Showing 99001 words to 102000 words out of 109651 words

Chapter 34 - A KAN SHI complete by Maman Abdallah

31 Oct 2025

3142

ruwan gora, da hanzari ta mi?awa Mama da nufin ta karSa ta bata, amma ina hakan bai kai ga faruwa ba Husnah ta dafe ?irjinta, dan wani nauyi taji ya mata fiye da kowane lokaci, a hankali ta fara motsa bakinta wanda da alama magana take son yi amma ba hali.

Hannun Maina ta kama ta ri?e game da iya ?arfinta.
Ganin hakan da kuma abinda hankalinta ya bata ne Ammy ta matso kusa da kan Husnan, a hankali ta fara nanata mata kalmar shahada.
Sau biyu Ammy'n ta faWa kafin Husnan ta amsa tana maimaitawa. Hankalin Mama ya yi matu?ar tashi, ita ko a kanta bata sa wannan abun a cikin tunaninta ba, idan har abinda take gani dai-dai ne to Husnah barinta take shirin yi bari na har abada, ai bata iya dai-daita nunfashinta ba sai kawai gani suka yi ta sulale a ?asa babu alamun nunfashi a tare da ita. A kuma dai-dai wannan lokacin ne baki da idanun Husnah suka gama rufe wa ruf alamar an gama amsa kiran Ubangiji.
A sanyayye Maina ya saki hannunnta daya gama sakewa gaba Waya ya Wauki wani irin sanyi, baya yayi ya zauna daSas a ?asa kamar wani gala. Ita kuma Hasiya mutuwar tsaye ta yi a wajan da take, babu baki kuma ga dukkan alamu idanunta ?iftawa kwai suke amma ba lallai tana iya tuna abinda idanunta suka gani ko suke kan gani yanzun ba.

Dr Hadiza ce ta Wauko dara a cikin kayan tarbar haihuwar da suka zo da su ta rufa Mamaciyar dashi, kafin ta dokawa Dr kira, yana Wagawa ta ce dashi ''sai hakuri Dr ta rasu'', da jimami sosai Dr Yahuza ya ce ''to dama ya za'ayi? Ai dole sai ha?urin kam, Allah ya yi mata rahama ya bamu guzurin tarda su, ga ni nan zuwa'' ya faWa yana katse kiran lokaci Waya kuma ya fito daga ofishinsa da nufin zuwa Wakin, Dady ya hanga a zaune sai faman duba agogon hannunsa yake yana kuma le?en ?ofar, dan ba dama ya shiga Wakin da sarakuwa take nakuWa ne amma da tuni ya daWe da shiga ciki dan ganin halin da take ciki.
Mi?ewa tsaye ya yi ganin Dr Yahuza, sai dai bai gama tantance yanayin fuskarsa Dr'n ba yaji yana yi masa ta'aziyya da ce wa ''sai ha?uri Alhaji, rai fa ya yi halinsa, sai fatan Allah ya karSi shahadarta'', ai Dady bai san lokacin daya koma inda ya tashi ya zauna daSar cikin ficewar hayyaci na wuccin gadi ba.

Wasu ma'aikatan asibitin guda biyu ne suka fito da Mama Zainabu kwance akan gadon ?an jinya, dan suman da ta yi an yayyafa mata ruwa amma shiru bata farfaWo ba, shi ne za'a kaita da?in daya dace dan bata taimakon gaggawa.

