Showing 9001 words to 12000 words out of 109651 words

Chapter 4 - A KAN SHI complete by Maman Abdallah

31 Oct 2025

3141

yaja tsoki.


Cikin dariya kalil yace '' hali hanji, kowa ka gani da Nasa yake yawo''.
Shiru Maina yayi masa , a haka har su iso ?ofar gidan su Hasiya.


Kalil ne a gaba Maina yana bin bayan sa, a bakin soron dake gidan suka tsaya suna neman iso daga ma'abota gidan.


Baba Ibrahim ne ya fito da Fara'a a fuskarsa, dama tun Wazu suke dakon isowar su, batun zai taimaka musu da yayi shi ya kwana a zukatan su.


A tabarmar da Mama ta shinfida a kai suka zauna, suke shiga gaishe da su, tare suke amsa wa bakin su yaki rufuwa ya kamar Mama da take ganin kamar Ubangiji ne yayi niyyar yaye musu ibtila'in y'daya jarabeau dashi.

Ruwa Mama ta kawo musu, dayake da Wan sanyin Safiya Sai ba su shaba.
Cike da girmamawa Maina yayi gyaran murya yace '' Baba nazo ne dan naji gaskiyar abinda ya Faru dan gane da Hasiya, daga aurenta zuwa lokacin da komai ya faru'' ya tsure Baba da ido kamar shine wanda yayi laifin.

Tuni Mama ta fara goge kwallar data fara taruwa a idanun ta, cikin sanyin murya ya kuma cewa '' kiyi ha?uri Mama, ba bu abinda zan iya yi idan har banji gaskiyar abinda yake zahiri ba '' , cikin dakiya Baba yace '' yaro zan faWa maka abinda muka Sani, sauran kuma sai Allah ne kawai zai bakwa haske akan abinda Yake sirrin boye''.



Hausa Baba ya Zayyane wa Maina komai, tun daga kan yadda aka yi auren da zaman da Sukayi na Tsayin watanni biyu, har izuwa kan rasuwar Mukhtar din.


Tabbas ya fahimci abubuwa da dama a labarin, wani bangare nata zuciyarsa take jin labarin yana taSa masa, ba shi ba , ko kalil saida yaji jikin sa yayi sanyi jin irin soyayyar da take tsakanin Hasiyar da mijin ta, amma ya a Kayi hakan ya faru, bayan daga ita sai shi a gidan, tabbas abin da kulle kai kam.
Basu jima. Ba. Suka yiwa su Mama da Har yanzu kakan take sallama suka Bar gidan .


Suna tafiya ba wanda yake Cewa komai can Madina yaga shurun ba amfanin da zai yi masa yace '' mi ka fahimta?'' ya tambayi kalil.
''kaii wai ni kake tambaya, kaima da yake aikin kane abun ta daure maka kai ina ga ni, Wallahi duka. Kaina ya kulle dan kaji, ta kaka za'ace ita. Ta kashe Mukhtar bayan tarin soyayyar da take masa , kawai duk yadda akayi kawai abinda ba Daidai ba ''.

'' tabbas rabin amsar tambayar yana wajansa'' Maina ya FaWa da yakinin state dashi.
'' wake nan?'' kalil ya maido wa Maina kai tsaye.

'' Eh tabbas Barister Lawali ya zama dole Ka amsan tambayoyi na'' ya faWa tare da buga Sitiyarin Motar cikin ?o?arin rai, ji yake dama Lawali ya bayyana gaban sa yanzu, Wallahi da sai yayi masa matsar Awara har sai yaji ya matsu kafin ya bashi damar dazai maida masa Yadda akayi .

Sosai kalil ya tsira yasa ganin halin da Maina na yake ciki, ganin ya nufi gidan yari yace dashi '' Please abokina dan Allah mu koma gida, idan ka sami relif sai muzo'' dan Allah.
Da har zai Musa shi daga baya kuma komai ya gani oho, ya. Juya akalan motar zuwa gida.

