Showing 93001 words to 96000 words out of 109651 words

Chapter 32 - A KAN SHI complete by Maman Abdallah

31 Oct 2025

3125

da ya yi tasan sarari saboda sar?afa ne ya ce hakanan, tun ba yau ba ta gane da halin yaron nata yana da sarai sosai a game da matar tasa.


Yanzu ma kwance take a gado tana barci, wanda da alama baya mata daWi ko kaWan, duk da sanyin ac'n dake Wakin ga kuma ranka hakan bai tsayar da tsatsafowar jiSi daga ko'ina na jikinta ba, mirginawa ta yi da nufin ta rungume mijinta ko Allah zai gawo mata karshen abinda take ji amma sai taji wayan babu mutun a kusa da ita, a kuma dai-dai nan ne ta kurma ihu tana kiran Mo..........

Ayi ha?uri dan Allah ba editing, abubuwan ne dayawa>?y?
[15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: _*A KAN SHI*_
Amma ba editing fa>?s?>?s?>?s?>?s?
Page 42 __________ Dai-dai da fitowar sa daga toilet ya Wauro alwala da nufin yin ?iyamullaili yaji ta ?urma wannan ihun tana ambaton sunan Momyn ta, da gudu ya isa kusa da gadon yana hayewa sama tare da sakata a jikinsa bayan dama ta tashi zaune a gigice, wani irin nunfashi take fitarwa wanda sai da ya bawa Hisham tsoro, a lokacin kuma duk addu'ar data zo bakinsa tofa mata yake yi, sun fi mintuna goma a haka kafin ta saki wani irin kuka mai ban tausayi, ai kuwa nan hankalin Hisham ya kuma tashi, ji da ganin kumar matarsa tana kuka cikin yanayin tsoro da firgici da kuma tashin hankali.
Sai da ya Soye rauninsa kafin ya shiga share mata hawayenta tare da tambayar ta ba'asin kuka da firgita a tsakiyar daren nan.

Cikin kuka ta ke faWin ''Momy na! My Hisham Momy ce na gani a cikin wani hali tana neman taimako na, da iya ?arfinta take kirana akan in ceceta daga hannun wasu mutun biyu dana kasa ganin fuskokinsu, yau nin dake jikina yasa na kasa koda tashi daga inda nake Hisham, ina kallo mahaifiyata ta bacewa ganima cikin yanayin da bazan iya tamtance ba damuwa ne ko al'adun hakan ba, nidai abu Waya naji ta ce shi ne in ceceta ko ba anan ba.
Ka faWa min miye ma'ar wannan mafarkin nawa My? Mi yake faruwa da Momy? shhhin dama zunubban data aikata har yanzu basu daina bibiyar ta ba, shin duk da an yanke mata hukunci 5un anan duniya ba zata samu salama ba? Dan Allah ka tashi muje ka kaini in ganta, dan Allah'' ta ?arasa da sakin wani marayan kukan da yafi na farko tayar da hankalin mai sauraro.

Sai da ya share hawayenta fuskarsa kafin ya fara magana cike da tausasawa, dan a'har ga Allah shi yakan manta ma da wata Momy a cikin rayuwar matar tasa, gashi shi ne ma ya yanke mata hukunci dai-dai da laifukanta a lokacin, ''kina ji ko matar? Ki kwantar da hankalin ki mafarki ai ba gaskiya ba ne, kuma ma yanzu kinga dare ne sosai ya za'ayi mu fita yanzu, kuma koda mun fita kinsan dai warahaka bazamu iske gidan yarin a buWe ba ko?'' ya tambaye ta cikin rarrashi, cikin kukanta har yanzu ta ce ''ba sai kayi anfani da alfarmarka ba, nasan dole zasu barka mu shiga'', ''kinsan Allah ko! Koma waye bana jin ce wa warahaka za'a iya buWe mata kofar magar?ama ya shiga ko ya fito idan har ba safiya ta yi ba, ki daure kiyi shiru dan Allah, nayi miki al?awari da sanyin safiya kuma a lokutan farko na buWe gidan yarin zan kaiki mu dubota'', nan ta fara sassauta kukan nata, zuwa wani lokaci ta naye shi da ajiyar zuciya kai da kai, sun fi awa Waya a haka kafin wani barcin ya kuma Waukar ta a jikinsa, kwanciya kawai ya gyara mata kafin ya tofe su da addu'a, shima rufe idanunsa ya yi da nufin ya Wan samu ya yi barcin amma ya gagaresa, da zaran ya rufe ido fuskar Momy'n shima yake gani, a haka har aka kira sallar asuba hi, tashin ta ya yi dan yin sallah, da ?yar ta iya tashi ga nauyin ciki ga na ido ta nufi bayi dan yin alwala, a daddafe ta yi sallar kafin ido rufe ta koma kan gado ta kwanta idanunta duk nauyi, kafin kace kwabo barci ya kuma Wibarta.

