Showing 1 words to 3000 words out of 109651 words

Chapter 1 - A KAN SHI complete by Maman Abdallah

31 Oct 2025

3117

??????>?? ? ????????????? ? ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F? WordDocument????1R0Table?????????
Data
????????????????????? P?B?KSKS?1R??????????kkkk38????k??
?
?
?
?
?
?
? ?? >?kk?
?
kkkk?
? ?k? ?
k?
? k?
?
kk [15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: =??? AKANNN SHI =???
BY
KADIDJA BASHIR
(Maman Abdallah)

Marubuciyar Littafin
=?G?
MUGUNTA FITSARIN FAKO
And new

AKAN SHI
`(Paid Book ne, ya koma free akan wani dalilina na daban, ?ar uwa gyara zama kisha karatu, A KANSHI labari ne mai shiga zuci)```


_ Bismillahir rahamanir rahamin


Page 1&2

Shuru kake ji kamar babu wani mai rai a cikin wajan, baka jin komai sai Saukar Nunfashin Mutanan dake zaune .
Yadda tsarin wajan yake shi ya tabbatar mini da kotu ne , gyara tsayuwa ta nayi na fuskanci inda nake Tunanin nan ne aka tanada dan zaman Al?ali, wani Babban mutun nagani mai cikar kamala da haiba, sanye da Manyan Kaya na Alfarma, da Hirami akan shi, ya sanya farin glass a Idanunsa, wanda yake ?ara masa ?arfin gani, Sakamakon yana fama da lalurar Idanu, ga kuma Shekaru da suka fara ja.


Dattijo dan kimanin shekaru sattin da uku Duniya, Malam Inuwa Masa'ud kenan, Al?ali mai Gaskiya a cikin jerin Al?alan da da jama'a suke alfaharin dasu.a wannan Gari, Wan gani Kashenin Gaskiya ne komai ?acinta, akan ri?on Gaskiyar sa, dayin Hukunci kamar yadda ya sauka daga sama , aka yi masa sanadin duka Iyalan sa har lahira.


Ameen ameen naji suna faWa duka wajan , sai yanzu na lura ashe tun Shigowa ta wajan adu'ar buWe taro ake, tare da yin salati ga Ma'aikin Allah .
yana daga cikin ?a'idar Malam Inuwa komai ayi shi akan sunnar Ma'aiki s.a.w , shi ya Umar cemu da mu ?awata wajan zaman mu , da yin Salati a gareshi, dan haskene a garemu ranar tashin Al?iyama.
Ubangiji da kansa yayi al?awarin duk wani abun da aka Sudasa da sunan Habibin sa, to yanajin ?unya maido da wannan abu ba tare da an duba kuma an karSe sa ba.
Jama'a nace Annabi Muhammadu ...........
Duk wanda bai ce S.A.W ba to shine babban marowaci a wannan Duniyar, haka ya faWa s.a.w.

Wajan zama nima na nema na zauna a kusa da wata Mata, kukan da take ne a hankali yasa na kalli sashen da take zaune, Farar Mace ce amma ba fara cancan ba, tanada tsago guda biyu a gefe da gefen Fuskar ta, Fuskar nan duk ta Kumbura alamar kodai tasha kuka ko kuma batada Cikakkiyar Lafiya, Atamfa ce a jikin ta mai Mafaidaitan kuWi wajan saya, da alama matar tana da tsabta sosai dan ko takalman da ke ?at'farta a wanke yake tas kamar ba ?asa ta tako kafin ta iso kotun ba.
Juyowa tayi Sashen da nake, ganin zata kamani ina kallon ta yasa na maida Hankali na wajan Al?ali.

