Showing 42001 words to 45000 words out of 109651 words

Chapter 15 - A KAN SHI complete by Maman Abdallah

31 Oct 2025

3122

abinda zance daku face Allah yayi muku fiye da abinda kuke kan yi mana, naji daWin wannan al'amari, duk daraja da komar da mace take tunananin tana da ita banza ne matu?ar babu igiyar aure a kanta komai girma matsayi da martabar ta, ha?i?a kuWin mutanen arziki ne, da ana samun irin masu karamcin ku a rayuwa da kowa yayi rayuwar ?anci, nagode sosai ?allaSai Allah ya kaimu goben lafiya sai muje can ?auyan kawai, daya ke ma babu iyayen duk Allah yayi musu rasuwa, sai magabata da bara'a rasa ba, sai maganar Hamdiyya! Alhaji sai nake ganin kamar akwai tauyewa a cikin wannan abun duba da irin abunda iyayenta suka aikata muku, zaifi ni in cigaba da ri?eta a waje na koba komai Ni tilashi na c...'' kafin takai ga ?arara maganar data soma Ammy ta bayyana a gaban ta ri?e da hannayen ta, cikin rarrashi tace ''Anty Baraka zaki ya, tabbas zaki iya bar mana ita kamar yadda kika bamu yardar ki wajan haWin auren nan, dan Allah ki bani ita , wallahi zan ri?eta fiye da zato da tunaninki, alfarma nake nema dan Allah karki ?ara kawo maganar Iyayen ta, ki ?addara kamar wasu iyayen Allah ya kawo mata bagtatan dan Allah''.

Ajiyar zuciya Inna tayi tare da maida hannayen ta a saman na Ammy, saSanin farko ammyn ce ta ri?e na Innar, cike da jin daWin jin maganganun Ammy Innar tace ''Naji kuma na yarda ?anwata, Allah ya taya ku ri?o ya saka da alkhairi'' saboda tsabar daWi Ammy batasan sanda ta sunbaci hannun Inna ba, kafin ta tashi ta isa gefen Dady daf dashi tana faWin ''Kaji ko Alhaji ta amince zata bar mini ita, dan Allah ka tayani godiya'' basu san lokacin da Inna ta bar falon ba, sai gani suka yi batanan ganin Ammyn na cike da shau?i kamar ta faWa jikin mijin nata, a ranar kwana Inna tayi tana yiwa Allah godiya da kirari, ha?i?a sun rasa mutunci da kima ta dalilin Mu'azzam da Hadiza, sai gashi ba'a jima ba sun sami wata daraja da kimar ta wani dalilin, Allah kenan mai yadda yaso, ka duba yadda Iyayen Yarinyar nan suka kai ?ololuwa wajan cutar da mutanen nan, sai gashi su sun kai matakin ?arshe wajan kyautata musu.
[15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: *_AKAN SHI_*

Page 28
A washe garin ranar aka Wauka auren Malam Inuwa da Inna Baraka a ?auyen su a cikin dangi da sauran ?an uwanta, inda suka tare a gidan sa wanda yake zaune.

Ba laifi suna zaune lafiya cikin aminci da girmama juna, dayake ba wasu yara bane cikin sati Waya suka gama sanin ?a'idoji da abinda kowannen su yake bu?ata na kyautatawa.

Haka rayuwa taci gaba da tafi ana kwanaki aka shike satittika, daga sati aka rufa wata guda, inda a yaune Mukhtar ya cika watanni huWu da rasuwa, a ?a'idar shari'ar muslunci idan namiji ya rasu mata ko matan sa zasuyi masa idda ta cawon watanni huWu da goma goma, inda mu Hausawa muke mata la?abi da sunan (Takaba), a hikimar Ubangiji na zartar da wannan shine Wan kiyaye shiga hurumin da ba na muba, a Misali idan mijin mutun ya rasu ya barta da shigar kwaa wanda su kansu basusan dashi ba, ta yiyu jiya aka samesa, ko shekaran jiya, koma kwanaki uku ko huWu da suka wuce, ba lallai a irin wadannan kwanaki a gane mace tana dauke da ciki ba, to shine hikimar, a wannan watanni huWu matukar ma e dana juna zai bayyana inma sabo ne ko kuma ba'a jima da samun sa ba mutuwa ta ziyarci ma'auratan.


