Showing 96001 words to 99000 words out of 109651 words

Chapter 33 - A KAN SHI complete by Maman Abdallah

31 Oct 2025

3126

suke dadawa da kansu, to ita Husnan da har ta ce ta yafe kwana wa Hasiya har sai bayan ta haihu, sai ita Hasiyar ta ?iya ta ce indai har girkin ne aiki ita zata dinga yi duka daga nan har Allah ya buWe ido lafiya.
In dai aka ce maka yau Hasiya ce da girki to haka za kaga malam Jalalu an rasa in da za'a tsunduma rai a samu sukuni, komai shi dai Shukuriyyarsa, haka za'a kwana a yini ana zuba love da kulawa da juna.

Kwanan Hamdiyya arba'in da biyar a gidan Dady tana wanka, kafin aka tattara ta aka maida ita gidan ta, ana ya jibi Waurin auren Kalil da Sajida, yaya Issa kuma da Safiyya, wacce har wannan lokacin take gidan Inna Baraka acan ake komai na hidimar auren, dan malan Inuwa shi ne baban amarya bakwai Alhaji Badamasi ba, dan shi sai dai ma a kiransa da baban ango, dan ko a hidimar auren na abubuwa dayawa shi ne ya yi wa Issa bisa kyautata.

Zo kaga murna da farin ciki a gurin Hisham kamar wanda a ranar ne aka kawo masa ita gidan a karo na farko, bawan Allah! Haka ya rasa ta yadda zai nuna mata iya farin cikin daya shiga a zuwan nan nata, dan shi kam abun a bazata yazo masa, dan ko jiya yaje gidan har yana mata Rakin yaushe zata dawo ne, take faWa masa wai sai ta cika watanni biyu a gida, ashe ma Ammy ta gama shirye-shiryen ta tsab dan dawowar Tata, shi yasa a ?an kwanakin nan ta fita matsawa da bata irin tsume tsumen nan da sirrikan da su iyayen mu sun fimu sanin anfanin da zai yi mana, da kuma irin daraja da Waukar da yake kawowa yl?a mace a rayuwar gidan aure.
Magana ake ta gyaran jiki Mata, ki siya ko ki saida zaSinki ne, nidai abu Waya na ce ki Winda gyara jikinki, za kiga miye za'a fasa.=??

Ammy hidima har ta kusan ta yi mata yawa, gashi dai hidima ta kasu kashi kusan uku, gidan su Hasiya, gidan malam Inuwa ga kuma uwa uba gidan Mariya, wanda abu nasu ne maganin a ?oSesu, shi yasa ma ta maida hankali ta maida Hamdiyya Wakin mijinta dan kar abun ya mata yawa.

Maina babban abokin ango Kalil kuma ya'yan amarya Sajida, a Sangare Waya kuma ?anin ango yaya Issa.
Yadda matarsa ta kasance ba tada lokaci a ?an kwanakin nan haka ma shi da kansa, wasu ayyukan sai jingine su ma ya yi, dan kam suna cikin hidima ba ?arya......
[15/04 ? 21:24] Ummu Khalifa>??>??=??: *_A KAN SHI_* Page 43
''Anty Husnah na gama shiryawa tafiya zanyi, ni wallahi dan kin ce kina so dole sai kinje amma wallahi da kin yi zaman ki a gida ki huta duba da yanayin ki, tunda ai yau daren auren ne, in yaso gobe basai kije ba'' ce war Hasiya da take dai-daita zaman mayafin da ta naWe kanta dashi tare da saka Wan abin dannawa ta danne.
Sai da ta dan cije labbanta kafin ta Wan iya muskutawa ta mi?e zaune daga kwanciyar da ta yi a ?asan carpet din dake falon, fuskar nan duk ta kumbura dama duka sauran jikinta musamman ma ?afarta, duk ta canja kamar ba ita ba.
A hankali ta shiga faWin ''kinsan Allah sai naje, kawai haka sai in zauna ni Waya a gida kamar mayya, ai kawai kije sai kin ganni Madam'' ta faWa tana mai yun?urin son tashi daga ?asan carpet Win zuwa kan kujera.