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya dawo daga masallaci ya isko har ta yi salla ta koma ta kwanta, ya zata a rigimar zuwa gidan yarin zata motsa ashe ba haka bane, doguwar jallabiyar jikinsa ya cire tare da hayewa kan gadon yana mai lulluSe su, dan shima wani azababben barci yake ji, shi ne dalili cire rigar da yayi dan baya samun nutsuwar barci matu?ar da kayan da zasu ta?urasa a jikinsa.

?arfe takwas da ashirin dai-dai wayarsa ta Wauki ruri, wanda shi ne ya yi sanadiyyar farkawarsu dukkanin su, hannu yasa ya Wauki wayar yana mai duba malanocin yin kiran.
Da sauri ya mi?e zaune daga kwancan da yake tare da kara wayar a kunne yana mai faWin ''barka da asuba Dady, ina kwanan mu?'', ''lafiya ?alau Hisham ya gida? Da alama ma yanzu sagiyarka ta waye ba? Ka Wauko Hamdiyya zuwa nan gida akwai wani meeting na gaggawa daya tashi, idan da hali yanzu ba sai an jima ba'' Dady bai jira abinda Hisham zai maida masa ba ya katse kiran, bin wayar Hisham ya yi da ido yana tattaro jawaban Dady tare da Wora su bisa ma'aunin hankali, nan take yaji gabansa ya faWi, sashan Hamdiyya ya kalla da ta masa ?uri tana kallonsa kamar mai don nazartar yanayinsa, a hankali ya Waya baki da biyar faWa mata abinda Dady ya ce ta Waga masa hannu alamar dakatarwa, cikin sanyin murya ta ce ''naji duka abinda suka ce, to mi muke jiradda bazamu fara shiryawa ba, maza kama ni in mi?e, dan duka gaSoSina ki nake kamar ba'a jikina suke ba''.

Da taimakon Hisham ta gama shiryawa cikin riga da zabi na atanfa, zanin simple ne sai rigar iya daWo miyar nan irin na da, kuma ita ne tasa aka mata irinsu dan tafi jin dadin saka irinsu indai har zasu fita ne, inda a cikin gida kuma kullum daga dogayan rigina marasa nauyi ne a jikinta.

Motoci ne birjig a kofar gidan Dady, ga mutane da suke hangowa a zazzaune kamar a tabarma irin idan an yi mutuwar nan, tun daga cikin motar ta fara zubar da hawaye tun batadan wanda ya mutun ba, tadai san koma waye to anyi babban rashi.
?asa taka ?afarta ta yi da kanta lokacin da suka fito daga motar, gashi a wajan harda Papa da wasu makusantan su duka a wajan bare ya taimaka mata ta isa daga ciki, ana haka sai ga motar iyalan gidan Jalaluddeen Umar Mainasara ta iso baya kaWan daga inda Hisham Win ya yi parcking, hamdala Hisham ya yi a ransa dan Allah ne ya kawo masa mafita kai tsaye, a haka har suka iso kusa da su, Hasiya da Husnah kowa kansa a ?asa kamar yadda Hamdiyya ma nata kan a ?asa, a hankali Hisham ya kalli Hasiya da take kusa da Hamdiyya ya ce ''yawwa dan Allah ku taimaka ku isa da ita cikin gida, ta kasa isa da kanta ne, da to kawai Hasiya ta amsa shi lokacin Waya tana mai kama hannun Hamdiyya, inda itama Husnah Wayan hannun nata ta kama suka nufi cikin gida duk da ita ma idan ta samu mai kamatan so zata yi, tunda haka kawai Dady ya kira Maina akan suzo gida yanzun nan akwai meeting na gaggawa, sai iya abinda suka gani yanzu da suka tardo a ?ofar gidan, gashi basusan mi zasu iske a cikin gidan ba, sai dai dukkanninsu ukun sun sa arai kawai Grany ce Allah ya yi wa cikawa, tunda sunga alamar hakan tun a waje.