Kamar haka ne ya faru da Hasiya wandayau saura kwanaki goma ta kammala cike kwanakin iddar ta, kuma. har wannan lokaci bata saka Maina a idanun taba, wani sa'in takan ji muryarsa wai yazo gaishe dasu Baba, amma har ya tafi basa yaWuwa Kasan cewar yanzu duka rayuwar ta a cikin Waki take yinta, wanka alwala kaWai suke fito da ita waje, ko abinci ma Waki Mama take kaiwa suci idan ta gama girkawa, a cewar Mama mai takaba a zaune aka santa sai yawan ibada da kuma nemawa mamaci rahama da gafara shine kawai aikin ta matu?ar da halin yin hakan, akasin hakan idan ya kasance bakada wanda zai tai maka maka wajan yin aikace-aikace gida, ko kuma ma ba kada mai baka abinci saika nema da kanka to tsananin iddar mace kwana arba'in ne, zata iya fita neman abincin da zata ci matu?ar ba tada maWaukin Wawainiyar ta.

Yanzun ma a zaune suke suna cin abincin rana a Waki kamar kullum, sallamar Baba ne ta isar musu da cewa ya iso gidan daga fitar da yayi da misalin karfe tara na safe, Mama Kuburah ta fidda hanunta daga kwanan danbun shinkafar data musu tana mai amsa sallamar mai gidan nata.

A rumfar su ta tarar da ledar daya shigo da ita amma baya wajan, ?an dube_dube ta shiga yi kafin ta gane ashe ya shiga banWaki ne a shigowarsa, ta yiyu ya shigo a matse ne shi yasa.


Tabarmar da suke zama a kanta a zaman waje ta Wauki ta shinfiWa tare da ?ar shinfiWar da yake kishingiWa dan hutawa da rana, ruwa da kuma abincinsa duk a ajiye kafin ya fito daga bayin.


Saida ya gabatar da alwala kafin ya isa shinfiWar ya zauna yana mai yiwa Mama alama data ?araso inda yake, ledar daya shigo da ita ya bata izinin mi?o masa ita, ba Sata lokaci ta isa mazauninta kamar kullum wato kusa dashi, cikin farin ciki yace da ita ''Kuburah ina da albishir mai daWin gaske dazan miki, wane irin hoto za'a bani inji kafin in faWa''.


Cikin farin cikin da ya baibaye ta tun kafin taji daga bai n mijin nata tace ''Ka faWa kanka tsaye Baban su, banda jan rai kasan ni da ?aguwa, ga wannan nan na baka a matsayin goron albishir, kuma nasan za kaji daWin sa sosai''.

Da mirmushi Baba ya buWe kwanon abincin sa da aka bashi a matsayin tukuici, da ?arin farin ciki yace ''Ai kuwa goro yayi kyau kuma daga gani zai yi daWin sosai, yanzu abinda za'ayi ki bari har in gama cinye duka abincin nan kafin na faWa miki ko miye abun, sannan wannan ma a mana kasafin sa, dan ina jin wannan labari na wuce wurin ?an kifi na siya mana mai Wan yawa mu morawa ran mu'' ya faWa yana nuna mata ledar daya shigo da ita tare da fara cin abincin da bismillah a bakin sa.

Mama ce ta kira Hasiya tazo ta karSi rabonta, inda suka ci-gaba da cin abincin da Baba a tare, har kifin ma tare suka ci.

