zuge zip d'in rigarta yana kokarin yin kasa da rigar.

kara ta kwalla ta yanka masa cizo a kafad'a.

da sauri ya sake ta yana murza gurin.

ta mike da gudu ta duro a gadon, ta isa bakin kofa tana kokarin murza ki, ya bita ya ruko ta.

ya janyo ta ya ku

ma tura ta a kan gadon.

ya bita yana kokuwan tub'e rigar jikin ta.

jikin ta na b'ari tarika ture shi tana kuka kamar zata shid'e.

ganin yana daf da cire mata riga, takuma takarkarewa ta yanka masa cizo a kunne.

yana sakin ta ta mike aguje ta shige toilet t

a danna kofa ta murza key tana haki.

ta sulale kasa tare da kuma fashewa da kuka, tana toshe bakin ta...

A b'angaren su Miemie kuwa, har sun d'au hanyar A.A FIYA STREET.

d'aya daga cikin matan da suke cikin motar, ta ce da 'yan uwan ta

"Gaskiya fa dare

ya yi karfe 12 da wani abu, yaushe har muje gidan amarya mu kuma juyawa gida, dare zai mana sosai,

gaskiya muwuce gida kawai in yaso gobe sai muje,

dan Allah direba ka sauke mu ko a kan titin,

Area-rod ne mu karasa kaga babu masu abin hawan ma."

Miemie ta

juya ta kalle ta ta ce

"To ai muma dare zai mana yaushe har muje can."

"Dan Allah kiyi hakuri baiwar Allah tun da motar gida ce zaku koma ai, yanzu mu idan aka sauke mu a nan babu abin hawan da zata kwashe mu,

ki tai maka a sauke mu a can d'in.

Miemie ta y

i shiru tana jan kwafa a kasan ranta.

direba ya juya akalar tafiyar ta su izuwa Area-rod.

a bakin titi suka sauke su kafin su suka juyo gida.

Ko da suka iso gida, duk motoci sun dawo har kowa ya shige b'angaren su.

amarya tana side d'in angon ta a b'anga

re d'aya na cikin side d'in.

a babban parking lot ya gyara fakin ta fito.

ta nufi sashin su.

tun daga nesa ta hango Abdurrahim tsaye cikin lambon gefen sashin hajiya.

yana sanye da wando 3qtr da singilet, hannunsa d'aya ya zura cikin aljuhun wandon d'aya h

annun nasa kuma yana rike da mug, yana d'an kurb'ar Coffee.

a hankali ta karaso batayi sammanin zai tare ta ya tambaye ta ina ta fito ba dan yasan daga gun bikin sa suke,

sai kuma ta ji akasin haka.

"Ina kika tsaya sai yanzu kika dawo, ina sauran suke."

d

a sauri ta ce

"Wasu 'yan uwan amarya ne suka bi motar mu muka sauke su a unguwar su,

su Ameerah kuma sun riga mu dawowa ma."

"Kowa ya dawo ke kad'ai ce a waje?."

kai ta gyad'a ta ce "Eh."

kai ya jinjina tare da kai mug d'in bakin sa yad'an kurb'a.

sannan y

a juya a hankali.

Har itama zata juya ta jiyo maganar Aunty.

"Miemie har kun bani tsoro ina kuka tsaya ne, har sai yanzu kuka dawo, ina Feeryal d'in take?, kowa ya dawo gida ku kuna waje."

Miemie ta ce

"Feeryal kuma ai tun d'azu ta dawo motar su ma ya r

iga namu dawowa, dan mu sai da muka biya muka sauke mutane kafin muka juyo gida."

"To ina ta shiga ke nan ban ganta ba, dan tun d'azu nake zaune a parlour ina zaman jiran dawowar ku, a wata motar ce ta dawo?."

Miemie ta ce

"A motar 'yan'uwan amarya, motar

mu data cika ne wata 'yar'uwar amarya ta ce tazo su shiga motar,

mun rigasu tashi kam amma nasan dole zasu rigamu isowa dan mu sai da mukaje Area-rod kafin muka juyo gida."

da sauri Aunty ta juya tana fad'in

"To ko tazo ta shige d'aki ne san da na tashi a

parlor'n banga shigar ta ba.

Abdurrahim ya tsaida tafiyar da yake a hankali wanda yake jin duk abin da suke fad'a.

Miemie ta juya tana shirin bin bayan Aunty ya ce

"Ke Miemie zo nan."

da sauri ta zo inda yake.

ya tsare ta da ido tare da fad'in

"Ya akayi k

un tafi tare ke kika dawo ke kad'ai, wace ce 'yar'uwar amaryar da ta biyo, dama ta santa ne?."

da sauri ta girgiza kai

"Aa bata santa ba a gun bikin muka had'u."

