Showing 21001 words to 24000 words out of 109651 words

Chapter 8 - A KAN SHI complete by Maman Abdallah

31 Oct 2025

3124

damar yiba, dayake dama da ?aramin gajeren wandonsa a jikinsa a hakan nan suka kwanta a gadon sa, a rana ta farko da suka kwana rungume da junansu, ita a wayonta dole ta sanbarwa Maina da jikinta ta yadda bazai iya dugon fushi da ita ba, shi kuma gogan tun yana kallon abun a matsayin neman wuri irin nata har ya lura cewa da gasken gaske itafa a tare dashi zata kwana, bai wanija ba kashe musu fitala suka kwanat, kowa da tarin tunaninnika a ?wa?walwar sa har bacci ya dauke su.
[15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: *_AKAN SHI_*

Page 20
_____Kwanaki suna ja tafiya tana ?ara tsayi, yayin da Maina yake ?ara faWaWa binciken da, ya kuma zuwa gidan su Hasiya sai kusan biyu ma, sai ita Hasiyar yake sau Waya dan neman karin haske game da abinda ya shige masa duhu dangane da labarin data bashi, kuma koda wasa bai wani sakar mata fuska ba, a cewar sa ta rainashi, tun data ita kallon idanunsa kuma agaban tayi masa tsaki, baisan itama abun bai mata daWi ba, dan tun ranar dayabar wajan take kan dana sanin tsakin data masa, to yazatayi itama al'adarta ce kamar yadda yake shima Wabi'ar sace yin tsaki.

A Sangaren iyayensa komai ya daidaita, kulama wa musamman take samu daga Dady yake bawa Ammy, nutsuwar da suke samu a zamantakewar su kamar a shakarun amarcinsu, lokacin Hadiza bata shigo cikin rayuwasu ba, Ammy daWi kamar zai hanata fahimtar yanayin da take ciki ayanzu, tabbas mahakurci mawadaci, tasha wahalar rabata da miji da kuma Wanta da akayi, sai gashi lokaci Waya Ubangiji ya dawo mata dasu cikin rayuwar ta, batare da taje gurin kuwa tayi ?ar murya ba, sosai take samun kulawa daga Dady da kuma Jalaluddeen Win ta, zuwa yanzu har Grany Win Jalal tasan Wanta Umar Allah yayi belinsa, ta jima tana adu'ar Allah ya kare mata shi ya kuma tsare gaba, dan a lokacin babu wanda baisan Dady baya cikin hayyacin ba.

A Sangaren Momy abu duk ya jagule mata, ta rasa ta'ina zata soma Winke bakin buhun musibar data fara turo musu kai, daga ita har Mu'azzam Win sun fita a hayyacin su, dama tun azal yafi ita Momyn tsoro, duk da shi namiji ne amma tafishi jajircewa, suna kan neman mafita baki ba gani, duk wasu malamai da bokayen su sun tabbatar suna cikin damuwa, yayin da kowannen su ya daukar musu al?awarin magance musu damuwoyinsu, sun yarda da hakan tunda sunada ya?inin akansu da kuma ayyukan tare da kaifin al?alummansu.
(Wa'izu billahi) Allah ka mana tsari da munanan Wabi'u da halayan da zasu kaimu ga hallaka a duniya da kuma taSewa a filin hisabi ameen.


Yau goma sha tara ga wata, yayin da al?awarin saurenron shari'ar Hasiya zai cika gobe cikin hukuncin Ubangiji.
Malam Inuwa ne zaune akan sallaya hannayen sa biyu a sama yana fadawa Allah kukansa, wanda tunkafin a halicce sa Allah ya gama sanin damuwar sa, hawaye ne ke anbaliya daga idanunsa zuwa kan fuskarsa, a bayyane ya shiga yiwa Allah kirari, tare kai ?aran mutanen da suka sakance sune sanadiyyar yake rayuwa kamar maraya, badan Allah ya rufa masa asiri da al?ur'ani ba, da a ranar sun gama nakasa masa rayuwa na har abada '' Ya Allah kagani kuma kana kallo, Allah gobe ne ranar, sai ka nufa mu risketa ko akasin hakan ayi babumu muna bayan ?asa, Allah ka hukunta da rayuwata zuwa gobe, ingani da idona yadda shari'ar nan zata kasance, Allah kabi mana kaWi mu, ka kwata mana ha?in mu, Allah ka ji?an iyalai na ka sadani da Wan'uwa na ya Ubangiji ka...........''
[15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: *_AKAN SHI_*