Sai bayan gama tattare kayan abincin da Mama tayi ta dawo ta zauna tana mai hamdala a bakinta, Baba Ibrahim ta fuskanta, kafin tace wani abun ya rigata cewa ''Alhamdulillah Kuburah mu godewa Allah, shike bawa Kowa rabonsa a lokacin baya ga dama, a jiya da yamma Alhaji Umaru ya kirani akan yau da safe mu haWu a ofishin kasuwancin sa, to abinda yasa ban faWa muku ba shine bansan abinda zai yi magana akai ba, kinsan mijin naki da tsoro'' Wan nunfasawa yayi kafin ya ci-gaba da cewa '' Ina zuwa muka gaida kamar yadda muka saba kawai sai cewa yayi na zaSi kasuwancin da nake tunananin zan iya yi, da na masa musu na ce dashi wannan hidimar da suke yi da mu ma kaWai ya isa basai ya kuma Worawa kansa wani yaunineba, amma sai ya nuna mini Sacin ransa, yace na nuna masa iyakarsa da iya matsayin da yake da a gina, jin wannan, zance nasa yasa nayi gaggawar kawai masa da wannan tunanin daga ransa ta hanyar faWa masa inaso na buWe shagon kayan masarufi dana bu?atar yau da kullum, kinsan abinda zai baki mamaki kuwa?'' Baba yayi wa Mama Kuburah wannan tanbaya.

Cike da san jin inda zancen ya kwana tace ''Ina sauraronka Malam sai ka faWa'' da ?ar dariyar sa ya ci-gaba da bata labari ''Ina faWar haka ya Waya waya ya kira wani layi, ban ida tantance abinda wayar ta ?unsa ba yace sani na tashi mu tafi, ba musu nabi bayansa, a mota muka nufi sabuwar unguwar nan da ake kan ginawa a yanzu, muna zuwa ya nuna mini wasu dan?ara_dan?aran shaguna guda biyu masu kama da juna, abun mamaki Wayan atanfofi ne da les da materiel, da kuma kayan kwalliya na mata irin su takalmin haka da sauransu, Wayan kuma kayan masarufi ne irin su shinkafa taliya kofin gwongwani man shafawa sabulu da dai kayan bu?ata na yau da kullum, kuma duka daga bahhuna sai kwalaye ba wai WaWWaya ba, abun mamaki ashe Alhaji ya zuba wayan'nan kayan, Wayan shagon na Malam Haruna ne wato sirikin sa, ko ince mahaifin Husnahn Jalaluddeeni, Waya kuma nawane, Kuburah ban kuma tabbartar da karamcin Alhaji Umaru ba sai da naji yana faWin ''Wannan shagonka ne Malam Ibrahim, na baka shi halak malak, ba kuma haya zaku biya ba dan duka shagunan a cikin gidajen ku suke, ma'a kowannen ku gida da shagon cikin sa nasa ne har abada, tare da Malam Haruna da bai jima da isowa wajan ba sakamakon kiran sa da alhaji yayi zuwa nan ya faWa mana wannan banban abun alkhairi, ai bamusan lokacin da muka rungumi junan mu ba nisa Harunan, godiya kuwa kamar bakin mu zai cire, shine da muka taho mu duka a tare da su, saida muka iso masana'antar Alhaji muka rarraba kofi wa ya kama hanyar zuwa gidansa da tarin farin ciki dal rai da zukatan mu''.

Sujudu shukur Mama tana mai yiwa Allah kirari, kafin kuka ya kufce mata harda jan majina, shidai Baba kawai ido ya saka mata yana kallon ta, cikin kukan ta ke faWin ''Issa kana ina ne, ina ka tafi ka barmu ba waiwaye ba juya baya, dan Allah ka dawo kaji abun farin cikin daya same mu bayan yayewar ?unci da damuwar mu, kai yafi tsantsanta a yau kaje da sunan godiya a gaban wan'yanda suka sauya rayuwar ?anwarka daga ?unci da ?angi zuwa rayuwar samun ?anci, gashi yau Iyayen ka suka wanka ta tarin alkhairinsa da ba lallai mu kwatanta saka musu ba, kana ina ne yarona?A yanzun dawowar ka garemu iya kaWai ya rage mana cikar samun nutsuwa''.

Tsabar takai cin da Mama take ba shi ne yasa ya tashi daga wajan jin ana kiran sallar azahar, ya fice daga gidan ya nufi masallaci da ?uncin barin su da Isan yayi ba tare da ya taSa koda kiran su a waya bane, ada yayi masa uzurin Sacin ran daya gani a tattare dashi a daren da zai sulale yabar gidan, yanzu kuma ganin tsawon lokacin da aka Wauka yasa ya fara tunanin ko dama da nufin barin su na har abada ya bar gida, koma dai minene suna nan wata rana zai dawo da ?afafuwan sa koda basa raye, saidai kuwa idan shima baya rayen ne.