A nan ma sai da ta yi kamar zata faWi ?asa ba shiri, dan ?afafuwan nata taji sun kasa Waukar ka.
Da sauri Hasiya ta ri?ota da iya ?arfinta, da taimakon ta ta iya zama akan kujerar tana mayar da nunfashi.
A hankali Hasiya ta koma ta zauna a kusa da ita, cikin sanyin murya ta ce ''na fasa fitar nan gaskiya, haka kina faman faWuwar ne kike ?o?ari fita daga gida? Na ha?ura kawai zuwa gobe da sanyin safiya sai mu tafi mu duka harda ke, kafin nan kin Wan warware'' ta yi maganar cikin jimami.

Kama hannuwanta Husnah ta yi tana faWin ''kinga ba za'a yi haka ba wallahi, kawai kije ni na fasa tafiyar, dama kawai ?arfin hali zan yi amma badan inajin daWin jikina ba, Yaro ko Yarinryar nan na bani wahala fiye da tunaninki, kiyi masa/ta bulala akan azabtar da Anty'n ki da suka, muna zama na amana da ke Hasiya, amma a watannin baya naso in Sata wannan zaman, da Allah baisa ke Win mai hankali bace da tuni na munana zaman mu, duk da kuwa nasan ni ce a ciki kuma akaina zata ?are, ki gafarceni dan Allah, wallahi komai da kika ga nayi tun farkon tafiyar nan A KAN SHI ne, ina sanshi! Ina mutuwar ?aunarsa Hasiya, nayi ta danasanin biye wa su Momy Hadiza a lokacin da tayi nufin cutar da My, wanda wannan shi ne mummunan mafarin daya munana duk wata kalmar ?aunar da naji ina masa a cikin raina, nasha wahala sosai kafin ya yarda ya saurareni, ko yanzun nasan albarkacin ki nake ci da nake samun cikakkiyar walwala a gidan nan, yana da kyaukyawar zuciya Hasiya, ki ri?e shi da ?arfin cin tuwon ki, nasan keWin farin cikinsa ce da duk wani wanda yake nasa ne, ki kula da shi da duka zuri'arsa dan duka mallakinki ne, ni a jikina nake jin ce wa zama na daku ba mai tsayi bane, ban san ko ta Allah ta kusan riska nane sanadiyyar wannan'' ta nuna cikinta da ayanzun ma ji take yana wani haucina mata kamar ana cakuWa duka kayan cikin ta, ?asan mararta kuwa da mutun zai Wan danna hannunsa to ba shakka zai yi tunanin ko dutse ta haWiye yake shirin fasowa ta marar ta.

?an rintse idanunta Hasiya ta yi tare da ?ara jin?e hannun Husnah gan-gan a nata hannun.
Da karyayyiyar muryata data fara shiga tashin hankalin jin kalaman abokiyar zaman nata ta shiga ce wa ''ki daina faWar irin wannan Anty, kamata ya yi ace muna manta baya da duk wani abinda ya shuWe matu?ar ba na alkhairi bane, ai an riga da an wuce wannan babin, yanzun dama tun can keWin matarsa, kuma gashi yanzun ma kina amsa sunan matarsa, a matan nasa ma kuma Uwargida, Uwargidan ma kuma farkon wacce zata bashi farin ciki kuma abun ?awa na rayuwa wato ?a?a, gaskiya ki gode wa Allah ke ?ar gatan Jalaluddeen ce, yana ji dake wallahi da gaske, kuma kema kin sani ce wa yanzun yana ?aunar ki sosai, saboda haka ki kwantar da hankalin ki, koda ban taSa haihuwa ba naji ana ce wa ko wane Yaro da irin zuwan da yake yi, to shima wannan haka ne, ta yiyu za kisha wahalar rainon cikin ne kawai, idan haihuwar tazo za kiga ba za kisha wata wahala ba zaki haife mana yaron mu salin alin, kafin bayan wani wata taran ki kuma haifo mana ?an biyu kuma, a haka duk sai kin cika mana gidan nan da kyawawan yara kamar ki masu ha?uri juriya da kauda kai kamar dai Mamansu, Anty Husnah akwai wani hali nakidda har gobe yake ?ara birgeni, wato kauda kai, Allah ya bani kamar ki ina fata'' ta kai karshen maganar da goge ?ar kwallar da haka kawai ta ji ta sauko mata.