Suna isowa falon Ammy waje suka samu suka zauna, inda anan duka hango Grany zaune Ware Ware a kujera tana zaune da carbi a hannunta tana ta nanata kalmar shahada, da kuma nemawa magabata gafarar Ubangiji.

Duka cikinsu Hasiya ce tayi ?arfin halin gaishe da mutanen da suke falon, inda kowa ya amsa cikin jimami.
Wayar Ammy ce ta yi ?ara, tana Wagawa Dady ya ce da ita ''zamu tafi Waukar gawar a asibiti, dagacan zamu wuce da ita gidanta na gaskiya, ki faWawa jama'ar dake zaune, banda kuka! Sannan kowa ya yi mata addu'ar samun rahamar Ubangiji'', yana kai wa nan ya katse kiran.
?asa Ammy ta yi da kanta tare da fakaitar idanun mutane ta share hawayen da ta kasa rike su daga zubowa.
duka wannan abun da Ammy ta yi a kan idanun Hamdiyya, kawai sai taji ?irjinta ya yi mata nauyi sosai, kafin kace miye tuni ta ciri jiki ta isa gaban Ammy, luuu ta yi zata faWi Ammy'n ta taro ta tana faWin ''subahanallahi mi yake damunki Hamdiyya?'', cikin kuka ta ce ''Ammy ko baku faWa min da bakunanku ba ya isa in fahimta da ?aramar ?wa?walwata ce wa Momy ce ta rasu, dama kamar naso ganin hakan a mafarki na, shikenan yanzu banida uwa banida uba sai ku, Allah ya gafarta miki Momy ya mik....'' bata ?arasa ba nunfashinta ya fara fin ?arfin ?o?arin ta wajan fizgowa, cikin kidima jama'ar dake falon suka rufu a kansu, cikin tsananin tashin hankali ganin ta fasa nunfasawa Ammy ta ce ''dan Allah wani yaje ya kira Hisham'', da gudu Hasiya ta fita waje, amma ina duka mazan sun tafi wajan jana'izar kamar yadda Dady ya faWawa Ammy, an yi sa'a Wayan direban gidan yana nan, nan Hasiya y'ta sanar dashi ya dai-daita mota zasu fita da gaggawa, ba Sata lokaci ta koma cikin falon da sassarfa, nan take fada musu duka mazan babu kowa, amma zasu iya kaita asibiti kuma ta faWawa direba ma.

Hasiyar dai ita ce ta kama wa Ammy suka saka Hamdiyya a mota, inda Anty Mariya da Ammy suka shige gidan baya tallabe da ita, juyawa Hasiya ta yi da nufin komawa ciki wajan sauran mutanen amma sai taji Ammy tana faWin ''ina kuma zaki je? Yi ki shiga mu tafi lokaci yana ?ara tafiya''.

Asibitin su na yau da kullum suka nufa, kamar kullum haka aka tarbe su cikin karanci da girmamawa, an shiga da Hamdiyya Wakin da za'a duba ta, inda manyan likitoci guda biyu ne akan ta, ciki kuwa harda Dr Yahuzan daya duba Ammy ranar.

Kai kawo kowanensu yake ba zama, hankali duk ya tashi, musamman Ammy da take tunanin idan wani abun ya samu yarinyar ita kanta batasan halin da zata shiga ba, sai da ta ce wa Dady kar a sanar da duka yaran batun mutuwar Hadizan amma ya ce ba za'ayi haka ba.
Suna zaune a falon Hajiya jiya bayan sallar isha'i, Grany Dady da kuma Ammy, wayar Dady ta shiga ruri, yana dubawa yaga number da ake kiransa ce da ita daga gidan yarin da Hadiza take ko da bu?atar wani abun, yana Wagawa aka ce yazo gata nan ba lafiya tun jiya take ma?yar?yata, ba jira Dady ya faWawa su Hajiya kafin direba ya Wauke shi suka nufi gidan yarin.

