Showing 36001 words to 39000 words out of 109651 words

Chapter 13 - A KAN SHI complete by Maman Abdallah

31 Oct 2025

3127

tsira kake ba bare ka zama Wan iska, abun bazai yiwa kowa naka kyau ba, misali gashi a Malam Inuwa mutumin kirki mai ri?o da gaskiya tun daga tushen tafiya, amma lokaci daga rayuwa ta juye ta sauya masa daga farin ciki zuwa ?unci da kaWaici, ga Mukhtar nan shi rayuwarsa ma ya rasa bayan bai ci kuma bai taka na kowa ba, to su da suke gina rayuwarsu data iyalansu da haram da rashin gaskiya ina tasu tafiyar zata kaisu kenan, da wayan'nan tarin nazari da tunanin sukabar kotun da kyawawan ?udururruka aransu nayin aiki tu?uru dan zama nagari abun koyi kamar dai Jalaluddeen Umar Mainasara.

Da kotancen da Malam Inuwa yayiwa Dady akayi nasarar Wauko Inna Baraka wato marikiyar Hamdiyya, tare da faWa mata duk abinda ya faru lokacin da aka isodda ita asibitin da aka kwantar da Hamdiyya bisa kulawar Dady da Malam Inuwa.

Yau kwana shida kenan ta kasa samun isasshen baccin da zata samu nutsuwar zuciya, ita bamai zazzaSi ba bakuma mai ciwon kai ba, da ace mijinta ya taSa saninta ?a mace da tace ciki ne da ita a daidai lokacin lokacin, hankalinta baya jikinta tun ranar da aka yi ta antayo da bayanai a kotu kan cewa duka akan mijinta ne wayan'nan abubuwan suka faru, sai yakejin dama an haWa da ita a wayan'da aka yiwa hukunci ko zata samu hankalinta ya dawo jikinta idan bata kusa dashi, a kullum tananinta shine idan wannan Hamdiyya tanasan Maina to ita mi take masa kenan? Ta tambayi kanta, so nama, ai ke kinfi kowa sanshi, ta bawa kanta, dum ?irjinta ya buga tunawa da tayi Maina fa zai iya auro Hasiya bayan ta gama takaba, to idan ya auri muradin zuciyarsa ita ya sunanta kenan? Sorry ta anbata da iya ?arfinta lokaci Waya tana mai dafe saitin ?irjinta.

Shigowarsa kenan gidan sai sorryn dayaji ta faWa, da sassarfa ya isa kujerar da take yana faWin ''Lafiyar ki kuwa Husnah'' jin tafin hannayan sa a kan nata hannun data Wora a ?irjinta yasa ta sauke ajiyar zuciya mai karfi kafin takai idanunta daidai inda hannayen su suke, da sauri ya Wauke hannunsa yana ?ara maimaita tanbayar da yayi mata da farko.

Duba yanayin zamansu tayi, tareda ?ara kusanta kanta dashi sosai ta yadda suna iya sha?ar nunfashin juna, hannunsa ta kama ta maida daidai inda ta Wora nata a Wazu wato saitin zuciyar ta, runtse idanunsu sukayi a lokaci guda kafin cikin sanyin murya tace ''Ka ji yadda zuciyata take bugawa da sauri-sauri Maina, kamar zata faso ?irjina haka nakeji aduk lokacin dana tuna cewa bakwa sona ?addarar ka da tawa ce suka haWe gu Waya suka bada aurena dakai, ina sanka dayawa, tsoro ya hanani sukuni na cewa karka barni, dan Allah karka cireni daga cikin rayuwar ka, koda zakayi rayuwa da wayan'da kake so to Ni ko a ?ar kallan kuce ka bari na kasance dan Allah' cikin cananin kuka ta karasa maganar datake fitowa daga cikin zuciyarta.

Tsabar tausayin ta daya cika masa ciki baisan sanda ya sakata gaba Waya a cikin jikinsa ba, bayanta ya shiga shafawa alamar rarrashi, sunfi mintuna goma tana kwance a faffaWan ?irjinsa kafin ya Wago ta suna fuskantar juna, da hannayen sa biyu ya ri?e kewayayyiyar fuskarta, idanunsa ya tsaida cikin nata dan lura da wani abun, ya kuwa gani kuma ya tabbata akwai tarin ?auna da Wunbin soyayyar sa a tattare da ita, taga hakan ne a cikin ?oyar idanta daya fara narkewa da shagwaba jinta kwance a jikin muraWi kuma abincin rai da ruhinta.