Wani ?aramin ?aran da Husnah ta saki ne tare da dafe cikinta ya yi mugun Waga mata hankali, dafata ta yi tana kiran sunanta hankali tashe, sai dai Husnan bata sami zarafin amsa wannan kiran ba, sai sulalewa da ta yi daga saman kujerar zuwa ?asa, hannunta dafe da mararta, kafin kace miye tuni zufa ta fara yanko mata ta ko'ina.
Hankalin Hasiya in ya yi dubu to ya tashi, tsaye ta yi amma ta rasa miye ya kamata ta yi, kama Husnan ta yi da niyyar ta Waga ta amma ta kasa, komai sai ya tsaya mata, ta ma rasa abun yi.

Jin wani salati da sallallamin da Husnah ke yi yasa da gudu ta yi inda ta ajiye jakar ta a hannun kujera tun shihowarta falon, wayarta ta ciro hannunta na karkarwa, kai tsaye number mijin nasu tashi ga sanbaWawa kira amma sai aka yi rashin Sa'a baya Wagawa, ta kira yafi sau shida amma haka wayan zata gaji da ruri ba amsa.
Duka wannan abun da take yi hannunta na a cikin na Husnah da yanzun wani irin karkarwa take kamar wacce aka tsoma a cikin ruwan ?an?ara bata shirya ba.
Zuwa wannan lokacin Hasiya ta gama ?ulewa da rashin amsa mata waya da Maina bai yi ba, a ce war ta wane irin nisa ne mutun zai yi yabar wayarsa da har za'a masa kira kusan goma ba tare daya Waga ko guda Waya ba, katse kiran data kuma turawa a lanbarsa a karo na barkatai ta yi jin wani tunani ya faWo mata a kwakwalwa.
Layin Ammy ta kira bugu biyu ana uku ta Wauka da sallama a bakinta, dama tana kusa da wayar bata yi nisa ba.
Da mugun tashin hankali Ammy'n ta ce yanzu ya jikin nata? Ina shi Jalaluddeen Win yake ne? Kuma tun yaushe ne ta fara na?udar bai kula an kai ta asibiti ba, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un'' Ammy ta faWa lokacin da Hasiya ta faWa mata halin da Husnar take ciki.

Kafin Hasiyar ta gama bata amsar tambayoyinta Ammy'n ta katse ta da ce wa ''gani nan zuwa yanzun nan'' kai tsaye ta katse kiran tana mai Waukar mayafinta ta yane jikinta dashi, dan dama ta gama shirin ta kenan fita kawai ya rage mata zuwa gidan Anty Mariya dan cigaba da shirye shiryen daurin aure gobe.

Koda suka isa gidan lokacin har Hu???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?snah ta fice daga hayyacinta, ga wani ruwa da ta fara zubdawa irin na haihuwa tazo kan gaba Win nan, ba Sata lokaci suka nufi asibiti da komai da komai na tarbar haihuwa kamar yadda suka tanada.

Ammy ma sau kusan uku ta kira Maina amma ita ma bai Waga ba, tun suna hanya take kiransa sai dai shiru.
Bayan sun iso asibitin aka sa Husnah Wakin haihuwa bayan Likitoci sun karSe su, Ammy ta kalli Hasiya cike da bacin rai ta ce ''ina ya ce muku zai tafi ne?'', a daburce ta ce ''Ammy ba dai zai wuce game da shirye-shiryen auren nan na ?a Issa da Kalil ba, amma nima nayi ta mamaki da har ake ta kiransa haka bai Waga ba.''
?wafa Ammy'n ta yi lokaci Waya kuma tana lalubar number Hajiya dan ta faWa mata, dan a lokacin hankalinta ya dauku ko kowa bata faWa wa za ta fita ba, ciki kuwa harda Dady da shima yau ya yi massakon fita zuwa halartar wani taro na manya manyan ?an kasuwa masu Kanfanoni da Masana'antu.

Sai da ta tabbatar ta faWawa duk wanda ya dace a ce yasan Husnar tana asibiti kafin ta nemi guri ta zauna a Waya daga cikin kujerun ?arfen dake a nanne da jikin bangon asibitin da aka ?awata su ta hanyar yi musu ado da penture ( kalar) da aka kewaye asibitin dashi.