Page 21
....... Ya Ubangiji kasa nufi ?arfin zuciyar mu ka bamu ikon aikata abun kirki tun kafin mutuwa ta riske mu, Allah ka gafarta mana zunubanmu ka yaye mana damuwar mu, ka tsaya mana ka haWamu da abokanan mu'amala nagari abin koyi, haka ya kwana a zaune yana yiwa Allah kirari, sai kusan asubahi ya kwanta, shima dan ba'acin bashin bacci a zauna lafiya, ga kuma jikin tsufa sai ahaniali, baifi mintuna talatin da kwanciya ba aka kira sallar asubahi.


?arfe takwas da kwata ya gama shirinsa tsaf dan zuwa kotun shari'ar muslunci, dan yaune rana ta ?arshe wacce za'a saurari shari'ar Hasiya, har a ransa yanada ya?inin insha Allah zasuyi nasara, tuni ya gama sanin ba ita ta aikata wannan kisan kanba, kwanakin baya yaransa daya hayo asuna masa aiki suka kama Barister ya fito daga gidan su Maina Win, kuma alamu sun nuna daga gun Momy yake, shine yasa suka tsare masa shi , kwana da yini a hannunsu, badan Jalaluddeen Win ya hana su taSa lafiyar jikinsa bada yagama ganin takansa a hannun garadan nan, Maina ne yabi dashi asannu har ya faWa masa komai daya sani game da wannan shari'ar, abun bazai wa kowa kyau ba a yadda yaji komai.

Tsaye take a bayansa tana kallonsa ta cikin mirron dayake fuskanta yana caje gashin kansa, har yanzu abun ya kasa barin rai da ruhinsa, yau shine yake kwana Waki Waya da mace, a Waki Wayan ma a mashinfiWa daya, har yanzu abun mamaki yake basa daya kasa yiwa yarinyar komai, yadda take kwantawa haka ta wayar gari, abinda ya dade yana damunsa, yana kuma adu'ar Allah ya sassauta masa game da yanayin da yakeji aduk lokacin da ya Warsa wani abu arai ko zuciyarsa, shi mutun ne mai yawan bu?ata, amma yakkanan yake daurewa yana kame kansa, zai iya rantsuwa da Ubangiji bai taSa yin zina ba, koda kusantarta bai taSayi a, kuma ya godewa Allah daya da Shukuriyyar sace a kusa dashi har haka ba lallai ya iya Waga mata ?afa har haka ba, yana tsaka da wannan tunane tunanen har ya gama kintsa komai, ?ar ?aramar kakar hannun daya tsara takaddun sa ya dauka yana shirin barin Wakin.


'' Na ce abincin fa, tun Wazu na faWa maka nayi mana breakfast kai kawai nake jira '' ta faWa a marairaice. Kallonta yayi yayi cikin yanayin data kasa fassara da yace '' banajin yunwa, kuma ma na makara, ?arfe tara za'a fara sauraron shari'ar danake a kai, saidai idan nadawo'' ya faWa lokaci Waya yana mai barin Wakin.

Daidai tsakiyar falon gidan ba zato ba tsammani yaji ta shige jikinsa kamar dai jiya, saidai na yau da gayya sosai tayi, saidai tanada dalilinsa bayin hakan.

Rasa ta inda zai taro kansa yayi, dama ga a yadda ya kwana ya tashi, miye wannan yarinyar take nufi dashi, bayan afuwar data nema yayi mata yanzu kuma miye na wani shige masa jiki yanzu.

Cike da salon jan hankali take magana'' Yayana dan Allah kayi ha?uri ka tsaya muci abincin nan, kaga kace ?arfe tara ne zaku fara ko, yanzu kuma takwas ne da rabi ne, mu gaggauta muci abincin nan kafin lokacin ya rufa dan Allah, kuma ma ai ya kamata ace mun tafi tare dan nima akwai rawar da nake tunanin zan iya takawa'' duka dana jikinsa take wannan bayanin, kasa mata musu yayi, saima samun kansa yayi da yarda da duk abinda tace, to amma wani hanzari ba gudu ba, bayaso take taga Ummanta acen, dan duk wanda yake da hannu a wannan shari'ar babu wanda bai yi dabarar daya ziyarci wannan kotun da kafafunsa ba.