Gam, gam, gam ya buga Teburin da yake gabansa da Gudumar Hannun sa, nan waje ya sake yin tsit kamar ba kowa, cikin DaddaWan Muryar shi mai Cikar kamala yace '' maga takarda muna sauraron ka'' , wani dan Matashi ya mike daga inda yake a Zaune, ya mi?a wa al?ali takardun da yake Hannunsa ta ?ar kantar da take tsakanin su kafin ya daidaita tsayuwar sa yace '' yau muna biyar ga watan Rabi'ul Auwal , wanda yayi daidai da Bakwai ga september, ya dauko wata Takardar da take ajiye akan sauran takardun da yake gaban sa , ya cigaba da cewa yau za'aci gaba da sauran Shari'ar da ake yiwa Hasiya Ibrahim, ana zargin ta kashe Mijin Auren ta Mukhtar, bayan basu fi watanni Biyu da Kasancewa Ma'aurata ba '' yana faWin hakan ya zauna a Mazaunin sa .
Al?ali inuwa ya kalli securityn da yake kusa da kanshi a tsaye yace ''a shigo da wacce ake zargi '' , cikin Girmamawa ya Amsa tare da barin wajan.
Wannan tsarin Malam Inuwa ne , killace wanda ake kan Shari'a dashi daga wajan Mutane, dan kar yawan zantuttukansu ya giSi tashi ya kasa bada Amsar Tambaya yayin da ake masa, ?arfe bakwai daidai Motar ?an'sanda ta kawo ta Kotun tare da Rakiyar jami'an da zasu tsare ta har a gama Shari'ar a ga Sakamakon da ta bada, shine aka fice da ita can Cikin kafin lokacin Shari'a yayi.


Shigowa akayi da ita kanta a kasa , Matashiyar da za'a iya kiranta Budurwa a inda ba'asan anyi mata Aure ba, sanye take da ba?ar abata ajikinta, da kuma ba?in hijaSi, Hannun ta a cikin ancor haka securitys guda biyu mata suka shigo da ita, bisa jagorancin wannan securityn Wan aike.
Har wajan da aka saba sakata ta tsaya suka kaita, kafin daya ta tsaya daga dama Waya kuma daga hagu, har yanzu kanta a kasa .
Gyaran murya Malam Inuwa yayi yace '' Masha Allah, Allah ya kuma nuna mana yau a Matsayin Rana ta ?arshe da za'a gama wannan Shari'a, Hasiya '' ya ambaci sunan ta .


?ago da kanta ta tayi , masha Allah babu wanda zai ga Fuskar Hasiya bai yaba da kyawun ta, ba fata bace, ba kuma za'a kirata da ba?a ba, rashin walwalar da yake kan Fuskar ta shi ya bayyanar da Tsananin Tashin Hankalin da take ciki, a da yarinya ce mai yawon raha , amma yanzu ?unci shine abokin rayuwar ta.
Sashen da mutane suke zaune ta kallo, karaf suka haWa ido da Mahaifiyar ta, wacce har ta sauya kamanni a kamar data santa a da, da sauri ta kauda kanta zuwa wani gefen, dan bata san Wan ?warin gwiwar data samu ya ?oranye Sanadiyar ganin rauni a tare da Mahaifiyar Tata.
'' Hasiya '' ya kuma kiranta a karo na biyu, cikin Muryar ta data gaji da kuka har ta dashe ta amsa da '' na'am '' , '' yau ne rana ta ?arshe dan gane da zaman da muke akan Mutuwar mai gidan ki Mukhtar, shin sami lauyan da zai kare ki '' al?ali ya tambaye ta cikin Mutuntawa. '' a'a Ni har yanzu banida lauya '' ta faWi kanta a ?asa , ''shin Lauyan wa'yanda suke ?ara yana kusa ?'' yayi Tambaya yana kallon sashen da Lauyoyi suke zaune, '' eh ina nan Allah ya Gafarta Malam '' cewar Barister Lawali ?alha tare da mekewa daga inda yake zaune , ya fito dan filin dakeTsakanin su da inda Hasiya take , ya kuma cewa '' Allah ya Gafarta Malam wannan abu a bayyane yake cewa Hasiya ita ta kashe Mukhtar bisa La'akari da Hujjoji dana bayar tun a Zaman farko, saboda haka ina neman Alfarmar wannan kotun Muslunci mai albarka data Hukunta wannan baiwar Allah daidai da Hukuncin da Ubangiji ya zartas akan duk wanda ya kashe rai ba akan hakkin Shari'a ba '' ya kara da cewa idan har ba ita ta kashe shiba ai da tuni sun nemi Lauyan da zai kare ta, ranka ya daWe tsawan lokaci ana ta Waga wannan Shari'ar a wannan karon ina neman Alfarma da ayi Gaggawar yanke Hukunci Nagode '' ya karasa maganar da risinawa alamar Girmamawa kafin ya komawa wajan zaman sa ya zauna.
Malam Inuwa ya fara wasu ?an rubuce rubuce a takardar dake gaban sa.