Shigowar Dr Yahuza Wakin ne ya yi dai-dai da dawowar Maina da kuma Hasiya cikin tunaninsu, da gudu Maina'n ya je ya kama hannun Dr yana faWin ''Dr ka duba min matata dan Allah, wai ta mutu! A ce war wannan likitar, amma Ni na kasa yarda, na kasa yarda Husnah ta barmu bari na har abada daga wannan lokaci, wallahi da nasan wannan cikin zai bata wahala har daga karshe ya yi ajalinta dana kaita an cire mata shi tun bai je ko'ina, Dr dan Allah ka duba min'' wasu siraren hawaye ne masu zafin gaske suke bin fuskarsa lokacin da yake wannan magana.
Kama hannunsa Dr'n ya yi yana girgiza masa kai tare da faWin ''kayi istigfari Jalaluddeen, ka tubarwa Ubangiji, kaifa musulmi ne kuma mumini, nasan kasan muhimmancin ?arSar ?addara koda bata zama dole Mutun ya karSa ba, bare wannan da ta zama dole a rungumeta, babu wanda ya taSa mutuwa kuma ya dawo Jalal, mutuwa guda Waya ce kuma ita matarka ta yi sai ha?uri, kayi mata addu'a Allah ya sadata da rahamarsa duk dama ana kyautata mata zato, yanzun za'a kaita mutuware, sai ayi gaggawar kintsa ta a kaita gidanta na gaskiya duba da yanayin yadda abun yazo'', yana kaiwa nan ya cire zaren karin ruwan nan da yayi mata, dayake dama Dr Hadiza ta kashe shi tun lokacin da rai ya yi wa Mamaciyar na ba?o.

Tura gadon Dr ya yi dan ficewa daga Wakin, yayinda su duka suke bin bayansa, Ammy da har yanzu ta kasa cewa komai sai addu'a da take ta yia cikin rai da zuciyarta, Maina daya gama ficewa daga hayyacinsa da kuma Hasiya da ta zama mutun mutumi.

''Docter ka tsaya wallahi Anty na bata mutu ba dan yanzun nan ma naga cikinta ya yi motsi'' Hasiya ce ta ?wolla wannan ?ara da i?irarin Husnar bata mutu ba ya dawo mata da Anty'nta.
Da gudu tayi kan gawar Husnan a ?ar tazarar da Dr'n ya basu, Maina ne ya yi ?arfin halin zuwa ya ri?e ta da nufin ri?e ta karta isa wajan, dan su a tunaninsu ko abun ne ya taSa ta dayawa.
Wata iriyar juyowa ta yi da dukkanin ?arfinta ta to?areshi da hannayenta duka biyu, ba wani sassauci a cikin muryarta ta shiga faWin ''kar ma ka fara wallahi, babu wanda zai yimin shamaki da Antyna alhali naga da sauran rayuwarta, ku duba ku gani idan har ?arya nake yi'' tana faWin hakan ta fara kokawwa da nunfashinta wanda dama tun Wazu yake ?o?arin barin gangar jikinta, ko second biyar bata ?ara a tsaye ba ta faWa jikin Maina babu alamar nunfashi a tare da ita.

FaWin tashin hankalin da Uba, Uwa da kuma Yaronsu guda Waya tilo suka shiga to Sata lokaci ne, da yake wannan dattijuwar da suka zo tare da Mama tana can tare da ita a Wakin da aka kwantar da ita, bayan an gama bata taimakon gaggawa sai aka mata allurar bacci, dan kwakwalwarta ta samu nutsuwa zuwa wani lokaci.

A kafaWa Maina ya Wauki Hasiya zuwa wani Wakin, nan ita ma aka shinfiWar da ita, inda Dr Hadiza ce akan ta.

A bangaren Dr Yahuza kuwa har ya gusa daga wajan sai yaja tunga ya tsaya yana mai rarraba idanu, idan har gaskiya yake gani a gabansa kuma a zahiri to tabbas shima yaga cikin Mamaciyar ya motsa, to kodai da gaske bata mutun ba? Ya tambayi kansa.
Yaye malulluSin da aka lulluSeta ya yi, ai baisan lokacin daya ja da baya ba cike da girmama lamarin Ubangiji. Ganin hakan da Dady ya yi ne yasa ya matso kusa dan tabbatar da abinda yake tunanin kodai da gaske ne bata mutu ba.
Sai dai yadda yaga abun shima sai ?amewa ya yi guri guda yana tashibi da kirari wa Ubangiji a cikin zuciya da duka gaSSan jikinsa.
Ammy ce kawai bayan ta iso gab dasu taga abinda suka gani ta yi ?arfin halin faWin ''to miye kuke jira Dr? Dan Allah kayi wani abu mana tunda har Allah ya nufa Wan cikinta yana raye duk da mahaifiyarsa Allah ya Wauki abinsa, dan Allah kar a yi sake a hanzarta''.
Ajiyar zuciya Dr Yahuza ya yi, lokaci Waya kuma ya ce ''Allah ya hukunta'', yana faWar hakan ya juya akalar tafiyarsa zuwa Wakin tiyata.
Cikin ikon Allah da taimakon abokan aiki suka ciro wani santalelen Yaro mai mugun kama da Jalaluddeen sak kamar an tsaga kara, babu wani abinda kai tsaye za kace gashi yana kama a mahaifiyarsa.