A hanya ya tsaya a wani Rastauran yayi musu odar abinci, dan ka'idar shi baya cin abinci idan ba 'a gida ba .
Sai da ya sauke kalil tare da tasa ledar kafin ya wuce gida, duk jikin sa da daWi, zuwa wannan lokaci ?arfe sha goman rana harda wasu Mintuna a kai
[15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: *_AKAN SHI_*

Page 12

Da sallama shiga falon ya tarar da Husy zaune a kujera, wayar ta a hannun ta da alama ta gama anfani da ita ne ko dai zata yi, a hankali ya ?arasa kan doguwar kujera ya zube da ledar abincin daya siya a hannun sa, rubda ciki yayi yana maida nunfashi, ba zai iya tantance abinda yake ji a ransa ba, tabbas damuwa tayi masa yawa.


Cike da kulawa ta matso inda yake kamar mai shakkar wani abu, a hankali takai hannun ta saitin wuyan shi, nan tai kamar mai zazzaSi, yana jinta saidai bai ce da ita komai, takalmin ?afarsa ta soma cirewa, kafin ta dawo kan agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, nan ma tsirewa tayi , kanta ta Waga ta duba lokaci, a ranta tace ko dai yunwa yake ji ne ta tambayi kanta, da sauri ta tashi zata nufi kicthing dan ta zubo masa abinci, Wazu bayan fitar sa tadan gyara cuscus da ?ar ?aramar sauce, ?afarta ce ta Wan buge ledar daya ?ar kusa da kujerar da yake kwance, Wauka tayi ta nufi kicthing din da ita , tare da cuscus din ta jero da gasashiyar kazar daya shigo da ita ta nufo falon, a zaunetagan shi yayi tagumi kamar wanda aka turawa sakon mutuwa, karasowa tayi ta ajiye tiren a gabansa, ta koma ta dauko ruwa a frige ta da cup ta dawo ta zauna, akaro na farko ta kawo ko wa mijinta abinci da ruwan sha dan ibadar aure, cikin kasa da murya da kuma lan?washeta tace '' dan Allah ka daure kaci abincin kaji, kaga kamar zazzaSi ne a jikin ka'' kamar zata yi kuka take maganar, kollonta yayi da lumsassun fararen idanun sa da suka sauya launi zuwa ja, labarin da Baban Hasiya ya bashi ya Waga masa hankali, ya akayi hakan duka ya faru bai sani ba, dama har akwai wani abu da yayi ta wanzuwa a rayuwar Shukuriyya wanda bai san shiba, ya tambayi kanshi, tabbas hakan zai iya faruwa tunda yanzu da da bane, akwai wani shingen dazai hana yasan kamai da komai, ya bawa kansa amsa.
Ba zato taga ya fara cin abincin kamar bayaso, a sace take kallon sa , tabbas Mainasara yakai asoshi ko bashi da komai, bare alhamdulillah babu abinda bayada dan gane da rayuwa kyau, ilimi, nasaba, wayewa da kuma kyakkyawan ala?a da kowa, abu biyu ne game da rayuwar sa basu yi mata ba , na farko shine haramtacciyar da yake yiwa Shukuriyya, ko tamtama batayi akanta ya shiga wannan halin, tana fatan Ubangiji ya sassauta masa ya kuma yaye masa abunda yake kansa game da ita, Allah ya kawo hasken da zai haskaka masa gabansa ya gane cewa tayi masa nisa, bazata ce nisa na har abada ba, amma tanada yakinin ba lallai yasameta a rayuwa ba, sai abu na biyu game da iyayen sa, bazataso ace mijin da take tunanin samun aljannah domin sa ya rasa tasa aljannahr sakamakon rashin kula da lamarin iyayen saba, duk da tasan ba banza haka aka barshi ba zata yi kokarin ganin ta haWa fuskokin su dashi da mahaifiyar sa, tabbas sai ta kalubalenci makiya ta kowane bangare, a wannan karon bazata dagawa kowa kafa ba, zata tsaya tsayin daka A KANSHI, zata nuna musu A KANSHI babu abinda ba zata iya yiba.
Tana tsaka da wannan tunanin har ya gama cin abincin, sai alamar tafiya ta lura har ya kai bakin ?ofar dakin sa, saida ya kama mu kofar ya juyo gare ta, karaf ya kamata tana kallon sa, da saurinta ta kauda kai cike da boren kunya ta fara tattare kayan daya gama cin abinci, '' Please idan kinada maganin ciwon kai kiban'' ya faWa kamar zai yi kuka.Saida gabanta ya fadi jin muryar sa a cikin damuwa, Ba ta iya amsa shi da baki ba, saidai ta Waga masa kai alamar toh, bai jira wani abinda zata ce ba ya shigewar sa Waki.*Gidan yari*