Duka abinda suke Hasiya tana jinsu kuma tana fahimtar duka bayanan Baban nata, abu biyu suka taSa mata zuciya a bayanin Baba, anbatar sunan Husnah da yayi saida gaban ta ya daWi, ita da wata rana mantawa take da wata Husnah a rayuwa, kai har Mainan da kansa wata rantakan manta dashi a kanta, amma a zuciyar ta tayi kaWan ta ita gushe tunanin sa koda na second biyu ne, sosai take jin tsoron yadda goben ta zata kasance bayan jiyan ta da bata ma kowa kyau ba, sai abu na biyu maganar Mama akan Yayanta Issa, a kullum idan ta tuna a kanta yabar gida ya nisanta kansa da kowa nasa sai taji babu daWi.


A Sangaren Husnah zata iya cewa alhamdulillah, dan yanzu kam ba tada matsalar komai a gidan auren ta, babu ta?ura daga Momy, babu yawan kira daga Mama samuwar kulawa daga Maina, wannan itace rayuwar da take yi a yanzu, ta zama cikakkiyar sirukar Ammy da Dady, saidai har zuwa yanzu ta kasa zama cikakkiyar matar Maina, abun yana dama ta a kullum kuma a koda yaushe, za tayi abinci ta bawa mijinta yaci cikin annashuwa, zata gyara masa makwanci kuma har su kwana tare akan gado Waya, amma har gobe ta kasa jan ra'ayinsa akanta, a ?an kwanakin nan yakan Wan taSa wasa da ita kaWan a yawa, kamar. wanda aka yiwa iyaka da ita haka suke zaune, kuma da alama shiWin ko a jikinsa, haka take gani tunda bata ganin shau?i ko shiga wani yanayi a tattare da shi, wannan shine babbar damuwar ta a yanzu duk da tana jin tsoro aduk lokacin daya kasance a kyau kusanci a tsakanin su, amma tafi bu?atar samun ci?ar matsayi fiye da tsoron dake ranta.

Hamdiyya an gama zama ?ar gidan Ammy, duk da fatan da mahaifinta ya nuna mata a baya zata iya cewa yanzu take ganin gata cikin gata, dan wancen wasa ne akan wanda take cikin gani a yanzu, ta ko ina ita Win shalele ce, a Sangaren Dady, Malam Inuwa, Inna Baraka, Ammy tace kau bani guri, wata rana haka kawai Ammy zata ce ita da kanta zata bata abinci a baki, koda tana jin kunya haka za tayi ta ?arSa tana cinyewa gudun kar Ammyn taga ko ta raina kulawarta gareta ne.

Wata rana Ammy zata kwantar da ita a gadon dake Wauki na musamman da aka gyara ya zama nata, haka za ta zauna a kusa da kanta bayan ta lulluSe ta tana shafa kanta alamar rarrashi har sai tayi bacci.

A duk lokacin da akayi katari aka yi makamancin hakan a gaban Maina sai yaji yarinyar tana ?ara fita a ransa, ba zaice ya tsane ta ba amma sam baya yinta, idan ya tuna cewa saboda ita Shukuriyya ta taSa zaman gidan yari a rayuwar ta sai yaji duk ba daWi.


Amma wata rana yakan zauna ya auna matakin laifin yarinyar a duka abubuwan da suka faru sai yaga ba tada laifi ko kaWan, takan bashi tausayi wani sa'in idan yaji tana tambayar amma yaushe zasu je gidan yari dan su ziyarci Momy da Baban ta, dan bata san da rasuwar Mu'azzam Win ba.


Su Baba Haruna da Inna Zainab tuni suka fara shirye-shiryen ?aura sabon gidan da Alhaji ya bawa su, dan tun ranar daya shigo gida yake faWawa Maman Husnah Win tayi kukan nadamar rashin ha?urin data nuna a rayuwa, kuma a ranar ta gane cewa duk abinda kaga baizo hannunka ba to dama can ba raban ka bane, abunda yake raban ka kuwa ko bai riskeka a inda kake ba to kai zaka sameshi a duk inda yake, ta kuma yarda cewa arziki rashi da su duka na Allah ne, ada daya barsu a babu badan baya sansu bane, kuma yanzu daya basu badan yafi ?aunar su bane, ta gane wannan karatun ne a dalilin fashin ba?in da Baba Haruna yayi mata, wanda dama yakan mata saidai bata bashi damar da zai gama bayanin ma bare ta fahimta, saboda san abun duniya daya rufe mata ido wanda shine silar shigar Husnah cikin rayuwar Maina.