Allahu akbar Allah mai iko, shike Wauke wanda yaso a lokacin yaso, ya kuma raya wanda yaso a lokacin daya ga dama. Allah gagara misali wanda yafi misali, Hayyun laa ya mutu abadan.( Labarin yadda Husnah ta rasu yayin na?uda da yadda aka ciro yaro daga cikinta bayan ta rasu ta hanyar tiyata wannan gaskiya ne, ya faru a inda nagani da idona bawai aka bani labari ba) dan haka jama'a mu kiyayi Allah kuma mu tsarkake shi, babu wani abu a duniyar nan da yake wanzuwa kuma ya Wore idan ba buwaya da girman zatin Allah ba, kai Mutun ne, Ni Mutun ce, ku Mutane ne, muma kuma Mutane ne, Allah da kansa ya ce ( Wama khala?tal Jinna wal Insa illaa li ya'abudun) Allah bai halicci jinsi na Mutun da Aljani ba face dan su bauta masa. Kuma da duka halittun duniya za su dore a bautar Allah dare da rana babu abinda zamu ?ara wa Ubangiji, kuma da zamu bijire gaba Waya halitta muna saSawa Allah dai-dai da ?ayar zarra ba zai ragu daga cikin mulki da buwayar Ubangiji ba. Allah yasa mu dace amin.


Zuwa bayan la'asar tuni aka kaita gidanta na gaskiya, bayan an sanar da ?an'uwa da abokan arziki. Gidaje uku na gidan biki haka suka koma gidan makoki dan mutuwar tazo musu a bazata kuma bagtatan, gidan malan Inuwa, gidan Anty Mariya, da kuma gidan su Hasiya. Ko gidan su Kalil ma ba wani shagali da aka ci-gaba da yi sam.

Mama Zainabu ta riga Hasiya farkawa, dan ita tana cikin hayyacinta lokacin da aka tafi sutura, sai dai ta sanyawa ranta dangana sosai, ta yadda ko kuka ta hana kanta yi bayan ta farfaWo, sai ma godiya da kirari data shiga jerowa Ubangiji jin ance mata an ciro yaro daga cikin matattar ?ar tata, dayake yaron yana wani Waki da aka saka shi, sakamakon wahalar daya sha da kuma neman hanyar fitowa daga cikin mahaifiya ba tare da taimakon uwa ba, wannan gwagwarmayar daya sha ita ta haddasa masa kaikawo na nunfashi bayan an ciro shi, wanda hakan na iya bashi matsala kamar na cutar asuma ko makamancin ta, sai dai abinda hali ya yi, a ce war Dr Yahuza da shi kanshi na tsawon shekarun aikinsa a bangaren likitanci ya yi ta gamuwa da haihuwa kala da kala, amma bai taSa ganin irin hakan ba sai yau.
Dayawa za kaga sai bayan an gama aikin uwa zata mutu tabar yaronta, ko kuma shi yaron a ciro shi babu rai, ko kuma uwar ta mutu da cikin jikinta kafin ko bayan an gama aikin, maganar ciro yaro bayan mutuwar mahaifiyarsa kam yau ne farko.