Tunbayan da suka gama ayyukan da sukeyi a matsayin horo suke zaune a karkashin wata bishiyar mangwaro, Ikleema ce ta kalli Hasiya data zufafa a tunani tace '' ?awata ina sauraron ki, kinyi alkawarin yau zaki bani labarin ki ko ?'' , '' eh tabbas yanzu saiki gyara zama danjin wace asalin Hasiya da kuma abinda ya shigo dani wannan gida da kuma bakar kaddarar rayuwa'' , sun dauki tsawon lokaci a zaune, Hasiya tana bawa Ikleema labari, sosai Ikleema ke kukan tausayin Hasiyan da iyayen ta, kukan rashin Wan'uwanta Issa da kuma rashin abun kauna da bagenta a duniya baki daya, kasa cinye tambayar dake Wauke a bakin ta tayi tace da Hasiya '' to waye wannan wanda yace zai taimaka miki, miye alakar ki dashi ?'' Ikleema tayi tambaya cike da san sanin karshen wannan labari mai sarkakiyar gaske.*Gidan yari*


Tunbayan da suka gama ayyukan da sukeyi a matsayin horo suke zaune a karkashin wata bishiyar mangwaro, Ikleema ce ta kalli Hasiya data zufafa a tunani tace '' ?awata ina sauraron ki, kinyi alkawarin yau zaki bani labarin ki ko ?'' , '' eh tabbas yanzu saiki gyara zama danjin wace asalin Hasiya da kuma abinda ya shigo dani wannan gida da kuma bakar kaddarar rayuwa'' , sun dauki tsawon lokaci a zaune, Hasiya tana bawa Ikleema labari, sosai Ikleema ke kukan tausayin Hasiyan da iyayen ta, kukan rashin Wan'uwanta Issa da kuma rashin abun kauna da bagenta a duniya baki daya, kasa cinye tambayar dake Wauke a bakin ta tayi tace da Hasiya '' to waye wannan wanda yace zai taimaka miki, miye alakar ki dashi ?'' Ikleema tayi tambaya cike da san sanin karshen wannan labari mai sarkakiyar gaske.'' ba wanda yasan shi ko a gidan mu, kawai ina ga Ubangiji ya kawo mana shine a matsayin garkuwa da tsanin fitar mu a ?angin rayuwa , nasan zai yi nasara insha Allah, duk da inaji araina A kANSHI komai ya faru'' cewar Hasiya Ibrahim mai Tattasai.................
[15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: *_AKAN SHI_*

Page 13

Karfe uku da minti ashirin ya tashi daga nannayan bacci daya Wauke shi tun lokacin da Husnah ta kawo masa maganin ciwon kan kamar yadda ya bukata.


Dafe kansa yayi duk da yanzu ya daina masa ciwo ba kamar Wazu ba, ganin lokacin sallahr azatar ya wuce yana bacci, zuro da ?afarsa yayi daga saman gadon yan shirin sabka, daidai nan Husy ta turo kofar wa?o?in da sallama bakin ta.

Wannan shine shigowar ta na uku bayan kwanciyar sa, cikin kulawa ta iso kusa da bakin gadon tace '' sannu ya sau?in jikin?'', sosai yaji dadin kulawar da take basa daga jiya zuwa yau, a hankali ya Waga bakinsa yace '' alhamdulillah nasami sau?i sosai karki damu''

Yun?urawa yayi ya tashi tare da faWa toilet, ruwa ya sakarwa kansa tare da lunshe idanunsa, tunanin ta inda zai fara yake, ya zama dole a yau yaje gidan yari wajan Hasiya danjin sauran bayanin abunda ya faru, gashi a tashin nan da yayi daga bacci yaji yanasan ganin Ammin sa, so yake yaje ya ganta yaga yanayin da take ciki a yanzu, yana wannan tunane tunanen har ya gama wanka tare da Wauro alwala.