"Baku santa ba ta biyo ta?."

ya jefa mata tambayar yana dad'a tsare ta da ido.

in'ina ta soma

da tsoron kar ta karb'i tsarabar bulala ta ce

"Am..im dama...dama muna zaune ne tazo gurin zaman mu ta ce tana son Feeryal da kawa,

bayan antashi kuma mutane suka cika motar mu, shine ta ce Feeryal ta sauko ga mota can suje su shiga, itama nan gidan zataz

o dama kawo amarya zasuyi."

Ido ya tsare ta dashi da kyau kamar mai son karantar wani abu.

"Uhum dama ku da wasu kuka je?."

yakuma jefa mata tambayar.

"Aa ni da ita kawai mukaje, mutanen da suka biyo motar mu kuma cewa sukayi motar da suka zo ciki ya taf

i."

Kai ya jinjina bai kuma cewa ko mai ba ya nufi side d'in sa ta kofar baya.

ita kuma ta bi bayan Aunty da sauri.

Bai jima da shiga ba ya fito rike da makullin mota.

motar da ya dawo da ita d'azu ya aje ta a babban parking lot ya shige ya yi wa motar k

ey masu gadi suka bud'e masa get ya fi.

Karfe 1 da mintuna 30 ya isa Hall d'in da akayi shagalin bikin nasa.

a wajen get ya faka motar kana ya fito ya yi yi knocking d'in get d'in.

masu gadi suka bud'e karamar kofa.

ganin shine suka ce ya shigo,

hannu suk

a mika masa suna yi masa ban gajiyar biki.

ba yabo ba fallasa ya amsa su.

d'aya daga cikin su ya washe baki yana cewa

"Ranka shidad'e ya muka gan ka a irin wannan lokacin ko amarya ce tayi mantuwa aka zo d'auka mata."

tsayuwar sa ya gyara ya ce

"No! kowa

ya tafi an gama watsewa ko a kwai sauran mutane?."

"Ai ranka shidad'e tun karfe 1 aka gama watsewa babu ko wa a nan."

"Ina ma'aikatan CCTV camera na nan?."

Suka nuna masa da hanu suna cewa gasu ta can.

da d'an sauri ya nufi kofar da aka nuna masa.

ya bu

bbuga kofar aka bud'e.

mutane uku ne cikin office d'in zaune gaban computer.

ya mika musu hannu yana cewa

"I'm Dr Abdurrahim A.A FIYA."

da sauri suma suka miko masa hannu suna fad'in

"Ango mun gane ka ai daga ta cikin nan muke hango ka, muna taya ka murna

."

kai ya jinjina kasa ya ce

"Yauwa d'aukar nan nake son gani a fito min da shi."

"To an gama yellab'oi."

Nan da nan suka kusa cikin na'urar suka soma zakulo duk abin da ya faru a gurin. tun daga soma decoration d'in gurin har zuwa san da aka tashi kowa

ya watse.

shiru ya yi idanunsa akan Computer, da alamun nazari yake cikin kwakwalwarsa sai kuma da sauri ya ce

"D'an dawo da baya ka zuko nan."

dai-dai in da ya hango budurwar da ta zo gurin su Feeryal d'in.

ya kuma cewa a koma baya, daga in da ta taso dag

a gurin zaman ta.

ido ya kurawa mutanen da take tare da su.

da ganin su ba sai an fad'a ba b'ata garin samaruka ne,

sosai ya maida hankalin sa kan wanda yake busa sigari yana yi wa yarinyar nuni da hanu,

in da su Miemie suke.

da sauri ya ce

"Kunna mad'auki

n magana, zuko muryar me yake gaya mata!."

"Sir mad'aukin maganar gurin ya d'an sami masala ba'a jin magana ta gurin."

tsayuwar sa ya gyara tare da kalmashe hannayen sa a kirji yana karantar lab'b'ansu tare da fassara kalmomin su cikin kwakwalwa da zuciya

r sa.

Zare hannayen sa ya yi a kirji tare da shafa sumar kansa san da yaga, ta iso gurin zaman su,

a takaitaccen lokaci sun saki jiki da ita, har Feeryal tana yi mata murmushi.

ya yi musu alama da hanu suyi gaba, dai-dai san da aka tashi har suka fito gu

rin mota,

da in da budurwar ta tafi taje ta sami mutanen da tace suje su shiga motar su,

sannan ta wuce gurin samarukan daga nan kuma ta kuma dawowa gurin motar ta fidda

Feeryal daga cikin motar.

suka shiga wata mota, da wad'an nan maza uku da suke tare d

a yarinyar.