Da cikakkiyar muryarsa ta asalin Jalaluddeen ya fara magana, again fuskarta a cikin hanunsa ''Ni bance zan rayu dake na har abada ke kaWai ba, amma kuma zancan zan rabu dake kar na sake ji daga bakinki, Ubangijin daya ?addara haWuwar mu a gu Waya kuma a cikin inuwa Waya wato aure shi yasan abinda yasa hakan ta faru, ni da ke babu wanda yasan gobensa, mu Wauki kanmu kamar wayan'da aka bawa amanar junan mu, ta yadda zamu rayu cikin aminci da girmama juna kinji ?ar ?anwata'' ya faWa yana mai kashe mata ido Waya.


A wannan karon itace da kanta ta koma cikin jikinsa tare da zagaye bayansa da hannayen ta, cike da nushaWi tace ''Naji kuma na fahimta Yayana, kuma insha Allah zaka sameni fiye da yadda kayi zato ko tunani'' haka suka yi yinin ranar a tare da juna, a ?o?arin ta na mantar dashi wata Hamdiyya daya kasa zama yaci abincin kirki akan jinyarta tun bayan da aka kaita asibiti.


Kwance take akan katifar baccinta tana juyi, koda babu agogon da zata duba lokaci tasan yanzu ana zancen sha biyun dare saidai ?arfe Waya, batasan mi take damunta bayan dawowar ta gida daga gidan yari, a kwanaki shidan da tayi a gida ita kanta bayan sallah bazata ita tuna abunda tayi a azo agani koda kuwa Wauke shinfaWar baccin ta da shinfiWa ta, komai na gidan Mama ce take yinsa, hatta jama'ar unguwa da suke shigowa dan yi musu jaje da barka wani sa'in Mama Kuburah ce take karSa.

Yanzun ma tafi awanni a kwance tana juyi kafin tunanin ta ya tsaya waje Waya, tashi tayi ta zauna tana sautin Wan mayafin daya musu tsakani da su Maman ta, dama haka suke wannan tsarin indai lokacin kwanan waje ne.
Shuru tayi tana kallon yatsutsan hannunta, a hankali labarin rayuwarta ya fara dawo mata cikin kwakwalwar ta, tun daga haihuwar ta har girman ta, har zuwa lokacin data mutu kuma ta rayu dasan ganin maWaukin Wawainiyar ta tun tana tsumman haihuwa, tabbas ta samu labari daga Mahaifiyarta cewa tun daga ranar haihuwar ta Allah ya kawo mai musu alkhairi a Soye wanda har gobe bai daina yi musu ba, ko a dawowarnan tata gidan saida aka kamusu dangin kayan abinci amma a wannan karon a bayyane yake tunda kowa yasan waye da wannan aikin, a lokutan baya sau tari takan zauna tunanin wanda bai san ma da wanzuwar taba acewar ta, a lokacin tanaji dama Allah zai bata dama sau Waya ta gansa a rayuwa, ta nuna masa irin farin cikin da ahalinsu suke ciki duk a dalilin haskaka rayuwarsu, idan sukayi jarabawa a makaranta tanaji a ranta dama tanada ikon ganin wanda ya Wauki yaunin karatun ta dashi zai fara ganin sakamakon ta, a lokacin bata damu indai har zai bayyana a gaban koda yakai sa'an Babanta ba laifi saita kirashi da kawunta, ashe lokacin bayyanar sane bai yiba, da Allah ya bayyana mata shi a farko ita wannan ?addarar da yaza'a da ita kenan, tabbas ko shigowar Mukhtar cikin rayuwar ta shima ?addara be, kai duka rayuwar nan ta duniya a ?addara take farawa, sannan kuma da ita take ?arewa, baka kwana da abu ba sai ka wuni dashi, baka rayu da mutun ba saika mutu atare da shi, wannan duka hukuncin Allah ne, yakanyi abinda yaga dama kuma a lokacin da yake so, Allah gagari misali wanda yafi misali, hayyun laa ya mutu abadan.

Haka tayi tayiwa Allah kirari bayan gama tunane_tunanen ta, kafin daga bisani ta tashi ta Wauro alwala tashiga ganawa da Allah tare da kai masa kukanta, daga ?arshe ta rufe da yiwa Mukhtar adu'ar samun salama da rahama da kuma yalwatuwar haske a ?abarin sa.