Kamar Ra?umi da alaka haka taja hannunsa har wajan data shirya musu kayan abincin, soyayan dankalin turawane da kwai, da kuma wainar fulawa wacce taji kayan kanshi da suka gama haWata, sai ruwan shayin da ta kawatashi da kayan kayan ?anshi na musamman, dayake dama babu abinda babu agidan, ko rayuwar ?angin da yace zatayi a gidan sai zuwa kayan amfanin sun gama ?arewa ne zata tabbar ta fara ganin u?ubar rayuwa kamar yadda ya faWa, ba shakka Allah ya sota sosai, ga dukkan alamu bazata sha wani wahala ba wajan shayo kan Maina.

Sosai ya buWe ciki yaci kalacin, dayake dama da ?ar sauran yunwar sa ta jiya daya kwana da ita, tsaye ya tashi lokacin daya kammala tare da yin godiya ga Ubangiji daya rayashi kuma ya basa abinda zai ci.

A ta?aice ya kalleta lokacin da take kintsa wajan dasuka gama cin abincin, farin ciki dal ranta, insha Allah bazata gajiya wajan faranta masa ba, da sannu tasan zata samu gurbi a zuciyarsa koda bata samu kwatankwacin matsayin da Shukuriyya take dashi a gunsa ba, tana sonsa kuma tana ?aunar sa koda bazai so taba indai zai zauna da ita zatayi farin ciki da hakan.

Tana tsaka da wannan tunani taji yana faWin ''Ki gaggauta please zan makara fa'' batare da tace dashi komai ba ta nufi kicthing ta kai kayan dake hannun ta, kafin cikin hanzari ta faWa Wakinta ta sako hijab Winta har ?asa, harda wata nigab ta saka dan badda kama.


Tafiya yake tana binsa a baya har suka isa bakin Motar sa, shine a mazaunin direba ita kuma a kujerar mai zaman banza, mamaki ne a kama Maigadin gidan ganin Ubangidan nasa da kuma matar gidan a tare, lallai igiyar aure daban take, shekaran jiya jiyan nan ya gama masa kashedi akan kar yabar wani kowa ya shigo kuma itama kar ta fita, kuma ga dukkan alamu tayi masa wani laifin ne shi yasa ya dauki wannan mataki, duba da yanayin sa lokacin da yake bashi umarnin.

Har suka bar gidan yana wannan tunanin bayan yana shirin rufe get Winne yaga kamar gittawar wasu mutane guda huWu akan mashina guda biyu, mutun biyu ne a kowane mashine, da gudun tsiya sukabi bayan motar Maina Win, sosai hankalin Isiyaku Maigadi ya tashi, ganin mutanen biyu na baya kowanne da yu?uwa a gefen cikinsa, da gudu ya koma cikin gidan tare da dauko wayarsa, duk wani abunda zai yi dan bawa gidan tsaro saida yayi kafin ya fito ya rufe gidan, Wan Mashin Winsa ya hau ya tashe sa yabi bayan wayan'nan mutanen da har yanzu zuciyarsa bata gama yarda da ingancin su ba, shi sai yake gama kamar yasan fuskar mutun daya daga cikin su, wannan na Waya matu?in Mashin Win, saidai bazai iya tuna inda yasan shi ba, dayake shima wani ?a??arfan gwarzo ne kuma sadauki, take ya ?ure gudun mashin dinsa ya me?i hanya, sosai yake gudu kafin kace miye har yana cinkayar su, zuwa wannan lokacin sun kusan cimma motar su Maina, ba tare dashi Maina ko Husnahn sun sani ba.


Kiran wayar daya shigo wayarsa shi ya bashi damar ganin lokaci a agogon wayar, tsaki yaja ganin kiran daga Isiyaku ne, ko miye kuma yake kiransa, bayan yanzu ya fito daga gidan? Ya tanbayi kasan lokacin da yake Waga kiran tare da saka wayar a handsfree, bai kai ga ?arasa sallama daya dokawa isiyakun ba yaji muryar da cike da amo yana faWin '' YallaSai ka duba bayanka akwai wasu mutun huWu da suke binka a baya, idan da hali ma kawai ka canja hanya dan Allah'' .