?aure da tawul a ?ugunsa ya fito daga toilet din, ta gyara gadon tsab, ta feshe dakin da turaren Waki na ruwa, saida ya lumshe ido yashaki daddaWan kanshi da sanyin da Wakin ya Wauka, dresing mirror ya nufa, crem ya shafa sama sama kafin ya nufi drauwer kayansa, doguwar jallabiya kalar maroon ya ciro tare da wandonta, kayan irin na indiyawan nan ne masu dogon hannu , sosai kayan suka amshi shi lokacin daya saka, turaren daya kasance shine asalin kanshin jikinsa koda baya waje ya feshe jikinsa dashi , nan Wakin ya kuma Waukan ?anshi na musamman, key din Motar sa ya dauka akan bedsed drowa da Husy ce ta shigo masa dashi ya fice a Wakin.


Bai ganta a falo ba saboda haka direct hanyar fita ya nufa, har yakusan ficewa sai kuma ya dawo tunawa da yayi zuwa yanzu ya kamata ace tana sanin fita da kuma shigowar sa gidan, dan ko ba komai tana bashi kulawar daya dace, a dalili da haka shima zai yi ?o?arin ganin yana kyautata mata ko ya'ya ne .


Tura kofar Wakin yayi ya saka kai da sallama a bakinsa, bata Wakin sai wayar ta daya gani a kan gado tana neman agajin gaggawa, da yake ba wani kara take ba, sai haske da km badowa alamar kira ne shigowa, takawa yayi har tsakiyar Wakin , sai yanzu ya gane tana bayi ne, dan yana jin karar zubar ruwa alamar tana wanka, wani kirana ya kuma shigowa wayar karo na biyu bayan tsayuwar sa, hannu yasa ya Wauki wayar yana ?arewa number kallo, ras ras ras gabansa ya fadi, idan har idanunsa daidai suka gani to number Momyn sa yake gani tana yawo akan screen din wayar Husnah, to miye alakar ta da Momy , ya tambayi kansa bashida amsar tambayar a wajan sa '' ya Ilahi'' ya faWa a bayyane, miye yasa mutane suke so su tarwatsa masa ?wa?walwa ne, '' ya Allah ka haskaka mini dubun dayake gaba ''.


Tashn hankalin sa ne ya karu lokacin da yaga shigowar sako daga Momy, sosai yaso jurewa kar ya duba amma ya kasa.

......Kinsan ni kuma Kinsan halina da kuma abinda zan iya aikatawa dama akasin haka, wallahi tallafi kika kuskura kika bada hanyar da Son ya gane wani abu yanaa tafiya ba daidai ba zakisha mamaki na, ki barni da abinda ya tunkaro ni kawai ya isarmini, kija baya dashi kamar yadda na horeki tun farko sabanin hak abun bazai yi kyau ba ! wannan shine abindaddanawarrr gida akan shi bazai iya tsayawa a Waura aure na yana nan ba matukar da Mukhtar za'a Waura, haka ya tsallake iyayen mu dani ?ar'uwarsa yayi tafiyar sa, hakan da yayi baisa naji na fasa auren Mukhtar ba, duk da bansan dalilin sa nayin hakan ba .


A daren da a ka kai ni gidan Mukhtar naga tashin hankali da idona, tsantsagworan tsana haushi da kuma kyama kawai nake gani a idon mijina a madadin tarairaya, lallashi , riritawa da kuma shauki, tun a wannan daren ranar na fara shan ukuba rayuwa daga garesa, bansan mi ya shigo tsakani ba, amma nasan wannan ba Mukhtar dina bane mai so da kuma nuna mini ?auna tun a lokacin ?uruciya, kwanan mu goma da aure amma ba abinda ya sauya, sai ma ci baya da aka samu, Mukhtar ya hana kowa zuwa inda nake, ko wutar nefa banidashi a gidan, kuma ya karSe waya ta, sai na zama kamar kurma, ba umm ba um'um, bazanyi fira dashiba, kuma bazai barni nayi da wani ba, har a wannan lokacin bana ganin laifin sa, ina ganin akwai wani abun daya gifta wanda ba daidai ba, dama bashida yawan dangi a gari, ko lokacin aure danginsa da suka zo gidan wani amintaccen sa ya sauke su, aHnan akayi komai kafin ana gama hidima suka tafiyar su.