''Amina na kusan makara fa jirgin ?arfe tara ne dani yanzu takwas harda rabi'' Dady ne da gamana lokacin da yake duba agogon dake Waure a tsintsiyar hannunsa, tsaye yake da ?ar ?aramar jaka da kayan cikinta bazasu wuce saiti uku ba, sai takardun kasuwancin da sune ma?asudin tafiyar da zai yi zuwa ?asar Maroko yanzun nan.

Da ?ar ?aramar kula na silba ta fito a hanunta sai she?i yake da alama sabo ne yanzu aka fara aiki dashi, sanye take cikin dokuwar ba?ar abaya data gama ?arSar cikinta, sai ?aramin mayafin ta data yane kanta dashi, dama Ammy ba wata mai wawan jiki bace sai tayi tsab kamar wata yarinya ?ar shekaru ashirin da biyar.


Hannunsa na dama ta kama ta sunbata kafin tace ''Gani nazo da sauri Alhajina muje ko, Allah ya kiyaye ya tsare ya dawo dakai gida lafiya, ya baka fiye da abinda kaje nema mai albarka da anfani, Allah ya kusanta ka da halal ya kuma nisanta gani da ji da samun ka daga haramun, Allah yayi maka jagora ya tsare adawo lafiya'' suna tafiya tana jero masa da wayan'nan adu'oin har suka isa ?ofar falon, tunga yaja ya tsaya yana kallon ta, ba shakka yayi missing na komai nata har adu'oin ta, duk da yasan tana masa amma yanajin daWin irin wannan na fuska da fuska, amsar kular danbun naman da tayi masa yayi tare da ri?e hannunta gan yace ''Nagode sosai da wannan karamci naki Amina, Allah yayi miki albarka ya shirya mana zuri'a, yasa an sami ?ani ko ?anwa wa Jalaluddeen a makon nan'' ya faWa yana kashe mata ido Waya, da sauri ta ?wace hanunta tare da rufe fuskarta alamar jin kunya, a kunne ya raWa mata cewa ''Zaki iya duba Hamdiyya a asibiti zuwa yamma, direba zai kaiki'' a bazata taji saukar laSSansa akan goshinta kafin ya wuce.

''Allah ?adirun alaa man yasha'u'' Ammy ta faWa kafin ta buWe idonta da suka yi mata yaunin buWewa lokacin da yake kusa da ita, alhamdulillah ta kuma faWa kafin ta rufe ?ofar falon lokacin da motar mai gidan nata take ?o?arin fita daga gidan.


Ri?e yake da karfen dake kewaye da inda yake yana kallon katangar data ?arazzama ?ara zama garkuwa a wajan tsoro gudun kar mutun yasamu damar guduwa, har yanzu ?arsa yake tunawa ko a wane hali take oho, tun da aka kawoshi gidan nan yau mako guda kenan ya kasa saka wani abun kirki a bakinsa ba, sai aikin wahala da yake kusan nasa masa ?irji, gashi sauro kwanaki uku a zartar masa da hukunci kuma har yanzu bai samu sani bayani game da halin da yarinyar sa take ba, ita Hadiza rabo da ya ganta tun lokacin da aka shigo dasu wannan gida, su Musa kuwa ba Wakinsu Waya b, duk damuwarsa ta ta'alla?a ne da rashin sanin halin da Hamdiyya take.


Asibiti
Kwance take a mi?e akan gadon jinyar dake Waki na musamman, idanunta a rufe saidai ba bacci take ba, Inna Baraka dake kan abin sallah tana lazumi bayan ta gama sallahr la'asar, sallamar Ammy ce ta isar da zuwansu wajan, Maina ne a tare da ita ri?e da kwandon abinci da Ammy ce ta Wauki Wawauniyar kowowa tunda aka ri?esu, yanzun ma tana shirin fitowa direba ya kawo ta kamar yadda mijinta ya bata oda saiga Jalal din ya shigo da niyyar daga can nan zai taho, shine yace kawai direba ya zauna yau shi zai draiving Ammynsa.