Kukan Maman Hasiya ne ya cika ilahirin kotun , da gudu tazo wajan da tarin Lauyoyin da zasu kai takwas wasunsu suna jiran lokacin da za'a gabatar da Shari'ar da suke Jagoranta, kusa da ?afafuwan su ta zube tana kuka mai tsuma rai, Nunfashin kamar zai bar Gangar jikin ta, tabbas wannan Jarabawar Hasiya ce amma ita tafi ta jin zafi da raWaWin wannan Intila'in daya tunkaro su Bagtatan ba Tsammani, cikin kuka mai Tsuma rai tace '' dan Allah ku taimaka mana , kamar yadda Allah ya taimake ku ya baku dama, wallahi bata aikata abinda ake zargin ta dashi ba, ta ?a?a zata kashe mutumin datafi so sama da Rayuwar ta, *AKANSHI* bata ji , kuma bata gani, wallahi ba ita bace, dan Allah ka taimake Ni ka tsaya wa ?ata dan Allah'' Mama Kuburah ta ?arasa Maganar leka ri?e ?afar Lauya Lawali wanda ya gama zuba zance da bada Hujjoji akan Lallai Hasiyar ita ta kashe Mijin ta Mukhtar, cike da Dubara ya janye ?afar sa daga ri?on da tayi masa, yayi wani Murmushi mai sauti, wanda sai da ya Hankalin jama'ar dake Kotun, wanda kowa yake faWin albarkacin bakin sa game da Shari'ar .
Cikin Kissa, Makirci da iya Waure Mutun yayi kalar tausayi yace '' haba Mama wannan ai ba Girman ki bane, koma miye ai bai kai har ki dafa ?afafuwa naba, wannan abu dai anriga da anyi shi, ina mai baki Shawara Wazu mai?a wuya ku faWi Gaskiya, ta yiyu ta sami Sassauci wajan yanke mata Hukunci, koda dai kowa yasan Hukuncin wanda ya kashe Mutun a Shari'ar Muslunci '' ya ci gaba da cewa nidai abinda nake gani kenan, amma idan har kina Tunanin zaki samu wanda zai kare ta shikenan, sai Ku Gabatar dashi a Matsayin Lauyan da zai kare ta , wannan Shawara ce '' ya faWa yana Waga kafaWa alamar ya rage nata.

Malam Inuwa ya kuma buga Guduma a karo na uku, jin duka kotun ta Hargice da Cecekucen jama'a , nan kuwa waje yayi tsit , kowa ya haWi sauran zancen da yake bakin sa, bakajin komai sai kukan Mama da Ajiyar Zuciyar Hasiya, cikin Waga Murya Al?ali yace '' Malama Kuburah a karo na karshe zan Waga wannan Shari'a a karo na huWu kenan, jiya iyau, babu abinda ya canja a Tsakanin kwanakin da muka baku akan ku sami Lauyan da zai kare ku, baki shike yanka wuya, idan zaki tuna akwai Lokacin da ita kanta Hasiyar ta amsa cewa *AKANSHI* ne , bazamu san ma'anar wannan kalma ba , sai dai idan ita ce ta faWa da bakin ta, ko kuma munji daga bakin Lauyan ta, saboda haka , na daga wannan Shari'ar har zuwa Ashirin ga wata, zuwa wannan Lokaci ina fatan zaku sami Mafita da yardar Ubangiji, sannan kuma za'a cigaba da tsare Hasiya a Gidan Yari har Lokacin da muka Wauka ya ?araso, abu na biyu a wannan karon za'a iya Ziyartar ta, kama daga Iyayenta, kodai wasu Makusantan ta'' Malam Inuwa ya faWa haka tare da yin Rubutu a Takardar dake gaban sa .

'' Ninan zan Tsaya mata '' suka ji Magana daga Bakin ?ofar shigowa Kotun................
[15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: *_AKAN SHI_*


Page 3&4
__________''Ninan zan Tsaya mata '' suka ji Magana daga bakin ?ofar shigowa Kotun.