Cikin tsananin firgici da tashin hankali Husnah ta duba baya Wan ganewa idanunta, yayin da Maina ya ?ure gilashin motar da ido dan tabbatarwa, a mugun kiWime Husnah take faWin '' Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wannan musiba dami tayi kama, sai yaushe zasu bar mu mu rayu kamar kowa ne, miye duk wannan dan Allah, wallahi Momy bata tsoron Allah, kuma bata tsoron saduwar ta dashi daga ita har mabiya bayanta'', wata wawar kwana Jalaluddeen yayi da mugun gudu, ya shiga wata kwanar da batada wadataccan fili jin ta ambaci sunan Momy, kenan ita ce ta turo su komai?

Kafin kace mai har sun saka motar Maina a tsakiya, sai faman kai musu hari suke da yu?uwayan hannayan su, sosai hankalin Isiyaku ya tashi lokacin daya shigo kwanar ganin ta'asar da suke shirin tafkawa, dan sosai suka barshi a bayan sakamakon mutuwa da babur Winsa yayi yana tsaka da gudu, dama ?arfen nasara bashida tabbas, koda ana anfani dashi yau da kullum, bare shi nasa a ajiye yake a Wakinsa sai ta kama yakan fito dashi, zuwa wani aike na gaggawa kodai wani aikin ujila kamar dai wannan, wayarsa ya ciro ya danna number da yake tunanin itace kai tsaye zaka samu mahukunta da zaran ka kira ta, ba wani Sata lokaci ya tura kira cike da ?aguwar a amsa masa.
[15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: *_AKAN SHI_*

Page 22

A kotu
______Tun ?arfe tara ake zaune zaman jiran mutun biyu dan gabatar da shari'ar, a duka bangarorin nan babu wanda bai halarci zaman kotun ba, kama daga kan iyayen hasiya da ita kanta Hasiyar, dan tun takwas aka kawo ta daga gidan yarin, ga kuma Barister Lawali da abokanan aikin da aka ?aro masa har guda biyu wanda sai kama masa gwabzawa da Maina, ga kuma Momy da ta shigar da Dady kara akan ya tauye mata hakkin ta na fitar da ita da yayi a duka jadawalin rayuwar sa bayan bai saketa ba, kuma duka shirin Maina ba tare da tasani ba, harda Ammy itama tazo tare da Dady, daga share Waya ga Malam Inuwa a zaune, yau a matsayin mai kallon shari'a yazo ba'a mai yanke hukunci ba, abun mamaki da baya karewa har ?arfe tara da arba'in babu Maina babu sabon al?alin da zai jagorancin wannan shari'a.


''Ya ilahi'' Maina ya faWa lokacin da Waya daga cikin mutanan nan ya sami nasarar taSa lafiyar jikin sa, daidai dantsen hannunsa ya yankesa, daidai da fara isowar kururuwar jiniya na ?an'sanda, Husnah sai kuka take ganin Maina yaja birkin motar jin hannunsa yana so ya fasa amfanuwa, da gudun tsiya suka juya kan mashinan su ganin motar ?ansandan ta nufo inda suke, wata irin sufa Isiyaku yayi, ta taryi Wayan mashin Win da gudu wuce sa'a, kamar zasu takashi haka sukayi, sai kuma yayi gefe tare da buga tayar mashin Win ta gaba da iya ?arfinsa, gwadawa yayi amma badan yasan zai iya ba, aikuwa jikake jirif babur Win yayi ta Sangaren sa ma'ata hawansama haka, da gudu uku daga cikin ?ansandan nan sukawo kansu, daya yayi wajan Isiyaku, yayinda biyu suka yi inda wayan'nan muyagun mutanen dake da Waya yake kwance yana fitar da nunfashi, Wayan kuma yana gurfane yayin da yake ?o?arin murza guiwar gafarsa da yakejin alamu kamar tafi daga mazaunin ta.

Cikin fito da idanu Isiyaku yace '' Kawu Mu'azzam dama kaine da wannan aikin, tabbas hali hanjine kowa kagani da nasa yake yawo'' ya faWa lokacin da idanuwansa suka sauka akan Mu'azzam Win da tun suna yara bakunan su suka saba kiransa da Kawu.