Inna Baraka tayi musu tare da kara jaddada godiya agaresu, Ammy ce ta kace yawan godiyar da tanbayar jikin Hamdiyyar ''Da sau?i sosai Hajiya dan da safen nan aka cire mata na'urar nunfashin nan kinga kuwa ai da sau?i, haka ma likitan yace a kwantar da hankali tana samun sau?i sosai, saidai ta rage damuwa dan zata iya maidata ruwa''.

BuWe idanunta tayi tana binsu da kallo Waya bayan Waya, dubanta ta tsayar akan Maina da yake jingine da wata ?ar drowar adana kayan bu?ata dake Wakin, sanye take da ensenble na suite a jikinsa kamar anta, sosai kayan sukayi masa matu?ar kyau, na yau kawai zata iya cewa ta taSa ganinsa a daf da ita ido da ido, dan duk zuwan da yake tana bacci yake zuwa har ya tafiyar sa.

A jikinsa yaji kamar ido yana yawo ajikinsa, ai kuwa dai ya kamata tana kallonsa, fuskar shanu yasha kamar ba shine ya gama gaisar da Inna cikin walwala yanzu ba, muryarsa ce ta dawo da ita cikin tunananin ta ''Inna ko akwai abinda kuke bu?ata a yanzu?'' ya tambayi Inna.

Cikin jin daWin rashin ri?o da karamci irin nasu tace ''Babu komai yaron kirki ai babu abinda zamu ce daku gaba Waya sai fatan Allah ya saka muku da mafificin alkhairinsa, Allah yayi maka albarka ya albarkaci zuri'a ya biya maka buktunka na alkhairi'' da ameen suka amsa harda Ammy da tamafi Maina Win jin daWin wannan addu'a da Innar tayi musu, cikin sakin fuska Ammy tace ''Inna kuci abinci ko kar yayi sanyi'', ba musu kuwa ta tashi ta fara buWe kwanikan da suka shigo dasu, kallon Ammyn nasa yayi yace ''Ammy ku sameni a mota, Inna sai anjima'' yayi wa Inna sallama tare da ficewa daga Wakin ko kallon inda take kwance bai sake yi ba.


Da taimakon Ammy Inna ta samu Hamdiyya taci abinci mai yawon da tunda tasamu kanta bata taSa cin irinsa ba, kusan awa Waya Ammy ta samu asibitin kafin tayiwa Inna sallama tare da Waukan kwanikan jiya dake gefe ajiye a wanke tas, dan Inna badai tsabta ba.

Ganin fitowar ta Wauke da wani kwandon daban ba wanda suka zo dashiba yasa saida murmushi ya suSuce masa, a ransa yake yaba irin kyawawan halayya irin na Ammy, macece wacce ta fita daban a cikin jerin matan Malam Bahaushe, komai nata na daban ne kama daga mu'amalantar jama'a zama dasu da karSar rayuwa a yadda tazo, tarbar ta yayi tare da karSar kwandon, zagayawa yayi ya buWe mata ?ofar motar gidan baya, saida tashiga sannan ya ajiye kwandon a gefenta ya rufe ya dawo mazaunin direba ya tashi motar, ahankali yake tu?in kamar wanda yake gudun kar yayi abinda ba daidai ba, gudun kar wani abu daban ya faru da mahaifiyartasa da ayanzu yakeji tamkar ya rama mata duk wata riritawar da Wa yakewa uwarsa wacce ta rasa samu daga gareshi a baya, sosai a yanzu yakeson ya kyautata mata har ?arshen nunfashinsa, ba shakka soyayyar Iyaye daban take, sai yanzu da yake da kyakkyawar ala?a da Iyayensa yakeji yana rayuwar ?anci saSanin da da yake rayuwa da lami ba WanWanun manda da barkono, ?arfe biyar da mintuna ashirin da hudu suka iso gida, inda yana ajiyeta ya juya kan motar zuwa shopping Win da yayi niyyar zuwa a maraicen nan.

Siyyaya yayi sosai kamar zai buWe sabon shago, inda har motarsa ta kasa Waukan kayan daya loda kamar ba kuWi ya zuba aka bashi su ba, daga karshe dai sai Kalil ya kira tare da faWa masa inda zai samesa yayi, ba jimawa kuwa saiga shi da tasa motar, sauran kayan da basu samu waje a motar Maina aka zuba ata Kalil kafin sukaja motacin a jere suna tafiya.

Kalil ne yace dashi ta ?ar tazarar dake tsakanin su ''Wai wa?an'nan uban kayayyakin duk na minene Malam Jalalu, ko har an baka damar fitowa ne a gidansu Shukuriyya kana haWa lefe banida labari?''.