Ita kuma Hasiya sai kai da kawo take a wajan, duk adu'ar da tazo bakinta kuwa yi take dan nemawa Yar'uwarta ta sau?i da rangwame a wajan Ubangiji daya ?addara duk wata mace ta duniya sai tai na?uda kafin ta haihu.

Dai-dai da isowarsu Mama Zainabu da wata dattijuwa daga cikin danginsu Husnan wata Dr Hadiza abokiyar aikin Dr Yahuza ta fito daga Wakin da aka sa Husnah Win.

Daga fuskarta kawai ya isa ka gane ce wa ba sau?i a lamarin.
Dai-dai da Waga bakinta dan ta yi musu bayani taji wani ?aran da ita kanta sai daya girgiza ta, da gudu ta koma Wakin data fito dan ganin ko da wani abun da faru ne, dama ta fito ne ta faWa musu ce wa haihuwar tazo mata da gardama, amma sudan bata lokaci nan da mintuna goma sha biyar, bayan cikar wa?an'nan mintotin matu?a bata haihu da kanta ba to da yiyuwar sai an yi mata aiki ita ma kamar dai Hamdiyya.

Hankalin Dr Hadiza ya tashi sosai ganin jini ya Sallewa Husnah, kuma zuba yake ba ?a??autawa, cike ta tashin hankali tazo ta gaban su Ammy ta wuce ofishinta, a waya ta kira Dr Yahuza take faWa masa ce wa ya kawo mata agajin gaggawa, kafin ta katse kiran ta koma Wakin da hanzari dan ganin wane mataki na gaba zata Wauka.


Zuwa wannan lokacin Maman Zainabu ta fara cire rai da ?ar tata, babbar likita irin wannan idan har hankalinta zai tashi ganin halin da Husnar take ciki to ina ga su da suke da rauni, su da ba kullum suke ganin koda lafiyayyiyar na?uda ce bare mai tattare da haWarin na mutu fakwai rai fakwai.

Kusan a tare Dr Yahuza da Dady suka iso asibitin, a Wan gurguje suka gaisa kafin kai tsaye Dr ya faWa dakin da yake tunanin anan suke ciki.
Tana shiga Dr Hadiza ta tarbe shi fuska duk ta ji?e mata sharkaf da zufar da ba tada lokacin jin tana yawo a jikinta ma bare har ta yi tunanin share ta.
Cikin tsananin tashin hankali ta shiga faWin ''yawwa Dr ka zo ka duba min irin wannan tahin hankalin, da farko da suka kawo ta ruwa take zubarwa, to ina dubawa sai naga faya ce ta fashe ba wata damuwa, nan muka fara bata agajin gaggawa kamar yadda aka saba, to amma daga baya sai abun ya fara bani tsoro ganin ta fara fita hayyacinta, da farko nace mu bata wasu yan mintuna idan bata haihu da kanta ba sai ayi mata cs, to kawai sai jini ya yanke mata, da kyar dai yanzun mun tsayar da zubar jinin, sai dai babu abinda ya sauya daga ba?ar wahalar da yarinyar take sha.''

Duka suna kan Husnah ne Dr Hadiza ke yiwa Yahuza wanna ?arin bayani akan abinda ake kan fuskanta a yanzun haka.
Wani ?arin taimakon suka kuma bata ta hanyar gar?ama mata na'urar fitar ta nunfashi, dan yanzun sosai take kokawwa dashi wajan fitowa da kuma sha?a.

Adduo'in da take sha daga bakunan jama'ar dake bakin ?ofar Wakin suna jiran suga fitowar Waya daga cikin Dr's Win ne ta fara riskar ta, wanda a ciki harda mahaifiyarta wanda addu'ar ta kai tsaye ba tada hijabi tsakaninta da Mahaliccinmu, nan take ta fara jin sau?i, hankalinta ya fara dawowwa jikinta, ta fara sauke nunfarfashi kamar mai son tayi ta gama iyakar wanda ya yi mata saura a duka rayuwarta, ta cikin mesar dake a dai-dai saitin bakinta suka ji tana faWin a kirawo mata Mamanta, Mijinta da kuma abokiyar zamanta.