A dai-dai lokacin da Hamdiyya take wannan mafarkin Momy tana neman taimakonta a lokacin tana kan gaSar barin wannan duniya, ba tare da likitoci sun yi nasara gano matsalar ta ba bayan yawan jinin daya sameta bayan faruwar komai ba, haka Allah ya karSi abarsa. Sai fatan Allah yasa da ta da rahamar sa wacce ta wanzu ga kowa da kowa.

Dr Ne ya fito daga Wakin fuska cike da alhini, da sassarfa su duka ukun suka nufi inda yake, abunka da mata kusan a tare suke tambayarsa ya lafiyar ta yanzu.

Cire farin gilashin dake idonsa ya yi kafin ya kalli Ammy ya ce ''ya kamata inganta idowar Alhaji wajan nan ko kuma mijin yarinyar, dan za'a mata aiki ne da gaggawa'', yana faWar hakan ya fito waya yana ?o?arin kiran wayar Dady.

Suna farfajiyar asibitin, shi yasa bai wani tsaya Waga wayar ba tunda yaga wanda yake kan kiran nasa.

Dady da Alhaji Badamasi ne a gaba, sai Maina, Kalil, Issa da kuma baban gayya wato Hisham, a haka suka iso ciki inda suka hango su Ammy a tsaitsaiye cikin tashin hankalin jin Dr ya ce dole sai an yi wa Hamdiyya aiki, inda tashin hankalin Ammy ya yawaita ma datasan ba watan haihuwar ta, idan dai har suna lissafi dai-dai to wannan watan ta na takwas ne, a haka har su Dady suka iso.

Koda Dady'n ya tambaya ya jikin nata wadda kai ?asa kawai Ammy ta yi, sai bayan daya tambayi ina Dr'n kafin ta nuna masa hanyar ofishin Dr Yahuza ba tare data Waya baki ta yi magana ba, dan tana daga baki kuwa kuka ne zai biyo baya, dan dama akwai ta da saurin kuka in dai a fagen nuna tausayi ne.

''Alhaji abun ya bamu mamaki sosai lokacin da muka ga Wan cikinta sam ma ba shida rai kusan kwana biyu kenan bai motsa ba, magana ta gaskiya yanzun sai dai ayi mata aiki a cire abinda ke cikin nata gudun kar ya cutar da ita, dama a mafi yawan lokuta ana samun makamantan irin wannan, saboda haka sa hannu muke bu?ata a yanxu'' ce War Dr Yahuza yana fadawa Dady a matsayin da Hamdiyyar take.
Furzar da huci Dady ya yi lokaci Waya idanunsa suka kaWa, wayarsa da dama take hannunsa tun lokacin da Ammy ke kira ya dannawa Hisham kira kai tsaye.
A wannan lokacin shi kuma Hisham tuni ya sulale ya zauna a ?asa jin ?afafuwansa suna ?o?arin kasa Waukar sa, hannu yasa yana kalubalen bakin aljihunsa lokacin daya ji rurin wayarsa, kamar makaho yana lalube haka ya dam?o wayar ya kanta a kunne ba tare da yasan wanda ya kira shin ba, tunda ba wani duba fuskar wayar ya yi ba, kiran ma ta mabuWin yatsa ya Waga shi.
''Ka shigo ofishin Dr'' yaji muryar Dady kai tsaye yana bashi umarni, yun?urin tashi tsaye yake amma yana yun?urawa zai kuma sulalewa ya koma ya zauna, ganin hakan ne yasa Maina kama gefen kafaWarsa na dama ya tallafa masa ya mi?e tsaye kamar wani mara lakka a jiki, ko tafiyar daya fara yana yi yana tangaWi kamar dan maye, ganin hakan ne Ammy ta ce da Jalal yari?e shi su tafi.