Cike da izz ayake ?araso wa cikin Tsakiyar wajan, yanayin tafiyar sa kaWai ya isar maka kasan yana ji da karfin samar taka da kuma tsayuwa akan Digadigin sa, farar shaddar ce a jikin sa da kuma hula zanna, fari ba fari sosai ba, Wan ?aramin kewayayyan sakan sa, shi ya ?ara ?awata kyakkyawar Fuskar sa,har inda Maman Hasiya yake tsaye ya iso, hannu yasa ya goke mata Hawayen da suke ?oranya daga Idanun ta.
Ba jama'ar da suke wajan ba, hatta Malam Inuwa sai da yayi Mamakin Ganin wannan bawan Allah da kuma aikin sakan daya sa kansa aciki da ranar gari.
Kama Hannun Mama Kuburah yayi ya isa da ita wata kujera mafi kusa da inda suke ya Zaunar da ita, tissu ya ciro daga aljihunsa ya mi?a mata , da har yayi gaba , sai kuma ya dawo kusa da ita ya ce '' Mama daga Rana Mai kamar ta yau bazaki sake kuka a wannan Duniyar ba Matu?ar ina Nunfashi, idan kuma har hakan ta faru, to ki tabbar na farin ciki ne zakiyi, akasin hakan bazan taSa yafewa kaina ba'' yana gama faWin hakan yayi gaba abinda, ya bar Mama da sar?ekken baki tana kallon ikon Allah.


Malam Inuwa daya tafka tafimu hannu bibbiyu ya sauke yana mai Godiya ga Ubangiji a cikin ransa.
tun shigowar sa wajan yake kallon sa, yasan komai zai zo masa da sau?i dan gane da wannan Shari'rar da take hana sa bacci da idanun sa.


'' Sunana Barister Jalaluddeen Umar Mainasara , amma anfi sanina da Maina, nine Lauyan wacce ake kara, Allah ya Gafarta Malam yanzun haka daga tafiya nake bansan komai game da abunda ake zargin ta dashi '' ya nuna sashen da Hasiya take ba tare da ya kalli inda take ba, ya kuma cewa '' ina neman Alfarma da a kara lokacin da aka yanka na zaman ?arshe na wannan Shari'ar '' Maina ya faWa ana kallon Malam Inuwa da farin cikin ganin Jalaluddeen din , jin yaron yake kamar shi ya haifeshi da kansa, yayi Mamaki sosai daya ganshi a daidai wannan lokaci, bayan har gida yazo ya gaya masa zai tafi wani coz na tsawon wata uku, kuma zancan baifi wata daya ba yanzu, kuma ko bayan ya isa ?asar Garmany sai da suka yi Magana kusan sau biyu.Ajiyar zuciya Al?ali ya sauke kafin yace '' wannan kotu mai tarihi ta kara tsawon lokacin sauraron shari'ar Hasiya, daga Ashirin ga wata zuwa Waya da sabon wata, bisa neman Alfarmar da Lauyan wacce ake zargi ya nema '', ya buga Gudumar sa alamar anka karshen zaman shari'ar, nan wajan ya amsa da kabbara Allahu Akbar.
Bajimawa aka fita da Hasiya dan maidata gidan yarin da ake tsare da ita.


A Bakin motar ?an sandan suke tsaye, sosai Maman take kuka,A kullum abun ?ara daure mata kai yake , a e wai Hasiya ce ta kashe Mukhtar, gaskiya ba abinda Hankali zai iya Wauka bane .
Da sallama ya iso inda suke , kan Hasiya a ?asa , sai dai ta wayi Murya a ?an mintunan da Bazasu gaza talatin ba ta hardace ta , Anty Zuwaira ma?obciyar su da tayiwa Mama kara ta biyo ta , ita kaWai ta iya amsa sallamar da yayi .
dan shuru yayi yana ?ara Nazarin su baki Waya kafin yace '' Mama kuyi Ha?uri dan Allah, insha Allah komai zai zo mana da sau?i, nidai kawai ku bani haWin kai game da duk wata tambayar da zan muku .
'' yallaSai lokacin da aka bata ya kare '' cewar wani securityn da yake tsaye a kusa dasu, ajiyar zuciya Hasiya ta sauke ta kalli Mahaifiyar ta tace '' Mama zamu tafi, dan Allah karki gaza wajan yimin adu'a, nasan kina yi amma dan Allah ki ?ara, Allah ya na gani, Kuma shi ya Hukumta hakan ya faru, sannan dan Allah ki rage damuwa Umma na dan Allah '' Juyawa tayi wajan Maina tace Nagode, kafin ta shiga Motar da aka tsare ta hagu da daman ta ba Hanyar guduwa, haka suka bar wajan.