Bayan kwana uku
Zaman makoki ake yi kamar yadda ake yi a ko'ina, kowa ya sawa ransa dangana kama daga kan iyayen Mamaciyar ?annai da sauran danginsa, kowa ya rungumi ?addarar da wata rana dole tasa za'a runguma.
Sai dai abun ba sau?i a bangaren Maina, dan sosai mutuwar ta dakesa fiye da kima, uwa uba kuma Hasiya da har yanzun aka kasa gane kanta, duk ta sawa kanta damuwa gashi kuma Dr Hadiza sosai ta yi gargaWin a kula da ita sosai, kar a barta ta sanya damuwar da zata cutar da ita ko ta illata dan tayin cikin dake jikinta wanda sai yanzu da tayi dalili aka san da wanzuwar sa. A haka dai a ke ta musu a taro a taro daga shi har ita, matsalar tana wajan cin abinci idan lokaci ya yi, musamman ma ita Hasiyar, dan a kwana ba biyu da rasuwar da ta ?i ta saka komai a bakinta koda kuwa ruwa ne a bakinta, sai aka kaita Wakinta aka haWa da abincin, aka kirawo Maina akan yayi mata dubara ko Allah zai sa ta yarda ta ci idan har shi ne ya bata.
Amma fafur ta?i koda bari su haWa ido dashi bare har yaga bakin da zai bata abinci ta ci, a kuma wannan lokacin ne Maina yasan Shukuriyyarsa tana fushi dashi sosai, dan yanayi da kuma lafuzzan da tayi anfani dasu wajan yi masa magana ya Wauka ya dora akan mizanin da zai iya gane maganarta a matsayinsa na lauya, ya kuma gane cewa tana fushi dashi ne game da kiran da suka sha tayi masa ba adadi daga ita har Ammy amma bai Waga ba.
Bai ji dadin yadda ta yi masa mummunar fahimta ba har take jifansa da maganar da bai kamata a ce an jita adaga bakin mai cikakken imani ba.
Dan cewa tayi yana da alhaki a mutuwar yayarta , tunda tun farkon fara na?udar da tayi take kiransa yazo ya kai su asibiti amma ya?i daga kiran, har hakan yazo ya faru.


Yau ne addu'ar mako, kuma a yau ne bayan an gama addu'a aka daura wannan auren da ba'a samu damar Waurawa kwanaki shida da suka wuce, an daura auren Issa Ibrahim da Safiyya Badamasi, da kuma Ibrahim Khalil Mustapha da amaryarsa Sajida Umar, haka aka mai?a amare Wakunan aurensu ba tare da wani shagali ba, yaro ma a yau ne aka yi masa fatihar suna, inda aci sunan ?alhat daga maln Inuwa da shi Dady ya bawo zaSi akan ya zaSawa yaro sunan daya dace, bayan shima baba Haruna ne ta bashi damar ya zaSa, inda shi kuma Babban yaro ne da kansa ya bawa baba Haruna'n zaSi, amma sai zuciyarsa ta raunana dayawa, shi ne ya bawa Dady'n zaSi.


Yau kwanaki goma kenan da faruwar komai, kuma a yau ne aka bawa su Maina yaron nan daga asibiti, bayan jikinsa yayi kyau ba laifi.
Dama uwarsa Hasiya kusan kullum sai taje ta daWe a asibitin duk da inda aka saka yaron ko masu zama babu, Likitoci ne suke kulawa da komai matukar Yaro yana wannan Waki, da yawansu dama madara ne ake basu ta ?ar mesar da ake jona musu wacce tabi daga cikin hancinsu har zuwa cikin cikinsu.

Haka suka dawo gida Hasiya na rungume da yaron.

Bayan zaman da aka yi a washe garin ranar da aka karSo yaro daga asibiti, inda Dady ya tambayi mama Zainabu cewa tana da sha'awar a bata yaron ta ri?e ko kuma a bawa uwarsa Hasiya ya zauna a wajanta kamar yadda ta nemi alfarma?. BuWar bakinta sai cewa tayi ''da Hasiya da Husnah ai duka Waya ne Alhaji, ku bar mata ta ri?e shi ai yaronta ne, koda a ce Husnah tana raye nasan yaron zai rayu ne tamkar ita Hasiyar ce ta haife shi, dan haka babu wani anfanin bara uwa da Wanta.

Wannan magana babu wanda bata yiwa daWi ba musanman ma Hasiya da take jin wata iriyar soyayyar yaron ta kuma nunkuwa a cikin ranta, ta kuma ganin girma da kimar Mama Zainabu sun kuma hauhawa zuwa farashin da ba wani mai kuWin da zai iya siya ko a goge ba, cikin kuka ta ce ''na gode sosai Mama, Allah ya saka da mafificin alkhairi ya ?ara girma da shekaru masu albarka, na gode sosai! Kuma in sha Allahu zan ri?e wannan yaron nawa fiye da yadda kowa yake zato, fatana dai Allah ya taya Ni ri?o ya kuma yiwa rayuwar yaron albarka, ya jikansa mahaifiyarsa ya kyautata makwancinta, yasa tana kwanciyar hutawa ya kuma bamu guzurin tarda su'', nan kowa ya amsa da amin kafin taro ya watse, aka bar daga Maina sai iyalansa.