"Oh sheet!."

ya furta tare da naushin iska.

suma ma'aikatan jikin su ya yi sanyi sosai duk da basu san me ke faruwa ba amma sun fahimci shirine na kwamushe.

"Sir kalli nan."

suka fad'a suna nuna masa cikin computer.

da sauri ya sauke idanunsa k

an dai-dai in da budurwar ta sauka ta shige wata mota tana yiwa Feeryal bye bye, sukayi gaba.

motar da Feeryal d'in take ciki shima yabi wata hanyar.

Da sauri ya ce

"Bi bayan motar ta ina sukayi!."

"Daga nan ne camera'n mu dake wannan kusurwar ta tsaya."

da sauri ya juya ya fita.

masu gadi suna yi masa sai da safe, hannu kawai ya d'aga mu ya yi waje cikin hanzari ya shige motar sa...

Feeryal na durkushe cikin toilet sai b'ari take da rusar kuka.

shiko sai bubbuga kofar ya ke yana cewa

idan bata bud'e

ba idan ya b'alla kofar ya shigo sai ya yi mata kaca-kaca, ba shi kad'ai ba sai ya kira yaransa ma sun yi,

daga nan su jefar da ita a titi.

ganin zata bashi wuya ne har ta fara gajiyar da shi.

ya zaro wayarsa ya daddanna ya kai kunne

"Kuyi sauri ku shigo y

arinyar nan zata bani matsala."

yana fad'in haka ya sauke wayar.

Kai ta girgiza murya na rawa kamar tana gaban sa cikin muryar kuka take fad'in

"Ka dubi girman Allah karabu da ni, kar ka cutar da ni kaji tsoron Allah wayyo Ammie na, dan Allah kayi hakuri,

ka barni na tafi kada ku cutar da ni,

na rokeka dan Allah."

ta kuma fashewa da kuka tana dad'a rab'ewa jikin murfin kofar toilet d'in.

bata rufa baki ba mazan nan biyu suka shigo.

ya ce

"Ku b'alla kofar nan ku fito min da ita,

ku baje min ita anan, idan n

a gama na baku ku karasa."

Wani karfe suka d'auka suka rika dukan kofar da shi..

Wani kyakkyawan bugu sukayi wa kofar sai da ta b'alle.

kara ta saka tana ja da baya cikin matukar tashin hankali.

suka shige toilet d'in suka ciccib'o ta suka fito da ita.

a

kan gado suka wurgata.

suka shiga jan kayan jikinta suna yagashi.

wani irin kuka take kamar ranta zai fita.

da sauri ya shiga tub'e kayan jikin sa yana fad'in

"Wannan yarinyar akwai masifar taurin kai, duk yadda za'ayi ku tub'e min ita gaba d'aya ku baje m

in ita, na nuna mata taurin kai."

Wani irin zabura waziri Kutup ya yi ya zube gaban sarki Matip, ya murza gashin bakin sa fuskar sa tayi tsananin baki sabar b'acin rai.

"Tuba nake ya shugaba na, nakasa jure ganin halin da take ciki ne,

ka gafarce ni akan

maganar da zan kuma duk da ka hane ni,

da zaka bani dama da na umurci runduna, mun cinmusu,

ta firgita kwarai da gaske da lamarin su."

Chuchu da Chulu da suke durkushe bisa gwuiwowin su, suna haki cikin sananin tafasar zuciya.

suka ce

"Ba sai an je da ru

nduna ba mu d'in nan kad'ai zamu iya da su ko da sun kai runduna guda ne."

sarki Matip ya girgiza kai yana cewa

"Tabbaci da yakini kariyar da yafi namu yana gare sa,

kafin tabbaci akan koren ganye izuwa ja,

idan ya bari wani abu ya faru da ita to tabbas ya

tabbata an sami rud'anin bincike, da kuwa ba zamu yafewa kanmu ba sai mun binciko shi a fad'in duniyar nan,

ku da kanku kuka zo min da amsar koren ganye izuwa ja,

ku d'ora yakini da tabbaci a kansa yana d'aure da nauyin da shi kansa bai san da shi a kansa

ba,

shi d'in garkuwa ne a gare ta."

duk sukayi kasa da kawunan su suna d'aukar tabbaci...

Da karfi yaja burki a dai-dai kwanar da yaga motar ta shiga ya kurawa hanyar ido, kana da karfi ya kuma figar motar ya kusa cikin layin.

har ya yi nisa ya kuma j

uyowa ya rage gudun motar yana son tabbatar wa kansa rubutun da ke jikin sainbot d'in da ya wuce.

Shanawa Hotel.

sunan da ke rubuce a jikin sainbot d'in ke nan.

da sauri ya kashe motar ya fito ya nufi get d'in ya shige cikin hanzari....!