Kukan Mama ne ya tsanan ta , Anty Zuwaira tana bata baki, tare da Tunatar da ita Muhimmanci yarda da ?addara ko wace iri, Allah yakan Jarabceka dan yaga ?arfin Imanin ka.
Wayar sa ya ciro daga aljihunsa ya kira wata number, dai ji suka yi yana faWin '' kazo da Wauke ni'' nan ya kwatanta wanda ya kira inda zai sameshi.
Juyawa yayi ya kalli Mama yace '' Mama yanzu zamu ajiyeku a gida , insha Allah zuwa safe zan shigo sai muyi Magana, pls ki rage damuwa da wannan kukan , zai iya haifar miki da wani ciwon, mu kuma Bama fatan hakan, ki kula da ita tana cikin damuwa sosai'' ya karasa maganar yana kallon anty Zuwaira.


Cikin Mintunan da Bazasu wuce goma ba Kalil ya iso da Motar sa ?irar TOYOTA sabuwar shigowar da batafi wata biyu da yayi odar taba , kusan ma zasu fara hidimar bikin abokin nasa Maina ya siye ta, parking yayi a daidai inda suke tsaye , daidai da Fitowar Barister Lawali daga kotun yana shirin Waga kiran daya Shigo wayar sa, duk a tsorace yake, tun lokacin da yaga Shigowar Maina kotun ya shiga tashin hankali mara Misali, har wani kaWawa yaji cikin sa yana masa, tun Wazu yake so ya fito ya sami wajan daya zagaya, amma yana tsorn kar ya fito ya kuma yin arba dashi, dai ya dake yana ta Matsematse daga zaune, ko Shari'ar da aka fara bayan tasu bazai iya faWin yadda take kaya waba, yanzu ma kiran uwar Wakinsa ne ya hana shi sukunin zama har ya fito dan amsa kiran.


Karaf suka haWa ido da Maina, lokacin yana buWewa su Mama murfin Mota da ido yayi musu alama da su shiga , dan shi ba ma'abocin yawan Magana bane , ba musu suka shiga ya rufe , har yanzu idanunsa akan Lawali, shidai Kalil kawai kallon su yake , ya kalli Lawali, ya kalli Maina.

Cikin Daburcewa ya Waga wayar ganin wani kiran ya kuma shigowa a karo na ba adadi , '' wai mi yake faruwa ne naji an daga Shari'ar nan , Lawali anya zaka iya wannan aikin kuwa?'' aka tambaye shi da Murya da bansan ko ta waye ba, amma Muryar Babbar Macece.
In ina ya fara wajan bata amsa, dan mamaki yake yi jin har an gaya Mata yadda aka yi wajan Shari'ar, '' tabbas Shaidaniya ce '' ya faWa a bayyane ba tare da yasan bayi duSutar baki ba.
'' Miye kake cewa Lawali, Kasan dawa kake Magana kuwa ?'' , ta faWa a fusace .
'' Kiyi Hakuri Hajiya, wallahi nasake nake ba, mistake ne, kuma ma ai kinsan bazan fadi hakan akan kiba'' ya faWa duk jiSi ya jika masa jiki jin ?anyan aikin daya kwai ya Wauko wa kansa, '' kazo gida ina neman ka'' bata jira amsar da zai bata ba ta kashe wayar .


Juyawar da zai yi suka yi karo da Maina da yaWade a bayan sa tun lokacin daya daga wayar, Murmushin gefen baki yayi masa , ya kashe masa ido Waya , cikin sha?iyanci yace '' sai wani ji?on '' ya faWa tare da barin wajan, shiga motar yayi Kalil yaja suka bar wajen, suka bar Barister Lawali da jike??en wando, wanda ni kaina bazan iya faWin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login