Har na rufa wata ba wani sauyi, dama bamu taSa hada wajan zama ko kwanciya dashi, daga karshe sai ya zama hatta abinci baya bani wadatacce, babu wanda zan fadawa tunda babu inda nake zuwa, haka na hakura naci gaba da zama a wahale, a watanni biyun dana yi a gidan sa sau Waya tak ya taba barina naje na gaishe da iyaye na , kuma shima tare dashi muka tafi , cikin mintinan da badugi ashirin ba muka dawo gida, duk ya tsare gaba ya tsare baya wai kar ya bada baya ayi maganar wannan munafikin mutumin mai ?yetare iyakar Ubangiji, duk da bai fito fili ya fada mini da bakin sa yan zargin mu nida Iyaye naba, to na fahimta daga kalaman bakin sa da a kullum yake mini munanan kalamai, tare da kushe tarbiyyar gidan mu, zuwa wannan lokaci ya fara kaini a bango, na kasa jurar cin zarafi hadi da zagin da yake yiwa magabata na, nabi duk hanyar da yakamata a ce nabi wajan ganin na daidai zaman mu a matsayina na mace, amma bawan Allahn nan yaki ya saurare ni, a ranar da abun zai faru ina zaune bayan sallahr magariba, ya shigo da leda a hannun sa abinda ban taSa gani ba tun shigowar ta gidan sa a matsayin mata, saSanin da a duk nemansa na duniya nata ne.
[15/04 ? 21:17] Ummu Khalifa>??>??=??: *__AKAN SHI_*_

Page 14
_______Da sallama ya shigo a bakinsa a karo na farko, tsananin mamakin nada nake ciki har kasa amsa sallamar nayi, har ya shigo ya wuce Wan ?aramin falon mu mamaki bai barni ba, shida idan zai shigo baya shigowa da fuskar rahama, yau shine harda sallama? na tambayi kaina, ban tsure da lamarin ba saida ya fito yana kallo na kamar wani maye, ya iso kusa da inda nake zaune akan dardumar dana gama yin sallah ina lazumi, duk da ana Wan sanyi a garin amma rashin batiri a ?ar fitilar hannu da Mama na ne ta maso mini ita a kaya na tun lokacin da za'a kawo ni gidan, a cewar ta mu yaran zamani akwai sakaci, haka zakaga Mace an Wauke wutar nefa ga ba caji a waya ba tocilan, sai kaga ana shiga wani hali a lokuta da dama.


Kama hanuna yayi ya tasheni tsaye ban ankare ba naji na manna Ni da jikin sa , Wan shiru tayi tana nunfasawa.

Barister Jalaluddeen ya kureta da ido yana jiran yaji karashen maganar da take so ta faWa, duk da yasan yin hakan kamar zunubi yake aikatawa kallon matar da ba tasa ba, ...... ai kamawa tayi ya bawa kansa amsa lokacin da ya gyara zama dan ya yaji karshen iskancin marigayi Mukhtar din a cewar sa.

'' yallaSai kamar lokacin da aika baka ya ?are'' wani kurtu ya faWa yana kallon agogon dake Waure a tsintsiyar hannun sa, da yake dama yana wajan a tsaye da ?ar sandar .

Kallon nasa agogon shima Maina yayi yace '' Please a ?ara mini wani lokacin dan Allah alfarma nake nema'' ya fada tare da haWa hannaye biyu alamar ro?o.


Shikansi securityn yasan bayada wata alfarmar da Jalaluddeen Umar Maisara zai nema a wajansa, duk gari babu wanda baisan ahalin Mainasara ba, dan haka yace '' a tashi lafiya yallaSai '' cikin girmamawa yayi maganar tare da barin wajan gabaki daya.

Kallon sashen da Hasiya take Maina yayi sai yaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login