*Naso na baku y

afi haka amma ban samu dama ba, sai kuyi maneji da shi, idan bacci bai d'auke ni ba zan iya kara muku abin da ya sauwaka zuwa da safe na baku,

ba alkawari bane idan Allah ya nufe ni banyi bacci ba na ce zan yi*

😂

16

Da karfi ya tura kofar get d'in mas

u gadin suka mike, suna kokarin dakatar da shi.

idanun sa ya sauka a kan lambar motar da a ka d'auke ta.

cikin karaji ya ce

"Ina suke ta ina sukayi masu wancan motar."

yana maganar yana nufa gurin motar.

masu gadin suka biyo shi suna cewa

"Babu wan da suk

azo a motar nan wannan motar kamma tun jiya take nan, ba'a fita da ita ko ina ba."

a zafafe ya bud'e murfin motar tare da zaro wayar sa cikin aljuhu ya kunna torch d'in wayar, yana haska cikin motar.

da sauri

ya mika hanu ya janyo gyalenta da yagani kasan

sit ya d'ago yana kare masa kallo.

"An ce maka wannan motar tun jiya take nan, me kake nima cikin sa."

wani irin juyawa ya yi tare da d'auke shi da wani irin gigitaccen marin da sai da ya yi tangad'i ya zube kasa.

da sauri d'ayan ya ja baya jiki na rawa.

c

ikin fusatacciyar murya mai had'e da tafasar zuciya ya ce

"Idan kuka kuma da katar da ni sai na yanke harshenan ku!."

Da sauri duk sukayi baya har da wan da yake kasa dafe da kuncin sa, da yake jin sa kamar jini na fita sabar azabar marin da ya sha.

Da k

arfi ya juya yana taka kasa har ana jiyo sautin takun sa, dip-dip-dip!.

yana dad'a damke gyalenta dake hannunsa ya shige cikin hotel d'in.

Direct gurin ma'aikatan hotel d'in ya nufa masu kula da kyamarorin tsaro.

ya ce su binciko masa list d'in wad'an da

suke cikin hotel d'in da time d'in da kowa ya zo.

ganin binciken nasu na yi masa nawa ya juya da sauri har yana had'awa da gudu-gudu,

yana bin kofafin room d'in kasa yana kasa kunnen sa.

sai da ya zaga kofofin kusan duka, ya d'aga kafa zai haura stairs, a

hankali ya dawo da baya ya juya yana kallon wata kofa dake ta can gefe da stairs d'in.

sai kuma da sauri ya isa kofar room d'in idanunsa a kasa yana kallon abin da ke yashe a kasa dai-dai bakin kofar.

a hankali ya durkusa ya d'auko shi yana juyashi a han

nunsa,

ya yin da yashiga hasko yanda ya ganta a gun shagalin bikin su tabbas d'ankwalin ta ne wannan.

bai dawo daga tunanin da yake ba yajiyo ihu cikin d'akin.

Ido ya waro da karfi tare da sakin d'ankwali da gyalen hannunsa kasa.

cikin tsananin tafasar zu

ciya ya yi wa kofar wani irin naushi d'aya a take ta b'alle.

A razane suka sake ta tare da d'agowa suna duban kofar.

Zazuu da ke kanta yana ta kokarin zare pant d'in ta, su kuma sun rirtike hannayenta sun bankare masa ita a haka ba tare da sun gama cire k

ayan jikin nata ba.

da sauri ya mike a kanta yana kallonsa, sai kuma ya ce

"Dalla ku bankare min ita kun tsaya kallon sa, idan nayi na gama sai kuyi ku bashi sauran da gani shima a hanu yake,

jira ka more kayan dad'i kaima,

bari na gama na baku sauran."

ya

koma yana kokarin bin jikin ta.

Wani irin takowa ya yi tamkar walkiya mai tafiya kan iska.

ya wani kai masa naushi a hanci tare da shako makogwaron sa, da sai da idanunsa suka firfito kamar zasu fad'o kasa.

nan da nan jini yashi tsastsafowa a hancinsa ga

mi da bakin sa.

ya wani irin janyo shi ya had'a sa da jikin garu-bango.

ji kake gomm!

ya saki wani wahalellen kara.

da gudu mutane biyun sukayiyo kansa, dukansu ya had'e su ya shako wuyan su, ya rika had'a su da jikin garu sai da ya yi musu jina-jina kafin

ya sake su suka zube kasa suna numfarfashin azaba.

yakuma bin su da naushi dukan su da ogan nasu dake zube kasa yana ganin guri na juya masa.

rai b'ace ya ke fad'in

"Ku ga kunan tantiran 'yan iska ko daga kan yau bazaku sake kokarin yi wa wata fyad'e ba."

sai da yaga basa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login