A mota aka jefasu su duka ukun har Isiyaku, tare da rakiyar ?ansanda biyu, matu?i da kuma Waya mai bindiga a hannunsa suka nufi station, yayin da biyu da daga cikin su suke tare da Maina a yanzu haka an gama yi masa dresin Win cewon da Mu'azzam ne ya yankesa bayan an wanke wajan sosai gudun sharrin ?arfe, harda arzikin Winki saida yasamu baici baishaba.

Zuwa wannan lokaci Husnah taci kuka ta ?oshi akan wannan mummunan ?addarar da taso ta faWa akan tilon mijinta, tama faWa saidai Allah ya ta?aita a haka daya kasa ce ba wuyansa suka yanka ba.


?arfe sha biyun rana a kotu

Zuwa wannan lokacin kowa ya gama sakawa a ransa ba lafiya ba, daga Sangaren Maina har sabon Al?alin babu labarin koWaya daga ciki, hankalin Ammy da Dady duk ya tashi, ga Mama da Malam Ibrahim da shima yasami halartar kotun duk sun damu, ran Momy fari ?wal kamar gonar auduga, kuma har a fuska idan ka kalleta kasan tana cikin shau?i sosai, fargabarta Waya ce da take kiran Mu'azzam da sabuwar wayar data yi bayan Sacewar waccan amma baya shiga, batasan dalili ba amma bata kawo komai a ranta ba, ko tunanin rashin nasara a'a, ita tafi tunanin kawai ya gama da babin Maina Win ne saidai labarin ne bai gama isowa kotun ba.

Ita batasan ba idan bacci suke su Allah baya bacci, kuma ba'a kowane lokaci abokin hamayya kanyi nasaraba koda yanada ya?inin samun taba, lamarin Allah daban ne, shike yadda yaso kuma a lokacin dayaso, Allah kenan gagari misali wanda yafi misali, malikal mulki zuljalalu wal'ikram.

?arfe Waya da mintuna arba'in maga takardar kotun ya kira sallah azahar kamar yadda aka saba, zuwa wannan lokaci tuni kowa ya sare da lamarin harda Momy ma, can cikin kotun akayi wa mata iso dan suyi sallah yayin da maza suka tayar da jam'i a cikin kotun bayan an inganta wajan da za'a sallar.

Jin labarin har zuwa wannan lokaci akwai mutane a kotu yasa makwabtan wajan masu kayan sayarwa na cima suka anyato bakin kotun dan sunsan baza'a rasa masu siyaba, dan kaiwa bakinsu wani abu koda ruwane.


Farfajiyar kotun cike take taf ana siye da siyarwar nan, har wayan'da ba siyan zasuyi ba, kawai zaman ne ya ishesu har suma suka fito wajan, Malan Inuwa, Ammy da kuma Dady ne tsaye a jikin wata bishiyar mangwaro, Dady sai kuma kiran wayar Jalaluddeen yake amma ya kasa samunsa, ana haka sai ga jerin gwanon motoci sun fara shigowa cikin ainahin harabar kotun, wata arniyar mota ba?a ?urar jib, ta kunno kai tare da rakiyar wata motar guda biyu wanda suke take jibWin baya, bayan guda ukun da suke gabanta a matsayin kariya.

Anfi mintuna uku kafin mamallakin motar ya fito.
Masha Allah! Shine kawai abinda youioo yake faWa harma da wayan'da suke cikin damuwa musamman ma Momy, tuni idanunta suka sauka AKAN SHI, tuni ta shiga wani tunanin na daban.

Haka yake takawa ana take masa baya ya nufi hanyar shiga cikin asalin kotun, a al'ada mutane suke zaman jiran isowar al?ali, sai gashi bisa wani dalilin dayasa jama'a suka fita farfajiyar kotun sai gashi zaune a kujerar al?ali yana jiran mutane su gama zama a mazaunan su kafin a shiga mataki zai biyu, Maittre Hashim Mansur Kazaure kenan, matashin mai jini a jika mai kuma ji da kuWi da da kuma izza, a wani Sangaren za'a iya kiransa da jinin sarauta, Wan kimanin shekara talatin da tara a duniya, duk da ya kusan rufe shekaru arba'in a duniya hakan bazai sa ka kirashi magidanci ba, dan ko auren fari bashida shi, cikekken sunan sa shine Hashim Mansur, mahaifinsa shine ministan ilimi a daidai shekarar daya kammala makarantar secondary a hamsha?iyar makarantar da tafi kowace makaranta kuWi kyau da kuma inganci,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login