An yi nasar cire yaron da Allah bai nufa zai iso duniya a raye ba daga cikin mahaifiyarsa ta hanyar cs, an kuma sallamesu daga asibiti bayan kwanaki uku da faruwar hakan, sosai Hisham ya girgiza na rasa tsaronsa na farko da ya yi, babu shakka ya yi wawta da har ya kasa lura da lafiyar matarsa har haka, kenan nadan an yi wannan rasuwar ba ta yi sanadiyyar shigar matar tasa wannan halin da har aka gane ce wa yaron ya yi kusan kwana biyu da mutuwa a cikin ciki da sai ya gama rinewa a ciki, daga karshe yazo ya cutar har uwar tasa ma, tunda ko yanzu da aka ciro yarontsagin jikinsa har ya fara canja launi daga yanayin fatan mutun zuwa kalar tsanwa, haka dangi da yan'uwansa suke ta zuwa yi masa jaje kamar wanda ya rasa wani babban mutun.


''Ki daure ki tashi ki shanye wannan kunun dan Allah, kinfa da Wan zafi-zafinsa kuma ke kika ce in zuba miki kunun kanwa ko za ki iya sha, babu wani anfanin zama da yunwa Hamdiyya'', Ammy ta faWa duk ranta ba daWi, tun lokacin da aka sallamesu daga asibiti yau ana shirin mako biyu kenan babu wani sauyi, sosai take ?o?ari wajan ganin tasa Hamdiyyar ta manta da duk wani damuwarta amma kamar a banza, daga kuka sai ?in cin abinci, ko Hisham Win yazo gidan shima haka zai yi ta fama akan ta daure tana cin abinci, kuma ta cire damuwa daga ranta dan allan daya fita don Momy shi ya Wauke abinda, kuma shi Win ne dai ya bata yaron nan kuma shi ya karbe abunsa, shi kam yanzu ya dangana kuma ya fawwalawa Allah komai, bisa jajircewar mai martaba kakansa da kuma Annarsa wato kakarsa, dan tun lokacin da Ammy ta wuce da Hamdiyya gida daga asibiti shima ya koma can gidan kakaninsa da zama, a ce war s bazai iya zama a gidan ba matu?ar ba matarsa a ciki.

A hankali ta mi?e daga kwancan da take ta karSi kwanon sham ruwa na silba dake hannun Ammy wacce har da ludayi ta naso mata yadda zata iya kurSarsa da zafinsa, ta ko'uwa sha mai yawa kafin ta yi hamdala tana mai faWin ''ya kuwa yi daWi Ammy na, Allah ya ?ara girma da za?in hannu'' ta faWa da ?ar raha dan kawar da damuwar da take gani akan fuskar Ammy'n na ganinta a cikin ?unci da take yawan yi a lokuta da dama.
Ita ma Ammy'n mirmushi ta sakar mata tana mai shafa kanta tare da faWin ''Allah ya dawwamar da farin ciki a cikin rayuwarki duniya da lahira yarinya ta'' tana kai wa nan ta mi?e tana mai farin falon ta nufi kicthing, inda ta bar Hamdiyya da ?arin mamakin ?arfin imani da alkhairin Ammy'n da har kullum gaba yake ?ara yi ba zancan komawa baya.


A kwan a tashi asarar mai rai, kwanakin da aka dakanna auren yaya Issa da Kalil ya iso, wanda yake dai-dai da lissafin cikar watanni tara kenan na cikin dake jikin Husnah, duk wani gata da kulawar daya dace a rin?a bawa mai juna biyu Maina yana bawa matarsa dai-dai gwargwado, sai dai a bangaren mu'amalantar juna ne dai ta nemi daya Waga mata ?afa tun lokacin da ta shiga watanta na takwas, a ce war ta duka jikinta ji take kamar ba nata ba, gashi dai bata jin ciwo a ko'ina, amma kuma haka kawai take jin tana sarewa da rayuwar gaba Waya.
A Sangaren aikin daya shafi girka abincin gidan duka Hasiya ce ta Wauke mata nauyi, dama suna da masu yi musu aiki, abincin ne dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login