Sosai gaban Maina ya faWi jin Kalil ya ambaci sunan Shukuriyyarsa, to har yanzu zai ci gaba da kiranta da wannan sunan ko kuma zai kirata da asalin sunan da kowa yasanta dashi ne, shiga wallahi sai yanzu da kalil Win na tuna masa da zancen ta bawai ya manta da ita a duka rayuwar sa bane a'a, kawai idan ya tuna yanzu akwai wani shingen dazai hana koda maganar fatar baki ne ta haWasu yakanji ba daWi, tunda yanzu tana cikin takaba ne, duk da a gajeran tunanin sa yana ganin kamar ta kusan kammalawa tunda a fara shari'ar da akayi dashi ma yanzu anfi wata Waya har yanke hukuncin da aka yi, kuma kafin a fara sauraron shari'ar ma saida akayi adu'ar kwana arba'in duk a ?o?arin jami'ai na bincike, kenan idan har lissafin sa daidai ne yanzu ta kusan rufe wata uku kenan, ?aran horn Win da Kalil yashiga danna masa ne ya dawo dashi daga duniyar lissafin daya afka, cike da taraddadi Kalil yayi masa nuni da gabansu, ai kuwa da mugun ?arfi yayi gaggawar sauka daga layin gaba Waya, shima Kalil saukowa yayi tare da kashe motar, saukarsu daga titin ko second sha biyar baza'a rufa ba wata babbar motar Waukan kaya ta wuce a guje kamar babu matu?i a ciki kodai bai iya sarrafa linzamin motar ba.

?aga girarsa Waya Kalil yayi yana wa Maina wani irin kallo ba Ni ban shirya ba kafin yace ''Malam waye yace maka ana shiga shau?i a tsakiyar hanya iye, yanzu da wannan motar tabi ta kanmu ana shirin magaribar nan da ya zamuyi kenan, ?ar suturar nan ba zamu samu akan lokaci ba cewa za'ayi a kaimu mutuware mu kwana, Ni kuma wallahi wasiyya na bar maka duk lokacin dana rasu to kuyi gaggawar kai ni kushewa ta na kwanta ehe'' ya faWa yana mai ?ara tada motar tare da komawa kan layi ya cigaba da tu?insa cikin ?orewa kuma a hankali.

Kamar ba zai gusa daga wajan ba, yafi mintuna biyu kafin ya figi motar da mugun gudun tsiya, Ni kuwa nace hali hanji!Kowa da nasa yake yawo.


Kafin kace miye tuni ya kamo Kalil sakamakon Wan banzan gudun dayake tsulawa a titin, saida yazo daidai saiti da Kalil yayi wani ?aramin fito, ai kuwa rabin hankalin Kalil ya dawo garesa, kashe masa ido Waya yayi kafin yace ''Sunab Jalalu dka kirani dashi kaci bashi yaro, sai magana ta biyu miye ma kace, na shiga shau?i dajin sunan wannan yarinyar, ai Ni dai gani bana shiga hurumin Ubangiji, ban ma san akan waye kake magana ba, sai magana ta uku kace muyi gaggawar kaika makwancin ka, yaro da alamu ka shiryawa zuwan ?iyama tunda mafiyakake faWin wannan magana, ina jinka mika tanadar wa zuwan wannan rana?'' daidai nab suka iso harabar gidan Dady wanda shi Maina Win ne ya fara daidaita akalar tu?in nasa zuwa gidan.

Saida suka daidaita parking suka fito, zuwa wannan lokaci ana kiran sallar magariba, a na farfajiyar gidan suka samu sukayi alwala a fanfon dake tsakar gida na bawa shuka ruwa, a hanyarsu ta zuwa Masallaci ne Kalil ya kalli Maina cikin mutuwar jiki yace ''Abokina ka tambaye ni mi na tanada wa zuwan wannan rana, wallahi babu abinda na tanada , nidai nasan ina bautatawa Allah iya karfi na, duk da nasan halin da aikin mutun basa kaishi aljanna, haka kuma basa tseratar da kai daga wuta matu?ar Ubangiji ya hukunta itace makomar ka, bayan wannan har gobe ina ?o?arin ganin mun rabu da Iyayena lafiya, wanda babu wani abu da Wa namiji zaiyi a duniya bayan bautar Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login