Dai-dai da gama duk wani abinda ya kama ace sun tafi dashi Wakin tiyata da Dr Yahuza ya yi suka turo ?ofar Wakin suka shigo, Mama Zainabu da kuma Hasiya bisa jagorancin Dr Hadiza.

Da sauri Hasiya ta kawar da kanta daga duban Husnah da ta gama canja kamanni gaba Waya, an rufe mata daga cibiyarta zuwa kafafuwanta da wani sabon fallen zanen atanfa. Cikin ikon Allah kuma ba wata turjita da take ko mutsu-mutsu irin na mai na?uda, ba kamar Wazu ba da take faman faWowa daga gado lokacin da zubar jinin nan ya yawaita daga jikinta.

Da sassarfa Mama ta iso kusa da gadon tana kama Wayan hannun Husnah wanda bashi da komai, dan Wayan tuni Dr Yahuza ya haWa allurorin da duk ya kamata ya Wura a ruwa ya Waura mata.
Cikin kukan data kasa ri?e shi take ce wa ''Husnah ke ce kika koma haka? Ki duba yadda kika zama kamar ba ke ba, Ni dai har sanda haihuwa ta tsaya min ban taSa kalar cikin nan naki ba, Allah ya rangwamta miki ya yi miki sassauci, ya raba ki da wannan cikin lafiya, mahaifinki nacan yana miki fatan alkhairi da samun lafiya cikin gaggawa Yarinyata'' Mama ta faWa tana share hawayen da suke ta zaryar fitowa daga idanunta.

?an murmushin ya?e Husnan ta yi wa Maman, kafin ta Waga hannu tana mai yiwa Hasiya alamar ta iso gare ta. Ba musu kuwa ta iso tana ta faman ri?e kukan ta. ''Allah ya sauke ki lafiya Anty na'', shi ne kaWai abinda ta iya faWa tana mai ri?e bakinta da hannayenta.

Girgiza mata kai Husna ta yi, da ri?e??iyar muryata data fara wuyar fitowa ta ce ''ba lallai Allah ya karSi wannan addu'a taki ba ?ar'uwata, ina mai neman gafarar ki, a zama na dake nasan akwai lokuta da yawa dana Sata miki, dan Allah ki yafe mini'', juyawa ta yi wajan Mama ta ce ''Mama dan Allah ki yafe mini, ki kuma nema min yafiya a wajan Baba da ?an'uwana'' duka ba ko Wigon hawaye a idanunta take wannan maganar, ya yinda wa'yanda take yiwa maganar kowannensu kuka yake. Ta buWe baki da niyyar tambayar Hasiya ko Maina Win ya iso kawai wani irin tari ya sar?e ta, dai-dai da bankaWo ?ofar da Maina ya yi a gigice har yana shirin faWuwa, dan sosai ya bawa ?ofar ?arfi wajan bugota, alhali kuma kofar ba a kulle take ba.
Shi dai ya gansa kusa da gadon da take kwance, amma shi kanshi ba zai iya tuna da gudu ko da rarrafe ya iso wajan ba.
Hankalinsa a mugun tashe ya kama hannunta ya ri?e yana girgizawa.
Ganin tarin ya?i ?arewa yasa Hasiya ta fita da gudu dan kirawo Dr Hadiza, dan Dr Yahuza tun lokacin daya sanyawa Husnah wannan allurar ruwan yabar Wakin, su a tunaninsu ko duka cikin shirin yi mata aikin ne, shi kuma raina hankalinta ya yi, shi ne kawai ya yi mata ?arin ruwa da alluran da shi kanshi yasan ba zasu hana abinda Allah ya hukunta dole sai ya faru ba.

''Ka yafe min kukurai na agareka, ka kula min da ?ar'uwata sosai, a duk lokacin da ka tuna dani kayi min addu'a, ni kam tawa ta kare'' ta harhaWo wannan kalmomin ne da kyar, dan zuwa yanzun hatta idanunta sun fara ?afewa.
A dai-dai lokacin ne Dr Hadiza, Ammy, da kuma Hasiya suka shigo, hannun Hasiya ri?e da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login