Har ana shirin rufe kwana arba'in da rasuwar Husnah zaman Hasiya da Maina ba wani canji, zata Wora girki tayi, da duk wani abinda tasan dole ita ce za ta yi masa shi duk tana yi, sai dai suna gama cin abinci bayan ta bawa yaronta madararsa kamar yadda Dr ya faWa mata lokuta da kuma yadda ya kamata a ce tana bashi ita, haka zata Wauki yaron da a kullum yake cikin kyaukyawar shiga tayi wucewarta Wakinta, duk da ya taSa sakawa Wakunan key ba amma bai taSa gigin zuwa da sunan zai bi bayanta ba, haka shima zai wuce Waya Wakin daya jima da maida shi nasa tun a lokutan baya ya shiga ya kwanta, dan duka ya dawo nan sashen yanzu da zama, idan har ka ganshi a sashensa to wani abun yaje Waukowa.

Haka suke ta rayuwa a gidan kamar kurame, a haka har aka yi sadakar kwana arba'in, inda Dady yasa aka haWa duk wani abinda aka san na Husna'n ne aka sauke nata nauyin bawa magadanta, kama daga kan kayan Wakinta, irin su sar?o?inta masu daraja wa'yanda wasu a ?an watannin nan ne ta mallakesu ta hanyar mijinsu da kuma surukansu.
An raba komai kamar yadda shari'ar Muslunci ta tanada, inda abinda ya kasance na ?alhat wanda suke kira da Sultan ne Dady yasa aka masa kuWinsu, ya kuwa cire ya ajiye a gefe guda, in da aka yi sadaka da kayan, kuWin kuma ta Wauka ya bawa Maina akan ya kulawa da yaron kuWin gadonsa, da yake bawai iya kuWin bane Dady'n ya bayar kuWaWen sunada yawa yasa Maina yanke hukuncin buWe wani katafaren wajan wasan yara wanda ake matu?ar shigo da kuWaWen shiga a wannan zamanin bayan ya shawarci su baba Haruna da kuma Mama'n Husnah Win. Ita ma Hasiya koda ya tunkareta da maganar cewa tayi ya yi abinda ya dace, ba wani Sata lokacin aka tashi aiki ba kama hannun yaro.............. Maman Abdallah ce
[15/04 ? 21:28] Ummu Khalifa>??>??=??: https://chat.whatsapp.com/CIhb9DG7WaZCelVPAqy19T *_A KAN SHI_* Pages 44_____________ Tafiya tana ?ara tsayi, yau kusan watannin uku kenan da rasuwar Husnah, inda cikin Hasiya ya shiga wata na huWu kenan.
Sosai ta maida hankali wajan rainon yaronta Sultan, wanda yanzun idan ka ganshi ba zaka taSa ce wa Wan watanni uku bane, ya warware sosai bayada wata damuwa a rayuwa, wanka akan kari, shan marada akan tsari da duk wata hidima tasa uwarsa takan masa akan lokaci.
Kowa na dangi haka yake so da ?aunar yaron, dan sosai ya shiga ran jama'a harma wa'yanda ba na cikin dangi ba.

Har zuwa wannan lokacin Hasiya bata bawa Maina wata ?ofar da zasu koma rayuwarsu irin ta da kamar kowane ma'aurata.
Yanzun a Waki Waya suke kwana bayan ya matse mata waje, sai dai rabo da wata cikakkiyar mu'amalar auretayya ta shiga tsakaninsu tun asubar ranar da Husna zata bar duniya, a ranar sun faranta ran juna kamar ba gobe, ashe za'a daWe ba'a haWu ba bayan wannan.
A yau Maina yasha alwashin sai ya dai-daita tsakanin sa da matarsa farin cikin sa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login