Gidan Alhaji Mansur Kazaure

Zaune suke a babban falon gidan bayan gama cin abincin dare, kansa a ?asa yana wasa da yatsun ?afarsa musamman daya kasance yana zaune akan carpet ne.


Kyakkyawan dattijon mahaifinsa dake zaune da jarida a hannunsa yace ''Kai nake sauraro Hashim ka bani amsa! So kake mu ci-gaba da saka maka ido kana zaune babu aure, ka duba fa kagan ka yanzun shekaraka nawa, kana tunanin kullum zaka zauna a yadda kake ne ko, a'a ita ce amsar, yayin da ka wayi gari da safe kasa a ranka rana Waya daga cikin ranakun rayuwar ka ya ragu kuma ba zata taSa dawowa ba har abada, duk mintin da zai shuWe acikin rayuwar ka ya fita daga naka saidai wani ya zo nan gaba, yashe zaka cika kamalar ka ta cikekken bawan da babu abinda ya rage masa bayan bautar Ubangiji? Ka sani bana samun nutsuwa idan har na buWe ido nagani ka a gabansa babu aure, ?ananan ?annanka mata guda uku aka yiwa aure, acikin su harda wasu yara har bibbiyu, to kai sai yaushe eye?''.


Sosai maganganun Papan nasa ya kashe masa jiki, cikin girmamawa yace ''Kuyi ha?uri papa insha Allah nan bada jimawa ba za'ayi, kuma ma inaso dama na faWa maka akwai wacce nake so a raina, saidai dana duba cancanta sai naga kamar ba lallai ku aminta da ita ba''.

''Ka faWa kanka tsaye mu Son! Matu?ar ka yarda da tarbiyyar ta kuma ta fito daga gidan mutunci ai babu wani abun ?ara ko ?yama a tattare da ita'' cewar Mamma dake zaune isowa falon cikin takunta na ?asaita da jikima na Wiyan saraki.


Bai Soyewa iyayen nasa komai game da yarinyar da kuma yanayin rayuwar da take ciki a yanzu ba, kuma ya faWa musu cewa bai nemi yardar yarinyar ba saboda wani dalili, amma yana kusa da ya tinkare ta da ?o?on barar sa.

Cike da jin daWin bayanan sa suka masa fatan alkhairi tare da ?arfafa masa gwuiwa akan kar yayi sanya wajan ganin yarinyar ta ?aunacesa da duka zuciyar ta.


Yau ranar alhamis kuma yau ya kama ranar cda Hasiya ta cike ranakun iddar ta, a masallacin unguwar su maza suka gabatar da adu'a wa mamacin da kara jaddada nema masa gafara da kusanci da rahamar mahaliccin sa, Hasiya tayi wanka ta kuma saka Waya daga cikin kayanta wanda suke ba laifi ba sababbi bane, saidai Waya daga cikin kayan lefen da Mukhtar yayi mata ne, makwabta sai shigowa suke dan taya ta murnar gama zaman idda lafiya, har Ammy da Hamdiyya sunzo, a Wayan Sangaren kuma Inna Baraka ma tazo bisa jagorancin Malam.



?arfe takwas da mintuna talatin na daren ranar.

Sosai ya razana da maganar da yaji ta fito daga bakin Ammyn nasa, idanunsa da suka Wan soma canja kala daga fari zuwa ja ya Wago yana duban sashen da Dady yake danjin abinda zai ce game da maganar Ammy Win

Kamar baya wajan haka Dadyn yayi, kafin ya samu zarafin yin magana mahaifin nasa ya yun?ura ya tashi alamar babu shi a maganar kenan.


?an muskutawa yayi kansa a ?asa yashiga cewa ''Ki gafar ceni Ammy na! Wane irin laifi nayi miki dana cancanci wannan Wanyan hukuncin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login